← Book details Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 80

Sashe 22

Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gaba ɗayan su sun hallara a dinnig har da daddy da MOMY,batare da ɓata lokaci ba suka fara cin abincin.bayan sun gama ne mazan suka dawo falo aka zauna zaman hira,kowa tambatar HALIMATU yake yi akan jarabawa ita kuma tana basu amsa.mazan ne suka tashi domin tafiya part ɗinsu su kwanta ,bayan fitarsu ne daddy yayi gyaran murya tare da kiran sunan HALIMATU.

Amsawa tayi tare da sunkuyar da kanta ƙasa sabo da tasan abu me mahimman ci daddy zai faɗi.cikin hikima da dabara yafara bata labarin duk abin da yake faruwa,ya ƙara da cewa "umarni ne muka baki ba,da fatan zaki yi mana biyayya a matsayin mu na iyayen ki".tun lokacin da ya fara maganar taji gaban ta yana ta faman faɗuwa da ƙyar ta daure ta sai ta yanayin ta gudun kar su ga halin da take ciki.

Daddy yace "kin yi shiru baki ce komai ba HALIMATU , idan bakya so bazamu tilas taki ba!"ya ƙara sa maganar tare da duban ta .ai da sauri ta ɗago da kanta ta dube shi tace"a'a wallahi daddy ba haka bane ba,duk abinda da kuka yanke shine daidai ba Sai kun nemi shawara ta ba!!"cike da farin ciki har suna haɗa baki wajen cewa"Allah ubangiji yayi miki albarka"ta amsa da "ameen" daga haka ta tashi ta haye sama ta barsu anan,koda ta shiga daki saƙe saƙe tayi tayi a zuciyar ta har bacci yayi awon gaba da ita.

Washe gari tunda asuba suka tashi,bayan sun yi sallah ne suka shiga kitchen suka fara haɗa break fast, ƙarfe takwas suka gama komai tare da jera komai akan dining table .ƙarfe tara kowa ya hallara a kan dining ɗin kasan cewar weekend ne. bayan sun gama break fast ɗin ne MOMY ta ce da HALIMATU taje ta sako hija bin ta za su fita ita da farouq.

Miƙewa tayi tare da haye wa sama, ko minti biyu bata yi ba ta sakko sanye da hijabi.farouq MOMY ta kalla tare da cewa "ka kai HALIMATU wajen da muke zuwa ƙunshi da gyaran jiki, already nayi magana da matar,idan ka ajiye ta kaje gurin telan nan ka karɓo mata kayan ta mun yi waya da shi yace azo a karɓa".

Farouq yace to tare da ficewa HALIMATU ta bishi a baya.ba tare da ɓata lokaci ba suka ɗauki hanya,suna zuwa gurin aka karɓeta hannu bibbiyu tare da fara yi mata duk abinda MOMY ta faɗa musu. sai wajen azahar aka gama mata gyaran jiki da gyaran gashi harda su gyaran face, sannan aka yi mata ƙunshi ja da baƙi.

Ba ƙaramin kyau HALIMATU tayi ba, sabo da idan ka gan ta sai kayi da gaske zaka gane ta,fatar ta tayi fresh ta sha gyara sai glowing take yi .ana gamawa matar ta kirawo MOMY ta sanar da ita, ba tare da ɓata lokaci ba MOMY ta kirawo farouq tace yaje ya ɗakko HALIMATU.cikin abin da bai wuce minti talatin ba farouq ya iso ya ɗauke ta suka tafi gida.

Suna shigowa kallo ya koma kan HALIMATU,gaba ɗaya yaba irin kyan da tayi suke yi .baba ladi tace "ma sha Allahu jikan ya ta, Allah ubangiji ya kauda idon maƙiya, MOMY ta amsa da "ameen". ba tare da ɓata lokaci ba MOMY ta umarce ta da taje tayi wanka ta haɗa mata ruwan wankan.cike da bin umarni ta wuce zuwa sama taje tayi wanka da wani irin ruwa mai ƙamshi,bayan ta fito ne MOMY ta shigo tace mata tayi sauri ta shafa mai ga mai make up nan tazo zatayi mata, ta amsa da ".to"

Cikin sauri ta gama shafa man,jim kaɗan sai ga MOMY ta shigo tare da wata mata da kit a hannun ta,nan take aka fara tsara mata kwalliya ta ban mamaki............

Mu haɗu gobe idan Allah ya kaimu dan jin yadda zata kaya.

Ina muƙar godiya da addu'ar ku a gare ni tare da fatan alkhairi, kuɗin na musamman ne. Inai muku fatan alkhairi.

Daga alƙalamin FATIMA BINTU ABDULLAHI (UMMU AYSHA)..........

08162055134

💝💞HALIMATU💝💞

(Love, sacrifices, destiny & betrayed)

💝💞💝💞💝💞💝💞

Story & Writing

By

FATIMA BINTU ABDULLAHI (UMMU AYSHA)

Ƙarƙashin jagorancin

(MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION)

Golden pens..............✍🏻

💝💞💝💞💝💞💝💞

2024 novel

💝💞💝💞💝💞💝💞

Page_____________27&28

"MUKHTAR"

A ɓangaren mukhtar kuwa tunda yaje masallaci sallar asuba ya dawo bai kuma fita daga cikin gidan ba sai da aka yi sallar azahar,bayan an idar da sallar ne ya shigo cikin gidan direct kitchen ya nufa domin ya samu abin da zai sawa cikin sa.tun ranar da ya sallami rufaida bayan ya dawo gida ya sallami mai aikin su.

Indomie ya dafa tare da boil egg, sannan ya haɗa coffee a coffee maker,cup da plate ɗin ya ɗauko ya juye indomie a plate shi kuma coffee ɗin ya juyeshi a mug, direct parlour ya nufa hannun sa ɗauke da break fast ɗin.zama yayi a kan dining table tare da yin bismillah ya fara ci.

Yanaci yana yamutse fuska sakamakon rashin jin daɗin abincin.bai ɗauki lokaci ba ya gama yin break fast ɗin,direct sama ya nufa ya shige bedroom ɗin sa,ba tare da ɓata lokaci ba ya shiga bath room ya fesa lafiyayyan wanka ya fito da towel ɗaure a ƙugun sa da kuma ƙarami a hannun sa yana goge sumar kansa.

Wayarsa ya ɗauka da ke kan mirror tare da dialling numbern Meena,ringing ɗaya biyu ana ukun tayi picking call ɗin tare da yin sallama,amsawa yayi tare da cewa "ki shirya yanzu gani nan shigowa gidan zamu fita unguwa" ya ƙare maganar tare da tsinke kiran ya ajiye wayar.....

Cikin sauri ya ɗakko lotion ɗinsa mai matuƙar ƙamshi da tsada ya shafe jikinsa da shi, sannan ya gyara lallausar sumar kansa sai sheƙi da ƙamshi take zubawa.cikin sauri ya ɗauki singlet da boxers ya saka tare da ɗauko wata rantsar blue ɗin shadda ƴar ubansa ya saka.hula ya ɗakko zanna bukar wadda ta dace da shigar tashi ya ɗora a kansa.

Agogon dimon ɗinsa ya ɗakko ya ɗaura a hannun sa, sannan ya feshe jikin sa da daddaɗan turarukan sa,wow ba ƙaramin haɗuwa MUKHTAR yayi ba,idan ka ganshi sai ka dauka sabon angone,babu abinda yake tashi a jikinsa sai daddaɗan ƙamshin turare.

A hankali yake sakkowa daga staircase hannun sa riƙe da wayoyin sa guda biyu tare da mukullin mita, innocent face ɗin nan tasa cike da annuri.direct parking space ya nufa tare da buɗe wata danƙareriyar mota cikin motocin da suke parke a gurin,shiga motar yayi tare da yin bismillah ya kuna tare da jan motar.tun kafin ya ƙaraso bakin get ɗin megadi ya buɗe masa get ɗin,yana ƙarasowa direct ya fice daga cikin gidan.....

Direct gidan su ya nufa,yana ƙarasowa yayi parking motarsa a bakin get ɗin gidan tare da shigewa cikin gidan.sallama yayi tare da shigewar sa cikin parlon,daddy da MOMY ya tarar zaune akan kujera suna hira,durƙusawa yayi a gaban su ya gaishesu cike da ladabi,amsawa sukayi fuskar su ɗauke da murmushi.

Kallon sa MOMY ta yi tare da cewa "my son irin wannan gayu haka da kaci kamar zakaje gasar kyau "wata irin kunya ce ta rufeshi kamar ya nutse a ƙasa yaji.daddy ne yace"hmm lallai kina da mantuwa zainab,kin manta yaune zaije yaga HALIMATU "murmushi ne ya suɓucewa MOMY ta kalli daddy tace"ina zan manta da wannan rana mai mahimmanci a garemu, wallahi zolayarshi kawai nake yi sabo da naga ɗan nawa yayi kyau sosai ma sha Allah ba ƙarya".

Murmushi daddy yayi tare da cewa"ai dole yayi kwalliya sosai dan kar a raina mana shi ko my son" ya ƙarasa maganar yana kallon MUKHTAR fuskar sa ɗauke da murmushi,shi dai MUKHTAR ƙara sunkuyar da fuskar shi yayi domin gaba ɗaya kunya ta kama shi.

Daddy ne yayi gyaran murya tare da cewa "to my son yau dai Allah yayi zaka je ku gaisa da HALIMATU ka ganta ta ganka,ina so idan kaje ku fahimci juna kai da ita,ka lura da kyau sosai ka tsayar da hankalin ka kafuskan ceta sosai,duk da dai nasan banyi maka zaɓen tumun dare ba in sha Allahu zakaji daɗin zama da ita,ka ɗora ta akan turbar da duk kakeso ta kasance maka tunda yarinya ce ƙarama yanzu take shirin shiga jami'a, idan kuma kaga bata yi maka ba karkayi ƙwauron baki ka gaya min kawai".

Ya ƙarasa maganar yana kallon MUKHTAR tare da tabbatar masa da abin da yake faɗa masa.ɗago da kansa yayi tare da cewa"in sha Allahu daddy zanyi amfani da duk abin da ka faɗamin"daddy yace"to ma sha Allah, Allah ubangiji yayi maka albarka yasa a dace" ya amsa da"ameen" MOMY tace"ina yi maka fatan alkhairi my son Allah ubangiji ya tabbatar da alkhairin sa" yace"ameen MOMY.

Daddy ne yace "yakamata ka tashi ku tafi kar lokaci ya ƙure maka" tashi yayi tare da kallon MOMY yace "MOMY ki cewa meena ta sameni a bakin get ina jiran ta" "to" tace tare da ƙwalawa meena kira, nan take meena ta fito cikin shiga ta alfarma,ta saka wata gown ta purple ɗin less tare da yafa medium ɗin veil a kanta, ƙafar ta sanye da hill shoe.

Sakin baki MOMY tayi tana kallon ta tare da cewa "ikon Allah!wannan uwar kwalliyar da kikaci duk ta rakiyar ce??" "Kinga ki ƙyalemin yara na!ai gwara a gansu acan acan dasu"daddy ya faɗa yana murmushi.murmushin itama tayi ba tare da tace komai ba.mukhtar ya kalli daddy tare da cewa"daddy bari mu tafi sai mun dawo"okay son Allah ya dawo da ku lafiya,ka gaishe min da surukata.

Har ya ɗaga ƙafa da niyyar fita daga parlon ya tsinkayi muryar daddy yana cewa"ina fatan dai kasan gidan??"cak ya tsaya tare da juyowa,dan wallahi shi kwata kwata ya manta da cewa bai san gidan ba sabo da zumuɗin zuwa ya ga HALIMATU."bansan gidan ba daddy"ya faɗa kansa a sunkuye,murmushi daddy yayi irin na manya tare da cewa "okay son karka damu kaje zan tura maka address ɗin gidan nasu"girgiza kansa yayi tare da ficewa daga parlon meena ta mara masa baya,suna fitowa bakin get ɗin suka shiga cikin motar, shigarsu keda wuya yaji ƙarar shigowar message,yana dubawa yaga daddy ne ya turo masa address ɗin,nan take yayi bismillah ya kunna motar yaja suka ƙara gaba.

"HALIMATU"
Chapter 22 · 0% Book details