← Book details Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 80

Sashe 1

Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

💝💞HALIMATU💝💞

(Love,sacrifices, destiny betrayed)

💝💞💝💞💝💞💝

Story & Writing

By

*FATIMA BINTU ABDALLAHI (UMMU AYSHA)*

Ƙarƙashin jagorancin

*(MIKIYA WRITERS ASSOCIATION)*

Golden pens.............✍🏻

💝💞💝💞💝💞💝💞

2024 novel

💝💞💝💞💝💞💝💞

Ina godiya ga Allah subhanahu wata'ala da ya bani ikon fara rubuta wannan littafin,ina roƙon Allah ubangiji yasa na kammala shi lafiya🙏🏻🙏🏻.

Wannan labarin ƙirƙirarren labari ne, idan aka ga yayi shige da wani labarin to akasine aka samu.

Ban yarda wani ya juya min labarina ba,dai da izinina.................✍🏻

BISMILLAH RAHMANURRAHIM.

💝💞💝💞💝💞💝💞

Pg----------------------------1&2

Tsugunne take tana wanke wanke a bakin rijiya,tanayi tana share hawaye dake zuba akan fuskanta,duk da kasan cewar ruwan Saman da ake yi hakan baisa inna laure ta tausaya mata ba,duk jikinta ya jik'e ko ina d'igar ruwa yake a jikinta,hakan ya haifar mata da zazzafan zazzabi, haƙoranta sai faman karkarwa suke,amma duk hakan baisa inna ta tausaya mata ba.

Haka nan ta gama wanke wanke cikin ruwan,ta kwashe duk kwanikan da ta wanke,ta kaisu k'ofar d'akin inna laure ta ajiye.ta dakko tsintsiya ta share tsakar gidan tas,ta gama gyaran gidan tsaf,duk ka yanda inna laure ta yi amfani dasu sai da ta gyara su tsaf, sannan taje k'ofar d'akin inna laure tayi sallama tace"inna na gama"tafada tana da ga tsaye bakin k'ofar d'akin "to kuma mai kike so na yi miki jara babbiya!? Kunzo kinyi mini bake bake a k'ofar d'aki!??"

"Inna abinci zaki bani" halimatu ta fad'a.
Fitowa Inna laure tayi daga d'akin a fusace ta wurgo mata wani kwano da aka zuba k'anzo tuwo da kuma ra gowar shin kafar da aka ci aka rage ta zuba akan k'anzon."ga shinan idan kinga dama ki dauka".hawaye halimatu ta share, sannan ta sunkuya ta d'auki kwanan abincin ta tafi ta bude cikin d'akinta,wanda yake a matsayin na mahaifyarta,ta zauna a saman wata tsohuwar ta barma tayi bimillah ta fara ci,d'akin babu komai a cikinsa sai wata tsohuwar duk'un k'unanniyar tabarma da kuma wata tsohuwar bakko da 'yan kayan HALIMATU suke ciki.

Cikin sauri ta gama cin abincin dan gudun kar tayi lattin zuwa makaranta,duk da kasancewar zazzaɓin da ya sakko mata saka makon ruwan Saman da ya doke ta.
ta bude bakkon ta d'akko ya mutsatstsun uniform d'inta wanda duk sun ɗan fara ya gewa sakamakon tsufan da su kayi.
cikin sauri ta ke shiryawa saboda tayi lattin,kasan cewar suna zana jarabawar karshe a makarantar secondry.
ta fito tazo k'ofar d'akin inna laure ta tsaya"inna na shirya zan tafi makaranta"Inna laure ta d'aga labule ta lek'o daga cikin d'akinta tace"ke kika sani kina fakewa da zuwa makaranta kina yawonki kwararo kwararo ni fuce ki bani guri idan ba haka ba wallahi na fito na yi miki dukan tsiya"halimatu tayi sauri ta fice daga gidan,gudun kada inna laure ta hana mata zuwa makarantar,dan ba ƙaramin aikin ta bane.

har ta kai zaure na biyu ta jiyo muryar inna laure ta na cewa"kitabbatar kindawo gida da wuri idan ba haka ba wallahi kinsan sauran"halimatu dai ko waiwayowa ba ta yiba bare ta amsa mata tayi fice warta daga gidan.

tafe take tana ta sauri Kasan cewar tayi latti shiyasa taketa sauri gudun karta rasa paper ɗin da zasu zana,saboda itace paper ɗin k'arshe da zasu zana ta jarabawar gama secondry school.

da sauri ta k'ara so bakin get ɗin makarantar ta su ta shige.
tana shiga ta yi sauri ta shiga a jinsu ta samu waje ta zauna a kusa da mariya k'awarta,tana zama ko minti uku ba'ayiba aka fara raba nusu jarra bawa,juyowa mariya tayi ta kalle ta tace"Lallai HALIMATU sai yanzu!tun d'azu nazo inata jiranki amma baki zoba sai yanzu,hmmm Lallai Allah ya soki wallahi da baki ƙara soba da tuni yanzu kin rasa paper nan"

Kallonta HALIMATU tayi ta ce"wallahi mariya aiki ne ya tsayar da ni, kuma ga shi yau d'in mun tashi da ruwa,sannan kinsan dai inna ba zata bari na taho ba sai na gama yi mata aikin ta". numfashi mariya ta sauke tace"har yaushe ne zakiji dad'in rayuwarki HALIMATU, kullum cikin wahalar rayuwa kike,wallahi ina tausaya miki sosai,amma kiyi hak'uri wata rana sai labari "HALIMATU dai tayi shiru saboda k'wallar da ta taru acikin idonta,ta saka hannu ta share hawayenda suke gangarowa a kan fuskarta,ta d'au papern ta ta fara dubawa tana rubuta amsa.

tsawon awa ɗaya aka basu, amma cikin minti talatin HALIMATU ta kammala rubuta jarabawar ta kaifin kwa ƙwaƙwalwa tana da basira sosai,ta fito waje ta samu guri ta zauna tana jiran ƙawarta mariya.

Kusan minti talatin da zamanta a wajen sai ga mutane sun fara fitowa,can ta hango mariya ƙawarta tana ta howa inda take,tana ƙarasowa tace"haba HALIMATU tun ɗazu nake ta neman ki ban san nan kika zoba,ga ƙawayenmu can anata hotunan ban kwana,ta so muke"

ta kamo hannun HALIMATU suka fara tafiya zuwa gurin da ƙawayen su suke,nan fa aka fara hotuna ana run gume juna ana yin ban kwana,masu karɓar address suna yi,masu kuka nayi saboda ba lallai bane ka ƙara ganin wani ba,
wani kuma zaka daɗe kafin ma ka ƙara ganin sa,wani kuma rabuwar kenan har a bada.
suna cikin wannan yanayin gargad'in inna laure ya fad'o mata a rai,nan take gabanta ya fad'i hankalinta yayi masifar tashi saboda ta san wacece inna laure,nan da nan ta kamo hannun ƙawarta mariya tace"mutafi mariya wallahi inna ta gargad'eni tace kar na daɗe ,wallahi ina tsoron karta yi min duka"nan da nan suka yi sallama suka kama hanya sunata tafiya,suna tafe mariya na janta da hira amma hankalinta sam baya tareda mariya,hankalin nata yayi gida.

kana ganinta kasan fargaba da tsoro ne bayyane a tattare da ita,suna zuwa daidai kan layin su anan suka yi sallama ita da mariya suka rabu kowa yayi hanyar gidansu.

HALIMATU tana zuwa k'ofar gidan su ta tsaya, sai da tayi addu'a sannan ta shiga da bisimilla.
a tsakar gida ta iske inna laure tana k'uk'k'ulla gyad'a tace "inna na dawo barka da gida,da fatan na sameku lafiya"ai bata bari ta k'arasa maganar ba ta saka ƙafa ta shureta,ta d'auki ita ce a gefenta ta dinga jibgarta da shi.

HALIMATU tana ihu tana kuka tana bawa inna laure hak'uri amma inna laure bata tausaya mata ba haka tayi ta jibgarta san ranta,har sai da taga tana numfashi sama sama sannan ta k'yale ta .
HALIMATU banda kuka babu abinda take yi,inna laure tace "zaki ta shi ki ɗaukar min tallan gyad'ar kokuwa sai nazo na sabau taki.

saboda kin raina ni da nace ki dawo gida da wuri ai baki dawoba,sai da kika gama yawon bin kwararo sannan yanzu zaki dawomin saboda kin raina ni .
da sauri HALIMATU ta tashi ta shiga d'akinta ta cire kayan Makarantar ta, ta ajiye a kan tabarma ta buɗe bakkonta ta d'akko wasu riga da zani kod'ad'd'u tayi sauri ta saka ta ɗauko wani tsohon hijabin ta,ta saka ta fito ta ɗauki bokitin gyad'ar ta fita daga cikin gidan...............

tafe take tana share hawayen fuskarta,ga wani irin ciwo da jikinta yake yimata,ga yunwa ga kuma zazzaɓi da take ji ya taso mata.

a haka ta cigaba da tafiya har tazo bakin wata 'yar kasuwa,wadda 'yan matan garin suke zuwa talla,kowa da irin kalar abinda yake siyarwa,masu saida dafaffen rogo ne,masu saida gujjiya da gyad'a ne, masu sai da fura da nono ne, masu saida shin Kafa da wake ne, da dai sauransu.

anan ta samu waje ta zauna, bata daɗe da zama a gurin ba sai ga wata mota ta faka a bakin wajen,wani mutum ne ya fito daga cikin motar,ya tako a hankali cikin nutsuwa da kamala,yana tafiya a nutse ya nufaci inda take yazo ya tsaya a wajen.

daga ganin mutumin sai mutane suka zo suka cika gurin,domin sun saba duk lokacin da yazo wajen shine yake siye gyad'ar gaba ɗayanta a raba musu ita sadaka!

yayi sallama cikin muryarsa mai sanyi da kuma daɗin sauraro.HALIMATU ta amsa ciki ciki tana mai sun kuyarda fuskarta,ta rasa mai yasa take jin kunyar mutumin nan,kwata kwata bata iya haɗa idanu dashi,saboda ba k'aramin kwarjini yake mata ba,fuskarsa kadaran kadahan.

ya d'ago fuskarsa ya zuba mata dara daran idanuwansa,yace da ita"me ya sameki ne k'anwata naga kamar kinyi kuka ko wani abu ne ya sameki ne,ina fatan kina lafiya!!"ya ƙarasa maganar yana mai zuba mata dara daran idanuwansa.

HALIMATU ta d'ago fuskarta a hankali kamar mai tsoron haɗa idanu da shi tace"lafiya ta k'alau ciwon kaine yake damuna amma na sha magani ya dena!"girgiza kansa kawai yayi badan ya yarda da abin da ta fad'a masa ba,saboda yana da labarin komai da ya shafi rayuwar HALIMATU babu abinda bai sani ba.

yace mata"Allah ya sawwak'e! ni zan koma ki kula da kanki,ki raba musu gyad'ar sadaka!"ya saka hannu cikin aljihun sa ya fito da rafar kuɗi 'yan naira d'ari biyu ya ɗora mata a kan cin yarta yace"ga kuɗin gyad'ar inna nan ki bata, Please kice mata ta dena ɗora miki tallan nan wallahi bana so, ta fad'i ko nawa ne ta keso in bata zan bata,amma Please ta dena ɗora miki tallan nan bana so"

Ita dai HALIMATU sun kuyar da kanta ƙasa tayi tana sau raronsa har ya gama,ya juya zai tafi tace masa"Allah ya tsare Allah ya kiyaye, Allah ya ƙara bud'i "ta ƙarasa maganar tana sun kuyarda kanta a ƙasa"

har cikin ransa ya ji daɗin addu'ar da ta yi masa amma bai juyoba ya cigaba da tafiya ya buɗe motarsa ya shige ya tada ita yayi tafiyarsa.

a hankali ta sauke wata a jiyar zuciya.nan da nan ta mik'e tsaye ta fara rarraba gyad'ar har ta gama,ta ɗauki bokitin gyad'ar ta ruƙe kuɗin da ya bata a hannunta ta juya ta nufi hanyar komawa gida,tana tafe tana sauri saboda maraice yayi.

tana cikin sauri sai taga mutum ya sha gabanta,tayi sauri ta d'ago kanta suka haɗa ido,bakowa bane ba face buba,tayi sauri ta matsa gefe ta cigaba da tafiya,ya kuma zuwa ya sha gabanta yace"haba HALIMATU wai me yasa kike yimin haka ne!!?? ko saboda kinsan ina sonki shiyasa kike yi min wulak'anci , sannan kuma kinsan dai bakida miji sai ni,saboda haka ko kina so ko bakya so sai na aure ki,tunda laure ta riga ta bani ke"
Chapter 1 · 0% Book details