Sashe 34
Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Daga kan kayan sawa,hijabi,mayafi,turare,man shafawa,sabulun wanka da nawanki, duk ya siya wa ko wacce daga cikin su.
Hatta da yaran su da maza jen su sai da ya yi musu ta su siyayyar,sannan ya haɗa wa ko wacce daga cikin su kayan abin ci irin su shinkafa,taliya, macaroni,in domie,mai,manja,maggi da dai sauransu.
Hatta maƙotan sa sai da ya yi musu tsaraba suma.
A motar sa siyana aka loda kayan gaba ɗayan su.
Ba su suka dawo gida ba sai yamma liƙis suka dawo a gajiye.
Washe gari aunty AMINA ta yi cin cin da doughnut da cake,dama ta riga da tayi dambun nama.
Wunin ranar aikin da ta yi kenan domin ta na jin kunyar taje bata kai musu komai ba,bayan ta gama ne ta yi packaging ɗin su a madai dai tan robobi masu kyau tare da ware wa kowa na sa.
Ɗakin baba ta shiga ta kimtsa masa kayan sa a cikin akwati mai kyau,bayan ta gama ne taje ta ƙarasa kimtsa kayan ta da na Ahmad sabo da gobe idan Allah ya kaimu da wuri za su wuce.
Washe gari bayan sun yi sallar asuba suka fara shirin tafiya,sai da suka yi break fast sannan suka ɗauki hanyar zuwa garin HAƊEJA,sai dai muce Allah ubangiji ya kai su lafiya.......
"INNA LAURE"
A ɓangaren inna laure kuwa,gaba ɗaya ta rasa sukuni a cikin zuciyar ta,bata da nutsuwa kwata kwata,ta rasa meye matsalar ta.
Gaba ɗaya jin kanta take yi kamar ta rasa wani abu mai mahimmanci a cikin rayuwar ta,duk da cewa jikin ta ya yi sauƙi sosai Alhamdulillah, amma kallo ɗaya zaka yi mata kasan tana da damuwa sosai a cikin ranta.
Fuskantar hakan da HANNE ta yi ne yasa take kwantar mata da hankali,domin bata so ta ganta a cikin ƙunci da baƙin ciki,duk da murnar da ta yi na tsayar da ranar bikin HANNE da za'a yi gobe,domin maƙocin su abokin baba wanda suke yin waya da shi ne ya tsaya wa HANNE a matsayin uba.
Kuma hakan umarnin baba ne,sabo da duk abin da yake faruwa yana gaya wa baban, wannan dalilin ne yasa malam ummaru ya wakilta malam sabo akan ragamar komai na gidan da kuma sa masa ido akan iyalin na sa.
Shi yasa ma ya tawo domin a yi komai a kan idanun sa.
Wannan kenan......
"BUBA"
A ɓangaren BUBA kuwa,yaran sa sun ƙara duba wa saƙo da lungu amma basu ga ko masu kama da su HANSAI ba, wannan dalilin ne ya ƙara hasala BUBA,domin ba ƙaramin azabtuwa yake yi da soyayyar Safara'u ba.
Duk da cewa shi ɗin bai cika samun zama sosai a ƙauyen ba,sabo da ayyukan da suka yi masa yawa,domin zuwa yanzu yaran sa sun ƙara yawa sosai,har ya sake buɗe wata sabuwar ƙungiyar, Sabo da yana da iyayen gida da suke bashi dukkan wani umarni,kuma sune suke basu mugayen makamai.
Yana kai wata ɗaya ma bai shigo ƙauyen haɗeja ba,sabo da ako da yaushe cikin aiki suke, kuma yana nan da batun HANSAI da Safara'u bai man ce da su ba, domin har yanzu asirin da boka ya yi yana nan yana aiki a jikin shi,yana fatan Allah ya haɗa su wata rana.
Wannan kenan....
"HANSAI"
A ɓangaren su HANSAI da Safara'u kuwa,rayuwa suke hankalin su kwance abin su,domin yanzu babu fargabar cutar War BUBA a tattare da su.
Zuwa yanzu sun saki jikin su sosai kuma mutane sun sansu sun saba da su,a gefe guda kuma Safara'u nata zuwa makarantar islamiyya da boko,kuma Alhamdulillahi tana fahimta sosai saɓani zaman da ta yi a ƙauye cikin jahilci da duhun kai bata san komai ba sai talla.
Ta fara gogewa da waye wa abin ta, sakamakon wayayyun ƙawaye da ta samu,kuma babu laifi SANA'AR da suke yi suna samun abin rufin asiri,gashi har mane ma sun fara kawo mata hari.
Sai dai mu ce Allah ya kare su daga sharrin BUBA.
Wannan kenan....
"HALIMATU"
A ɓangaren su HALIMATU kuwa,kamar kullum a gajiye ta dawo daga makaranta,sallah azahar kawai ta yi sannan ta ci abinci,har ta miƙe da nufin hawa up stairs MOMY ta kirawo ta.
Dawowa ta yi ta durƙusa a gaban MOMY tace:
"MOMY gani"
"Yauwa dama MUKHTAR ne ya kirawo waya ɗazu bayan kin tafi makaranta,yace a gaya miki yana nan tafe zai zo anjima".
Gaban ta ne ta ji ya faɗi! nan take ta yi sauri ta sun kuyar da kanta ƙasa ba tare da tace komai ba,ta rasa mai zata yi! Farin ciki ko baƙin ciki!.
Shirun da MOMY ta ji ne yasa ta ce mata:
"Kin yi shiru baki ce komai ba...?"
"Maza tashi ki shiga kitchen ki shirya masa wani abun mai sauƙi!!"
Cike da jin matsananciyar kunya tace "to MOMY" tare da miƙewa ta shige cikin kitchen.
Tunani ta tsaya yi na abin da zata girka masa,daga bisani ta yanke hukuncin girka masa spicey
rice and stew da cowslow, sannan da kuma fruit salad sai chiken bread da kuma haɗaɗɗen shayi mai daɗin gaske.
Tukunya ta ɗauka ta ɗauraye tare da zuba ruwa ta ɗaura akan gas,sake ɗaukko wata tunyar ta yi ta kuma zuba ruwa a cikin ta, sannan ta ɗakko ƙwai guda biyar ta zuba a cikin tukunyar tare da green peas.
Irrish potatoes ta ɗakko tare da feraye wa ta yanka shi ƙana na. wanke wa ta yi ta zuba a cikin tukunyar da ta zuba ƙwai da green pies,salt ta ɗakko kaɗan ta zuba tare da rufe wa.
Basmati rice ta ɗakko ta wanke ta zuba a abin tace shinkafa domin ta tsane,kaza ta ɗakko a cikin freezer ta wanke da white veniger.
Sauke ɗaya tukunyar ta yi da ruwan ya tafasa tare da juye wa a wata roba mai murfi ta rufe. kazar ta kawo ta zuba a cikin tukunyar ta mai da tukunyar kan gas.kalolin spices ta ɗakko da seasoning da tafarnuwa da ginger ta zuba tare da saka ruwa kaɗan domin kazar turawa bata daɗewa a wuta sosai.
Kayan miya ta ɗakko ta gyara tare da yin blending ɗin su ta ajiye su a gefe,sannan ta ɗakko cabbage, cucumber, carrots ta wanke su tsaf da white veniger sannan ta yi greating ɗin su ta ajiye a gefe.
Komawa ta yi ta sauke kwai da su irrish potatoes ta zuba su a cikin coolender domin su tsane.tukunyar dafa shayi ta ɗakko ta ɗauraye ta zuba ruwa a ciki, sannan ta kawo cloves,ginger, cinnamon, Star anis,goruba, mints leaves,lemon grass da kuma lemon tsami ta matsa a ciki.
Suger ta ɗakko ta ɗan zuba a ciki ta ɗiga straw berry plavour a ciki sannan ta ɗora tukunyar a kan wuta.
Kazar da ta ɗora ta sauke domin ta nuna,juyewa ta yi a cikin container sannan ta ɗaukko wata tukunyar ta zuba mai a ciki tare da saka albasa kaɗan,sai da ta bari albasar ta fara soyuwa sannan ta fara zuba kazar a cikin man tana soyawa,idan ɗayan ɓangaren ya yi golden brown sai ta juya ɗaya ɓangaren.
Haka tayi ta yi har ta gama,rage man ta yi sannan ta ɗakko albasa ta zuba da ɗan yawa, niƙaƙƙen nama ta ɗakko ta zuba tare da zuba mix spices a ciki.
Bayan naman ya ɗan soyu ne ta ɗakko kayan miyan da ta yi blending ta zuba a kai ta juya sannan ta ɗan rufe,komawa ta yi ta ɓaɓɓare kwan ta yayyan ka shi ta ajiye a gefe, sannan ta ɗakko irrish ɗin da ta dafa shima ta ajiye a gefe.
Pies ɗin ma ajiye shi ta yi a gefe guda.
Koma wa tayi wajen stew ɗin ta buɗe ta juya tare da zuba seasoning da spices, sannan ta kawo ruwan da ta tafasa kazar ta zuba a cikin stew ɗin.
Soyayyen naman kazar da ta soya ta kawo ta zuba a kai ta ƙara juyawa tare da rage wutar a medium low plame sannan ta rufe.babu abin da yake tashi sai ƙamshin girkin HALIMATU.
Tukunya ta ɗakko ta ɗora a kan wuta tare da zuba mai kaɗan,sannan ta kawo cardamon, star anis, cinnamon clove ta ɗan watsa su kaɗan a cikin man tare da yankakkiyar albasa, basmati rice ɗin da ta wanke ta tsane ta ɗakko ta zuba a kai tafara juyawa, seasoning ta saka kaɗan sannan ta ci-gaba da juyawa.
Sai da ta fara soyuwa sannan ta zuba tafasashen ruwan zafi a cikin ta wanda tasan zai dafa mata shikafar ta, sannan ta ɗakko pies ɗin da ta ɗan dafa ta zuba a kai ta juya ta rufe.
Komawa tayi ta buɗe stew ɗin ta taga tayi mata yanda take so,sauke wa ta yi sannan ta sauke shayin ta wanda ƙamshin sa kawai zai tabbatar maka cewa ya haɗu sosai.
Rariyar tace shayi ta ɗakko ta tace sannan ta ɗakko haɗaɗɗun plask ɗin shayi ta zuba a ciki.
Komawa ta yi ta buɗe shinkafar ta ta zuba yankakken carrots,red bells pepper ,soyayyar albasa tare da saka orange food colour kaɗan ta rufe.
Koma wa ta yi ta ɗauki bowl mai ɗan girma ta zuba cabbage ɗin da ta yi greating tare da carrots, cucumber, sweets corn,red kidney beans,dafaffen ƙwan da ta yanka da kuma dafaffen irrish ɗin da ta yanka.
Sannan ta kawo ƙaramin bowl ta zuba Bama,madarar gari, suger,garin black papper salt da maggi kaɗan tayi mix ɗin su sosai sannan ta kawo ta zuba a cikin cowslow ɗin ta juya sosai.
Shinkafar ta sauke tare da ɗakko haɗaɗɗun food wamers ta zuba a ciki, sannan ta ɗakko set ɗin wasu haɗaɗɗun bowl ta zuba cowslow ɗin a ciki ta saka a fridge.koma wa ta yi ta ɗakko wasu food wamers ɗin ta zuba stew ɗin a ciki.
Kayan fruit ta ɗakko ta wanke tare da yayyan kawa ta zuba a cikin babban bowl, couscous ta ɗakko tare da dora pan a kan wuta butter ta zuba a cikin pan ɗin,tana yin melting ta ɗebo couscous half cup ta zuba ta fara soyawa,yana yin colden brown ta sauke.
Zuba soyayyen couscous ɗin ta yi a cikin yankakkun fruit salad ɗin,ta kawo fresh yoghurt ta zuba a kai, sannan ta ɗakko madarar gari da condens milk ta zuba a kai, Syrup ta kawo ta zuba kaɗan tare da ɗiga vanilla extract kaɗan a ciki sannan ta juya sosai ta saka a fridge.