← Book details Domin Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 84

Sashe 2

Domin Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

alh Kabiru hausaweee haifaffan garin yola ne su biyar ne awajan iyayan su maza 3 mata biyu amma biyu sun rasu su uku suka rage shine babba se kanin jamilu da kuma kanwarsa ladidi duk da cewa alh kabiru yayi karatu sosai amma harkar kasuwanci ya sama gaba tun yana karami haka yataso wannan dalilin ne yasa aminin mahaifinsa yadawko shi daga yola yadawo dashi Abuja Dan yarika taya shi harkar kasuwan cin sa ganin kwazo da kuma experience dinsa ne yasa ya Dora shi aharkar kasuwancin su inda yake tura shi kasashan waje kan harkar kasuwancin su wani zuwa da alh kabiru yayi kasar yaman ya shafe kimanin watanni 5 yahadu da hafsat diyar abokin kasuwancinsu suka kulla soyayya da yarinyar daga bisani maganar aure tashigo ciki sunsha gwagwar Maya ba kadan ba kafin iyayansu su yarda da zancan auran amma abunda Allah ya qaddara se ya faru
Haka akayi auran ya taho da ita Nigeria arzikinsa Yanata habaka sun samu karuwar da namiji inda aksamishi sunan baban Hafsat wato ABID bayan rasuwar mahaifin alh kabiru wata rana yaje gida ya isko kananshi ya saida gidan da suke ciki ya barnatar da kudin ganin haka ne yasa yadawko shi da mamansu suka dawo abuja ya maidashi makaranta dama ladidi tayi aure a can yola
Bayan wani lokaci alh kabiru suka sake samun karuwa ta ai mace inda taci sunan Sarah
Batare da sanin kowa ba alh kabiru yafara Gina wani katafaran gida da kyakkyawar niyyansa ta hada family dinshi wuri guda seda yakammala gidan sannan ya Sanar dasu suka tattara suka koma murna wurinsu ba magana se ma dasuka ga gidan aljannar duniya
Haka suka ci gaba dazama acikin wannan gidan cikin farin ciki da kaunar juna har kanin alh kabiru wato jamilu yayi aure ya auri sadiya wata diyar kawunsu itama aka kawota wannan gidan
Wata rana alh kabiru ya shirya tafiya yola ganin dangi shi da matarsa wato Hafsat akabar su ABID awurin hjy Maryam mamar alh kabiru ahanyar su tadawowa ne sukayi hatsari Wanda wannan shine dalilin rasuwarsu family ya girgiza da wannan al'amari kasancewar alh kabiru mutum me mai zumunci da son talakawa bayan rasuwar ne baban Hafsat ya zo yace abashi amma hjy Maryam tayi mirsisi tahana da kyar yasamu tabashi Sarah yatafi da ita ABID kuma ya zauna awurin hjy Maryam wato (grany) kenan
Haka taci gaba da kula dashi da karatunsa inda yagaji mahaifinsa wato kasuwanci haka yataso yana masifan son garny da kuma Sarah duk abunda suke so zai yi kokarin yaga ya musu indai baifi karfinsa ba

Ko bayan rasuwar alh kabiru family bai watse ba ABID yana iya kokarinsa wajan ganin yahada kan family din wannan dalilin ne yasa ya je yadawko ladidi da yaranta 5 kasacewar mijinta yarasu haka kuma yaje yaman yadawo da Sarah Nigeria

Cigaban labari!!!

karasawa yayi cikin palon ya zauna kusa da grany suka gaisa da sauran mutanan gidan Sarah ce tazo tazauna kusa dashi tace yaya yau ranar family meeting ne murmushi yayi yace nasani KANWATA ai dai kyabari inje inyi wanka inci abinci ko ?? Languabar da kai tayi tace to yaya tashi na kosa afara grany tamaka mata harara tace ai dama dole ki kosa tunda kina so kuje yawan gantali
Shuru tayi ta hade fuska batace komai ba
Daga nan kuma kowa yayi shuru a palon ABID ne ya katse shurun da cewa bari in je inshirya in fito nan fa kowa ya wangale baki tare da fadin to shi kuma ya haura sama yanufi bangaransa
[18/07, 15:03] Hubbey Frd Ameena Kn: 📚📚📚📚📚📚
👨‍👧DOMUN KANWATA👩‍👧

🖊na marubuciya HUSNA kabir zarewa( the mammah girl)

🖊 da sunan Allah mai Rahma mai jinkai....

👨‍👧DOMUN KANWATA👩‍👧

5⃣⏭1⃣0⃣

Ahankali yake takunsa har ya isa bangaran sa mamaki ne ya kamashi ganin palon shi abude can kuma yayi murmushi yace hmm nasan aikin Sarah ne
Yana shiga palon yaji anrufe mashi ido datafukan hannaye murmushi yayi yace
Aysha na ganoki Hannunta Yakama yazagayo da ita ta gabansa tare dasakar mata lallausan murmushi

Aysha kenan ya ce agurin uncle jamilu wato kanin baban ABID kyakkyawa ce daidai gwargwado Shekarunta zasu kai 20 Akwai soyayya mai karfi tsakaninta da ABID kuma suna fata ta kaisu ga aure
hura mashi iska tayi a fuska ahankali ya lumshe idanuwanshi Hannayanta ta sakalo abayan wuyanshi cikin muryanta mai Jan hankali tace kallon fan!!??
Ajiyar zuciya ya sauke tare da fadin nayi missing dinki ne banganki ba kuana biyu ina kika shiga!!?
Shagwabe fuska tayi
tace ai baka neme niba kuma dama nasan nice nake sonka kai ba ka sona
Zare jikinsa yayi daga nata yana fadin
Kullun haka kike cewa amma kema kinsan da bana sonki bazan tsaya bata lokacina akanki ba hangar dakin shi yanufa can kuma ya jiyo ya kalleta yace jike kasa yanzu zan shirya inzo
Murmushi tayi tace to se kazo ko in jiraka
dakin ya shiga yana fadin jeki kawai

Asma'u da khadeeja ne akan hanyar so ta dawowa daga islamiyya suna tafe suna fira
Sun wuce daidai masallacin unguwar su sukaji ana kiran Asma'u!!! gaba dayan su suka juya amma basu ga kowa ba suka ci gaba da tafiya aka ce khadeeja!!!!
suka kara juyawa basuga kowa ba khadeeja tace amma( sunan da take kiran Asma'u dashi kenan tun tana yarinya )
asma'u tace na'am
Tace amma ko munyi gamo ne
Asma'u tayi dariya tace haba khdy wane irin gamo?? Ni kamar ma nasan muryan nan
Ganin dagaske khadeeja tafara tsorata yasa taja hannunta suka fara tafiya suna cikin tafiya khadeeja taji anja hijabinta ta baya haba tafara ihu tana daka tsalle gashi tarufe idon ta Asma'u duk ta rikeci ta rirrike khadeeja can ta dago Dan ganin Wanda yaja hijabin fa'iz(yaron yayan babansu ) ta gani atsaye yana kwasan dariya harara ta makamai tace kaga abunda kaja ko??
Se alokacin khadeeja ta bude idonta ta kalli fa'iz
Har yanzu dariya yake yace ke wallahi khadeeja Allah yayi maki tsoron tsiya duk hijabin nan naki da islamiyyar maimaikon ki ambaci sunan Allah kin tsaya kina ihu kina amma!! Amma!!!
me amma zata iya yi maki bayan ita....
Ganin tamike tanufo shi yasa bai karasa maganar ba ya ruga aguje yanufi gida khadeeja tarufa mashi baya aguje
Asma'u tayi murmushi itama tabi bayansu

Aguje fa'iz ya shigo gidan Yana haki
Wajan yanufa Umma dake zaune akarkashin bishiya tana gyaran wake tace tsaya nan ni kar ka fado mun wakaje katsokano kuma daga zuwan ka?? Tana rufe baki khadeeja tashigo gidan rai ahade wurin fa'iz tanufa Umma tarike ta tana tasya me yahadaku??
Khadeeja bata ce komai se haki takeyi fa'iz yace
Umma wai Dan na jamata hijabi shine fah
Umma tace fa'iz kai dkasan halin khadeeja abun laifi baya mata kadan me yakaika tsokanarta murmushi yayi ya kalli khadeeja to yi hakuri bata ce komai tayi kwfa tare da wucewa daki Asma'u tashigo tazauna kusan Umma takarba wakyan tana gyarawa fa'iz ya matso kusa da ita yana tayata can ya dago yace AMMA saura kuana hudu fa !!
Tace name fahh???
Yace kituna mana
🤔 Tayi shuru can tace kai gaskiya ban tuna ba gira yafara daga mata yana cewa birthdayyyyyyyyy
dariya tayi itama tare da kwafan yanda yayi magar tace ohhhh na tunaaaaaaaa

Dariya sukayi su duka yace to me zaki bamu gift tace to ai ita gift ba'afada sedai kawai in ambaka kaga ko miye yace hakane khadeeja da fitowar ta kenan daga Palo tace dama tunda naganka nasan maula kazo yi Dan baka zuwa hakanan daure fuska yayi 😠yace to wa yakasa dake dazaki kwasa?? Ita ma fuska adaure tace tunda kakasa da amma ai kuwa dole in kuasa Asma'u ce ta katse fadan da cewa haba wai se yaushe zaku daina Abu kamar yara ne yanzu fa shekarun ku 17 amma har yanzu Baku girma ba
fa'iz ne yayi gyaran murya yace
😎 hmm hmm amma nifa 19 ne
tsaki tayi tace to miye maraban dambe da fada?? Umma ce tayi
dariya kana suma suka kwashe da dariya🤣
Chapter 2 · 0% Book details