← Book details Domin Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 84

Sashe 46

Domin Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dariya Wanda aka kira da bala yayi yana dora yatsanshi kan photon khadeeja yace amma dai kasan wannan tafi gogewa ko haka sukaci gaba da jayayya kowa dawacce tafimashi kyew

Tunsafe asma'u taje dawko khadeeja daga gida kasancewar yau ne ake sa lalle

Har sunkawo bakin get zasu fito khadeeja takoma wai tayi mantuwa fita asma'u tayi tanufi mota tana jiranta

yaran JJ suna daga gefe cikin mota suna jiran fitowar yarinyar daga gidan saboda yanda sukayi da sarah kenan ganin asma'u yasa dayan wanda yace tafi kyew yayi saurin nufar inda take cikin sanda yana ciro handkerchief a aljihunsa yana zuwa tabayanta yakai hannu zai shaka mata handkerchief din kawai yaji ana kokarin fitowa daga gida saurin jadabaya yayi yalabe bayan mota yana kallonsu har suka shiga driver yaja suka tafi

dunkule hannu yayi yanaushe iska cike da takaici ya koma wurin dan uwansa dake cikin mota

anan suka kira JJ suka sanardashi yanda akayi nan take ya hau zaginsu kuma yamusu kashedin idan suka dawo batare da yarinyar ba sai ya aikasu barzahu

sanin zai iya yin hakan yasa ba shiri suka bi bayan motar su asma'u

sarah tana ganin su khadeeja takira JJ tafara masifa akan ba haka sukayi dashiba idan yasan bazai iyaba ya dawo mata da kudinta tanemi wani hakuri yabata akan komai zai tafi daidai kawai dai tayi kokarin turo yarinyar waje sukuma zasu cika sauran aikin

Bayan asma'u takai khadeeja bangaren grany ita kuma tawuce dakinta dan tashirya

Tsaye take agaban dressing mirror tana gyara fuskarta

AK yashigo cikin shirinsa tsap na kananun kaya yayi kyew matuka kusa da ita yamatso yadauki turarensa yafara fesawa

Dagowa tayi tana kallonsa tace ABI ya isa haka mana turare in yayi yawa hawa kai yake kuma ma da lalle namata ne kawai why are u dressing up

daure fuska yayi yace stop treating me like a child I know what I am doing

Dariya tayi tace ohhh fita zakayi ne

"eh ko inzauna baki gaji da ganina ba

juyowa tayi tana kallonsa baki bude tace waaaaa meye anan dabazan gaji daganiba

Dariya yayi yajera da ita a gaban dressing mirror suna kallon Kansu yace kalla da kyew kiga ba yabon kaiba amma kema kinsan kinfini.....bai karasaba yayi sairin fadin I mean nafiki haduwa

Dariya tayi tana tafa hannu tace ABI bakinka yanaso yafadi gaskiya kana hanashi kama daina yaudaran kanka dan kasan nidin dabance

dariya yayi yana kallon bayan rigarta yace ohhh naga alama duk cikin gayun ne kika bar zip abude

Saurin juyawa tayi tana taba bayan rigarta tajishi abude

Murmushin yake tayi tana kokarin jan zip din tace nakasa zipping dinshi ne

"zo in taimaka miki

"to amma karufe idonka tukunna

Juyo da ita yayi yana fadin dan allah can mezan gani abayanki

kokarin Jan zip din yake amma yakiyi dagowa yayi yana kallonta tajikin mirror yace chitti wai dole se wannan kayan kicanza wasu mana

"kaja dakarfi mana se kace ba namiji ba

bata karasaba yaja zip din da karfi yayi sama dashi

thank you ...
tafada tana fita daga dakin

Zaro ido yayi yana kallon abun zip dinta dake hannunsa ahankali ya furta I am in trouble

bayan mutane sun taru aka fara shagali gidan yacika da mutane hakan yasa sarah bata samu damar aiwatar da aikinta ba gashi Sam khadeeja taki bata fuska bare tasamu damar fitar da ita waje

asma'u na hidima da baki Sam bata lura da zip dinta daya fara budewa ba AK yazo yana magana da grany kawai ya hango zip din abude gashi da mutane dayawa awurin har da yan samari

Kusa da ita yaje ya tsaya daga bayanta yana kokarin boye wurin

juyowa tayi da mamki tace miye haka wani Abu kake so ne

Kara dawowa bayanta yayi cikin rada yace muje dakinmu

Zaro ido tayi tace what kamar ya muje daki wai ma bakace fita zakayi ba

hannunsa yadora kan bayanta yace kedai idan munje zan miki bayani

kokarin juyowa take amma yahanata ga mutane sun fara kallonsu ana gulma

aysha dake gefe tana hangosu tuni idonta yaciko da hawaye sarah kuma ko ajikinta abunda yadameta daban

"ABI kabari mana baka ganin mutane suna kallonmu ne

Barin wurin yayi yana fadin shikenan nabari amma kinemi wani Abu kirufe bayanki dan har bra....

bai karasa ba tayi wata irin supper tashige gabansa tana fadin ya ....ya....kuma haka bayan kace kayi zipping dinsa

Matsawa yayi takara shiga gabansa tana fadin ina kuma zakaje tunda kai kabatamun kai zaka kaini na gyara

dariya yayi yace se kinroka kuma da girmamawa

langwabar dakai tayi cikin siriruwar murya tace ABI can u help me please nasan kanada kirki da taimako to nima kataimaka mun kaji

Dariya yayi yace se kince nafiki haduwa haduwa

bai karasa ba tayi saurin fadin haba ai fada ma bata baki ne yanda kake handsome dinnan ina zan hada kaina dakai

Now please muje kakaini daki

sun juya zasu tafi kenan inna ameena ta taresu tana danne dariyarta tace ina zuwa haka

Murmushi AK yayi yace inna daki zamuje akwai abunda zamuyi

kallonsu tayi sama da kasa tace naga alaaaaama to Ku koma bayanzu ba bakwa ganin da mutane ne

Langwabar dakai yayi yace inna please emergency ne yanzu zamu dawo

Dariya tayi tace ohhh bazaku iya jira har awatse ba

Zai yi magana kenan asma'u ta taka kafarsa cikin murya mai kaman rada tace u better keep quite daban abunda kake nufi ita kuma daban inda tafassara maganarka

basu kara cewa komai ba suka raba tagefenta suka wuce ita agaba shi abaya yadora hannunsa akan bayanta
[19/07, 17:04] Hubbey Frd Ameena Kn: Suna hawa kan stairs suka hadu da aysha tana atsaye taharde hannaye tana kallonsu

Meyake faruwa ne.....
tafada tana kallonsu daya bayan daya

Murmushi yayi yana kallon asma'u yace ba abunda yafaru kidan bamu waje muwuce

Fashewa tayi da kuka tana fadin AK wallahi abunda kake mun yafara isata ina alkwarin da kadaukamun haka mukayi dakai kuana biyu kacanza mun to wallahi zanje nafadama grany duk abunda yake faruwa

Saurin riko hannunta yayi yanuna mata bayan rigar asma'u yace kinga daki zan rakata ta gyara tunda ni nabata mata

Idan kuma zaki rakata shikenan

Murmushi tayi tana kallon asma'u tace eh zan kaita amma nima zaka fita dani

Mezai hana je kidawo

Hannunsa yakai yaja kuncinta yana fadin baby u know I love u na

saurin barin wurin asma'u tayi tana jin wani azababben kishi na dukan zuciyarta

juyawa sukayi shi da aysha suka fita da dabara dan kar wani yagansu

anyi shagali komai yatafi daidai amarya tasha lalle tayi tsap ga umm tun tuni tafara aikinta wato gyaran jiki kuana biyu khadeeja tayi fresh kyenta yakara fitowa yau zata koma gida saboda gobe daurin aure jibi kuma suci gaba da sauran shagulgulan kamar su sisters day dinner walima da dai sauransu

har yanzu yaran JJ suna waje suna jiran fitowar khadeeja amma shiru sarah najin asma'u da Ummi zasu maida khadeeja tayi saurin gayamusu

bayan asma'u takai Ummi da khadeeja tafito zata tafi tazo bude motar tajita arufe zagayowa tayi wurin driver tana knocking kawai taji an toshe mata hanci da handkerchief din dayasha powder

Kokarin kwace kanta take amma takasa sun jima suna kokawa dashi kafin daga karshi tafadi asume

saurin fitowa dayan yayi Yakama mishi suka sakata amota

Seda suka bar unguwar sannan suka kira JJ nan yagayamusu inda zasu kaita cikin wani dokar daji inda suka tanadeshi dan irin haka

Tafiya ce mai tsawo kafin sukai

bayan AK yadawo da aysha da daddare yawuce daki amma baiga asma'u baidamu ba yayi shirin kuanciyarsa ya kuanta dan atunaninsa tana bangaren grany suna hidimarsu

Ganin karfe daya tayi yaji yafara damuwa da rashinta adakin tashi yayi har zai fita se kuma yadawo yadauki wayansa yakirata tana ringing ba adauka

Yana nan zaune har karfe biyu tayi fita yayi daga dakin yanufi bangaren grany

Koda yaje har sun rufe Yajima awurin yana tunanin yatashesu ko yakyalesu amma zuciyarshi nabashi wani Abu yasamu chitti

Buga kofar yayi ahankali can anjima inna ameena tazo tabude da mamaki take kallonsa tace AK lafiya meyafaru...

Shiru yayi dan baisan mezai cemata ba

Kallon bayansa tayi tana fadin ina asma'u ko wani abune yafaru

Saurin dagowa yayi yana kallonta da mamaki yace inna bangane ina asma'u ba kina nufin batanan

anan dai suka fahimci asma'u tunda takai khadeeja bata dawo ba

Komawa bangarensa yayi ya kuanta hankali kuance yana fadin to wai meyasa nadamu da rashinta akusa dani murmushi yayi yace koda yake nasaba da shirmanta ne

da asuba Abba yafito zaije masallaci kenan yaga motar gidan AK awaje bai kulata ba yawuce saboda kar yamakara salla

Yana zuwa masallaci kuma yamanta se wajan karfe 7 fa'iz yamatso kusa dashi cikin rada yace Abba dazu dazan zo masallaci naga motar AK awaje

dafe kai Abba yayi yana salati yace kaga ni nama manta tashi muje muga allah sa lafiya kila paci tayi suka barta anan

Seda safe yaran JJ suka isa wannan wurin acikin dajin allah ko duhunsa kayane suna zuwa suka Shiga da ita runfarsu suka daureta ajikin iccan runfar sannan suka sanar da JJ sun isa

Cike dafarin ciki yace musu sukula da ita gayanan kan hanya

Su Abba nazuwa suka isko driver amotar knocking Abba yayi amma shiru seda yasakeyi dakarfi sannan drivan yatashi yana date kai yana runtse ido

Saurin gyara zamansa yayi yana kallon inda bude kofar yayi yafito suka gaisa da Abba kansa adaure yake kallon wurin yana kokarin tuna abunda yafaru jiya

kallon juna Abba da fa'iz sukayi sannan Abba ya kalli driver yana murmushi yace sannu ko allah sa dai Lafiya naga alama kamar anan ka kuana

Saurin riko hannun Abba yayi yana fadin malam ina madam

da mamki Abba yace wace madam kuma bayan tun jiya ta tafi gida

Shiru yayi nadan lokaci kana yazauna akan kujerar motar yana fadin dan allah zan samu ruwan alwalwala

kallon fa'iz Abba yayi yace jeka kakamasa ruwan alwalan daga nan kace khadeeja tadamo masa kunu ko tea yadan sha
Chapter 46 · 0% Book details