Sashe 28
Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A ɓangaren MOMY kuwa lokacin da ta sakko down stairs domin shiga kitchen,sai taji wani irin ƙamshin girki mai daɗi da yake tashi, kitchen ɗin ta nufa domin duk a tunanin ta baba ladi ce,turus tayi a bakin ƙofa lokacin da tayi arba da HALIMATU ta haƙiƙan ce tana ta aikin haɗa musu break fast.murmushi tayi tare da juyawa ta koma sama ba tare da ta bari HALIMATU ta ganta ba, domin dama tana da niyyar fara practice ɗinta a wajen girki.
Kowa ya hallara a dinnig ɗin ana yin break fast,ba su MOMY kaɗai ba hatta su yaya ya hafiz sun cika da mamakin cewa HALIMATU ita ce tayi girkin nan, daddy kuwa gyaɗa kansa kawai yake yi sakamakon daɗin da girkin yayi masa.halimatu kuwa babu abin da take yi sai murmushin jin daɗi,ita kanta ta yaba wa kanta ƙokarin girkin da tayi.
Bayan sun gama yin break fast ɗin ne daddy yayi gyaran murya tare da kallon HALIMATU yace "gaskiya naji daɗin abincin da kika girka mana ƴata Allah ubangiji ya ƙara zaƙin hannu,ki ci-gaba da maida hankali kina koyon abubuwa kinji" HALIMATU tace " tom daddy in sha Allahu na gode" MOMY ce ta kalle ta tace " tun da kin shirya tashi farouq ya kai ki makaranta" cike da zumuɗi da jin daɗi tace"to". Miƙewa tayi tare da ɗaukar jakar makarantar ta suka fita .
"MUKHTAR"
A ɓangaren mukhtar kuwa, lokacin da ya koma gida wanka yayi tare da yin sallar isha'i yayi addu'a,yana idar wa ya sakko ƙasa zuwa kitchen ya haɗa coffe ya zuba a cikin mug.plate d bowl ya ɗakko ya zuba spring rolls da samosa,sannan ya zuba dambun nama,sauran ragowar kuma ya zuba a cikin frizer.ɗakkowa yayi ya fito daga kitchen ɗin zuwa dining, zama yayi tare da yin bismillah ya fara cin abincin sa, sai da yacin ye gaba ɗaya yana santi sannan ya tashi ya kai kitchen ya ɗauraye ya kife tare da kashe glove ɗin ya rufo kitchen ɗin.
Glove ɗin parlorn ya kashe tare da haye wa sama yayi kwanciyar sa.ƙarfe huɗu ya tashi yayi nafil fili tare da yin addu'a sosai Allah ubangiji ya tabbatar musu da Alkhairin sa shida HALIMATU.bashi ya tashi a gurin ba sai da aka kirawo sallar asuba sannan ya sakko ya nufi masallaci.sai da gari yayi haske sosai sannan ya baro masallacin,yana shigowa gida kitchen ya nufa ya haɗa coffee tare da warming ɗin snacks ɗin sa yayi break fast.
Bayan ya gama ne ya haye up stairs zuwa ɗakin sa tare da yin wanka ya shirya cikin suit black colour baƙaramin kyau MUKHTAR yayi ba sai tashin ƙamshin ddaɗan turarukan shi yake yi.brief case ɗin sa ya ɗauka tare da sakkowa ƙasa,cikin sauri ya fice daga cikin gidan sabo da yana da ayyukan da zai yi da yawa a office..
Ina matuƙar godiya a gareku masoya na masu Albarka abin alfharina,babu abin da zance muku sai godiya tare da fatan Alkhairi
Dafa alƙalamin FATIMA BINTU (UMMU AYSHA)...................✍🏻
Share fisabilillahi......
O8162055134
💝💞HALIMATU💝💞
(Love, sacrifices, destiny & betrayed)
💝💞💝💞💝💞💝💞
Story & Writing
By
FATIMA BINTU ABDULLAHI (UMMU AYSHA)
Ƙarƙashin jagorancin
(MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION)
Golden pens..............✍🏻
💝💞💝💞💝💞💝💞
A 2024 novel
💝💞💝💞💝💞💝💞
Pages____________31&32
"UMMA"
A ɓangaren umma mahaifiyar RUFAIDA kuwa, lokacin da boka ya gama yi mata bayani take ta miƙe tsaye kamar an watsa mata ruwan zafi a jikin ta,ta dube shi da idanun ta da suka yi jajur sabo da ɓacin rai da tashin hankali tace "da kata malam!! Wannan wacce iriyar magana kake gaya min mara daɗin sauraro!! To bari kaji in gaya maka! Idan kai ɗin ba zaka iya yin wannan aikin ba ai sai ka gaya min! Amma bawai ka zauna kana tsara min ƙarya ba!!" Ta ƙara sa maganar tana masa wani irin mugun kallo.
Wani irin murmushin takaici malam ya saki sannan ya dube ta tare da cewa "Hajiya Hauwa kenan,haƙiƙa kin bani mamaki! Shekara ɗai ɗai har takwas ina yi miki aiki babu gajiya wa, kuma duk irin aikin da nayi miki yana tafiya dai dai kuma ana samun biyan buƙata sosai da sosai,amma shine yanzu sabo da ke ɗin butulu ce wadda kwata kwata bata san halacci ba zaki dubi tsabar idanu na ki gaya min wannan maganar!! Ai ko ba komai na haife ki!! Ko dan furfura ta ya kama ta ki girmama Ni!!"
Ajiyar zuciya ya sauke yana jin wani irin ɓacin rai na taso masa, cikin ƙunan rai ya ci-gaba da cewa "ina so ki buɗe kunnuwan ki ki saurari abin da zan faɗa miki!! Duk inda zaki je abin da na faɗa miki shi za'a ƙara faɗa miki! Idan kuma kin ji akasin haka to kuɗin ki kawai za'a ci!! Duk abin da kika ga na kasa lalubu shi to ba ƙaramin al'amari bane ba! Don haka ki fice min daga nan!! Kuma ina gargaɗin ki da kyau kar na ƙara ganin ƙafafuwan ki anan gurin!idan kuma ba haka ba kin san sauran!!".
Ya ƙara sa maganar cike da wata irin tsawa yana nuna mata hanyar fita.cike da tsoro jikin ta yana rawa ta juya cikin sauri ta fice daga ɗakin nasa,domin bata taɓa ganin ɓacin ran malam irin haka ba.ajiyar zuciya ta sauke tare da share gumin da ya tsatstsafo mata a goshin ta , sannan ta fita daga gidan ta miƙi hanya!tana tafe tana zancen zuci.
"INNA LAURE"
Babu abin da yake tashi a cikin gidan sai koke koke,da gudu su rahinatu suka ƙaraso ita da Hanne sakamakon mugun labarin da suka ji.wani irin kuka mai tsuma zuciya da ruhi suka saki lokacin da suka ga halin da su inna laure suke ciki,kuka suke yi babu mai rarrashin wani,musamman ma rahine da abin ya haɗe mata biyu mahaifiyar ta da kuma mijin ta.
INNA LAURE suman ta uku,da an yayyafa mata ruwa ta farfaɗo zafin ciwo sai ya sake sumar da ita,shi kuwa baban kamilu suman shi ɗaya, tun da ya farfaɗo bai ƙara sume wa ba,sai dai kuma numfarfashin da yake na wahala sabo da zafin ciwo.ɗago da kansa yayi ya dubi rahane da ta tsura masa idanu babu ko ƙiftawa,suna haɗa idanu ya fashe da wani kuka mai ban tausayi,kana jin kukan kasan daga cikin zuciyar shi yake fitowa.
Sai da yayi mai isar sa sannan ya buɗe baki cikin azabar ciwo da raɗaɗi yace "rahane kinga abin da ya same ni ko?? Ashe dama tsau-tsayi ne yake kira na!! banji ba ban gani ba an cutar da ni! Wallahi da nason haka ce zata faru da duk abin da za'ayi bazan zo kawo kuɗin nan ba,yanzu ga shi nan gurin taimako sun nakasa min rayuwa ta.ya ƙarasa maganar yana mai fashewa da sabon kuka.
Kuka take yi sosai harda sheshsheƙa ba ƙaramin tausayi ya bata ba,musamman yadda taga ƙafar tashi har ta fara kumbura,cikin kuka tace"kayi haƙuri baban kamilu,ƙaddara ta riga fata,dama Allah ya ƙaddara hakan zai faru daku" ta ƙarasa maganar tare share hawayen da ya zubo akan kuncin ta.
Sallamar HARUNA mijin altine ce ta katse su daga zancen da suke yi, shigowa yayi tare da wani tsohon mutum hannun sa ɗauke da wata jakar fata, tsuguna wa tsohon yayi a gaban babban kamilu ya ajiye jakar da take ruƙe a hannun shi.duban baban kamilu yayi sannan yace masa "sannu! bari na ɗan duba maka ƙafar taka!!". Yana gama faɗin haka bai jirawo cewar baban kamilu ba ya damƙi ƙafar da hannayen shi guda biyu ya tattaɓa tare da lallatsawa.
Wani irin ihu mai firgitarwa haɗe da wani gawur taccen gurnani baban kamilu ya saki,babu shiri baba lado ya sakar masa ƙafar sa,duban sa ya kai gun mijin altine yace masa "a gaskiya Haruna sai an samu waɗan da zasu iya ruƙe min baban kamilu,idan ba haka ba kuwa ba zai taɓa bari a gyara ƙafar nan ba,kuma kaga karayar guda uku ce! Sannan ga yanka!! Idan kuma aka ƙyale shi ƙafar zata iya samun gagarumar matsala!!".
Jin furucin da baba lado yayi ne yasa baban kamilu ƙara fashewa da wani sabon kuka mai tsuma zuciya,babu abinda yake yi sai surutai.miƙewa HARUNA mijin altine yayi tare da kallon jerin mutanan da suke gurin yace "dan Allah ku taimaka mana a samu waɗan da zasu taya ni ruƙe bawan Allah n nan!!"ya faɗa yana duban baban kamilu.
Mutum biyu ne suka fito majiya ƙarfi suka haɗu su uku harda HARUNA suka yiwa baban kamilu ruƙo bana wasa ba.ba tare da ɓata lokaci ba baba lado ya damƙi ƙafar baban kamilu ya fara gyarawa,wani uban ihu ya saki wanda yafi na farko tare da zazzare idanu kamar zasu fito waje Sabo da azabar zafi.
Nan take ya saki kashi da fitsari a lokaci guda, runtse ido baba lado yayi ya murza ƙafar da kyau ji kake ƙaƙaƙas sakamakon komar da ƙashin yayi mazaunin sa,hakanne ya sa baban kamilu ya ƙara kurma wata razananniyar ƙara da tayi sanadiyar farfaɗowar Inna laure daga suman da tayi shi kuma ya sume,har aka gama gyaran bai san inda kansa yake ba.
Umarni baba lado ya bawa rahine akan tazo ta gyarawa baban kamilu jiki,"to"tace! Tare da miƙewa ta yafa mayafinta ta fita domin zuwa ɗakkowa baban kamilu wasu kayan idan ta gyara masa jikin shi ta canja mashi su.
Tashi baba lado ya yi ya ƙara so gurin da inna laure take kwan ce magashiyyan,altine da hanne ne suka ƙara so wajen tare da marka maƙociyar su.duban ƙafar baba lado yayi yaga ta kubura sosai,ɗagowa yayi yace su ruƙe masa Inna laure da kyau sabo da baya so a samu matsala.
Share hawayen da suka sakko akan kuncin ta tayi tare da cewa "to". bismillah malam lado yayi tare da sa hannu ya cafki ƙafar inna laure,nan take tayi wata iriyar zabura ta ƙwace kanta daga ruƙon da suka yi mata abin ka da mai jiki gaba ɗaya ta watsar dasu gefe tana wata iriyar girgiza,gaba ɗaya ilahirin jikin ta rawa yake yi sakamakon azabar da ƙafar take mata.