← Book details Domin Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 84

Sashe 82

Domin Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

rsuna isa aka Shiga da ita dakin haihuwa seda aka rirrike Ahmad dan kokarin bin bayanta yake dakyar AK ya lallabashi suka zauna amma yaki barin kofar dakin kuka yake kamar karamin yaro saboda tausayin halin da flying bird dinsa keciki ....

Ba'adau lokaciba su grany da Momy suka iso asibitin lokacin su Umma da inna suna masa mai tsarki basuda labarin halin da ake ciki ...

AK narike da hannun Ahmad yana fadin friend ka kawnatar da hankalinka dayardar allah ba abunda zaisameta lafiya zata haihu kaji....

sarah dake gefe tana sharan kwalla tace yihakuri yaya she will be fine ....

Haka sukaci gaba da kuantar masa dahankali itadai Asma'u tana daga gefe azaune ita tamakasa magana danji take gaba daya tafisu damuwa.....

suna nan zaune sukaji takwala ihu tana kiran Taaaaarzaaaaan ....

Afirgice Ahmad yamike tsaye yana kokarin Sakai cikin dakin AK yayi saurin riko hannunsa juyowa yayi yarungume AK dakarfi cikin muryan kuka yace kanaji ko friend....wahala takesha friend kataimakeni kabarni naje wurinta ...idan wani Abu yasameta bazan yafema kainaba ....

mikewa tsaye grany tayi tana fadin ahmadi kanatsu mana ....kowace macefa haka tayi nakudar nan masu ya'ya goma sha biyu fa suce mekenan ....

Janyo jikinsa yayi daga na AK yana share kwalla yace wallahi daga wannan bazata kara haihuwa ba wannan shine nafarko kuma nakarshe yakarashe maganar yana kara saka kuka su abunma dariya Yakoma basu sedai bahalin yinta saboda yanayin dasuke ciki ....

Suna nan zaune doctor yafito aguje Suka nufesa kowa najefomasa tambaya ganin yayi shiru yasa Ahmad yariko hannunsa hankali tashe yana fadin doctor what happened....please say something ....

Murmushi likitan yayi yana dafa kafadarsa yace congratulation .....matarka tasauka lafiya kunsamu karuwar beautiful princess a family dinku.....

wata wawar runguma AK yakaima ahmad seda suka fadi kasa doctor din yawuce yana fadin to sarkin kuka zaka iya zuwa kaga matarka yanzu ....duk kacikamana asibiti da ihu

gaba daya suka nufi dakin kowa narigan rigan daukan yarinyar
amma kafin su isa tuni AK yayi wata supa ya cafke jinjirar yana jujjuyata cike dafarin ciki yaware murya yana fadin oh my god....she is so... so... so beautiful ....chitti zo kiganta dake take kama....yayi maganar yana nufar Asma'u dake tsaye tana kallonsa cike datausayi aranta tana addu'ar allah yanuna musu nasu kodan taga farincikinsa

dakyar grany takwaci yarinyar ahannunsa sannan kowa yasami damar ganinta ahannunta ....
Cike dafarin ciki Asma'u tadaka tsalle tafada jikin khadeeja suka rungume juna cikin tsananin farin ciki

Sam Ahmad yaki matsawa daga kusan khadeeja seda grany tamasa Jan ido sannan yafita daga dakin badan yasoba ...

Shikam AK duk Wanda yazo barka idan bawanda yasani ba se adauka shine uban yar

ganin rawar kan Ahmad tayi yawa Momy tadauke khadeeja tamaidata gidanta dan tasamu kulawar data dace....

Saboda kaunar da AK kema jinjirar ranar suna kyakkyawar jinjirar taci sunan mahaifiyarsa wato Hafsat sunakiranta Hanan

bayan wani lokaci ....

AK abun tausayi jiyake da Hanan tamkar yarda ya Haifa dacikinsa har tafi shakuwa dashi fiye da Ahmad dan matukar yana gida to tana hannunsa duk dabaitaba Asma'u maganar haihuwa ba amma tasan yana matukar son yara arayuwarsa saboda daki namusamman yaware agidansa yacikasa makil dakayan wasan yara kullun yafita seyadawo da kayan jarirai idan tayi magana yace tanadai yakema babynsa maizuwa

tun tana namishi magana har tagaji tazuba mai ido sedai kullum bakinta baya rabuwa da addu'a tana rokon ubangiji ya arzutatta da haihuwa mai albarka....kuma duk addu'arta seta Santa aysha aciki saboda itama tana fuskantar rashin kuanciyar ahankali agidan mijinta dalilin rashin haihuwarta ....

Allah maji rokon bawa ya arzutta aysha da karuwar ya'mace inda kowa yatayata farinciki daganan bakin Hafsat yamutu suka samu kwanciyar hankali....

Ranar suna yarinya taci sunan grany suna kiranta ameera ....

Kullun AK yasaba idan yadawo gida daga bakin kofa Asma'u kezuwa aguje ta tarbesa amma ranan yashigo har cikin Palo bai ganta ba

Wurgi yayi da jakar hannunsa yanufi kan stairs din yana fadin chitti kina ina ne....gani nadawo fa...

Duk inda yake tunanin ganinta yaduba bai sameta awurin ba har hawana karshe yaduba amma bata ba alamunta

daga karshe ya yanke shawarar lekawa bangaren Ahmad yasan bata wuce wurin khadeeja

yazo daidai dakin babynsa yaji sautin wakar yara natashi ahankali daga ciki

Cak ya tsaya yana kallon dakin nadan lokaci kafin yatura kofar ahankali yashiga ....

Ko ina na dakin agyare tsap gaba daya kayan wasan ansaka kowanne amahallinsa

Wani lallausan murmushi yasaki yana bin ko ina dakallo yakarasa ahankali yake takawa cikin dakin har ya isa bakin dan karamin gadon lilun jariran dake tsakiyar dakin ....

Guywowinsa yakai kasa yana tura gadon ahankali yafara lilu wani dan karamin kwalin gift yagani ijiye akan gadon ....

damamki yake kallon box din danshidai yasan baya cikin siyayyar dayayi ahankali yadauki box din yana waige waige adakin amma ba alamar akwai mutum aciki ....

kamar ya ijiye se kuma yabude box din yana kalllon farar takardar dake ninke aciki

Cike da mamaki yafara warware takardar yana karantawa ....

Result din asma'u ne na asibiti Wanda yanuna tana dauke da............ *juna biyu har natsawon sati takwas*!!!

mamaki.... al'ajabi.... farincike ne suka bayyana lokaci guda afuskar AK hannunsa har rawa yake yana maimata sunan asm'au dayafito baro baro ajikin takardar ....

Jin adafa kafadarsa yadago dasauri yana kallon Asma'u still takardar tana hannunsa baigama yarda cewa ba mafarki yakeba

kallonta yake kamar ya hadiyeta farincikin dayamai yawa yama rasa ta ina zaifara nuna mata farin cikinsa ....wash yan siraran farin cikine suka gangaro akan kuncinsa

murmushi tayi tana kamo hannunsa tadora kan cikinta ahankali tafurta can't you say hello to ur baby......

Rungumota yayi daga durkushe dayake kansa adaidai cikinta yana manna mata kiss yama rasa inda zaisaka ransa

ahankali takai hannu tana shafa sumar kansa idonta alumshe itama hawayen farin cikin take dan ba abunda zasuyi dayawuce godema allah da ya amshi addu'arsu....

Fadar irin farincikin da sukayi aranan bata lokacine dan washe garin ranan gaba daya family din agidan suka wuni duk Wanda yaji labari seyazo dan kawai suga irin farin cikin da AK keciki....

Sosai take samun kulawa daga bangarori da dama grany kullun cikin aikomata da magungunan gargajiya take duk abunda tasan mai juna biyu zata bukata to kafin tanema har an aikomata dashi ....

Inna kam duk bayan kuana biyu setazo gidan dan duba lafiyar jikarta ....

Su khadeeja likita itace ma ke kula dakomai nata kullun se tadubata ko bata zoba AK zaije yataso keyarta gaba tazo tabincikata ....

kowa a family din na tsananin kaunar cikin Asma'u kowa nakokarin jiyamata dadi har so suke tace tana son Abu ....
Su khadeeja aysha da Sarah har fada suke idan tabukaci wani abu kowa setace ita zatayi sedai kafin suzo tuni AK yabiyamata bukatarta .....

kwance tashi ba wuya wajan allah haka sukaci gaba da renon cikin har allah yakaita lokacin haihuwa inda nan akaga rudewa awajan AK saboda duk rigimar da Ahmad yayi to AK yatakashi ya wuce awajan ....

Kasancewar haihuwar tazomata dawahala harseda aka yanke tammahar zata haihu dakanta ana shirin yimata operation kenan allah yasauketa lafiya tasambalo kyakkyawan yaronta mai kama da AK sak kamar antsaga kara

Koda tahaihu AK na masallacin dake cikin asibitin yana zabga addu'a dan tunda akace za'amata operation yabar wajan yanufi masallaci ....

aguje khadeeja tazo tamai albishir baimike tsaye ba seda yayi sajada tagodiya ga ubangiji sannan yafito masallacin aguje yanufi cikin asibitin

gaba daya dakin seda yacika makil da yan uwa da abokan arziki kowa na mamakin kama irinta AK da dansa dan abun sewanda yagani ....

Ranar suna akasha walimar da tatara manyan baki daga wurare daban daban anyi taro sosai inda yaron yaci suna Mus'ab

Haka rayuwa taci gaba da tafiya cike dafarin ciki inda Mus'ab yataso yaro mai farin jini wurin mutane yana wayo kyansa nakara fitowa kamarsa da mahaifinsa kuma nakara bayyana hakan ma yasa suke kiransa da junior bashir ne yasamasa sunan har yabishi kowa yafara kiransa dashi
Hanan tana tsananin son yaron tun yana jinjiri take rigimar agoyamata shi ko makaranta taje seta baiyomasa da tsaraba shima yashaku da ita sosai

*Bayan shekara biyar* .....

Asma'u ce tsaye agefen gado taci adon tsap tana kallon AK dake kuance yana bacci kamar wani karamin yaro ....

Murmushi tayi tafara kokarin tashinshi amma Sam yaki tashi sema janyota yayi tafado kansa yana kokarin rufesu dabargo takwace kanta tana mikewa tsaye takaimasa duka da pilo tana fadin karma katashi wallahi tafiya zanyi dan bazan jirakaba ....

Dakallo yabita yana murmushi har tafita daga dakin sannan yagyara kwanciyarsa yana Jan bargo yaci gaba dabaccinsa .....

tana fita dakinta tanufa tanata masifa ita kadai....

tana tura kofar dakin ta tsaya daga bakin kofar kamar zatayi kuka tana kallon kyakkyawan yaron dake kwance kan gado yana sharan bacci
[19/08, 06:18] Hassan Atk: wata dalleliyar motace tayi parking aharabar gidan

atare aka bude kofofin baya namotar AK yafito se ahmad ma tadayan bangaren sannan driver yaja motar zuwa inda aka tanada dan ijiye motoci....

Bashir kam yajima danufar amaryarsa sedai muce allah yabasu zaman lafiya.....

atare suka jero har sukazo tsakiyar gidan sannan suka juyo suna facing juna da murmushi afuskansu Ahmad yabashi hannu yana fadin fatan alkhairi friend....

murmushi AK yayi yana shafa kai yace kaima haka allah yasa tashin farko kabugu yan biyu kaga aka hada danawa hudu kenan ...

"Ohhh AK kaidai bakada wata matsala datawuce ta yara idan allah yabani nawa ma hada maka zanyi duka karike .....

dariya yayi yana juyawa yanufi bangarensa ahankali Ahmad yakira sunansa

Yanajuyowa yaji yarungemasa dakarfi yana hawaye ....

Rungumesa yayi damamaki yana fadin friend lafiya... meyafaru ....

Janyo jikinsa yayi yana share kwalla yace nothing.... kawai duk lokacinda nakalleka ne se inji inaso narigaka mutuwa dan kona second daya banajin zan iya rayuwa batare dakai ba....

murmushi AK yayi yana rungumosa jikinsa yace ya isa haka Superman....yau ranar farin ciki ce awurinmu baikamata kabata mana ita da wannan tunaninba ......yakarashe maganar yana share kwallar data zubomasa hade dajanye jikinsa daga na Ahmad yanufi bangarensa batare dayasake wata magana ba ....
Chapter 82 · 0% Book details