← Book details Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 80

Sashe 80

Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read

Rayuwa mai daɗi da farin ciki da kwanciyar hankali ce take gudana a tsakanin wannan halin,idan mukhtar ya yi ƙiba sosai kamar ba shi ba,ga arziƙinsa da kullum ƙara yawa yake yana ta albarka.har ya ƙara buɗe sabon Company na ƙera gwala-gwalai a dubai,bai cika zama a Nigeria ba, wannan dalilin ne ya sa ya bar komai a hannun nura ya tattara iyalinsa suka koma dubai da zama.da ƙyar ya bar halimatu ta koma makaranta.

BAYAN SHEKARA UKU

Halimatu ta kammala karatunta a fannin kasuwanci kamar yanda tun farko mukhtar ya zaɓa mata,a yanzu tana aiki a Company ɗinsa na dubai,idan ka ganta da ƙyar zaka gane ta.domin ta zama gogaggiyar ƴar boko,domin ta waye ta goge ta ƙara fari da kyau ta saje da larabawan dubai ɗin.ga kuma kulawa sosai da take samu a wajen mukhtar ita da yaranta,domin ba ƙaramin so yake yi musu ba.....

!!TAMMAT BI HAMDULILAH!!....

Abinda na rubuta daidai Allah ubangiji ya sa mu amfana da shi.

Abinda na rubuta ba daidai ba Allah ubangiji ya yafe mana baki ɗaya.

Ina matuƙar godiya ƙwarai da gaske masoyana da kuka biyo ni tun daga farkon labarin zuwa ƙarshe kuma kuka jure wa halina na rashin yin typing akai akai! Allah ubangiji ya saka muku da mafificin alkhairinsa ya biya muku buƙatun ku na Alkhairi🥰🙏🏻

Daga alƙalamin FATIMA BINTU ABDULLAHI(UMMU AYSHA)....✍🏻✍🏻

Sai mun haɗu a sabon book ɗina mai suna "JUYIN MULKI".....

Ina yi matuƙar sonku fan's ɗina tare da yi muku fatan Alkhairi a ko da yaushe,na gode sosai.🥰🙏🏻

08162055134...
Chapter 80 · 0% Book details