Sashe 71
Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Direct gida ya wuce ya yi wanka ya yi sallah ya shirya tsaf cikin ƙananan kaya da suka yi masa kyau sosai sai zuba ƙamshi yake yi sannan ya ɗauki mukullin motar sa ya sakko ƙasa ya fito daga parlon ya nufi parking space ya buɗe mota ya shiga yaja tare da barin gidan. A ɓangaren momy kuwa lokacin da suka ƙarasa gidan suna shiga parlon ta kama hannun halimatu suka haye sama,direct ɗakin meena ta shiga da ita ta zaunar da ita akan sofa, toilet ta wuce ta haɗa mata ruwa mai zafi ta fito ta umarci halimatu da ta shiga taje ta zauna a cikin ruwan zafin! Cike da kunya ta miƙe shiga cikin toilet ɗin ta cire kayan ta tare da shiga cikin ruwan zafin, ajiyar zuciya ta sauke saboda zafin ruwan da ya ratsa ta da kuma ƙasan ta da yake yi mata ciwo. A haka dai ta daure ta chanja wani ruwan daga ƙarshe kuma ta yi wanka ta gasa jikin ta sosai sannan ta fito daga cikin toilet ɗin ɗaure da towel a ƙugun ta,bata samu momy a ɗakin ba,hakan ba ƙaramin daɗi ya yi mata ba.cikin sauri ta nufi gurin mirror ta ja kujera ta zauna ta shafa mai da body spray, sannan ta miƙe ta ɗauki doguwar rigar da momy ta ajiye mata a kan bed ɗin ta saka,dadduma ta shimfiɗa tare da saka hijabi ta tada sallah. Tana idarwa momy ta shigo cikin ɗakin riƙe da ɗan ƙaramin ture a hannun ta ta ajiye a gaban halimatu tare da cewa, "Maza maza doughter ki cinye kin ji?" Girgiza kai ta yi tare da cewa, "To momy na gode sosai Allah ya ƙara girma" Murmushi momy ta yi tare da shafa kan ta tana jin wata irin ƙaunar yarinyar tana ƙara shiga cikin jikin ta. Miƙewa tayi ta fice daga cikin ɗakin ta bar halimatu zaune da try a gaban ta.a hankali ta buɗe wani kyakkyawan bowl mai murfi da aka zuba pepper soup na naman rago da yaji kayan haɗi sosai sai ƙamshi yake yi, sai kuma wani bowl shima da aka zuba fruit salad da yaji madara sosai a cikin. Spoon ta ɗauka ta ta saka a cikin bowl ɗin pepper soup ɗin ta fara sha a hankali,lumshe idanunta ta yi Sabo da ya yi mata daɗi sosai ta cigaba da sha tana tauna naman da ya yi laushi sosai,bayan ta gama cin pepper soup ɗin ne ta sha fruit ɗin kaɗan saboda cikin ta ya cika sosai,ta shi ta yi ta saka ragowar fruit ɗin a cikin ƙaramin fridge ɗin da ta gani a cikin ɗakin sannan ta ɗauki try ɗin ta fito daga cikin ɗakin ta sakko daga benan a hankali. Bata tadda kowa a parlon ba, ta nufi in da take tsammanin nan ne kitchen ta shiga ta ajiye ta wanke kwanikan tare da gyara kitchen ɗin tsaf.ganin babu wani abinci da aka ɗora ne ya sa ta zage ta fara haɗa musu lafiyayyan abinci! Doya ta ɗakko ta feraye ta wanke ta dafa ta tazuna ta a cikin grinder ta niƙa sakwara ta kwashe a ledodi ta zuba a haɗaɗen food wamer, sannan ta haɗa haɗaɗɗiyar a gusi soup da taji naman sa da ganda, sannan ta haɗa musu haɗaɗɗen gas meat da coconut jus. Cikin kanƙanin lokaci ta gama komai,tana cikin gyara kitchen ɗin ƙamshin girkin ya sakko da momy daga sama,turus ta yi tana kallon ta ikon Allah cike da tsananin mamaki!! "Doughter ba dai girki ki kayi ba!!" Sunkuyar da kanta ƙasa ta yi tare da yin shiru. "Haba doughter! ke da zaki kwanta ki huta shine kika fito kina wahala haka!!" A hankali ta ɗago ta dubi momy ta ce, "Momy wallahi naji sauƙin jikin sosai dam Allah kar ki hana ni yin aiki! kinga ko a gida nice nake yiwa momy girki,wani lokacin kuma Mu yi nida ita da baba ladi,dan Allah kar ki hana ni! ina so na samu kaɗan faranta wa nahaifiya ta" Ta faɗa muryar ta a rauna ce. Wani irin abu momy ta ji ya zo ya tsaya mata a rai! bata taɓa zaton zata samu suruka mai ladabi da biyayya da jin ƙai irin halimatu ba,a hankali ta ƙaraso in da take tsaye ta rungume ta tare da cewa, "Allah ya yi miki Albarka doughter!" A hankali ta amsa da, "Ameen" "Fitowa daga jikin momy ta yi tare da kwashe food wamers ɗin ta kai kan dining table ta jere su tsaf gwanin sha'awa sannan ta dawo parlon ta tsuguna a gaban momy ta sunkuyar da kanta ƙasa tare da cewa, "Momy a kawo miki abincin nan!" "A'a doughter sai dadyn ku ya dawo zamu ci kin ji!" "To" ta ce tare da komawa gefe ta zauna a ƙasa. Kallon ta momy ta yi tare da cewa, "A'a ta shi daga ƙasa mana doughter ki zauna a kan kujera" Cike da ladabi tace, "Zan zauna a nan momy" Ba dan ta so ba ta ƙyaketa,hira ta yi ta jan ta dashi tana amsa mata a hankali,wani abun kuma sai dai ta yi murmushi kawai. Kiran sallar magrib ne ya tashe su daga zaunan da suke suka wuce sama zuwa ɗakunan su gabatar da sallah. Alwala halimatu ta yi tare da yin sallar,bayan ta idar ta yi addu'o'i tare da yin azkar ta zauna har aka kirawo sallar isha'i,miƙewa ta yi ta gabar tare da yin addu'a. Bayan ta idar ta shiga toilet ta ta haɗa ruwan zafi ta shiga ciki ta yi wanka ta ƙara gasa jikin ta da kyau sosai sannan ta fito ta buɗe wardrove ta samo wata riga doguwa mara nauyi cikin kayan meena ta saka ta fesa body spray. Ragowar fruit ɗin ta na ɗazu ta ɗauka ta fara sha,tana cikin sha ne mukhtar ya shigo ɗakin bakinsa ɗauke da sallama,amsawa ta yi tare da turo bakin ta ta ɓata fuska, ƙarasowa ya yi ya samu waje ya zauna a kusa da ita tare da ɗaukar ta gaba ɗayan ta ya ɗora ta a kan cinyarsa,kukan shagwaɓa ta sakar masa tare da dukan ƙirjin sa tana cewa, "Ni ka sake ni bana so karka ƙara taɓa Ni idan ba haka ba zan faɗawa momy kuma babu ruwana da kai" Hannunsa ya sa karɓi bowl ɗin fruit salad ɗin ya ajiye a gefe sannan ya kamo fuskarta da hannunsa guda ɗaya ya ɗora yatsan sa akan lips ɗin ta yana shafawa a hankali tare da cewa, "Shhhhhhh" babu wannan kalmar a tsakanin mu har abada,mutuwa e zata raba mu!" Ya ƙarasa maganar yana lasar wuyan ta. Wani irin abu taji yana yi mata yawo a cikin jikinta,nan take jikin ta ya ɗauki rawa kamar an jona mata shocking,murmushi ya yi tare da kallon ta ya ce, "Me ya faru ne my love??" Cikin wata iriyar murya ta ce, "Wani irin abu nake ji yana yi min yawo a cikin jiki na" "Nuna min in da yake in cire miki shi" Ya faɗa yana ɗora hannunsa a kan ƙirjinta yana shafawa. Wata ƴar siririyar ƙara ta saki tare da ruƙe hannunsa tace, "Dan Allah Habibi ka yi haƙuri kabari kar momy ta shigo taga abin da kake yi!". "Ai nafi so ta shigo taga abin da nake yi kinga sai ta bani matata na tafi da ita ko.?" Kukan shagwaɓa ta ƙara sakar masa tare da cewa, "Ni wallahi ba zan bika ba a wajen momy zan zauna tunda kai mugunta kake yi min" "Me na yi miki na mugunta my love??" Ya faɗa yana lasar lips ɗin ta na ƙasa. "Ashhhhh! ka bari mana!!" "Baki bani amsa ta ba" "To ai kai ne ka yi min mugunta kayi min wannan abin mai ciwo sosai" "Oh! I'm sorry my love! to amma abin da nayi miki shine gundarin auren namu fa! dan haka ki daure ki zama jaruma sosai domin mijin ki babban jarumi ne baya wasa ta wannan ɓangaren kin ji.??" Kukan gaske ta fashe masa da shi tare da cewa, "Ni wallahi bana so zafi ne dashi!!" Janyo ta yayi jikinsa tare da ɗora bakinsa a kan nata ya fara kissing ɗin lungu da saƙo na cikin bakin ta yana zuƙe yawun yana haɗiye wa,ya ɗauki kusan thirty minutes yana abu ɗaya,saboda wani irin daɗi da garɗi da yake ji a cikin bakin ta,sai da yaji jikin ta ya yi laushi sosai sannan ya cire bakinsa a cikin nata. Faɗawa kan gado ta yi ragwab shikuma ya bita ya kwanta a saman jikinta,hannunsa ya ɗora a kan cikin ta yana shafawa tare da cewa, "Kar na sake jin kin ce bakya son sunnar ma'aiki s a w,kuma Mala'iku suna tsinewa matar da take hana mijin ta haƙƙinsa tare da gudunsa,kar ki zamo ɗaya daga cikin waɗannan matan da Allah ya la'ance su,ina da yaƙini a kan ki zaki zamo min farin ciki da kwanciyar hankali a rayuwata da ta danginsa,dan Allah kar ki rushe yardar da na yi miki! ki yi haƙuri ki jure duk wata ɗawainiya da zaki yi dani,kuma zan dinga bin ki sannu-sannu a hankali in riri taki kamar ƙwai! kiyi haƙuri dani in sha Allahu zan baki dukanin farin ciki dai-dai iyawa ta baza ku taɓa yin dana sanin aure na da ki ka yi ba kin ji.??" Gin jina kai ta yi a hankali tana sauke ajiyar zuciya.tashi ya yi zaune ya kamo ta ya saka ta a tsakanin ƙafafuwan sa suna fuskantar junan su,sannan ya miƙa hannu ya ɗakko bowl fruit salad ɗin a ka an bedside drawer. Ɗiba ya yi yakai bakinsa ya tauna sannan ya ƙara matsowa daf da ita sosai har suna jin numfashin junansu ya matso da fuskarsa dai-dai bakinta tare da saka hannu ya roƙo haɓarta sosai ya haɗe bakinsu waje ɗaya tare da juye mata narkakken fruit ɗin a cikin bakinta. Sai da ya tabbatar ta haɗiye shi sannan ya ƙara ɗibar wani ya zuba a cikin bakinsa ya ƙara taunawa ya juye mata,haka yayi ta bata fruit salad ɗin har suka shanye shi gaba ɗaya tas.tun tana noƙewa har ta saki jikinta ta narke masa tana ta zuba masa shagwaɓa,shi kuwa gogan dama haka yake so shi yasa ya biye mata.suna cikin wannan yanayin ne wayarsa dake cikin aljihu