← Book details Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 80

Sashe 68

Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lafiyayyen wanka ta yi ta tsane jikin ta tare da shafa lotion ɗin ta mai daɗin ƙamshi,wata gown ta ɗakko royal blue ta wani irin material mai ɗan karan kyau da tsada ta saka,sann ta saka hijabi ta tada sallar magriba,bata ta shi a gurin ba sai da ta yi sallar isha'i.
Bayan ta idar ta chan caɗa kwalliyar ta mai kyau tare da gyara gashin kanta ta kafa ɗaurin ɗan kwalin ta mai kyau,turare ta ɗakko ta fesa sannan ta saka plate shoe ta ɗauki wayar ta ta fito daga bedroom ɗin zuwa ƙasa,t v ta kunna tare da kamo tashar zeey world saboda tana son tashar sosai.

Zaman ta babu wuya ta ji ƙarar buɗe get ɗin, jim kaɗan ta ji an danna door bell ɗin ƙofar parlon, shigowa ya yi bakinsa ɗauke da sallama fuskarsa cike da annuri, mikewa ta yi tare da cewa,
"Sannu da zuwa"
Hannu ya buɗe mata ba tare da ya amsa mata ba,cike da kunya ta ƙarasa a hankali ta shige cikin jikin sa, rungumo ta ya yi tare da sauke ajiyar zuciya kamar wanda ya yi tseren gudu.
Cikin kunnen ta ya raɗa mata cewa,
"Haka ake yiwa miji sannu da zuwa kin ji!"
Jinjina kai tayi alamar to.
Hannun ta ya kama suka ƙaraso cikin parlon suka zauna akan sofa,ruwa mai sanyi ta ɗakko a fridge da glass cup ta zuba masa tare da tsugunawa ta miƙa masa.karɓa ya yi tare da kafawa a bakin sa ya shanye,ƙara miƙo mata kofin ya yi a karo na biyu taƙara zuba masa ruwan,sai da ya sha kofi uku sannan ya miƙa mata kofin tare da sauke ajiyar zuciya ya ce,
"Allah ya yi miki Albarka"
Amsawa ta yi da "ameen"

Hannun ta ya kama suka haye sama zuwa bedroom ɗin sa ya fara rage kayan jikinsa,ganin haka ya sa taje ta haɗa masa ruwan wanka tare da zuba turarurruka a ciki tayi sauri ta fito tare da barin ɗakin har tana tuntuɓe, Murmushi ya yi tare da girgiza kan sa ya shige bathroom.wanka ya yi a gurguje ya shirya cikin jallabiya milk colour tare da sakkowa ƙasa,a dining ya taradda ita ta yi serving ɗin su abin ci shi kawai take jira.
Kujera ta jawo masa ya zauna suka fara cin abincin su cike da nutsuwa,wani irin daɗin abincin ya yi masa sosai kamar ba ita ta yi ba,sai da ya cika cikinsa dam dam yasha fruit salad da kunun aya sannan ya yi hamdala ya godewa ubangijinsa a bisa ni'imar da ya yi masa.

Miƙewa ta yi ta kwashe kayan ta kai kitchen ta wanke su tsaf, sannan ta ƙarawa su baba maigadi abin cin da suka rage a cikin nasu ta fito da shi ta miƙawa mukhtar tare da cewa,
"Please ka miƙawa su baba maigadi"
"An gama gimbiyar mata"
Ya faɗa yana miƙewa.
Kitchen ɗin ta koma ta ɗakko magungunan da aunty AMINA tace mata ta dinga shan su,zubawa ta yi a cup tare da zuba fresh milk ta sha.

Fitowa ta yi daga kitchen ɗin ta haura sama zuwa bedroom ɗin ta, wanka ta ƙarayi tare da yin brush da alwalar kwanciya bacci sannan ta fito,lotion ta shafa sama -sama tare da mulke jikin ta da body misk da kuma humura masu daɗin ƙamshi, sannan ta ɗakko wannan turaren da aunty AMINA ta bata tace idan zata kwanta ta ɗan shafa shi kaɗan a jikin ta.

Shafa turaren ta yi a jikin ta sannan ta ɗakko wata red ɗin sleeping dress ta saka wadda ta kawo mata iya gwiwar ta, glove ɗin ɗakin ta kashe tare da hayewa gadon ta ta yi addu'a ta kwanta.

Koda mukhtar ya dawo bai tadda ita a parlon ba sai ya haye sama direct zuwa ɗakin sa,brush ya yi tare da saka pajamas milk colour masu santsi sosai,turare ya fesa tare da fitowa daga cikin ɗakin sa ya nufi cikin ɗakin halimatu, domin ya ƙudurta a ran sa daga yau tare da shi za su dinga kwana.
Buɗe bedroom ɗin nata ya yi tare da yin sallama ya shigo, ganin duhu ya sa ya kunna glove ɗin ɗakin,a hankali ta juyo suka haɗa idanu tayi sauri ta sauke nata kasa,murmushi ya yi tare da kashe glove ɗin ya rufe ƙofar tare kunna bedside lamp ya hawo kan gadon,cikin sauri ta tashi zaune tare da matsawa can ƙuryar gado tana rurrufe jikin ta.

Wani irin abu ne ya taso masa tun daga ɗan yatsan ƙafar sa zuwa cikin kwakwalwar sa, sakamakon wani irin ƙamshin turaren da yake ta shi daga jikin ta,nan take hankalin sa ya yi mutuƙar ta shi,cikin sauri ya nufo inda take tare da janyo ta jikin sa ya rungume ta yana sauke numfashi akai-akai kamar wanda asma ta taso masa,kuka ta saki tare da ƙanƙame jikin ta waje ɗaya,domin ta ji tsoron yanayin da ta ganshi.
Cikin wata iriyar shaƙaƙƙiyar murya yace mata,
"Relax my love! babu abin da zan yi miki ki saki jikin ki mu kwanta kin ji!"

Jin jina kai ta yi tare da sauke ajiyar zuciya.
A hankali ya janyo ta suka kwanta tare da gyara gyara mata kwanciyar ta akan ƙirjin sa, hannun sa ya ɗora a bayan ta yana shafawa haɗe da ɗan bubbugawa a hankali alamar rarrashi, ajiyar zuciya ta sauke tare da ƙara shigewa jikinsa ta ɗora hannun ta a kan ƙirjinsa,wani irin banƙarewa ya yi tare da ƙara shaƙar turaren jikin ta,nan take lissafin sa ya kwance gaba ɗaya,cikin rawar jiki ya zura hannuwan sa cikin sumar kan ta sannan ya haɗe bakinsu guri ɗaya....✍🏻✍🏻

Ina matuƙar godiya da addu'o'in ku a gare ni tare da fatan Alkhairi,ku ɗin na musamman ne a cikin zuciya ta, ina matuƙar alfahari da ku ƙwarai da gaske, Allah ubangiji ya saka muku da mafificin alkhairin sa,ya biya muku buƙatun ku na Alkhairi

Daga alƙalamin...✍🏻✍🏻

FATIMA BINTU ABDULLAHI(UMMU AYSHA)...✍🏻✍🏻

Share fisabilillahi.

Game buƙatar littafin HALIMATU tun daga farko zuwa in da aka tsaya ya tun tuɓe ni ta wannan numbern wayar👇🏻👇🏻

08162055134..

💝💞HALIMATU💝💞

(Love, sacrifices, destiny & betrayed)

💝💞💝💞💝💞💝💞

Story & Writing

By

FATIMA BINTU ABDULLAHI(UMMU AYSHA)...✍🏻✍🏻

Ƙarƙashin jagorancin

(MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION)

Golden pens....✍🏻✍🏻

💝💞💝💞💝💞💝💞

A 2024 novel

💝💞💝💞💝💞💝💞

Pages__________88&89

__________Wani babban al'amari ne ya kasance a tsakanin su cikin wannan dare mai matuƙar mahimmanci a rayuwar su musamman ma shi mukhtar ɗin,domin gaba ɗaya ya burkice ya rasa tunanin sa ya mance da Wadda yake tare,duk irin kukan da take yi mishi da magiya amma hakan bai sa hankalin sa ya dawo zuwa gare shi ba, domin ya kasa controling ɗin kan sa.

Bai tashi dawowa hankalin sa ba sai wajen ƙarfe uku na dare, a hankali ya murgina gefe tare da kwanciya a gefen ta yana sauke numfashi akai-akai kamar wanda ya yi gudun ceton rai,wata iriyar nutsuwa ce take saukar masa wadda bai taɓa jin makamanciyar irinta ba a cikin tarihin rayuwarsa ba.ji yake yi gaba ɗaya kamar ba shi ba sai kace wanda aka canja.
Bai taɓa zaton zai tsinci kansa a irin makamancin wannan lokacin ba,domin bai yi zaton akwai ni'ima da tarin nutsuwa irin wanda ya ji yanzu ba,duk yadda yake tunanin kasancewar abin ashe ba haka bane ba, domin gaba ɗaya ya zarta tunanin sa nesa ba kusa ba.tabbas mata suna suka tara,domin a yau ɗin nan ya tabbatarwa da kan sa hakan.

A hankali hawaye suka shiga zirarowa daga cikin idanuwan sa guda biyu suna gangarawa gefen kunne sa,shin ashe dama akwai ranar da zai yi farin ciki.?? alwai ranar da zai samu cikakkiyar nutsuwa irin wannan.?? tabbas yasan ba wayonsa ne ya bashi ba Allah ne ya bashi, sannan kuma da haƙurin da ya yi sai Allah ya yi masa babban sakamako mai kyau na Alkhairi.
Wata irin wutar mugun son ta ce ta kuma ruruwa a cikin ƙoƙon zuciyar sa,ji yake yi kamar ya haɗiye ta ya huta saboda tsananin son da yake yi mata,bai taɓa jin irin wannan tsananin son ba sai a kan HALIMATU.

A hankali ya miƙa hannu ya jawo ta zuwa cikin jikin sa,jin wani irin zafi da jikin ta ya ɗauka gashi kuma bata motsi ya sa ya zabura ya miƙe da sauri gabansa yana ya yi wani irin faɗuwa, kunna bedside lamp ɗin da take gefen bed ɗin ya yi,ganin bata motsi kwata-kwata ya sa hankalin sa ya yi wani irin masifar tashi.
Cikin sauri ya miƙe ya nufi in da ƙaramin fridge ɗin ɗakin yake ya ɗakko gorar ruwa mai sanyi, buɗe wa ya yi tare da zuwa dai-dai sai tin fuskarta ya ɗebi ruwan a hannunsa ya yayyafa mata a kan fuskarta.numfashi ta jawo da ƙyar tare da sauke ajiyar zuciya, a hankali ya jawota cikin jikin sa ya rungume ta yana shafa fuskarta tare da kiran sunan ta.

Buɗe kumburarrun idanuwanta ta yi da ƙyar ta kalleshi tare da fashewa da wani irin kuka mara sauti mai ban tausayi,kukan yana fitowa ne daga can cikin zuciyarta,kana gani kasan kukan azaba da raɗaɗi ne take yi.
A hankali ya ɗora bakinsa a dai-dai saitin kunnen ta ya ce,
"I'm so sorry my love,habibi ya yi miki laifi ko.? Please ki yi haƙuri ki yafe wa habibin ki ki bar kukan nan haka yana ci min zuciyata wallahi kin ji!!"
Ya ƙarasa maganar yana sumbatar goshinta tare da bubbuga mata bayan ta alamar rarrashi.

A hankali ta buɗe bakin ta da ƙyar cikin muryarta wadda ta dashe saboda kukan da ta sha tace,
"Ciwo nake ji ka kai ni wajen momy mutuwa zan yi!!"
Ta faɗa hawaye na gangaro mata ta gefen kunnen ta.
"Kar na sake ji kin faɗi wannan maganar kin ji my love"
Ya faɗa cikin sigar lallashi tare da ɗora harshen sa a kan kuncin ta yana lashe mata hawayen fuskarta.
Kwantar da ita ya yi a hankali sannan ya sakkowa daga saman bed ɗin ya nufi bathroom,a gurguje ya yi wanka ya tsaftace jikinsa sannan ya haɗa mata ruwa mai ɗan zafi ya cika bath tube ɗin ya ɗaura towel a ƙugun sa ya fito daga cikin toilet ɗin.
Chapter 68 · 0% Book details