← Book details Domin Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 84

Sashe 68

Domin Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shiru yayi yana kallonta nadan lokaci sannan yasauke wata nannauyar ajiyar zuciya yace to yanzu intanbayeki ....duk wannan abubuwan sakika aikata for god sake miye ribar dakika ci aciki banda wahala da zubar da mutunci da kima a idon mutane dama shikanshi Wanda kikayi domin shi ...daga karshe gashi kinga inda kikadawo ki godema allah da sakamakonki yafito tun aduniya da seda kika mutune yazakiyi ....nanfa sell ne bake kadaibace akwai mutane dayawa azagaye dake akwai masu tsaronku iska yanashigomiki kina shaka kinsan cewa kobadade kobajima zaki fita daga cikinsa amma kinajin tsoro kinkasa hakuri kinkasa jurewa inaga ace cikin kabari kika tsinci kanki a inda kintabbata bazaki taba dawowa ba har abada kekadai zaki zauna har tashin alkiyama wannan zuwan danamiki yanzu aikinki ne zaizo miki dan tayaki fira ....sarah wane aiki kika aikata mai kyew dakike tunanin zaki iya zaunawa dashi ....sarah meyasa son ahmad yarufe maki ido har kika manta da allah da manzonsa Wanda su yafi dacewa kiso fiye dakanki kinmanta cewa abunda allah yakaddara bawanda ya isa yacanzashi kinmanta cewa sodayawa kakanso abunda bashine alkhairi agareka ba abunda kake ki kuma yakasance shine mafi alkhairi agareka sarah ubangiji ya making ni'imomi dadama amma maimakon kigodemasa se kike anfani dawannan ni'imar kina saba masa har kika fifita Wanda kikeso akan dokokin allah kuma ahaka kike tunanin zaki samu abunda kike so ?

Tunda yafara magana tasadda kanta akasa banda sheshshekar kuka ba abunda take bai karasaba tasa kai aguywa tana fashewa da kuka mai ban tausayi lokaci guda taji ta tsani kanta nan take tafara nadamar abunda ta aikata kuka take sosai yana rarrashinta dakyar tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya akai akai

wata leda yaciro daga cikin aljihunsa yaciro take awaye da spoon guda biyu ya ijiye atsakiyarsu ai kamar jira take tafara ci ido kawai yazubamata yana kallon yanda takecin abincin kamar bata taba cin irinsa ba dagowa tayi tana kallonsa tace kaci mana

Girgiza kai yayi yana murmushi yace Ni nakoshi kici Kawai

To nima bazan ciba nakoshi nakoshi.....tafada tana ijiye spoon dinta

daukan spoon din yayi yagwada kamar yanaci sannan itama tafara ci har saida takoshi sannan ta ijiye tasha ruwa tana gyatsa tace Kaan me ....

" sekinfada ...

gyara zama tayi tana murmushi tace bantaba cin abinci maidadin wannan ba kodan naji yunwa sosai ne

seda yakai lomar abinci bakinsa sannan yadago yana kallonta yace nima haka kuma kinsan a ina nasaya....abakin titi
Dariya tayi tace wannan shi ake kira ga arha ga dadi

haka sukaci gaba dafiransu yanata sata dariya dama ganshi gwanin barkuanci hartayi bacci sannan ya lallaba yafita bayan yadamka ma yansandan kudi masu dan yawa har ya isa gida yana tunanin abunda sarah tafadamai shi abunda yabashi haushi yanda aysha take kara ingiza sarah tana aikata abubuwa marasa kyew

Haka bashir yaci gaba da kula da sarah kowace rana zaizo dasafe yazo daddare shakuwa mai karfi tashiga tsakaninsu kullun yana kara yimata nasihohi masu rasa zuciya cikin kankanin lokaci tasauya kamar ba itaba tundaga maganganunta da yanayinta da ibadarta komai yana birgeshi afannin aiki kuwa yana bakin kokarinsa aiki yake bawasa yana Tara kudin batare dakowa yasani ba se asma'u kawai yakeba labarin komai

abangaren AK kuwa ba karamar damuwa yashiga ba akan halin da sarah take ciki amma yazama dole ya jure kodan hakan zaisa tagane kuskurenta kowani lokaci asma'u taganshi adamuwa setayi kokarin kawarmasa da ita kodai tatsokaneshi ko kuma ta jashi dole sufita aiki

ita dasu ahmad suna iya kokarinsu wajan gano waye uban cikin aysha amma abun yacutura saboda aysha tagano shirinsu kuma tana taka tsantsan sosai Sam bata yarda suhadu da salim sedai awaya shima secikin dare ta tabbata bawanda zaijita

ranan sukaci karo da bashir zafita wata uwar harara ya watsamata zai wuce tayi saurin shan gabanshi tana fadin wai bashir menamaka ne kwana biyu ko ga maciji bamayi akan wane dalili idan wani Abu namaka kasanardani mana ba wai kadauki gaba daniba

Juyowa yayi yana kallonta cike datakaici yace ke bakikai matsayin dazan dauki gaba dakeba kawai dai idan kasan halin mutum ne sekasan yanda zaka zauna dashi

Sake shiga gabanshi tayi tana banbamin masifa nunata yayi dayatsa yana fadin matsamun inwuce kar intakaki awajan

Kinmatsawa tayi shikuma azuciye yasa hannu yatureta daga gabansa yawuce yana Jan tsaki

turetan dayayi ashe tafadi baisaniba daidai nan asma'u tasuko daga sama tana ganinta akasa tarugo aguje tana kiran sunanta ganin bata motsi yasa bada bata lokaciba takira grany ta taimakata suka nufi asibiti da ita

[26/07, 00:20] Hassan Atk: 📚📚📚📚📚📚
👨‍👧 _DOMUN kANWATA_ 👩‍👧

1⃣9⃣5⃣

Suna isa asibiti aka hau dubata se safa dawamarwa asma'u keyi cike da damuwa grany kam ko agefen gyalenta dan cewa tayi kinibibin aysha ne ba abunda yasameta suna nan tsaye khadeeja ta iso damamaki asma'u ta tareta tana fadin khady lafiya ....mekika zoyi asibiti

Seda suka gaisa da grany sannan tace wurinku nazo yanzu naje gida securities sukace kunzo asibiti waye ba lafiya....

Zaunawa asma'u tayi tana Ciro wayarta tace... aysha

tabe baki tay tana kauda kai kamar jira grany take tamike tana gyara gyalenta tace....to tunda ga khadeeja tazo bari ni inje gida in kintsa kinga daganan se asanar da iyayenta

Dakallo sukabita har tafita sannan khadeeja tajuyo tana fadin wai meyake damunta ne....
bata kulata ba takira Ak awaya tasanar dashi nan take segashi yashigo asibitin afujajan hankali tashe yakaraso wurinsu yana tambayar abunda yafaru

Mikewa asma'u tayi tana riko hannunsa tace kar kadamu ba wani abu bane anakan dubata yanzu .....nima bansan meyafaru ba I just found her on the floor....
juyawa yayi yana dafe kai cike da damuwa sannan yajuyo zaiyi magana kenan yahango khadeeja azaune cike da mamaki yace ke....kuma mekike anan dama tare kuke ne

Saurin mikewa tayi takoma gefensa tana fadin a'a ...ni baruwana da ita.. Kawai nazo karban magani ne naga grany anan ita tagayamun abunda kefaruwa shiyasa natsaya ....

atare suka wurgama asma'u harara sannan AK yakarasa kusan dakin yatsaya khadeeja nabiye dashi abaya tana kashema asma'u ido hade damurmushi

Suna nan zaune doctor yafito azabure suka nufeshi suna hada baki wajan tambayar lafiyarta

Murmushi doctor yayi yana gayamusu bawata matsala sudai kiyaye gaba idan irin haka tana faruwa za'a ita rasa abunda kecikinta

Murmushi AK yayi yanaba doctor hannu yace oh allah nagodema ....zamu iya shiga muganta

"eh ....amma yanzu zanturo nurse tamata allurar bacci dan tadan huta

atare suka fada dakin AK nagaba suna binsa abaya cike da damuwa yakarasa bakin gadon yana riko hannunta yace sannu aysha ....how can u be so careless...kullun inagayamaki kirinka kula dakanki ko kinmanta halin dakike ciki ne

Shiru tayi tana kallon su asma'u fuska adaure koda suka mata sannu ciki ciki ta amsa shi kwa AK se kallonta yake cike datausayi yana jin haushin kansa dayajefata cikin wannan halin kara damko hannunta yayi yana fadin baby tell me how did this happen ....garin Yaya kika fadi

Shagwabe fuska tayi tana kallon asma'u tace nidai AK gaskiya tsoro nakeji kafitar dani daga gidannan idan ba haka ba zata kasheni ko takashe abunda kecikina

Kallonta suke damamaki dan bawanda yafahimci Inda maganarta tadosa fashewa tayi dakuka tana kamo hannayen AK tace AK please ...do something our baby's life is in danger ....
Cike damamaki yace kamar ya bangane mekike nufi ba what is happening
kara kankamesa tayi tana nuna asma'u dayatsa tace gatanan itace ta turani nafadi kuma ranan ma haka tamun ....dama nagayamaka tace seta zubar dacikina amma bakayardaba tonidai gaskiya idan bakadau mataki ba zantafiyata zanyi nesa daku kodan naceci rayuwar dana tunda nalura kai bakasonsa dan batahanyar halal akasameshiba .....takarashe maganar tana fashewa dakuka

Juyowa yayi yana kallon asma'u da jajayen idanuwansa fuska adaure yamike daga zaunan dayake yafara nufota yana fadin you.....kinmanta abunda nagayamiki ranan ko ....ko kindauka wasa nakemiki kawai dan kinga ina kyaleki akan duk abubuwan da kike mun

Jadabaya tafarayi idonta pal kwalla cikin rawar murya tace wait....did u....just believed what she said ...AK karya takemun wallahi why will I do that....
Riko kafadunta yayi dakarfi cikin kakkausar murya yace shut..... up ...kinyi abubuwa dadama abaya nayi shiru nasamiki ido saboda bansan dalilinki nayin hakan ba amma ayanzu kina kokarin taba abunda nafiso fiye dakomai arayuwata ne idan ma kishi yakesaki kike aikata hakan u better stop it coz u have no place in my life .....yana kainan ya turata dakarfi yafita ahasale yana banko kofar

dagowa asma'u tayi tana kallon aysha nadan lokaci sannan tajuya afusace tafita daga dakin tana share kwallar datazubo mata
kauda kai aysha tayi tana Jan tsaki cike datakaici dan ita bahaka taso abun yakasance ba afusace khadeeja tanufeta tana fadin shegiya mai suffar agwagi bari naci ubanku daga ke har cikinki kinga sekiyi sharrin da hujja

Atsorace aysha ta tashi zaune tafara jadabaya tana kwalama AK kira kafin takai gareta nurse tashigo aguje tariko khadeeja tana bata hakuri suna cikin haka AK yashigo aguje yana tambayar meyafaru

aysha zatayi magana kenan suka hada ido da khadeeja tawatsa mata wata uwar harara bashiri tahadiye maganarta tana kalalo murmushin dole juyowa yayi yana kallon khadeeja kafin yayi magana tace Yaya kaje kawai bakomai bane ...adan tsorace takene shiyasa kasan masu ciki da rigima....
Murmushi yayi ya taimaka mata ta kuanta sannan yafita khadeeja tabi bayansa tana kallon nurse din tace sister dama kidankara mata ita awuya tayi mai gabadaya kowa yahuta
Dariya nurse din tayi tana shirya allurar tace a'a ba'ayi hakaba ai zaman tare sehakuri
suna fitowa AK yafita waje ita kuma khadeeja takarasa wurin asma'u tazauna tanata faman masifa itadai asma'u tayi shiru tana tunani ga wayan aysha ahannunta tana jujjuyawa

Dagowa khadeeja tayi tana kallonta cike datakaici tace wai mema yasa kikawota asibiti dakinbarta kawai tamutu awurin sedai aji labarin mutuwarta a social media kinga daganan ma se mugane shashashan daya duramata cikinnan

Saurin dago kai asma'u tayi tana kallonta cike dafarin ciki takamo kumatunta tana fadin kai khady u are too good tundazu ina tunanin abinyi gashi yanzu acikin shirmenki kinbamu shawara kuma ina tunanin zatamana aiki

"Kamar ya bangane ba....
Chapter 68 · 0% Book details