← Book details Domin Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 84

Sashe 27

Domin Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kuka tafara tana fadin wallahi batawa bace nima seyanzu naganta anan dan Allah kasaurareni

Kiran ogansa yayi ya nuna mashi nan take yabada umarnin ayi arresting dinta

Karasowa yahaya yayi yana rokon sukyaleta yasanta wannan ba sana'arta bace yarinyar yar gidan mutunci ce

Sunkuy dakanta tayi data tuna karyan datama yahya kenan dama yaganta awurin shiyasa yakirata

Ba rokon da bai musu ba amma sunce sedai yabiyosu office yabada shaida

Tana kuka haka suka tasa keyarta har cikin motarsu

Lekowa tayi tana kallon yahya cikin muryan kuka tace yaya dan Allah kar ka gayama su Umma abunda yafaru dan Allah!!!

AK na zaune da aysha suna fira amma baisan meyasa ba Sam baya jin dadi hankalinsa yakasa kuanciya

Kamar daga sama yahango grany tana zuwa
Azabure suka mike gaba daya suna kallonta har takaraso fuskarta adaure kamar bata taba dariya ba

Cikin kakkawsar murya tace mekake anan

Shiru yayi baice komai ba

Badakai nake ba uban me kake anan tare da wannan mara kunyar

Ina ka kai yar mutane kai yanzu baka jin kunya abid yaushe kazama haka ban saniba

Hannu tadaga da nufin wanka meshi mari daidai nan sarah takaraso aguje tana fadin a'a grany

Dakatawa tayi tana jifanta da wani irin kallo

Sunkuy dakai sarah tayi tace yanzu Yaya yakirani yana cikin matsala ne

Yayi signing contract ne dawani company kuma yau ne zasu gabatar da meeting idan har baijeba zasuyi tunanin ya yaudaresu ne kuma hakan zai jamai matsala shiyasa baisamu damar tafiya ba

Kallon AK grany tayi cikin kakkawsar murya tace ina asma'u

Sunkuy da kai yayi cikin rawar murya yace tana hotel dazu nabaro wurinta itace ma tabani kwarin guywar yin hakan tace zata miki bayani dakanta tasan zaki fahimta

Juyawa tayi tana fadin muje ka kaini wurinta dan ban yarda dakai ba

bin bayanta yayi suka fita

Ajiyar zuciya aysha tasauke tazauna kan kujera tana fadin natsani yarinyar nan

Tsaki sarah tayi tana hararanta tace ke bazaki iya hakura da AK na minti biyar bane se kin ruguza mana shiri

Kauda kai aysha tayi tana fadin gwara ni ai...

Suna isa dakin da asma'u take sukaga bata cike da mamaki yatambayi dai daga cikin ma'aikatan wurin shine yake bashi labarin abunda yafaru

Al'amarin ya girgiza shi matuka

Asma'u ce a police station tasasu agaba se kuka take masu tana fadin wallahi batasan komai akan wannan jakar ba

Waya dan sandan yabata yace takira yan uwanta suzo

Karban wayan tayi tana tunanin wazata kira itadai bazata iya kiran Umma ko abba ba

Numban AK takira tana ringing baidagawa

cikin muryan kuka tace ina kira baidagawa

Dariya yayi yace saurayinki ...

Kauda kai tayi tace mijina dai

Yasunan mijinki ...

Konafada bazaka yarda ba

Saboda me koshima dan safaran kayan mayen ne

Girgiza kai tayi alaman a'a

Koshine wanda muka gani a restaurant ...

Nan madai girgiza kai tayi

Ahasale yace to waye

a tsorace tace
AK hausawee

Gaba daya yan sandan suka kwashe da dariya

Seda sukayi mai isarsu sannan dayan officer din yace yallabai kila kowani AK din take nufi

Fashewa tayi da kuka tace shidai wanda kuka sani wallahi shine mijina idan baku yaradaba kuduba social media anyi posting pics dinmu

Dariya sukayi sannan Babban su ya umarci asata a cell idan wani nata bai zoba zai watsata a news kowa yagani

Kuka tafara tana rokonsu amma basu saurareta ba

Umma da khadeeja suna zaune tana tambayarta meke damunta kuana biyu ta sawya

Fa'iz dake gefe azaune yace Umma kila tana kewar asma'u ne

Shiru Umma tayi nadan lokaci sannan tace ni yau inaji ajikina kamar wani nawa yanacikin matsala

Saurin kallonta khadeeja tayi tana fadin Umma duk muna nan waye kuma amatsala

Fa'iz yace to ko asma'u ce

Hararansa khadeeja tayi tace ammah tana tare damijinta ba abunda yasameta

Umma kidaina damun kanki kawai shedan ne kesamaki waswasi

Tana rufe baki suka jiyo sallamar yahya daga waje

Saurin tashi khadeeja tayi tanufi get tana fadin mekuma yakawoshi nan gidan

Lekowa tayi bakin kofa suka gaisa

Sannan yace Umma naciki

Lafiya ....

akan asma'u ne

Saurin fitowa tayi waje tana fadin meyafaru

Dazu naje hotel nahadu da ita to kuma ina nan tsaye sega yan sanda sunzo suntafi da ita

Cike da damuwa tace yan sanda fa kace akan wane dalili suka kamata

Zaiyi magana kenan sukaji Umma nafadin wa aka kama

Murmushin dole khadeeja tayi tace ba kowa

Yahya yamatso kusan Umma yana fadin karya take Umma asma'u yan sanda suka kama

Innalillahi wa inna ilaihiraji'un

Asma'u fa kace yahya a ina

Riko hannunta khadeeja tayi cikin rawar murya tace Umma ki kuantar da hankalinki ba abunda zai sameta bari naje police station din yanzu naji meyafaru

a'a khadeeja shiga ciki kizauna bari ni naje naga ko dagaskene dan ni har yanzu ban yarda asma'u bace

suda sukayi tafiya da mijinta me kuma yahadata da yan sanda
[18/07, 15:04] Hubbey Frd Ameena Kn: Da kyar AK ya lallashi grany takoma gida shikuma ya wuce police station

Asma'u na cikin cell tana kuka fatan ta daya kar Umma tafahimci gaskiyar halin datake ciki

wani dan sanda ne yazo ya fito da ita

Tana zuwa ta isko Umma atsaye da gudu tazo ta rungumeta tana kuka

Rikota Umma tayi tana tambayr ta meyafaru taya tazo nan ina mijinta

Kuka kawai take takasa magana

Jijjigata Umma tayi dakarfi tana fadin asma'u kigayamun meyake faruwa ne

zatayi magana kenan taga AK yashigo office din fuska ahade

Yan sandan sunyi matukar mamakin ganinsa

Cikin kakkawsar murya yace akan wane dalili zaku kamata

DPO ne yace sorry AK banyarda ba lokacinda tace Kaine mijinta

Saboda me ?

bazan iya auren ordinary girl bane

I doesn't judge people by their looks but their character

Juyowa yayi yana kallon asma'u yace meyasa baki gayamusu ke matata bace

Matsowa tayi kusansa tace Nagayamusu amma basuyarda dani ba

Kamar daga sama yaji ta rungumesa tana fadin I am glad u are here

Cikin rada yace ke miye haka

Dagowa tayi takallesa tana mai alama da ido cewa Umma tana kallo

Saurin rungumeta yayi cikin kunne yarada mata

Kindamu da ummanku ni kuma nadamu da grany

Sannan ya dagota yana fadin is ok
I am here
U are safe now

Murmushi tayi tace I am sorry for troubling u

Hannunta yariko yace nagode allah Dana sameki anan

Namiki alkwarin bazan kara barinki ke kadai ba kema kuma kar kikara yin nesa dani kinsan yanda nake sonki idan wani abu yasameki yazanyi
I can't bear it

Rungume juna suka karayi bakinta takai setin kunnensa cikin rada tace

u are over reacting kafitar dani daganan wajan mana

Murmushi Umma tayi tana kallonsu cike da birgewa

Sabanin yahya da abun ya dawre mai kai

Janye jikinsa yayi daga nata yana kallon dan sandan yace akan wane dalili kuka kamata

Jakar yanuna masa yana fadin munsamu wannan jakar akusa da ita kuma drugs ne aciki
Daukan jakan yayi yace yanzu daka ganta ahannuna seka kamani kace ina safarar drugs

Wace hujja kake da ita datanuna jakan tatace

Kasan zan iya yin karar ka akan bata mata suna dakayi

Hakuri suka fara bashi akan basusan matarsa bace shiyasa

Hannunta yaja suka fito daga police station din
Su Umma nabiye dasu

Wurin Umma yazo
Yace Umma meyasa kika zo nan kinsan yanda asma'u tadamu da lafiyarki yanzu gashi kindaga mata hankali ni kuma natsani gabinta cikin damuwa

Naji ance asma'u tana nan ne shiyasa nazo

Hannunta yariko yana murmushi yace Umma ki kuantar da hankalinki asma'u matata ce hakki ne akaina na kula da ita wannan ma dayafaru kaddara ce amma namiki alkawarin zan kiyaye

Murmushi tayi tace ba komai abid nidama nasan bada saninka haka yafaru ba allah yatsare gaba

Ameen yafada yana kallon yahaya yace kamaida Umma gida tana bukatar Hutu

Sallama suka musu yahya yaja motar suka tafi

Cikin siriruwar murya tace I am sorry
Juyowa yayi yakalleta takara cewa
Sorry
Baice komai ba yanufi motarsa

Binbayansa tayi suka shiga tare

Khadeeja nagida hankalinta atashe jin shiru Umma batadawo ba

Fitowa tayi da nufin binsu taga ahmad akofar gida

Daure fuska tayi ta kauda kai kaman bata gansa ba

Karasowa wurinta yayi yana fadin yawwa dama ke nake jira

Ya akayi kasan zan fito

Kawai dai naji ajikina ne

To me yakawoka wurina

Cikin sassanyar murya yace gaskiyanki ne nagane nine mai laifi kuma ina so na gyara kuskuren da nayi

na amince zan auri sarah !!!

She was shocked

Ni dai nasan mace daya nakeso arayuwata kuma bana tunanin zanso wata bayan ke

Juyawa tayi takoma ciki tana danne kukanta

Tana shiga tasaki wani irin kuka mai ban tausayi

Tundaga waje yana jiyota runtse ido yayi yana jin zafin kukanta har kasan zuciyarsa yajima atsaye kafin ya juya jiki asanyaye yabar layin

Seda Umma tadawo tabata labarin abunda yafaru a station tana fadamata tayi farin cikin ganin yanda AK ke kula da asma'u

Shiru khadeeja tayi tana tunanin meyasa AK yake yaudaran kowa kawai saboda kanwarsa

Suna isa gida bangaren grany suka nufa

Tana zaune itada sarah suna jiran dawowarsu

Tana ganinsu tamike tana Cike da farin ciki tanufo asma'u tana fadin

Ba abinda yasameki dai ko meyasa baki kirani ba kinsa nashiga damuwa

Riko hannunta AK yayi yace shikenan grany ba gashi na maidomaki ita ba

Fizge hannunta tayi tana fadin dallah yimin shiru duk bakai kaja ba meyasa baka barta agidaba zaka kaita hotel

Riko hannunta asma'u tayi tace

Grany yi hakuri kidaina mishi fada laifi nane ni nace yatafi wurin aikinsa

Kima daina goyon bayansa dan ba yarda zanyi ba yana kokari wurin aikinsa amma yakasa wurin kula da matarsa

Nadauka idan yayi aure zai canza ashe nayi kuskure

Shidai AK yana tsaye kansa akasa yakasa cewa komai

Ba dole ne yadamu dani ba amma yazama dole yadamu dake amatsyinki na matarsa

Juyowa tayi tana kallon AK tace
To bari kaji nagayamaka idan har kasake maimaita irin wannan kuskuren zan dauki asma'u mubar maka gidan

Kudi dai suna iya karewa daga karshe duk watsewa zasuyi subarka kai kadai matarka ce kawai zata zauna dakai

Sekayi shawara...

Tana kai nan tanufi hanyar dakinta rai bace

Dagowa yayi yana kallon sarah da rinannun idanuwansa cikin wata iriyar murya yace

Yaune karo nafarko da grany ta taba mun magana haka
Chapter 27 · 0% Book details