Sashe 19
Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Farouq ne yayi musu bayanin duk abin da ya wakana,daddy yace"ma sha Allah Alhmdllhi" hannu ya saka tare da ɗakko briefcase ɗinsa ya buɗe ya ɗakko a t m ya miƙawa farouq yace"maza ka je ka siyo mata duk abinda ya kamata ka siyo mata,ya faɗa yana duban farouq ɗin.ya amsa da "to daddy" MOMY tace"daga nan ka biya ka kaiwa telan nan ɗinkin uniform ɗin,kace masa idan ya gama ya haɗo da sauran kayan gaba ɗaya ya kawo,daga nan sai kaje ka ɗakko yusra ku dawo gida".
Farouq yace "to MOMY"daga haka ya miƙe ya fice daga parlon.bayan tafiyarsa ne daddy ya dubi HALIMATU yace "doughter gobe idan Allah ya kaimu ki shirya da wuri Farouk zai kai ki gurin da zaki zana jam, Sabo da haka ki mai da hankali kinji ko!!" tace to daddy in sha Allah" ya cigaba da cewa"sannan ga islamiyya nan zaki shiga itama ki maida hankalin ki Allah ubangiji ya bada sa'a!! duk da nasan idan kin fara zuwa makaranta sai dai ki dinga zuwa asabar da lahadi" ya ƙarasa maganar yana mai tabbatar mata da zancen da yake yi mata.tace"tom daddy in sha Allah" ta faɗa tare da miƙewa ta haye sama.
"MUKHTAR"
Bayan ya gama cin abincin ne ya dawo parlon ya zauna,lokacin daddyn sa da momy sun wuce zuwa sama.yaran sa ne suka taso suka zauna a kan jikin sa suna ta faman bashi labarin school ɗin su, tsaya wa yayi yana sauraron su tare da biye musu.suna cikin hirar ne sai ga ƙanwarsa meena ta sakko ƙasa,guri ta samu ta zauna tare da gaishe da yayan nata,amsawa yayi cikin sakin fuska tare da tambayar ta school tace"wallahi yaya yau banje ba, sabo da na tashi bana ɗan jin daɗi shiyasa" yace ayya Allah ubangiji ya sawwak'e ya baki lafiya "tace ameen"
Ya ci-gaba cewa "amma duk da baki da lafiya haka kika yi ta ɗawainiya da yaran nan! ai da kinbar su da me aiki kawai" tace haba yaya meye amfani na idan banyi ɗawainiya da su ba?? bafa wani aiki ne me wahala ba! ni wallahi dama ka dawo da su nan ɗin gaba ɗaya domin naga sunfi saukewa a nan ɗin".ta faɗa tana duban shi.sannan ta ci-gaba da cewa" "ai ɗazu naji MOMY suna waya da aunty nadiya take faɗa mata duk abinda ya faru tsakanin ka da aunty RUFAIDA,wallahi bakaga yanda ran MOMY yayi bala'in ɓaci ba,ita ma aunty nadiyar tana ta faɗa"
Ta ci-gaba da cewa "aini wallahi nayi murna sosai da naji MOMY tace daddy ya zab'a maka matar da zaka aure,mudai fatan mu Allah ubangiji yasa a dace" ya amsa da "ameen" ƙara duban shi tayi tare da cewa"dan Allah yaya duk ranar da zakaje ganin ta zan bika na raka ka" ta faɗa tana marai raice fuskar ta.ya ɗago ya kalleta yace"okay tom shikenan,tashi kije ki shirya in kaiku kuyi shopping" cike da murna ta shi ta haye sama domin ta shirya.
Bata wani daɗe ba ta sakko cikin shigar rantsatsiysar dubai abaya coffee colour tayi mata mutuƙar kyau sosai sai ƙamshi take bazawa. yana ganin ta sakko ya miƙe tare da cewa "kije ki gayawa MOMY mun fita,ki same mu a mota" daga haka ya kama hannun yaran suka fita.cikin sauri taje ta gayawa MOMY sannan ta sakko ta fice daga parlon, parking space ta nufa inda ta same su a cikin mota suna jiran ta,ba tare da b'ata lokaci ta buɗe front seat ta shiga ta zauna,motar ya kunne tare da yin horn mai gadi ya buɗe musu get suka fice daga gidan....
"INNA LAURE"
Tafe take tana ta sauri har ta iso shiyar da yar ta rahinatu ƙanwar altine take aure,tana zuwa ta shiga cikin gidan tare da yin sallama,rahinatu dake du'ke a gaban murhu tana gyara wuta tana ganin ta tayi sauri ta taho gurin ta tare da cewa "lale maraba da innar mu kece nan tafe da maraicen nan" ta faɗa tana kallon ta da murmushi a fuskar ta.inna laure tace "kedai bari rahine, wallahi nice!"juyawa tayi tare da ɗakko tabarma tazo ta shimfid'awa inna laure.bayan ta zauna ne rahine taje ta ɗebo ruwa a randa ta kawo mata,nan take ta ɗauki ruwan tare da kafa bakin ta a bakin kofin ta hau kwan kwad'ar ruwan! sai da tukusan shanye ruwan sannan ta ajiye kofin tare da sauke ajiyar zuciya.
Kallon ta rahinatu tayi tare da cewa "innar mu lafiya dai ko??" inna laure tace ina lafiya rahane!! nan take ta fashe da kuka.cikin tashin hankali rahinatu ta dube ta cike da damuwa tace"innar mu dan Allah ki gayamin me ya ke faruwa da ke?? wallahi bakiji yadda hankali na ya tashi ba".inna laure ta sake fashewa da kuka a karo na biyu tare da buɗe baki ta fara bawa rahinatu labarin abinda yake faruwa.cike da tashin hankali ta dubi inna laure tace "innalillahi wainna ilaehi raji'un,innar mu mai ya kaiki shiga gonar buba!! yanzu gashi nan ai kin jawo mana masifa da bala'i!!".
Cikin raunatacciyar murya inna laure tace"wallahi ƙaddara ce rahine, da kuma san kuɗina had'i da san zuciya ta,sune suka jawo min" ta ci-gaba da cewa"ni yanzu bama wannan ba dan Allah ku rufamin asiri keda 'yar uwarki lamunde ku taimaka ku biyamun kuɗin nan ko na samu kwanciyar hankali a rayuwa ta."ta ƙarasa maganar tana share hawayen da yake zubo mata a kan fuskar ta.
Rahinatu ta dube ta tace "ki dena kuka innar mu in sha Allahu babu abinda zai sameki,yanzu nawa ne kuɗin gaba ɗaya??"Inna laure ta share hawaye tace"gaba ɗaya kuɗin dubu arba'in ne rahane" ta ƙarasa maganar tana kwallon rahinatu.tace"tom shikenan bari gobe idan Allah ya kaimu da rai da lafiya sai in bawa baban kamilu tunkiyar nan tawa ya kaita kasuwa ya siyar min da ita,idan yaso sai in baki kuɗin"
Inna laure ta ƙara fashewa da kuka a karo na uku tace"na gode rahine Allah ubangiji ya saka miki da mafificin alkhairi ya raya miki zuri'ar ki" "tace ameen Innar mu! kiyi shiru ki dena kukan nan haka! kuma dan Allah ina neman alfarma a gurin ki Innar mu!!" ta ci-gaba da cewa "dan Allah daga rana irin ta yau ki canja hali ki dena duk abinda kike yi wanda bashi da kyau,yanzu dubi irin cizgunawar da kikayiwa HALIMATU wallahi ko kaffara bazan yi ba hak'k'in tane yake biyar ki,dan haka daga yau ki canja ki tuba"ta ƙarasa maganar tana kallon inna laure.
Inna laure ta buɗe baki kenan zata yi magana suka jiyo muryar baban kamilu tun daga waje yana kwad'awa rahinatu kira,cike da tashin hankali suka miƙe tsaye,yana shigowa yayi arba dasu anan gurin suna rarraba idanu.baban kamilu ya dubi inna laure yace"innar mu dama ashe kina nan ban sani ba, wallahi yanzu daga gurin neman ki nake! naje gida bakya nan,yanzu haka daga gidan altine nake tace min baki zoba, shine nake bata labarin abinda ya faru,yanzu haka itama altinen ta tafi gidan malam musa!!" ya ƙarasa maganar fuskar sa ɗauke da damuwa.
Cikin tsananin fargaba da tashin hankali har suna haɗa baki gurin tambayar sa abin da yake faruwa,nan take ya zayyane musu abin da ya faru da malam musa da wasu daga cikin jama'ar gari.ya ƙara da cewa"yanzu haka mai gari ya sa an kirawo masu bada magani suna can suna ta duba waɗan da tsau tsayi ya rutsa da su.inna laure tace "to yanzu ya jikin ya'yan??"
Baban kamilu yace"to da sau'ki dai za'a ce,tun da anyi masa ɗori a karayar da ya samu a kafarsa,ita ma lamunde anyi mata ɗori a gwiwar ƙafar ta, shi kuma salmanu yanka ne aka yi masa a gadon bayan sa,yanzu haka zancen da nake yi miki suna gida suna jinyar jikin su.
Cikin kuka inna laure tace "innalillahi wainna ilaehi raji'un, wallahi duk ni naja musu wannan masifar" ta ƙarasa maganar tana dur'kushewa a ƙasa ,baban kamilu yace"a'a wallahi innar mu babu ruwanki ki dena faɗin haka! tsau tsayi ne dai ya rutsa da su.inna laure tace "wallahi na gaya maka nice na jawo musu,nan take ta bawa banan kamilu labarin abin da yake faruwa tsakanin ta da buba.
Cikin zaro idanu baban kamilu yace Innalillahi wainna ilaehi raji'un,innar mu garin yaya??" Ta ce wallahi ƙaddara baban kamilu" yace to yanzu abin da za'ayi ki tashi rahane ta raka ki kuje ku duba kawu,daga nan kisan inda zaki ki b'oye idan ba haka ba muddin BUBA ya samu labarin ki bazai ƙyaleki ba, kinga gobe idan Allah ya kaimu aka siyar da tun kiyar sai a bashi kuɗin sa!!"
Cikin rawar jiki inna laure ta mi'ke tsaye ta saka takalman ta,itama rahinatu takalman ta saka tare da ɗaukar hijabin ta a kan igiya ta zunduma suka fita daga gidan suka nufi gidan malam musa.suna fita baban kamilu yace"wallahi bazan bari ki zauna min a gidana ba salon azo ayi min yankan rago nida iyalina"ya ƙarasa maganar tare da shigewar sa cikin ɗaki.
"HANNE"
A ɓangaren su hanne kuwa bayan sun fito tsakar gidan suka hau aiki babu kama hannun yaro,inda suka yi dambun masara da yaji zogale da man ƙuli ƙuli sai tashin ƙamshi ya ke yi,sannan suka soya naman kaji,su kuma zabin suka yi pepper soup ɗin su.cikin ƙanƙanin lokaci suka gama komai suka zubawa Sama'ila nashi daban, suma kuma suka zuba nasu daban.altine ta umarci hanne ta kwashe kayan ta kai su cikin ɗaki...
Bayan ta kai kayan ne ta fito domin wanke kayan da suka yi amfani da su ne ta jiyo koke koke.tana dubawa taga ashe yaran gidan ne suka shigo tare da baban kamilu suna kuka suna bawa altine labarin abin da ya faru,nan take Hanne ta dubi altine da hankalin ta yayi mummunan tashi ta fashe da kuka tare da cewa "shikenan innar mu ta jayowa kawu masifa"altine da ke matsar ƙwallar da ta cika mata idanu tace "kedai bari Hanne!! Wallahi bakiji yanda hankali na ya tashi ba!! maza jeki ɗakko hijabin ki mu tafi,tace "to" tare da shigewa ɗaki.
Altine ta dubi yaran ta tace musu"ku zauna yanzu zamuje gidan kawu musa mu dawo,idan kawun ku Sama'ila yazo ku ɗakko masa abincin sa yana cikin ɗaki" suka amsa da "to" .daga haka suka fice daga cikin gidan suka nufi gidan malam musa.....