← Book details Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 80

Sashe 3

Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

hanne ta ce"dama yaushe zaki san na shigo innar mu,bayan kin faɗa duniyar tunani.hmmm to Allah ya kyauta"ta ƙarshe maganar tana keɓe baki tare da mi'kewa tsaye. ta kuma kai duba gurin inna laure tace"wai baƙi mukayi a gidan na mune??ina makewayi na tsinkayo sallama".

Inna laure ta ɗago ta dubi hanne tace"hmmm wannan muna fukar matar ce tazo ƙanwar uwar HALIMATU,ai bata ƙarasa maganar ba ma hanne ta rugo da gudu ta faɗo ɗakin HALIMATU bakinta ɗauke da sallama ta dur'kusa cike da farin ciki tana gaishe da hajiya maryam.

hajiya maryam ta ɗago da kanta daga latsar wayar ta da take yi,ta dubi hanne cike da farin ciki ta amsa mata,tace"hanne ya gida,ya makaranta???"fuskar hanne cike da murmushi tace lafiya k'alau momy,ya hanya?? yasu mahmud?? dafatan duk suna lafiya"

Tace"kowa yana lafiya, duk suna gaisheku"ta ƙarasa maganar da murmushi a fuskarta.

nan hanne ta zauna hira ta barke anata bada labari.

Suna cikin hirar ne suka jiyo muryar inna laure tana kwad'awa hanne kira babu 'ka'k'kautawa,hajiya maryam ta dubi hanne da fuskatarta ta nuna alamar damuwa tace mata "maza tashi kije innarki na kiranki".

ba dan tasoba ta tashi ta fita daga d'akin.
hajiya maryam ta bita da kallo tana girgiza kai,tana tausayin hanne saboda tana da hankali,gashi kwata kwata batayo halin uwarta ba,bama hanne kaɗai ba,duk cikin yaran inna laure babu mai irin mugun halinta, sannan dukkanin su suna mutu'kar son HALIMATU.

Hajiya Maryam ta sauke ajiyar zuciya,tana tunanin irin zaman da yayar ta mahaifiyar HALIMATU tayi da inna laure, zamane wanda kwata kwata babu daɗi a cikin sa sai gallazawa da cutarwa,haka 'yar uwarta ta sha wahalar rayuwa har ta koma ga Allah.

ta kai hannu a fakaice tayi maza ta share hawan da suka zubo a ku akan fuskarta,gudun kada HALIMATU ta ga halin da take ciki.

*************************

A ɓangaren inna laure kuwa lokacin da hanne ta fito da gudu ta barta a d'aki ita kaɗai saboda murnar zuwan hajiya maryam ba ƙaramin baƙin ciki ta tsinci kanta a ciki ba,ita fa abinda yake 'kona mata rai shine yanda kwata kwata 'ya'yanta basu yo halinta ba,duk cikin su babu mai goyon bayan mugun abinda takeyi,ita babban takaicin tama yadda autarta hanne ta biyewa 'yan uwanta,jibi fa daga ganin wannan munafukar matar tazo ta she'ka da gudu cike da murna.

tab wlh da sake,nidai banyi sa'ar haihuwa ba,lallai dole na sake sabon shiri idan ba haka ba wankin hula zai kaini dare,banga ta zama ba,
bazan taba bari HALIMATU taji da ɗin rayuwar ta ba,kamar yadda na hana uwarta,ita ma hakan zan yi mata, dole ne yanzu na tafi wajen Aminiya ta hansai saboda mutattauna, dole ne musan abin yi.

Ta ƙarshe maganar tare da sauke ajiyar zuciya.
ba tare da b'ata lokaci ba,tayi maza ta mi'ke ta zari cukur kuɗaɗen mayafin ta tayafa a kanta,tun daga d'aki take kwad'awa hanne kira cike da fusata "zaki fito daga d'akin nan ko sai nazo naci ubanki,mara zuciya kawai,kin maida ma'kiya na masoyan ki,tunda ke baki san ciwon kanki ba ni ai nasan nawa ciwon kan".

Kafin ta gama rufe bakin ta hanne ta fito daga cikin d'akin HALIMATU tana ta kumbure kumbure tace "wai ni innar mu lafiya kike ta kwad'amin irin wanga kira haka, sai kace nayi miki wani abu" ta ƙarasa maganar ranta a b'ace.

To uwata na kiraki ɗin ko zaki dake ni ne, sarkin rashin kunya,wlh da badan lokacin da na haife ki ina cikin hayyaci na ba,da sai nace canza min ke akayi.ni dalla can wuce ki d'akko mayafin ki kizo ki rakani gidan hansai".

Badan ran hanne yaso ba ta shiga ɗaki ta d'akko hijabinta ta saka,inna laure ta saka ta a gaba suka bar gidan.

A ɓangaren su HALIMATU kuwa bayan fitar inna laure da hanne hajiya maryam ta cewa HALIMATU ta fara shirin tafiya tun yanzu,saboda gobe take son su wuce,idan malam ummaru ya dawo yau.

Cike da zumud'i HALIMATU ta janyo tsohuwar bakkon ta,ta zazzage ta a kan tabarma ta fara ninke kayan ta, fuskarta cike da farin ciki.
Hajiya Maryam ta kai duba kan kayan da take ninkewa, kwata kwata babu kayan kirki,gaba ɗaya duk tsunmokara ne kayan, ta girgiza kanta cike da tausayin HALIMATU ta na maida ƙwallar da ke shirin zubo mata,tace "daughter ki ajiye kayan nan gaba ɗayan su, ba zamu tafi da ko ɗaya ba,yanzu ki tashi mu tafi cikin gari in duba miki wasu kayan ko kala biyu ne,idan munje gida sai muje na yi miki shopping".

HALIMATU tace"to momy, Allah ubangiji ya saka da alkhairi ,ina alfahari da ke uwa ta gari".
ta ƙarshe maganar fuskar ta ɗauke da murmushi.
Hajiya Maryam "tace karki ƙara yi min godiya,ha'k'kina ne wannan na kula da ke,ko dama can mahaifin ki ne ya hanani ɗaukar ki,amma yanzu in sha Allah komai ya zo ƙarshe ".ta ƙarshe maganar tana mi'kewa tsaye tare da ɗaukar hand bag ɗin ta da mayafinta ta yafa,tacewa HALIMATU wuce mu tafi.

HALIMATU ta ɗakko hijabin ta ta saka,suka fito daga cikin gidan,ta jawo ganbun gidan ta rufe,suka kama hanya suka tafi.

Suna tafe suna hirar uwa da 'yarta,har suka zo inda za su hau mashin ɗin da suke kai mutane cikin gari.bisa dole momy ta hau mashin ɗin ba dan ta soja,itama HALIMATU ta hau nata,aka kama hanyar fita da su cikin garin.

*************************

A ɓangaren inna laure kuwa lokacin da suka ƙarasa gidan aminiyarta hansai suna shiga ta samu hansai tana surfa hatsin kunun tsamiyar da take siyarwa,hansai tace"wa nake gani kamar laure cikin tsakiyar ranar nan haka"

Inna laure bata saurare taba ta nufi bakin randa ta d'ebo ruwa ta kafa baki tana kwankwad'a kamar wadda ta kwana biyu bata sha ruwa ba,sai da tasha ta ƙoshi sannan ta sauke ajiyar zuciya ta share gumin daya tsatstsafo mata a fuskarta sannan ta samu waje ta zauna,tana mayar da numfashin wahala tace"ai dole ce tasa kika ganni yanzu cikin ranar nan,ke kanki kinsan tunda kika ganni a irin wannan lokacin ai kinsan ba lafiya ba"ta faɗa tana ƙara share zufar fuskarta.

Hanne ta dubi hansai tace "inna ina wuni,ya gida?? Ina safara'u??"

Hansai ta ɗago da kanta ta dubi hanne tace "ikon Allah,ashe tare kuke ni wallahi ban kula ba,nayi zaton laure ita kaɗai ta shigo ashe tare kuke,jeki daki Safara'u na nan ciki,yanzun nan ta dawo daga talla".

Ta ƙare maganar tana nunawa hanne ƙofar d'akin.
bayan wucewar hanne hansai ta juyo ta sake kallon inna laure tace"wai me yake faruwa ne??kin saka ni a gaba kina kallo baki ce min komai ba ".

Inna laure ta sauke ajiyar zuciya a karo na uku tace"hmmm kedai bari hansai"ta kwashe komai da ya faru ta gaya mata .

Hansai ta ce" lallai a kwai matsala, dole ne boka ya ƙara yi mana wani aikin.
wannan karon aiki biyu za'ayi,na farko za'a ƙara aiki akan wanda akayi miki na mallake malam,na biyu kuma za'ayi aiki akan duk yadda za'ayi a hana matar nan tafiya da HALIMATU".

Ta ƙarshe maganar tana kallon inna laure ta kuma cewa "yanzu maza tashi mu tafi,ai zama bai gammu ba, ina fatan dai kinzo da shirin tafiya dajin ginzo,domin mu ziyarci boka ɗan maku,domin nima ina da niyyar zuwa wajen sa,saboda buƙatar da ta taso min.....................✍🏻

08162055134

💝💞HALIMATU 💝💞

(Love, sacrifices, destiny & betrayed)

💝💞💝💞💝💞

Story& writing

By

FATIMA BINTU ABDALLAHI (UMMU AYSHA)

Ƙarƙashin jagorancin

(MIKIYA WRITERS ASSOCIATION)

Golden pens...........................✍🏻

💝💞💝💞💝💞💝💞

2024 novel

💝💞💝💞💝💞💝💞

Pg-----------------------------5&6

A ɓangaren su HALIMATU kuwa lokacin da masu mashina suka shigo da su cikin garin Hajiya Maryam tace a sauke su a bakin kasuwar garin.
Bayan an sauke su ta kama hannun HALIMATU suka kutsa kai cikin kasuwar,babu abinda hajiya maryam take yi sai kallon yanayin kasuwar,kana gani kasan Irin local ɗin kasuwa ce ta ƙauye.

Suna tafe suna dudduba shagunan cikin kasuwar,amma bata ga abin da yayi mata ba.
Da ƙyar da tambaya suka sami wani shago wanda kusan shine babban shago a cikin kasuwar.
Anan suka shiga ta zab'arwa HALIMATU dogwayen riguna guda biyu, takalma flate guda biyu,hijabai guda biyu da kuma turare.
Farin ciki a fuskar HALIMATU yaƙi boyuwa,bayan ta biya kuɗin daga nan kuma suka fito suka shiga shagon masu sai da drinks,ta siya musu ruwa da lemo sannan suka tsaya gurin masu gashin mama,kifi da kaza ta siya musu, sannan suka kama hanyar komawa gida.

HALIMATU tana riƙe da ledojin siyayyar da suka yi.
Suka tari mashina suka hau aka juya da su cikin kauyen.koda suka isa gidan basu tadda kowa ba,yanda suka tafi suka bar gidan haka suka dawo suka taradda
shi.....

Bayan sunci sun ƙoshi suka ɗan watsa ruwa sakamakon ranar da suka kwaso suka zauna suna hira a tsakanin su, Hajiya Maryam tana ta yiwa HALIMATU tambayoyi a kan karatu,anan ne ta fahimci HALIMATU tana da ƙo'kari sosai a makaranta, wannan kenan..........

A ɓangaren su inna laure kuwa,lokacin da suka kama hanyar da zata sada su da garin ginzo domin ziyartar boka makau
Sai da suka hau mashina domin a kwai tazara a tsakanin su da garin ginzo,sai da suka ɗan yi tafiya mai nisa suka fita daga cikin garin,anan bakin wani daji masu mashina suka sauke su,daga nan suka kama hanya suna ta tafiya cikin dajin,duk inda ka duba manya manyan duwatsu ne da kuma bishiyoyi a cikin dajin,ga Kuma guguwa da take tasowa,duk ta baɗe musu idanu ko gaban su basa gani sosai!

Amma saboda bushewar zuciya haka suka cigaba da kutsa kansu cikin wannan dajin.

Suna cikin tafiya
Kwatsam suka ga wani irin gabjejen ƙaton mutum a gaban su,mummuna da shi bashi da kyan gani ko kaɗan ldanun sa ma abin tsoro ne,gasu ƙawala ƙawala dasu jajaye.
Ya kai duban sa gasu inna laure
ya doka wata sanda dake riƙe a hannun sa,nan take suka b'ace gaba ɗayan su kamar wal'kiya,sai gasu sun bayyana a cikin wani ƙaton kogon dutse zaune,shi kuma boka makau yana zaune a kan wani buzu na fatar damisa..........

Yayi duba zuwa gare su,inna laure har ta buɗe baki zatayi magana ya ɗaga mata hannu,nan take ta rufe bakin ta.
Boka ya dubi inna laure yace.......

"bana buƙatar ƙarin bayani,domin na samu labarin abin da yake tafe da ku tun kafin zuwan ku nan!!"
Chapter 3 · 0% Book details