← Book details Domin Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 84

Sashe 52

Domin Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

juyowa AK yayi ahasale yanufosa asma'u ta taresa tana dariya tama kasa magana

mota gali yashiga yana fadin hajiya allah kirabu dawannan yaron Sam Baku dace ba lashe money kawai

aguje AK yanufesa yayi saurin fadawa mota yatada yana daga ma asma'u hannu yayi gaba

Juyawa AK yayi yana watsamata harara yace to ai da kinbishi kuntafi tare kawai

Dariya take harda hawaye tanufi mota tashiga shima yashiga driver yaja suka tafi

suna shiga gari AK yafara washe baki yana kallon garin kamar dan kauye asma'u dai banda dariya ba abunda take yayi banza da ita kamar baisan tanayiba

kuantar dakansa yayi jikin kujera yana lumshe ido yace kai ba Inda yafi gida dadi

suna isowa gidan suka isko gaba daya mutanan gidan afilin gida ana jiransu kafin driver yagama parking suka fito aguje suka rungume juna se kukan farin ciki

Da kyar aka banbare khadeeja ajikin asma'u haka Umma da inna su grany ai ba amagana

Sunkusan awa daya ahaka kafin da kyar aka barsu suka karasa cikin gidan inda yasha gyara ba kadan ba se kanshin turaren wuta ke tashi ga kanshin girke girke kala kala

anan palon kasa suka zauna kan doguwar kujera sukasa grany atsakiya se Umma agefen AK inna kuma agefen asma'u khadeeja nazaune kan hannun kujera daga gefe se washe baki take

Kujeran kusa dasu kuma inna ameena ne da sarah dasu fa'iz se sauran mutane Abba kuma tundaga waje yakoma gida dan yaki shigowa ciki wai daga baya su samesa agida

tashi sukayi suka nufi dining kamar mayunwatan zakuna haka suka fara bude kuloli se dariya ake musu ko ajikinsu

Wayar khadeeja ce tayi kara tana dabuwa taga Tarzan cike da fadin ciki tadaga kiran tana fadin Tarzan albishirinka gasu amma sundawo suna gida yanzu haka

Dariya yayi yace dagaske kike to amma meyasa baki gayamun ba tun dazu ina cikin daji ina nemansu nayi fushi karki kara mun magana ....yana kai nan yakatse wayar yana murmushi cike dafarin ciki yakamo hanyar gida

abinci sukaci bana wasa ba seda sukayi tatil sannan suka dawo Palo aka ci gaba da fira

Ruwan dimi Umma tasa khadeeja takawo tagasa kafar asma'u lokaci guda suna basu labarin yanda abun ya kasance amma idan anzo wani wurin se suyi shiru suna sadda kai

tsakiyansu khadeeja tashigo cikin rada tace garama ku ijiye wannan kunyar agefe dan idan ahmad yadawo duk se kunbamu labarin abunda yafaru

kauda kai sukayi lokaci guda suka tuno abunda yafaru dazu

Saurin tashi AK yayi yana fadin ummm bari naje nayi wanka nagaji sosai

Dariya momy tayi tace ai gara kuje kuyi wankan kuhuta

Tashi su Umma sukayi suna musu sallama zasu tafi zunbur asma'u tamike tana fadin Umma Nima zanbiku muje

Kallonta sukayi da mamki inna tace jimun shashasha ina kuma zaki keda kika dawo yau kizauna kikula da mijinki bakya ganin yanda yadawo ne abun tausayi har kinfishi kumari da kyan gani

kallon juna sukayi da AK atare suka kauda kai yayi saurin wucewa bangarensa yana musu sallama

ba yanda batayiba amma sunki bari tabisu hakanan tahakura tazauna amma tana tunanin yadda zata kuana daki daya da AK dan se yanzu taji kunyarsa takamata

Shima haka abangarensa yana tunanin mezai cema asma'u idan takara gayamasa tana sonsa shi kunyarta ma yakeji yanzu yana tsaye apalo yana wannan tunanin yaji anturo kofa saurin juyawa yayi yana zaton itace jin muryan ahmad yasa ya juyowo dasauri suka rungume juna cike da farin ciki se dariya suke summa kasa magana

Sunjima ahaka sannan suka zauna kan kujera Ahmad yafara jera mai tambayoyi

Dafe kai yayi yace ohh ni wai yanzu sena kara maimaita labarin danabada dazu kaje wurin lhadeeja mana tagayamaka ai taji komai

Kauda yayi yana daure fuska yace banaso fada muke da ita nidai inzaka gayamun ka gayamun ai waka abakin mai ita tafi dadi

Gyara zama yayi yafara basa labarin abunda yafaru har wurinda suke zaune abakin rafi ya tambayi asma'u takosa taje gida ne...yana zuwa nan yayi shiru yana Sosa kai

Ahmad dayakashe kunne har da lumshe ido yana sauraronsa jin shiru yasa yabude idonsa yana fadin se tace me

Kauda kai AK yayi yana fadin se tace eh

jiyo dakansa ahmad yayi yana dariya yace ahh wallahi ban yardaba nasan bahaka tace wani Abu daban tafada gayamun metace u know I am ur friend naaaaa

Daure fuska AK yayi yana hararansa yace to kenan karya zan maka abunda tace kenan in kanaso inci gaba in bakaso kuma tashi katafi dama ni bacci nakeji

tashi ahmad yayi yana fadin bari inbarka ka huta amma kuma gobe ma ai zamuzo dole ma kubamu labarin abunda yafaru

tashi AK yayi ya wuce daki yana fadin kaida khadeeja dama jarida kukayi da yafiyemaku

dariya ahmad yayi yafita yana masa se dasafe

Haduwa sukayi da asma'u zatazo bangarensu tana ganinsa tajuya zata koma yayi saurin tarota yana dariya yace tsaya mana aunty munjima bamu haduba shine kuma kike guduna kamar kinga dodo

Washe baki tayi tana Sosa kai tafara kame kame

Dariya yayi yace karkidamu kitanadi amsoshin dazaki bamu gobe in allah yakaimu ina fata dai kin gayamasa kina sonsa dan har yanzu muna nan akan bakarmu indan baki gayamasa ba bazamuyi aure ba ....
Bata jira ya karasaba taruga aguje tashige bangarensu tana rufo kofar dakarfi

AK nazaune bakin gado yaji anturo kofa azabure ya kwanta yana tufa da bargo ya lumshe idanuwa kamar mai bacci

ahankali taturo kofar dakin tashigo tana lekensa

Ajiyar zuciya tasauke ganin yana bacci cikin sanda tawuce bathroom

Yana ganin tashiga yatashi zaune yajera pilullukan dasuke raba gadon tatsakiya sannan ya gyara kuanciyarsa yana lumshe ido

daren ranar aysha batayi bacci kuana tayi tana safa da marwa adakinta ga damuwar ta isheta ga batajin dadin jikinta ana gama sallar asuba tawuce asibiti bayan likita yadibi jininta yabama nurse tafita cikin minti 30 tadawo da result din yana dubawa yayi murmushi yace amm hajiya kinada aure ne ?

Kai tagirgiza mishi tana kafeshi da ido gabanta na dukan uku uku takosa taji mezai ce

Ajiyar zuciya ya sauke yana kallonta yace idan bazaki damu ba inaso kidan kuanta anan zammiki scanning dan tabbatar da abunda kecikin result dinki

Gabanta ne yayi mummunar faduwa nan take idonta yaciko da kwallal jiki asanyaye tahau kan gadon duba marasa lafiya doctor yafara dubata

Yajima yana mata scanning din kafin daga karshe ya girgiza kai yakoma ya zauna yana yan rubuce rubucensa

Sakkowa tayi daga kan fadin tazo tazauna cikin rawar murya tace doctor menene

Dagowa yayi yana kallonta nadan lokaci sanann yamika mata takardar yana fadin gaskiya hajiya duk wasu gwaje gwajen damuka mini sun nuna kina dauke da karamin

*CIKI* na sati biyu!!!! 😱"""""

?????AK ne yamata 🤔

Kubiyoni taku Maryam Mhd danjin cigaban labarin

[19/07, 17:05] Hubbey Frd Ameena Kn: 📚📚📚📚📚📚
👨‍👧 _DOMUN KANWATA_ 👩‍👧

Na( *Maryam Mhd*)

1⃣5⃣0⃣

har wannan lokacin su JJ nayawo acikin daji ganin mangoron dasukayi ayashe da alaman wurinda suka zauna shiyabasu tabbacin suna cikin dajin har yanzu dan haka sukaci gaba da nemansu ganin dare yayi yasa suka yada zango dan su huta se tsinema yaransa yake akan duk su sukaja mishi wannan wahalar

ba yanda ahmad baiyiba ba dayansandan akan suci gaba da nemansu tunda sunada torchlights amma sunce gaskiya sun gaji zasu huta gobe suci gaba

zaune asma'u take tasa AK agaba se kuka take tana tofa mai duk addu'ar datazo mata

Jikinsa yayi zafi rau gashi yana sauke nunfashi ahankali kana ganinsa kasan baccin wahala kawai yake dan da kyar yake Jan nunfashinsa

ganin jikinsa nakara zafi yasa ta tafita waje tadibo ruwa aroba sannan tamatso kusa dashi ahankali tafara balle buttons din rigarsa tana kallonsa cike datausayi hawayenta nadiga akan kirjinsa har tagama sannan tafara kokarin cire masa rigar cikin dabara gudun kar ta tasheshi

Har tagama cire masa rigar baisan tanayi ba

tsoma rigar tayi cikin ruwan tana dora masa akan goshi nan take ruwan robar yadau dumi seda tacanzo wani taci gaba dayimasa hakan har jikinsa yarage zafi sannan ta shanya rigar ajikin runfar

wurinsa tadawo ta gyara masa kuanciyarsa tadafa kansa tamishi addu'a

Sannan takoma gefe tazauna tana gyara daurin kafarta daya warware tun jini nazuba har ya daskare awurin seda tawanke ta kara gyara daurin sannan tafita tayo alwala tazo tafara jero sallolin da ake binta har tagama tashiga jero nafilfili tana rokammasa sauki awurin ubangiji tana rokon allah yakubutar dasu daga hannun wa'innan mutanen yamaidasu gida lafiya har alfijiri ya keto tana zaune batayi bacci ba seda tayi sallar asuba sannan tasake matsawa wurin AK ta taba jikinsa murmushi tayi jin ba zafi ajikinsa kuma nunfashinsa yafara daidaita

jin zai motsa yasa tayi saurin janye hannunta tamatsa baya

Gyara kuanciyarsa yayi yacigaba da baccinsa mai cike da mafarkai iri iri marasa kan gado

komawa tayi daga gefe ta kuanta nan take bacci yadauketa

hasken rana ne yadaki fuskar AK ahankali yabude idanuwansa yana bin runfar da kallo lokaci guda yana tuna abunda yafaru jiya

Murmushi yayi da yahango asma'u gefe akuance ta takura wuri guda tana bacci

ahankali yatashi zaune yana bin singlet din jikinsa dakallo tashi yayi yadauki rigarsa dayagani arataye yasaka sannan yafita waje

Roba yadauka yadibo ruwa arafi yayi alwala sannan yadawo cikin runfar yayi sallolinsa dayagama yayi addu'oinsa

sannan yamatsa kusa da asma'u yana duba kafarta daya kunbura yana so yataba kafar amma yana tsoro yatasheta yajima adurkushe kusa da ita yana kallon yanda take bacci kana ganinta kasan atsorace take

tashi yayi yafita daga cikin runfar yana bin wurinda suke da kallo

asma'u tajima tana bacci se wajan la'asar tafarka zunbur tamike tana kallon tabarmar da AK ke kuance amma bata gansa ba zunbur tamike zata fita kenan ta hango anyi rubutu akasa da mayyan harrufa kusa da inda takwanta

Durkusawa tayi tana karanta

DON'T GO ANYWAY I WILL BE BACK SOON

murmushi tayi tana shafe rubutun cikin siriruwar murya tafurta da wani Abu yasameka jiya zan mutu ina nadamar rashin sanar dakai cewa ina sonka amma nayi alkawarin yau zan Sanar dakai dan bansan mezai faru damu nan gaba ba

tashi tayi tafita waje tayo alwala tayi sallah sannan tayi addu'ointa taroki ubangiji ya kamusu karshen wannan wahalar
Chapter 52 · 0% Book details