← Book details Domin Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 84

Sashe 3

Domin Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bayan kaman minti talatin ABID ya sawko zuwa palon kasa yana sanye da 3quater da kuma jallabiyya milk color se kanshin turare ke tashi yayi kyaw sosai kamar black American tun da yafito suka kure shi da ido har ya iso ya zauna a dai daga kujerun palon sannan ya zaro check da bairo daga aljihun rigarsa yadora akan table din dake gabansa Sannan yadago ya kalle su daya bayan daya yayi gyaran murya yace to dafatan dai ba wata matsala babba dukansu suka ce a'a yace to alhamdu lillah kamar yanda muka saba zamu fara daga babba zuwa karami
Gaba dayansu kowa se washe baki yakeyi inkacire grany data hade girar sama da takasa
ABID ya kalli uncle jamilu
yace uncle bismillah uncle jamilu ya washe baki yace ni daman ba wani Abu bane kawai dai ciwon kafar nan na wane yadameni shine nakeso in fita Waje adubani yana magana yana kallon grany ganin yanda ta kafeshi da ido ko kiftawa bata yi ai kaman jira take yagamana tayi carab tace kai jamilu kaji tsoron allah yanzu fi sabilillahi duk asibitocin Nigeria basu isa suma maganin cewon Kafa harsai kafita waje ABID ne ya katseta da cewa ya isa haka grany wannan ba wani Abu bane duk kudin da nake nema ai saboda Ku ne So banga anfanin wannan dokiyar ba inhar bazan magance maku matsalolinku ba
Grany dai baki ya mutu se shuru da tai ta sa musu ido
Check din dayayi rubutu ya mikama uncle jamilu bansan konawa bane sedai naga yawashe baki yana godiya
ABID yajiyo ya kalli sadiya matar uncle jamilu yace
Aunt se ke
Baki ta washe tace dama jarina ne yayi yayi kasa shine nake so.....
Grany ce ta katseta da cewa ji wani jin dadi yo dan jarinki yayi kasa uban wa kike bi bashi anan??
ABID ne ya sake katseta da fadin
Grany please!!!!!
Saboda haka ta tashi azuciye ta nufi part dinta duk suka bita da kallon gwara da kika tafi Gyaran muryan da ABID yayi ne yasa suka dawo da dubansu gareshi nan ya mika mata check kowa ya cigaba da fadin nashi har akazo kan Sarah itama tafadi nata na fitan su London kuma ya amince aka zo kan aysha ita kuma tace tana so idan suka dawo daga London zata ji tayi degree dinta a abroad shima ya amince haka akacigaba har suka kare kowa yawatse cikin farin ciki da jin dadi
ABID yana tashi direct masallaci ya nufa kasancewar anata kiran sallah bayan yadawo ne ya wuce bangaran grany ahankali ya tura kofar tare dayin sallama sanyin AC da kuma daddadan kanshin turaran wuta ne sukamishi maraba
Zaune ya iskota kan sallaya tana lazimi kusa da yazo ya janyo pilo anan kasa ya kuanta ya dauki remote ya kamo tashar aljazeera yana kallon labarai se da yashafe kusan awa daya amma grany bata motsa ba sedai daga ya kalleta se ta kauda kai murmushi yayi yamatso ya dora kansa akan cinyarta yace grany nasan kin kare fa kawai shareni kikayi
Hannunta tadora akansa tana shafa suman kansa cikin sansanyar murya tafara magana kamar haka
ABID Nasha fada maka karage abunda kake ma yaran nan yayi yawa amma kakasa ganewa zaune yatashi yarike hannunta cikin nashi yace grany family nan sune rayuwata taya zan iya kuantawa inyi bacci mai dadi alhali family na suna cikin matsala na tabbata koda Abba yana raye da abunda yafi wannan ma zai iyayi grany tasauke ajiyar zuciya tace to shikenan Allah yasa albarka yace ameen ko kefa tace to ai bamu gama ba yace se kuma me zama ta gyara tace zancan iyali ABIDI anya kuwa lafiyanka kalau wajan shekara 30 amma baka zancan iyali
Dariya yayi yace grany kwantar da hankalin ki ankusa grany ta katse shi dacewa yo kai daga anyi magana se kace ankusa katsaya biye ma wannan shashan aysha ni kabani dama in zabo ma air mutunci mai tarbiyya kaki
Murmushi yayi yace grany ahalin danake ciki yanzu bakowace yarinya zan iya aure ba ina bukatar wadda tasanni da yanayin family na yarinya air baban gida wacce tasaba da rayuwar family house kinga seta taimakamun wajan kula da family na grany ni bawai macan dazatamun kwalliya ingani kawai nake bukata ba jarumar mace nake nema
To shiyasa kika ga ina bukatar lokaci
Grany ta sauke ajiyan zuciya tace
To banki ta taka sedai shekaru ja suke ABID ina so inga ya'yanka kafin lokaci na yayi ABID ya daure fuska yace ba nace idan muna magana kidaina kawo zancan mutuwa ba insha Allah har jikokina se kin gani Grany tayi saurin fadin
Um um daina mun fata ABID bana fata in kai lokacin da zan kasa tantance tsakanin gabas da yamma
Kiran sallan da ake ne ya katse masu firar ABID yatashi yana murmushi yace zanje masallaci daga can kuma zan wuce inkuanta nagaji dayawa
Grany tace yo ba dole ka gaji ba kazauna majalisar dinkin duniya
ABID yagane me take nufi shiyasa bai ce komai ba yanufi Hanyar fita har yakai bakin kofa ya jiyo yace grany kibada Lipton dina akamun tace to shi kuma ya fice

Misalin karfe 8 na dare Asma'u ce da hkadeeja zaune a Palo suna kallon shirin akushi da rufi Wanda ake atashar arewa24 can khadeeja ta waigo ta kalli Asma'u race amma alalan nan dagani zatayi dadi ko ??Asma'u tayi murmushi tace sosai ma ko kina sone ?
eh wallahi ina so zaki mun ne? Asma'u tace mezai hana khdy ko wannan din da suke girkawa yanzu in kina so se inje in karbo maki
Khadeeja ta shagwabe fuska tace uhm uhm nifa da gaske nake
Asma'u tayi dariya tace gobe zan maki naki khdy ta washe baki tace Allah ya kaimu Asma'u tace ameen suka ci gaba da kallon

Washegarin ranar ta kasance asabar misalin 10 nasafe Asma'u ta gyara wken alale tashirya ta tafi kai nika

ABID ne yafito daga bangaran sa cikin shiga ta kananan Maya wando light brown da faran riga ga fitinannan kanshi dake tashi daga jikinsa yayi kyau bakadan ba fitowarsa yayi daidai da fitowar Sarah daga nata part din da far'arta takaraso wurin shi tana gaida shi ya amsa shima dauke da murmushi afuskarsa yace bari inje ana jirana murmushi tayi tace AHMAD ko?? yace eh sannan yafara sauka har yakai kasa tace yaya kace mashi...se kuma tayi shuru kanshi ya dago ya kalleta yace ince mashi kina gaidashi ba??fuskanta ta rufe da tafukan hannayanta 🙈ta shige bangaranta shikuma ya wuce yama grany sallama daga nan ya nufi wajan motocinsa guards dinsa suna ganinsa suka tashi tsaye yadubi wani daga cikin su yace yahya bani makullin atare suka hada baki but sir !!!!
Fuska ya hade yace just give me the key Wanda aka kira da yahya ya mika mashi makullun ya karba naga ya nufi wata dakkareriyar Jeep baka se sheki takeyi ya fice daga gidan ahankali yake tukinsa kamar mai koyo har ya iso life camp akofar wani katafaran gida naga yayi parking mai gadin ne ya liko ya ganshi yace ah yallabai yafara kokarin bude get din ABID yace no barshi sauri nake yanzu zan fito kai tsaye cikin gidan ya nufa tare da sallama ya kutsa kanshi cikin palon wata matace ta amsa sallamar tana ta kokarin shirya abinci a dining Da murmushi ya karasa dining din yaja kujera ya zauna kana ya dago ya kalleta yace momy ina kuana bata dago ta kalleshi ba bare ta tankashi Shima kuma bai kara cewa komai ba Ya bude kula ya fara zuba soyayyan dankali da pepper soup yafara ci seda ya gama kana ya leka kitchen din ya iskota tana loda lemu a frig daga kofan kitchen din yace momy zan wuce se a lokacin tace toda wa yarikeka?? Murmushi yayi baice komai ba yafita daga palon wani bangare naga yanufa acikin gidan yana zuwa yatura kofar palon ya shiga babu kowa hakan yasa yawuce bedroom karasawa yayi kusan gadon tare da yaye bargon yana fadin AHMAD!! Ahmad ya gyara kuanciyarsa tare da Jan bargo ABID ya janye bargon gaba daya yace malan dallah tashi kai ko kunya baka ji tun baccin jiya har yanzu bai isheka ba Cikin murayan bacci Ahmad yace AK wai miye haka da sassafe kazo gidan mutum kahana shi hutawa ABID ya katse shi kai dallah tashi lokaci ya kure mukadai ake jira Tashi Ahmad yayi yana gunguni yanufi toilet ABID yace wai me kama Momy ne ?? Ya juyo ya harereshi da jajayan idon shi na bacci yace Ohoo!! meyasa baka tambaye taba yashige bayi ABID ya girgiza kai ya mike yaje drowan Ahmad ya Ciro masa kananan kaya wando baki da riga milk color bayan Ahmad yafito wanka ABID yace kashirya zan jiraka awaje kuma wallahi kadade kazo kaga bana nan Ahmad yace dadin abun dai Nima inada abun hawa ABID ya wuce ya barshi atsaye yana kallon kayan dake kan gadon
Chapter 3 · 0% Book details