← Book details Domin Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 84

Sashe 51

Domin Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kuka take kamar ranta zaifita tama kasa magana se girgiza takai take tana kallonsa cike da tausayi tana ji dama itace ahalin dayake ciki da tafijin saukin radadin datakeji ahalin yanzu

hannunsa yasa akan bakinta yana fadin shshshsh
Kiyi shiru chitti kar wa innan samudawan su jimu
kinga ni tafiya zanyi nasan bazan iya cigaba ahaka ba kiyi kokari ki koma gida kinji kibama Umma hakuri kice nayi iya kokarina nakawoki amma nakasa kicema grany tayi hakuri kuma taringa shan maganinta akaikai ki kularmun da ita kinji nasan ke kadai ce zaki iya ga sarah nan itama ki kula da ita kinji kizabamata miji nagari Wanda yadace da ita kihadasu kinji nasan tanada taurin kai batajin magana amma tanada tausayi da saurin karaya ki koyar da ita halayanki masu kyew kinji

Murmushi yayi yanajin wani yanayi ajikinsa cikin dasashshiyar muryansa yaci gaba dafadin

Kicema inna ameena nace takoma wurin dan tsohonta tadaina takurama granyta kinji

Kicema aysha tayi hakuri nasan tanasona amma ina jamata lokaci naki aurenta kigayamata ina Neman albarkar grany akan duk abunda zanyi shiyasa ban aureta ba inaso se grany ta amince amma kice cikin samarinta tazabi Wanda yafi sonta aciki ta auresa

Khadeeja kuma kicemata nace takula da ahmad sosai tayimai biyayya tazauna dashi lafiya shima kice nace yariketa amana kar yacutar da ita

Kuma kicemasa karyayi wani aboki bayanni kinji idan yana bukatar wata shawara ko wani Abu yasameki kar ya yarda dakowa cikin abokananmu

Chitti kinada hali mai kyew kinda kirki kicigaba da haluri kinji idan namutu kar kizauna hakanan kisamu wani mutum nagari ki aureshi amma kar ki manta dani kinji ko

Rungumeshi tayi dakarfi tana sakin wani kuka mai cin rai tace ABI ya isa haka dan allah ba abunda zai sameka ABI katashi kaji tare zamu koma gida muci abincin grany mai dadi sannan inkamaka coffee dinka mai zafi kasha kaji ni bawanda zan aura ABI Kaine mijina dakai kadai zan rayu saboda kai nakeso I LOVE YOU!!!

dago fuskansa tayi tana kallonsa idonsa alumshe ba alaman nunfashi atare dashi atsorace tafara daddabashi tana kiran sunansa Amma shiru

Hannunta tasa tana bubbuga gefen fuskarsa cikin rawar murya tace a'a a'a ABI u can't do this to me dan allah katashi ABI idan kamutu ina zan sa raina wallahi nima mutuwa zanyi dan allah katashi ABI

Surutai kala kala take tana jijjigashi dakarfi amma shiru kakeji jadaba tafarayi tana toshe bakinta tajinginu da iccen runfar tana kallonsa se kuka take kamar ranta zai fita tajima ahaka can kuma tayunkura kamar antsikareta tanufosa da rarrafe tana kara kiran sunansa tafara danna mai kirji amma baimasan tanayiba

Sunkoyo dakanta tayi kan fuskarsa hawayenta na diga akan idonsa ahankali takai bakinta kan nasa tafara hura masa iska tajima tanayi amma taji shiru fadawa tayi kan jikinsa takara fashewa da kuka tana addu'ar allah yadauki ranta itama da wannan halin datake ciki

Kamar daga sama taji yafara tari kadan kadan saurin dagowa tayi cike dafarin ciki ta riko fuskarsa tana kiran sunansa

amma bai bude idoba kuma bai motsaba se nunfashinsa dake fita ahankali ""'"
[19/07, 17:04] Hubbey Frd Ameena Kn: surutai yaketayi shikadai jin shiru yasa yaduba gefensa amma baiganta awurin ba cike da mamaki yafara waige waige yana kiran sunanta

Can bakin wani shago yahangota tana daga mai hannu

Girgiza kai yayi yakarasa wurinta yana tambayar metake anan

Waya takarba ahannun mai shagon tamika mishi tana murmushi

saurin kai hannu yayi ya fizgi wayan yana dariya yace ohhh chitti gaskiya kin hadu bari mukira grany

Nunmaban grany yayi dialing seda takusa katsewa tadauka jikin asanyaye tayi sallama

Hannunsa yasa yatoshe bakinsa hawaye nazuba afuskansa tsabar farin cikin jin muryan grany dayayi yama kasa magana se mikama asma'u wayar yayi bayan yasa a handsfree

Har grany zata kashe wayar taji muryan asma'u na sallama

Zunbur tamike tsaye cike da farin ciki tana fadin wanake ji haka kamar asma'u

da mamki kowa yajiyo yana kallonta kowa yakosa yaji meyake faruwa ba

kallon kallon aka fara tsakanin aysha jamilu da kuma sadiya bakaramin tashin hankali suka Shiga ba jin an ambaci asma'u

Cikin rawar murya asma'u tace eh nice grany ya kuke ya ummata

Dariya grany tayi mai hade da kuka tafara kai kawo cikin palon tana fadin lafiryamu kalau asma'u Ku yakuke ina Abidi badai abunda suka muku ko

matsowa kusan wayan AK yayi cikin rawar murya yace grany!!!

dariya tayi mai dan sauti jin muryansa datayi batasan lokacinda hawaye ya wankemata fuska ba

"Abidi ya kake kuna ina ne

dariya yayi yana goge hawayen fuskarsa yace grany lafiyarmu kalau muna hanya yanzu zamuzo kigayama su Umma su....

Bai karasaba Asma'u taturo bakinta kusan wayar tana fadin grany yunwa mukeji kicema Umma tayimana kunun gyada ke kuma kiyimana tuwo inna ameena kuma tamana dambu yaji hanta sosai .....takarashe maganar tana lashe baki

ture kanta yayi yajuya mata baya yana fadin grany kihadamun coffee na mai zafi ki kara citta sosai saboda makogorona yabushe

Dariya grany take harda rike ciki rabonta da tayi farin ciki irin haka har ta manta

Kokowa suka farayi akan wayar kowa da abunda yakeso yafada seda katin ciki yakare sannan ya mikamata wayar yana fadin to ai gashi se kicinye ko duk awane cikin zaki saka abinci kala 7 oho

Kin karban wayar tayi takauda kai tana turo baki tace seda kacinyemasa katin se ka maida masa wayarsa

Juyowa yayi yana kallon mai shagon yana murmushin yake yace malan yi hakuri muncinye maka kati

Murmushi yayi yace ah ai ba komai dama nagayamata katin ba yawa

se alokacin asma'u tajiyo tana mai godiya sannan tace

dan uwa ina zamu samu motar dazata kaimu cikin garin abuja

dariya yayi yace to gaskiya yarinya sedai babbar motar dake kamana kaya idan kunaso yanzu se inrakaku muga in yayi lodi se yarage muku hanya

Juyowa sukayi suka kalli juna sannan AK yakallesa yana murmushi yace malan munaso sedai fa ba kudi ajikina ya za'ayi

fitowa yayi daga cikin shagon yanufi wata hanya yana fadin kuzo muguada sa'armu mugani amma gaskiya da kyar zai yarda dan bashida mutunci

Haka yayita musu surutu suna binsa abaya har suka isa wurin babbar motar da tacika makil da buhuhhuna

Sallama yama wani mutun yajiyo yana hura sigari batare da ya amsa sallamarsa ba yace ya akayi ne idan ma kayane kaje ba wuri se gobe....

dariya mai shagon yayi yana nuna su AK yace gali dama wa'innan bayin allah zaka taimakama ka rage musu hanya zuwa cikin gari

Juyowa yayi da jajayen idanuwansa yana binsu da kallo yace nima ai bawan allah ne nawa zasu biyani

Juayawa mai shagon yayi yakoma yana fadin gashinan kudaidaita zan koma nabar shago ba kowa

Kallon juna sukayi sannan asma'u ta sassauta murya tace gali taimakonmu zakayi ba ko kwandala ajinkinmu amma idan munje zamu biyaka konawa kakeso

Kallonsu yayi ya tintsire da dariya yana fadin yanmata kin ma rainamun hankali ki kalleni da kyew kinga nayi kama da Wanda zaku yawdara daganinku irin yarannan ne masu gudowa daga gidan iyayensu sushiga duniya ...
Yakarashe maganar yana zukan sigari yahura musu

Hannu AK yasa yana kabe hayakin sigarin yana yamutsa fuska yamatso kusan asma'u cikin rada yace chitti wannan dan jagaliyan yayi kama da dai daga cikin wa'inda suke binmu ko zamu hadashi da yan kauyan nan suci uba.....

Bai karasaba gali ya katseshi dafadin kai nifa tafiya zanyi kuna batamun lokaci idan bazaku ba gara ma kuware

tsaki AK yayi yana ji kamar ya haushi da duka

ganin zai shiga motar yasa asma'u tayi saurin riko hannun AK tana Nuna ma gali tace to ka rike wannan agogon jingina idan munje muka baka kudin seka bamu abunmu

Saurin kwace hannunsa yayi yana fadin ke bakida hankali ne kwasan tsadar wannan agogon zakice inba wannan dan ta'addan haka kawai

juyowa gali yayi afusace yanufo AK asma'u tayi saurin shiga gabansa tana basa hakuri sannan ta lallashi AK da kyar yaciro agogonsa taba gali

Sannan suka shiga gidan gaba suduka biyun yaja motar suka tafi

Fada akayi sosai tsakanin yaran JJ da yan sanda sedai bawanda aka kashe atsakaninsu kuma yaran JJ sunyi nasarar guduwa daga hannunsu guda daya suka kama JJ dakansa yaharbesa gudun kar yatona musu asiri

shidai ahmad damuwarsa su AK seyawo yake yana nemansu amma bai gansuba

Tuni grany tasanar dasu Umma wayar dasukayi dasu asma'u nan take gida yacika cike dafarin ciki kamar gidan bigi haka ake hidima kowa nakokarin girmusu abunda sukeso

Aysha jitake kamar tamutu dan bakin ciki ga wani bakon al'amari da yaziyar ceta na sauyin yanayin datake gani kwana biyu takasa fahimtar komai kuma taki zuwa asibiti saboda tana tsoron abunda result zainuna kar aje abunda take zargi yazama gaskiya

suna cikin tafiya AK se toshe hanci yake kamar zaiyi amai saboda saitin hamatan gali yake sedariya asma'u kemishi suna fira da gali shidai AK takaici ya isheshi ko magana bayason yi

Juyowa yayi yana kallon gali yace kai wai ina zaka saukemu

Baijiyo ya kallesa ba yace duk inda kakeso konan kace insauleka tsaba zan iya taka birki

tsaki AK yayi yace kai nafaga alama ka rainani dayawa bakasan koni wayeba ko?

dariya gali yayi yana kallon AK yace to waye kwa kai banda mutun dan uwana kuma dan kauye mai guduwa da budurwa

dariya asma'u tayi tana kallonsu batace komai ba

cike datakaici AK yace yanda make dinnan bansan ko kasan AK hausawee ba to nine

Baki bude gali ke kallonsa sannan ya kwashe da dariya harda dukewa yace kai amma guy dinnan ka rainamun hankali wai AK hausawee kodayake zaka iya fadan haka

Kaga nima akauyanmu salman khan ake kirana saboda yanda nake da kirar karfi

Dariya AK yayi har yana kuantoma asma'u yace wai salman khan amma wallahi zaginka sukayi baka saniba kuuuut

daure fuska gali yayi bai kara magana ba har suka iso inda zai saukesu sannan asma'u takarba wayansa takira driver tamai kuatancen inda suke

sun jima atsaye kafin kafin driver ya iso cike da fadin ciki suka rungume juna da AK yana mai barka

karban kudi yayi ahannun driver yamika ma gali yana kwace agogonsa daga hannunsa ya wuce mota

dariya gali yayi yana fadin eh dai jeka kana tunkaho da kudin budurwa gara ni gumina nakeci se gayu ba ko sisi
Chapter 51 · 0% Book details