← Book details Domin Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 84

Sashe 14

Domin Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ahmad ne yashigo bangaran grany da sallama dawke abakin sa grany ya isko apalo tana zaune AK kuma ya zage yanata shirya abinci a dining dariya ahmad yayi yana nuna AK da hannu yace
wanake gani haka kaman AK grany??
yau kuma sarautar kice ta motsa kika hana AK zuwa office kika tura bawan allah kitchen??
Grany ta tabe baki tace babu sa hannuna awannan rashin aikin yi waifa yaran nan yazage yana ma hidima ga masu aiki yabarsu suyi wai shi yafiso yayi dakanshi se kace wani kuku
Ahmad yazauna yana fadin wa'yanne yara kuma grany ? Grany Tamaka mai harara tace kai karka rainamun hankali mana ayshan ce baka sani ba ko kwa ita budurwan taka sarah nasan zakayi mamakin ya akayi nasani ko
To dazu AK yake gayamun kuma yace wai tare zaku hada bikinku shine nace Abu yayi kyew ai gara kuyi auran kowa ma yahuta
Ahmad dai tunda grany tafara magana idonshi ne kawai akanta amma hankalinsa na wani wurin tunani yake na gaskiya fa akwai babban aiki agabansa yanzu ya zaiyi da Sarah taya zaima AK bayani yasan ayanda AK ke bala'in son Sarah ba lallene ya fahimce shiba
shi kuma ko Ana ha maza ha mata bazai rabu da fliyng Bird dinshi ba
maganar grany ne tadawo dashi hayyacin sa kallon ta yayi yace na'am grany
Grany tatafa hannu tana salati tace badai kana nufin duk surutun nan nikadai nayi shi ba ahmadi
Ahmad yamike yana murmushi yace najiki mana grany kidai tanadi maganin hawan jini Dan naga abun zai maki yawa kishiyoyi biyu lokaci guda
Grany ta tabe baki tace Allah na tuba dawa zanyi kishin
Mata kamar asuwaki ni wallahi kunma bani kunya duk gayun nan naku da haduwar Ku amma kukare akan wa'incan sandunan Ku gaku da kumari amma matan kamar masu ciwon kanjamau
AK ne yafito daga kitchen rike da jug din Ginger jus yanufi dining yana fadin ya isa haka grany tunda kikaji zancan auran nan kika tasa yaran nan agaba se figesu kike inace dai mu muka gani munaso kuma mu zamu zauna dasu ke naki ido ne se kuma addu'ar zaman lafiya dazaki rika yimana

Grany tamike tanufi daki tana fadin a'ah ABIDI yi hakuri abun baikai haka ba nayi shuru daga fadan gaskiya ai su Kansu matan sunsan kunfi karfinsu Dan Sam Baku dace ba Mata sekace ........
AK yabuga kafa da kasa kamar zaiyi kuka yace Gany please!!!
grany tasa hannu ta toshe baki tare da wucewa ciki Ahmad dai banda dariya ba abunda yake
AK yaja tsaki yace Kai har kaga abun dariya anan Allah intana fadan haka se duk inji badadi dama can bason auren nan nake ba ni bansan meyasa ba duk zumudin da akefadin angwaye nayi ni Sam bana jinshi
Ahmad yamatso kusan AK cikin sanyin murya yace AK inaso zamuyi wata magana Mai mahimmanci dakai kuma.....
AK yakatse shi tare da fadin no Ahmad bamada lokacin magana yanzu jirgin su ya kusa sauka kabari daga baya zamuyi maganar wata kula yanuna mashi yana fadin bani kular can naga miye aciki? Ahmad yadawko kulan yana fadin bakai zuba abincin bane AK yasosa Kai yace nine amma namanta mena saka aciki
Ahmad yabude kular tare da tintsirewa da dariya🤣 yace Kai waya gayamaka anasa salad a kula AK ya hade fuska yakwace kular yana😠 fadin to a ina ake sakawa
Ahmad ya kalli salad din yakara sa dariya yace wai yanaga yazama hakane kodai dafashi kayi ne
AK yafara cire kwan dake ciki yana fadin bandafashi ba inaga zafin kwan ne yasashi yazama haka can kuma yadago ya kalli Ahmad yace Kai Kama raina mun hankali to ai ko Dan kawye yasan ba'adafa salad Ahmad ya tsiyayi jus akofi yasha sannan yace kaidai Ina rabaka da aikin daba nakaba abun ai ba daga waye bane kofin ya ijiye sannan ya kwalama Mai aiki Kira tanazuwa yace am... Rebeka kidan kwashe kayan nan ki gyara zamuje mudawo yanzu ta amsa DA yes sir
Shidai AK yana tsaye baice komai ba Ahmad yaja hannunsa yana fadin muje mushirya se muje mudawko su AK yabi bayansa kamar wani karamin yaro wayar shima yaketa dannawa har saida sukaje bangaran shi sannan Ahmad yasakemai hannu ya wuce toilet koda yafito AK yaciro musu kayan dazasu sa kananun kaya ne masu tsada Ahmad nafitowa AK yashiga kayan sukasa sunyi masifan kyaw kaman yan biyu haka suka sawko kasa uncle jamilu ne kawai akasa yana karanta jarida bayan sungaidashi kasakasa ya amsa gaisuwar Ahmad
Suna wucewa Ahmad ya matso kusan AK cikin rada yake fadin wai shi wannan tsohon kuana biyu bana ganinsa a company konaje office dinsa arufe yana bala'in wasa da aiki amma wata nakarewa shi kake fara ba albashi ashekarunsa yanzu yaci ace ya daina aiki amma wai.......
AK ya katseshi dafadin Ahmad shut up!!
Ahmad yayi shuru tare da juyowa yakalli uncle jamilu carab suka hada ido dama suna wucewa ya sauke glass dinsa yabi Ahmad da kallo
Murmushin yake Ahmad yamishi tare da daga Mai hannu shidai uncle jamilu se binsa yake da kallo har suka fita kana yamaida idonsa kan jaridar dake hannunsa

Suna isa jirgin su Sarah nasauka dagudu suka zo suka rungume AK rumgume su yayi yana dariya Sarah ta juyo da nufin rugume Ahmad yayin saurin jan trolley dinta yana fadin kuzo muje nasan kun gaji Sarah bata damu ba suka bi bayansa suna tafe suna fira banda Ahmad da se ba'a rasa ba yakesa baki
Suna isa bangaran grany suka nufah bayan sun gaisa grany tawuce daki Dan ba inuwa daya suke shigaba
Wurin dining suka nufa suka AK yaja ma aysha kujera tazauna tare da fadin thank u Sarah tayi tsaye tana jira Ahmad yaja mata kujera taga yazauna baida niyyan kallon inda take baki ta zuburo taja kujera tazauna suka fara cin abinci
AK ne yadago yakalli aysha sukayi ido biyu murmushi yayi yakashe mata ido tare dafadin miss you baby
Murmushi tayi itama tace miss you too duk abunda suke Sarah DA Ahmad na kallonsu Ahmad naganin Sarah tajuyo zata kalleshi yayi saurin sadda Kai
baki ta zunburo cikin muryar shagwaba tace wai ni kan yaya kayi missing dina kuwa AK yayi saurin juyowa yace nayi missing dinki mana kallonshi tayi ta nuna Ahmad tace bakai ba shi AK yayi murmushi ya kauda kai yana fadin ok to kirinka banbanta sunan tunda shi sauranyiki ne kisa masa wani sunan
Ahmad yamike tare da fadin nizan wuce Allah huta gajiya ganin Sarah tamike da nufin binsa yayi saurin am...AK muje kadan rakani mana AK yadago da loman abinci abakinsa yace ban gane in raka kaba kai bako ne Ahmad ya langwaba Kai yace kazo mana akwai maganar dazamuyi AK yatashi yana fadin Kai wallahi ka iya katsema mutun jin dadinshi

suna fita aysha ta kalli Sarah da mamaki afuskanta tace wai ya naga kaman Ahmad yana avoiding dinki ne Sarah ta zauna jiki asanyaye tace Ashe kema kin Lura ko?
aysha ta tabe baki taci gaba da cin abincinta

Seda Ahmad yashiga mota yadago yakalli AK yace AK gobe muhadu a office Ina so mu tattauna wata magana AK yaleko ta window yace haba Ahmad be a man mana nasan akan zancan auren nan ne duk kadaga hankalinka don't worry ni zanyi komai kuma ba dogwon lokaci za adauka ba yana kainan yajuya yana fadin se munyi waya
Ahmad yadaki stiyarin motar da karfi ya dafe Kai shi yanzu ya zaiyi afili ya furta Kai Ina!!! dasake wayanshi yadauka ya lalubo numban khadeeja bugu biyu ta daga tare da fadin Tarzan ya akayi Ahmad ya jingina jikin kujera ya lumshe ido yana fadin flying Bird kina Ina ne khadeeja takalli Asma'u da takafeta da ido tace Ina gida lafiya ?? Ahmad yatada motar tare da fadin gani nan zuwa khadeeja ta tashi azabure tana fadin gaka nan zuwa Ina? mema zakazo yi ?
Ahmad bai jira tagama magana ba yakatse wayar khadeeja ta juyo ta kalli Asma'u tana murmushin yake Asma'u takauda Kai taci gaba da aikinta khadeeja tazo kusanta ta zugunna tace ammah yazanyi tunda naji yace zaizo to Abu Mai mahinmanci zai kawoshi gashi Umma bata nan bata Masan da alakar muba
Asma'u tamike tana fadin idan yazo kije in Umma tadawo Zan Mata bayani amma kiyi ahankali ni soyayyar nan taku tsoro take bani duka duka KO sati bakuyi ba da haduwa amma kamar kun shekara tare kuma tun rashin kunyar da kika mishi yafara binki ni hankalina ya ki kunciya Anya bayada wata boyayyar manufa akanki kuwa khadeeja kinsan masu kudin nan basuda tabbas juyowa tayi tadawo wurin khadeeja tare da rike hannayanta duka biyu cikin sanyin murya tace khdy dan Allah ki kula da kanki ki tsare mutuncin ki kar kudi yarude ki kiyada tarbiyar da Umma Tasha wahala tabamu ba wai ban yarda dake bane a'a nasan kinada hankali kinsan Abu Mai kyew DA mara kyew amma shi Dan Adam Tara yake bai cika goma ba hawaye ne suka zubo a idonta tace khadeeja idan wani Abu yasameki mutuwa zanyi zuciyata bazata iya dauka ba
Da sauri khadeeja
tafada jikin Asma'u tafashe da kuka mai sauti Asma'u ta rungumeta tana shafa kanta cikin sheshshekar kuka khadeeja kefadin shi kenan ammah Allah nabari bazan Kara kulashi ba koda sonshi zaikasheni idan kikace bai maki ba Allah bazan aure shiba Asma'u ta dagota tana goge Mata hawaye tayi murmushi tace khdy bance bana son Ahmad ba duk abunda kike so nima Ina sonshi kawaidai Ina jin tsoro ne amma Zan sameshi muyi magana nakara bashi hakuri akan abunda kika masa kinga daganan se hankalina ya kuanta karar wayan khadeeja ce takatsesu
jiki asanyaye khadeeja tadaga Ahmad yacemata gashi akofan gida Asma'u tayi murmushi tace tashi kije amma karki dade kinga Umma batanan tashi tayi ta fita bata ce komai ba
Chapter 14 · 0% Book details