← Book details Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 80

Sashe 65

Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi ya yi yana kallon ɗan ƙaramin bakin ta daya sha wani irin janbaki sai shinning yake yi, wani irin yawu ya haɗiye maƙwat tare da kai bakin sa dai dai saitin kunnen ta ya ce,
"Kin yi kyau sosai amarya ta!!"
Ɗago hannayen ta tayi cike da kunya ta rufe fuskar ta,murmushi ya yi tare da sumbatar hanayen nata da suka sha jan lalle da baƙi gwanin ban sha'awa ya ce,
"Yau kuma kunya ta ake ji ne my love!!"
Ƙara rufe fuskar ta yi tare da juya masa baya.

Duk abinda yake faruwa Nura yana kallo ta jikin mirror yana sakin murmushi tare da girgiza kan sa,tsayawar da ya ji motar ta yi ne yasa ya ɗago kansa cike da mamakin ganin har sun iso girin, nan take ya gyara nutsuwar sa tare da ɗakko pos ɗin halimatu da ta fadi a ƙasa ya buɗe cikin ta.
Wayar tace a ciki da turare sai kuma kudi,zura hannun sa ya yi a cikin aljihun sa ya ɗakko rafar ƴan dubu-dubu guda biyu ya saka mata a cikin pos ɗin tare da rufewa ya ɗora mata a kan cinyar ta,ƙwanƙwasa musu motar Nura ya yi,ganin Nura ne ya sa ya buɗe ƙofar tare da cewa,
"Malam lafiya kake ƙwanƙwasa mana ƙofa.??"

Wata iriyar muguwar harara Nura ya maka masa tare da cewa,
"Ita ta kawo haka! idan kaga dama ku fito ana jiran ku!!".
Murmushi mukhtar ya yi tare da fitowa daga cikin motar ya zagaya ta ɗaya gefen ya buɗe wa halimatu ƙofar itama ta fito a hankali ta tsaya a jikin motar,tahowa mamy ta yi ƙanwar momyn su mukhtar ta kama hannun halimatu ta kawo ta in da Hafiz suke tsaye shi da MEENA cikin kyakkyawar shiga ta alfarma.

Cikin sauri mukhtar ya biyo bayan su tare da kama hannun halimatu ya riƙe gam gam,nan take masu vedeo Camera da masu pictures suka fara aikin su suna ɗaukar duk wani motsin su,duk in da ka duba hasken flash ne kawai yake tashi a wajen,nan take a ka sanar da shigowar angwaye da amare tare da rakiyar abokan su da ƙawayen su.

Kowanne abokin ango ya samu wata daga cikin ƙawayen amaren sun jone gwanin ban sha'awa,gaba ɗayan su mazan ankon farar shadda ce a jikin su,ya yin da matan suke sanye da ankon farin less mai ratsin golden gwanin burgewa.
Ƙwayen amaren da abokanan angon ne suka fara shigowa cike da tsari, sannan amaren suka biyo bayan su,masu fesa turare na aikin fesa musu,masu watsa furanni na aikin watsa musu.gaba ɗaya kallo ya koma kan amaren da angwayen domin sun bala'in yin kyau da dacewa da junan su sosai, halimatu da hafiz sune farare a cikin su,ya yin da MEENA da mukhtar suka kasan ce chocolate colour.

Wajen da aka tanadar musu na musamman suka je suka zazzauna,ba tare da ɓata lokaci ba aka fara gudanar da dinner ɗin cikin nutsuwa da burgewa,abin ka da ƴan boko komai cikin wayewa suke yin sa.
Deeje ne ya nemi babban abokin ango da ya fito ya buɗe taro da addu,a, ba tare da ɓata lokaci ba Nura ya fito ya buɗe taro da addu'a tare da fatan Alkhairi ya koma wajen zaman sa ya zauna.
Sake kirawo Nura mai deeje ya yi domin ya gabatar da ɗan takaitaccen tarihin ango mukhtar,nan ma tasowa Nura ya yi ya bada tarihin aminin nasa,gaba ɗaya wajen ya ɗauki tafi raf raf.

Kiran babban abokin Hafiz aka yi domin ya zo shima ya bada taƙaitaccen tarihin angon,ba tare da ɓata lokaci ba wani aminin sa Ahmad ya fito ya bada taƙaitaccen tarihin sa,nan ma tafi aka ɗauka raf raf.
Suma ɓangaren amaren haka aka kikkirawo ƙawayen su suka zo suka bada taƙaitaccen tarihin su.
ba tare da ɓata lokaci ba aka fara gudanar da dinner ɗin.

Haɗaɗɗun different colours ɗin abinci ne da snacks aka tanadar a wajen,ga kuma tarin kalolin nama iri iri daban daban a wajen,sai abun da kaga dama zaka yi saving kan ka da shi,sai kuma colour's ɗin drinks masu tsada har da su milk shakes.
Bayan an gama ciye-ciyen ne deeje ya umarci
Abokan angwaye da amare su fito su chashe,nan take kuwa fili ya cika da mutane ana ta rawa ana zuba ruwan kuɗi,bayan sun fita dangin amaren da angwayen suka fito suka shiga cikin filin suka chashe suma, sannan daga bisani aka umarci amaren da angwayen su fito fili su chashe suma.

HAFIZ da MEENA ne suka fara fita,ya yin da mukhtar yake ta fama da halimatu ta tashi su fito taƙi har sai da mamy ƙanawar momyn su mukhtar tazo ta rarrashe ta sannan ta miƙe mukhtar ya kama hannun ta suka fito filin.
Wani irin cool music ne yake tashi mai tsuma zuciyar masoya,nan take su Hafiz suka kama rawa cike da nutsuwa da burgewa,ya yin da mukhtar ya kamo ƙugun halimatu a hankali da hannayen sa guda biyu yana yin rawa yana jujjuya ta in a style,gaba ɗaya wajen ya kaure da tafi da ihu,nan take abokanan ango suka taso suka fara zuba musu ruwan kuɗi ƴan dubu dubu.

Kunya ce ta kama halimatu taji kamar ta nutse a ƙasa,shi kuwa mukhtar wani irin mayalwacin farin ciki ne shimfiɗe a saman fuskarsa.bayan abokanan angwaye sun fita Iyaye da ƴan uwa suka shigo,haka suka haɗu aka dinga zuba musu ruwan kuɗi kamar basu san ciwon su ba.hannu mukhtar ya sa a cikin aljihun sa ya ɗakko rafar ƴan dubu dubu ya rinƙa zubawa halimatu su babu ƙaƙƙautawa cike da farin ciki,nan take masu deeje suka dinga kwasar kuɗi domin su kakar su ce ta yanke saƙa.
Bayan sun gama rawar ne kowa ya koma gurin zaman sa ya zauna sannan aka umarci mukhtar da halimatu akan su tashi su yanka cake,kamo hannun ta ya yi suka miƙe tare da matsowa gaban cake ɗin ya ɗora hannun ta akan wuƙar shima ya ɗora nasa hannun a saman nata suka yanka cake ɗin.

Yankowa ya yi tare da nufar bakin ta dashi da nufin ya saka mata a baki,da sauri ta kau da kanta gefe sabo da ganin yanda idanun mutane suka yi yawa a kan su,kiran sunan ta ya yi ta juyo suka haɗa idanun su guri ɗaya ya tsare ta da manyan idanunsa masu kwarjini sannan ya kuma kai cake ɗin cikin bakin ta,cike da kunya ta buɗe baki da nufin yi masa magana ya yi sauri ya tura mata cake ɗin gaba ɗaya a cikin ɗan ƙaramin bakin ta.

Tafi aka saka da ihu saboda ba ƙaramin burge mutane suka yi ba, hannun ta ya ruƙe suka ƙara yanko cake ɗin sannan ya ranƙwafa dai dai tsahon ta ya tura mata bakin sa,cikin sauri itama ta tura masa cake ɗin a bakin sa har tana ɓata masa gefen bakin sa da cream ɗin cake ɗin, wannan karon kowa sai da ya yi tafi har da iyaye, domin salon soyayyar ta su ta burge kowa da yake wajen.
Bayan sun gama ne su Hafiz suma suka yanka nasu tare da bawa junan su a baki.

Hotuna aka shiga yi da angwayen da amaren da dangi da kuma abokai,haka taro ya tashi gwanin ban sha'awa da burgewa kowa ya koma gidansa lafiya tare da kyaututtukan da aka rarraba a wajen.
Washe gari da misalin ƙarfe takwas na dare aka miƙa duka amaren ɗakunan mazajen su,halimatu ta sha kuka sosai har sai da zazzabi mai zafi ya kama ta,da ƙyar aka ɓanɓare ta daga jikin momy lokacin da za'a tafi da ita,haka tana ji tana gani su altine da aunty AMINA suka miƙa ta ɗakin ta tare da yi mata wayo suka gudu suka bar ta ita kaɗai tana ta sharɓar kuka abin tausayi.

Wuraren ƙarfe goma na dare mukhtar da Nura suka shigo cikin gidan hannun su ɗauke da manyan ledodi guda uku, direct sama suka hau tare da yin masauki a katafaren parlon dake saman,zama Nura ya yi tare da kallon mukhtar yace,
"Yi maza ka kirawo ta kaga dare yana ƙara yi"
"Toh"
Yace tare da shige wa master bedroom ɗin halimatun bakinsa ɗauke da sallama.zaune ya same ta a saman gado ta rufe fuskar ta da hular alkyabbar da take saye a jikin ta tana ta faman kuka,zama ya yi a gefen gadon tare da matsawa kusa da ita yace,
"Subhanallahi! har yanzu kukan kike yi my love!!"
Ƙara ƙarfin kukan ta yi tare da ƙanƙame jikin ta waje ɗaya,a hankali ya ƙara matsowa kusa da ita ya jawo ta jikin sa ya rungume ta tsam yana sauke ajiyar zuciya tare da ɗan bubbuga bayan ta alamar rarrashi,cikin ƙasa ƙasa da murya yace,
Haba my love ki yi shiru mana ki bar kukan nan haka kar kan ki ya yi ciwo,kinga gashi nan ma har zazzaɓi mai zafi ya kama min ke pls kiyi haƙuri kin ji".

Girgiza kai ta yi tare da yin shiru ta lafe a kan ƙirjin sa tana sauke ajiyar zuciya,sai da yaga ta ɗan samu nutsuwa sannan ya raba jikinsa da nata ya sakko daga kan gadon tare da miƙar da ita ya kama hannun ta suka fice daga cikin ɗakin zuwa parlo.
Guri ya samu ya zaunar da ita a saman sofa tare da zama kusa da ita,nasiha Nura ya yi musu mai shiga jiki tare da yi musu addu'ar zama lafiya da junan su sannan ya yi musu sallama ya miƙe ya fita,bin bayan shi mukhtar ya yi tare da yi masa rakiya har bakin motar sa sannan ya juyo ya dawo cikin gidan.
Kitchen ya je ya ɗauko plates da cups ya kawo kusa da ita ya ajiye sannan ya ɗakko Ledodin da suka shigo da su ya jiye a ƙasan carpet tare da zama ya buɗe ledar farko,wasu irin manya manyan zabi ne guda uku da akayi musu haɗaɗɗen lafyayyen gashi na musamman mai kyau da inganci,a gefe guda kuma gas meat ne shima da yasha haɗi sosai sai ƙamshi yake yi.
Chapter 65 · 0% Book details