← Book details Domin Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 84

Sashe 4

Domin Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Asma'u ce tadawo daga kai nikan dataje tundazu tana tafe tana mitar dadewarta ita kadai shi yasa bataji horn da ake mata ba seda motan tazo kusa da ita Drivan yadaka mata tsawo afirgice tayi baya zata fadi Taji ta bige da wani har robar nikan ta karkace kadan ya zuba juyawan dazatai taga ashe mota ce ajiyan zuciya tayi tace kai amma Allah mai motanan albarka dayanzu nikan alalan khdy ya zube robar ta Dora akan motan tana gyara wanda yabata bakin robar tsawar da taji andaka mata ne yasata tajuya afirgice ABID tsaye abakin get Ya murtuke fuska kamar bai taba dariya ba ganin yana nufota gadan gadan yasa ta hadiye yawu tare da kura mashi ido tsabar tsoro yasa tama kasa motsa kafarta bare tayi yunkurin guduwa yana zuwa dap da ita bai yi watawata ba ya fisgota tare da zabgamata lafiyayyan mari a firgice ta dafe kuncanta 😨 Cikin Muryan kuka tace malam lafiya me namaka zaka mareni?? ABID da yagama hasala wato bata ma san abunda tayi bakenan cikin kakkausar murya yanuna motarshi da yatsa yana fadin
Dan ubanki nan yamaki kama da bola ko kwata dazaki zubamun wannan kazantar akai??
aranta tace ga mai mortar nan juyawa tayi takalli motar ita se a lokacin ma ta lura da Wanda ya zube akai maganar ABID ne yasa tamaido da dubanta garesa aranta take fadin hmm yanzu haka ma ita ce motar da yafara mallaka arayuwarsa shi yasa yaketa rawar kafa akanta ABID ne ya katseta da cewa ina magana kin wani kure in da ido sunkuy da kanta tayi kasa tace yi hakuri
What!!! apology dinki zai sa motata ta gyaru ne itama hade rai tayi dan abunshi yafara isarta kallonshi tayi tace inazuwa da Sauri ya sagabanta yana fadin ba inda zaki se kin... Bai karasa ba takatse shi dacewa dallah malam matsamun to in ban nemo abun gogewa ba da harshe na ka keso in llashe shi ko me ?? Tana gama fadan haka ta shiga gidan da ke kallon nasu Ahmad
ABID dai da kallo ya bita yana mamakin wai yau shine yake fada ana fada yayi danasanin rashin zuwa da guards dinshi da tuni sun tattaka wannan baby doll din ba Ba adau lokaci ba segata tafito daruwa aroba da wani dan karamun towel tazo tafara goge motar har tagama yana tsaye yana kallonta ko Inda yane bata kalla ba tadauki robar ta maida tadawo tadauki robar nikanta se alokacin ta kalleshi yana kokarin shiga mota tace Hey!!!
tsayawa yayi cike da mamaki yana kallonta matsowa tayi kusa dashi cikin sansanyar murya tace kasamu wani waje koda dan kadan ne acikin zuciyarka dazaka rika yafema Wanda yamaka laifi to gashi nagoge maka motar ka nikuma idan nace banyafe marin da kamun ba ya kenan tana kai tajuya tafara tafiya can kuma takara juyowa tace ohhh yes ina farin cikin sanar da kai
Kaine mutum na farko da yafara marina A tarihin rayuwata juyawa tayi tayi tafiyanta
Wani dogon tsaki ABID yaja se a lokacin ma yaji haushin kanshi da yatsaya sauraronta motan ya shiga ya zauna ba adau lokaci ba se ga Ahmad yafito yana daura agogo ahanunsa motar yabude ya shiga ya kalli ABID yace 😎AK nayi Sauri ko??
tsaki yaja baice komai ba ya tada motar suka wuce

Ahmad kenan yakasance aboki kuma amini awurin AK wato ABID tun suna yara suka taso tare koda wane lokaci suna tare Akwai shakuwa maikarfi atsakanisu Ahmad yakasance fari dogo mai dan matsakaicin jiki yanada surutu da barkuanci sabanin AK dabaicika yawan magana ba

Asma'u tana isa gida sukacikaro da khadeeja cikin muryar tausayi tace khdy yunwa ko ??
Khadeeja tace amma meya sami fuskar ki??
Asma'u ta kakalo murmushi tace ba komai muje in maki alalan rana tayi ko Umma ta aike ki ne
Khdy tace a'a wurinki naso inje naga kinjima Baki dawo ba batace komai ba taja hannun khdy suka karasa ciki..........
[18/07, 15:03] Hubbey Frd Ameena Kn: 📚📚📚📚📚📚
👨‍👧DOMUN KANWTA👩‍👧

🖊Na marubuciya Husnah kabir zarewa ( the mammah girl)

🖊dasunan Allah mai rahama mai jinkai ...

👨‍👧DOMUN KANWATA👩‍👧

1⃣0⃣⏭1⃣5⃣

Bayan sati daya da faruwar hakan misalin 11 na rana Asma'u ce da khadeeja a kitchen suna girka abincin rana khadeeja tasa wakar harsashe awayanta suna aiki suna bin wakar idan anzo baitin da namiji keyi se khadeeja tabi na mace kuma se Asma'u tayi sundage se yi suke kai kace su suka rera wakar
Khadeeja har da kwaykwayon muryar maza ta nuna Asma'u da yasa tace " tadaban ce ke ta kadaban aciki ke nawware!!! Araba mu anyi....." har dai zuwa karshe tadake kuwa kamar da gaske
Asma'u ta kwashe da dariya ita ma ta karkace tana kikkifta ido tana kallon khadeeja irin na moyannan tace " niii taka tun asali ba mai kuacema!!!
Khadeeja ta kwashe da dariya tace ammah dazakiyi acting zaki samu kudi
Umma ce ta leko kitchen din tace kuna nan kuna shirman da kuka saba ko to nidai kuyi sauri ku gama Asma'u zan aikeki kasuwa daga nan kibiya wurin inna tana nemanki tana kai nan tafita
Asma'u ta juyo ta kalli khadeeja tace khdy zaki rakani ??
Khadeeja ta zaro ido ta dafe kirji tace wa?? Niii dama bazaki biyo wajan inna bane dana rakaki amma kinfi kowa sanin bama shiga inuwa daya da ita Asma'u tayi murmushi suka ci gaba da aikinsu....

sarah ce da aysha zaune suna shirya yanda tafiyan su zai kasance can aysha ta dago ta kalli sarah tace wai nikan sarah ina dan gidanki ne kwana biyu banga yazo gidan nan ba sarah tayi murmushi tace yana nan dazuma muka gama chart dashi he is just busy that's why aysha tace ahh ahh kice kun fara soyewa kenan ?? Sarah tayi fuskar tausayi tace wace soyewa kuma aysha bayan nikadai nake azabtuwa da sonsa shi bai ma San inayi ba aysha ta gyara zama tace to shin wai ke meyasa bazaki fadamasa halin da kike ciki bane nasan dai ko giyar wake ya sha baza yayi rejecting din ki ba Sarah ta saki baki tana kallonta se can ta yi dariya tace wa?? ni?? Da matsayina da Class dina kanwar the richest man in town inje insamu namiji ince ina sonsa never!!!
Aysha tadaga kafada tace nidai shawara nabaki kina nan sake da baki wata zata kwacemaki shi sarah tayi wani malalacin murmushi tace ai ba'a haifi macan da zata kuace AHMAD a hannuna ba wallahi ke ni maganar nan ma da mukayi kinsa naji ina son ganinshi bari inje company nasan zan same shi aysha ma tamike tace muje narakaki toh daga nan nima naga AK
suna fitowa suka hadu da grany itama tafito cikin shirin ta nafita cikin rada sarah tace ita kuma wannan tsohuwar ko ina zata ohoo aysha ta matsa kusan grany tace ahh ahh grany ina zuwa haka? Grany ta tsuke fuska tace inda kika aikeni aysha ma tahade fuska tace shi mutum ba'a iya mashi idan kashareshi yace ka raina shi in kuma kamai magana ya gaya ma nakar magana cikin fushi grany tace zan bige maki baki wato futsarar da kika ga waccan mai kama da kazar yan burin tanamun shi ne kema zaki soma ko to kufita a idona aysha ta wuce tana gunaguni grany tabita da harara tace mace kamar pal waya kome ma ABIDI yagane anan da har tabirge shi ohoo koda tafito su sarah sun tafi guards suna ganinta suka mike Driver yaje ya fito da dai daga cikin motocin gidan grany ta juyo ta kalli guards din da ke biye da ita ta kankance ido tana kallon su cikin masifa tace kai wai lafiya kuke biye dani kamar kaza da yan tsaki?? Sunkuy da kai sukayi basu ce komai ba tace toh Ku koma bazani da Ku ba daya daga cikin su ne yace sorry ma but umarnin yallabai ne kar mubar kowa na gidan ya rinka fita shi kadai Grany ta wuce tana fadin ai kuma se kuyi naga Wanda zai biyoni acikin Ku mota ta wuce tana waiwayo su tare da nuna su da yatsa har ta shiga driver yaja suka fita se da suka hau titi driver ya juyo yace grany ina muka nufa fuska ta daure tace baka iya gaisuwa bane ?? kai ya Sosa yace ina wuni tace lafiya kasuwa zaka kaini ...

asma'u ce a kasuwa tazo wucewa taga grany a tsaye se waige waige take ga tulun kaya agabanta har ta wuce se kuma ta dawo wurin grany tace ina wuni grany ta washe baki tace lafiya kalau yarnan sannu Asma'u tace kina son keke napep ne grany tace a'a da driver mukazo anan ya saukeni kuma kinga nafito ban ganshi ba Asma'u ta waiga ko ina bata ga mota ba ta kalli grany tace bari muje can bakin hanya muga ko yana nan grany ta washe baki tace to Asma'u tadauki kayan da kyar take tafiya har suka iso bakin hanya grany tace kinga kwa gashi can zo muje suna isa wurinsa grany ta haushi da fada baice komai ba se hakurin da yake bata ya karbi kayan ahannun Asma'u yasa a boot grany ta kalli Asma'u tace sannu yar albarka baki gayamun sunanki ba Asma'u tayi murmushi tace ASMA'U suna mai dadi ni kuma sunana... Asma'u tace grany ko?? Grany ta washe baki tace ina kikasan sunana Asma'u tayi murmushi tanuna driver tace damuka zo nan naji ya kiraki da sunan grany tayi murmushi tace eh hakane jika nane yake kirana da sunan shine ya Bini hannu tasa ajaka ta dunkulo kudi masu yawa tamikama Asma'u amma Sam taki karba se ma juyawa datayi ta tafiyanta grany tayi tsaye tana kallonta cike da sha'awa aranta kuma tana fadin inama ABIDI na yasamu irinki amtsayin mata da yamore har saida Asma'u tabace mata sannan ta shiga mota suka fice...
Chapter 4 · 0% Book details