← Book details Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 80

Sashe 16

Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya cigaba da cewa "bama wannan ba,yanzu gashi nan kinje sabo da san kuɗinki kin b'allowa kanki ruwa kin shiga sabgar fitinan nan yaron nan, to wallahi babu ruwa na maza maza tashi ki fice min daga gida!! ya ƙarasa maganar yana ɗaukan wata ƙatuwar gora ya nufi kan inna laure gadan-gadan!!" ganin da tayi malam musa da gaske kwad'a mata yake shirin yayi ,ai da gudu ta tashi ta watsa a guje tana nishi,ba ita ta tsaya ba sai da tayi nisa da gidan sosai sannan ta ɗauki hanyar koma wa gida.

*************************************************

HALIMATU

A ɓangaren su HALIMATU kuwa lokacin da ta hau staircase ta shiga cikin ɗakin ta,gado ta hau direct ta kwanta,babu jimawa bacci yayi gaba da ita,ba ita ta tashi daga baccin ba sai wuraren sha biyu na rana. toilet ta nufa ta wanke fuskarta da bakin ta sannan ta sakko ƙasa ,nan ta tadda momy zaune a kan kujera tana kallo, ƙarasowa tayi gaban momy ta tsuguna tace"barka da rana momy" momy tace "yauwa my daughter ya kike??" tace "lafiya k'alau momy ina daddy??" tace"dadyn ku yana lafiya yanzu ya fita" jinjina kai HALIMATU tayi tare da cewa "to Allah ubangiji ya dawo mana da shi gida lfy!!" momy tace" ameen my dear".

'Dagowa momy tayi ta kalle ta tare da cewa"tashi ki shiga kitchen ki taya baba ladi ku haɗa mana lunch" HALIMATU tace"to"tare da mi'kewa ta shige kitchen.bayan tafiyar ta ne momy ta ɗauki waya ta kirawo faruq tace masa yazo tana neman sa,daga can ɓangaren sa yace mata ya fita baya gida amma yana kan hanya,tace masa tom shikenan idan ya shigo tana jiran shi,daga haka ta ajiye wayar.

A ɓangaren daddy kuwa yana can company tare da Alhaji Auwal,in da yake shaida masa yanda suka yi da momy,ba ƙaramin farin ciki Alhaji Auwal yayi ba da jin wannan labarin,ya dubi daddy yace"to yanzu ya kake gani game da lokacin da ya dace ayi auran??" daddy yace"to ina ga dai mu barshi zuwa nan da shekara biyu ko??kaga lokacin ta fara zuwa makarantar ta!!".

Shiru Alhaji Auwal yayi daga bisani ya ɗago ya dubi daddy yace"Alhaji ayi mana alfarma a barshi zuwa nan da shekara ɗaya mana" ya faɗa tare da marairai cewa,yace" to zamu duba mu gani in sha Allah" yace to Allah yasa muji alkhairi!!" dady yace "in sha Allah" daga haka ya miƙe daddy ya rakoshi har wajen motar sa,sai da yaga wucewar su sannan ya koma office ɗin sa.suna hawa kan titi ya ciro wayar sa a ajihu ya dannawa mukhtar Kira, mukhtar yana cikin tu'ki har ya ɗauki hanyar jigawa yaga kiran daddyn sa, guri ya samu yayi parking sannan yayi picking ɗin wayar, sallama yayi tare da gaishe da daddy,bayan sun gaisa ne daddy yace "masa maza maza duk abin da kake yi ka bari kazo gida ka same ni yanzu yanzun nan !!" yace "tom shikenan daddy gani nan zuwa in sha Allah" daga haka yayi reverse ya juya.

Rufaida

A ɓangaren rufaida kuwa lokacin da mukhtar ya kulle ƙofa ya tafi ya barta a nan tsaye ba ƙaramin tashin hankali ta shiga ba,ganin irin tozarcin da wulak'anci da yayi mata,yanzu kam ta gane da gaske sakin ta yayi ba da wasa yake yi ba,ita yanzu ya zatayi ta iya rayuwa ba tare da mukhtar ba, mukhtar shine farin cikin ta,duk wani iskan ci da take yi da bazar sa take taka rawa , gashi gidan su ma shine yake taimaka musu,to yanzu ya zatayi kenan??.

Ganin bata da mai bata amsa yasa ta ɗaga ƙafar ta da ƙyar ta nufi parking space da nufi buɗe mota ta shiga,tana zuwa ta tuna cewa ai bata da mukulli a hannun ta,gashi ya kulle kofa,hakan yasa tajuya ta nufi get ma'aikata na gaishe su amma ko bi takan su bata yiba,tana zuwa ta buɗe ƙaramar ƙofar get ɗin ta fita .

Tana fita batayi wata tafiya mai nisa ba ta samu a dai dai ta sahu ta gaya masa ɗorayi zai kai ta,yace mata "hajiya dai dai ina!!" tace masa"ƙarshen waya" yace mata "shiga ki bada ɗari biyar". ba tare da ta amsa masa ba ta shiga suka ɗauki hanya.lokacin da suka iso har kofar gidan su sai tace masa bari ta shiga cikin gidan ta karb'o masa kuɗin, girgiza kai yayi kawai.daga haka ta sa kai ta shige cikin gidan.

Tana shiga babu daɗewa ta fito hannun ta riƙe da ɗari biyar ta miƙawa mai adai daidai ta sahu ya karb'a ya ƙara gaba.komawa cikin madai dai cin gidan tayi a karo na biyu, tana zuwa ta faɗa jikin wata mata dake zaune a tsakar gidan tana ƙullin sobo,nan take ta fashe da kuka,cikin tashin hankali matar tace "subhanallahi me kuma ya faru da ke daga zuwa sai kuka?? dama tun da kika shigo ina ganin ki nasan ba lafiya ba!!".

Cikin kuka ta ɗago da kanta ta kalli uwar tare da bata labarin abin da ya faru,nan take ta zunduma ashar tace"lallai yaran nan ya cika ɗan iskan yaro,ai ban aura masa ke kije ki dinga yi masa bauta ba,mene amfanin arzi'kin sa da bazai zuba 'yan aiki ba su dinga yin komai a cikin gidan ba!! to wallahi da ni yake zancen sai nayi maganin sa,nasan babu mai zuga shi sai muna fukar uwarsa,kuma ina nan ina jiran zuwan sa,sabo da haka ki kwantar da hankalin ki dole ne ma ya mai dake ki koma ɗakin ki, a wannan karan dole ne a shirya min ke sosai sabo da haka zan yiwa 'yar Sokoto magana ta haɗa miki haɗad'd'un magun guna tare da na mallaka. daga haka ta mi'ke ta kama hannun rufaida suka wuce zuwa parlo...

BUBA

Zaune yake cikin dabar su a cikin daji suna tattaunawa da yaran sa,suna cikin tattaunawar ne sai ga wani yaran sa da ya tura ya bin ciko masa labarin Inna laure,yana zuwa ya kai bakin sa dai dai kunnen buba ya labar ta masa cewa inna laure tana gidan yayan ta malam musa.nan take buba yayi sauri ya miƙe tsaye tare da duban yaran sa yace musu "ko wannen ku ya fito da kayan aikin sa zamuje muyi wani muhimmin aiki" daga haka suka fara fito da makaman su masu haɗarin gaske, bayan sun gama ne buba ya miƙi hanya su kuma suka take masa baya runduna guda!! suna tafiya ƙura na tashi sama...................

Ina matuƙar godiya a gareku masoya na a duk inda kuke a faɗin ƙasar nan, sannan ina yi muku fatan alkhairi,na gode sosai da addu'o'in ku a gare ni......................

Daga al'kalamin FATIMA BINTU ABDULLAHI (UMMU AYSHA)..................

08162055134.

💝💞 HALIMATU💝💞

Love, sacrifices, destiny & betrayed)

💝💞💝💞💝💞💝💞

Story & Writing

By

FATIMA BINTU ABDULLAHI (UMMU AYSHA)

Ƙarƙashin jagorancin

(MIKIYA WRITERS ASSOCIATION)

Golden pens...............✍🏻

💝💞💝💞💝💞💝💞

2024 novel

💝💞💝💞💝💞💝💞

Page _____________21&22

MOMY

Zaune take akan two seater tana kallon news hannun ta riƙe da remote, HALIMATU ce ta fito daga cikin kitchen ita da baba ladi hannun su riƙe da food wamers suka nufi dining table suka jere akai,sake komawa su kayi suka kwaso sauran.bayan sun gama ne momy ta umarci HALIMATU da taje tayi wanka tazo suyi lunch idan sun gama zasu fita ita da farouq.

HALIMATU tace "to" tare da miƙewa ta haye sama.bata daɗe da tashi ba sai ga farouq ya iso,da sallama ya shigo ya zauna saman one seater tare da gaishe da momy bayan ta amsa ne take ce masa"ina so ka kai HALIMATU makarantar islamiyya, sabo da naga ba wani nisa tayi a karatun addini ba" yace "tom shikenan momy babu damuwa ta shirya idan na gama cin abinci sai na kai ta.

Daga haka ya miƙe ya nufi dining table ya zauna ya zuba abincin da ransa yake so domin shi baya wasa da Cikin sa.bayan ya gama ne ya miƙe ya kalli momy yace "momy bari naje part ɗin mu!! Idan ta shirya tayi min magana"momy tace"okey tom shikenan".daga haka ya fice daga cikin parlon.

Bayan fitar sa babu daɗewa HALIMATU ta sakko ƙasa cikin shirin mai kyau da tsari sai baza ƙamshi take yi, fuskarta tayi fresh sosai ba ƙaramin kyau tayi ba.momy tace "masha Allah doghter kinyi kyau sosai" HALIMATU tace thank u momy" daga haka momy ta jata suka nufi dining table suka yi lunch,bayan sun gama ne momy ta ɗauki waya ta kirawo farouq, yace gashi nan zuwa.

Ba'a wani ɗauki lokaci ba ya shigo parlon,momy tace "yauwa doughter tashi kije ki ɗakko hijab ɗinki ki zo ku tafi zai kaiki islamiyya ya yankar miki form". cike da murna da zumud'i HALIMATU ta mi'ke da sauri ta yi sama, momy ta kalli farouq tace"idan kunje ka kaita gurin ustaz duk abin da ya kama ta ayi mata sai ayi mata,idan kuma akwai ƙarin bayanin wani abun you will let me know"

Farouq yace"okay momy in sha Allah, miƙewa yayi sakamakon ganin HALIMATU ta sakko yace"momy sai mun dawo"tace"okay tom a dawo lafiya"daga haka itama momy ta tashi ta haye sama domin ta ƙara kimtsa wa sabo da tasan daddy zai iya dawowa a koda yaushe.

MUKHTAR

Bai ɗauki wani dogon lokaci ba ya iso gidan su domin amsa kiran da daddy yayi masa, babban parlon gidan ya nufa inda ya iske daddyn sa da hajiya zainab zaune suna hira,a gefe guda kuma ga sahal da amal suna ta wasa anyi musu wanka an shiya su gwanin ban sha'awa,yasan wannan aikin bana kowa bane ba sai na auta.

Yaran suna ganin sa suka taho da gudu ya buɗe musu hannun sa suka shige ya mayar da hannun ya rungume su yana shafa kansu.daddy yace"wato kunga daddyn ku ko?? Shine kuka gudu wajen sa ko??tom shikenan babu ruwa na daku" ya ƙarasa maganar yana musu murmushi,suma yaran murmushi suka yi masa tare da sakin daddyn su suka rugo da gudu suka rungume daddy.

Ƙarasowa yayi gaban su ya dur'kusa cike da ladabi ya gaishe su tare da tambayar su gidan,amsawa sukayi da lafiya k'alau .hira suka ɗan taɓa kafin daddy ya yi gyaran murya yace"mukhtar akwai maganar da nake so inyi maka" ɗagowa yayi tare da duban daddy yace "okay tom daddy inaji" ya faɗa tare da sunkuyar da kansa ƙasa .
Chapter 16 · 0% Book details