← Book details Domin Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 84

Sashe 38

Domin Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Girgiza kai yayi yace she is not amma komai zaiwuce dama nasan sarah zatayi abunda yafi haka idan tarasa ahmad

Ruwa tazubomai mai anyi akopi tamikamai

ahankali yakai hannu yakarba yasha sannan yamika mata sauran

Zama tayi kusa dashi cikin siriruwar murya tace karka damu nasan tayi fushi yanzu amma zata sauko daga baya

abunda zakayi shine kasamu wani Wanda kayarda dashi kasan zai iya jure wulakanci daga gareta kuma kasan yana sonta seka....

Katseta yayi da fadin se inyi me wai inhadasu aure ? nifa natsani hade haden nan..

Dawawa tayi gabanshi tazauna daga kasa tana fadin ha'an to kabari kaji mezan ce mana ai bangama ba

Kauda kai yayi yace to inajinki

Murmushi tayi tace yawwa idan kasamu sawrayin sekasan yanda zakayi kahadashi da sarah batare da saninta ba shi kuma kagayamasa idan har yana son kabasa auren kanwarka to seyanemi soyayyarta kafin nan

Juyowa yayi yana kallonta yace to amma miye hikimar yin hakan

Gyara zama tayi tana murmushi tace uhmmm kaga yanzu matukar sarah tana ganin ahmad kawai amatsayin saurayinta to bazata taba hakura dashiba amma idan taga Wanda yake haukan sonta tun tana wulakantashi tana koransa har tafara sawraronsa daga nan kuma bazama tasan lokacinda ahmad zai fita aranta ba

Murmushi yayi yace wow!!! what a brilliant idea chitti

dan kwalinta ta turo gaban goshi tana kauda kai tace ahh dabakaki saurarena ba

Murmushi yayi yace hmmm I am really impressed amma kintaba soyayya ne

Saurin joyowa tayi tana kallonsa tace no bantaba yiba banmasan ya akeyiba

dariya yayi yace shiyasa naganki gaki ga kamarki amma wannan Ali din nagidanku ai nadauka saurayinki ne

" ina ba saurayi na bane cousin dina ne da dai yaso ya aureni iyayenshi suka hanashi

dariya yayi yace kice kema kintaba kwantai shiyasa kika samu experience akan rasa masoyi

Hade fuska tayi tace allah ba kuantai nayiba kawaidai wai suna so ya auri wata yarinyane babanta yanada kudi to daga baya kuma yarinyar tafasa auren

zaiyi magana kenan sukaji anturo kofa
Aysha ce tashigo taci kwalliya tana taunan cingam

Juyowa AK yayi yana kallonta yace ohhh hello babyyyyy!!

Karasowa tayi cikin yanga tazauna kusa dashi tana hura hanci

Kallonta asma'u tayi takwashe da dariya

atare suka kalleta aysha na hade fuska

Daure fuska AK yayi yace ke kinada hankali kuwa me akayi nadariya

tashi tayi tawuce daki tana dariya

hade fuska aysha tayi tace wallahi AK kasakema yarinyar nan dayawa tagama raina mutane

Shiru yayi baice komai ba yana kallonta

Da daddare AK na zaune bakin gado yana danna laptop ga Earp akunnensa yana jin waka se gyada kai yake yana bin wakar

asma'u tashigo rike da coffee dinsa kan bedside drowa tadorashi tana fadin ga coffee dinka nan

Baimasan tanayiba yamika hannu zai dauki wani Abu kawai yajishi cikin zazzafan coffee

Yar kara yasaki yana yarfa hannun cike damasifa yace wayace ki ijiye anan baki gayamun ba

Karasowa tayi tana duba yatsunshi tace bakajiba nace ga coffee dinka anan

Kallon bakinta kawai yake yana motsi amma baijin metake fada
Kuace hannunsa yayi yace dubawan me zakiyi bayan dagangan kikayi dakika kawo ai sekibani ko kigayamun

"Wai bakaji menace bane

"Jiki kawai bawani hakurin dazaki bani

damamaki take kallonsa secan tahangi Earp akunnensa hannu takai tacire Earp din tawuce dressing mirror tana maimaita mishi abunda tafada dazu

Painkiller tadauko takama hannunsa zata shafamai ya kwace yafara shafa ma kansa

bathroom tawuce tayi shirin kwanciya cikin kayan baccinta wando da riga mai dogon hannu

Bayan tagama tafito yana kuance kan gado yarufa da bargo

Tsaye tayi daga gefe tana kallonsa idonsa arufe amma da alamun damuwa afuskansa kamar daga sama taji yace
Malama idan abun kallo kike nema ga TV can ki kunna stop staring at me

Saurin barin wurin tayi tanufi bookshelf( drowan litattafai) din dake jikin bangon dakin daga gefe tana fadin

ina ai ni bana kallo da daddare sedai nayi karatu

Wani storybook tadauko tadawo kan stool tazauna tafara karantawa afili sedaga baya tagane tatsuniyoyin naban tsoro ne

Shiru AK yayi yana kara cusa kansa cikin bargo

Kallonsa take tana kunshe dariyarta tacigaba da karantawa cikin muryan ban tsoro tace

Dazaran yamma tayi se kowa ya kulle kofarsa saboda wannan aljanan tana yawo cikin dare duk Wanda tahadu dashi to yagama yawo

Wannan tsohon yana kuance cikin dakinsa yalulluba dabargo yana karkarwa gashi garin ana wata irin iska mai karfi kamar daga sama yaji ana bugamasa kofa dakarfi .....

Daidai nan grany ta aiko Rebeka da wayan asma'u takamata kawai sukaji bugun kofa

atsorace AK yafito dakansa daga cikin bargo yana kallon asma'u itama adan tsoracen take kallonsa

atare suka juya suna kallon kofa

Dariya asma'u tayi tana kallon AK tace wai yanaga kamar katsorata ne to bari na aje

Daure fuska yayi yana gyara kuanciyarsa yace tsoron me zanji awannen shirmen

cigaba tayi dakarantawa ...

atsorace tsohon nan yatashi zaune jikinshi narawa jin ba akara buga kofan ba yasa yakoma yakuanta can anjima yakara jin anbuga kofar dakarfi ....

daidai nan Rebeka takara kuankuasa kofar

Wannan karon gaba dayan su sunkasa boye tsoronsu

kallon AK tayi tana hadiye yawu tace ABI kaima kaji buga kofar koni kadai keji

tashi zaune yayi yana fadin naji mana to amma waye zaizo awannan Daren

Jin shiru ba abude ba yasa rabeka tatura kofar ahankali ta ijiye wayar kusan TV tafita

ai sunaji anbude kofa asma'u tadaka tsalle tafada kan AK atsorace yaja bargon yarufesu tana kankame dashi har suna musayar nunfashi

cikin rada yace inajin motsi anan dakin

Itama cikin rada tace banan dakin bane Palo ne kuma kamar anfita muje muduba

Ahankali yafito dakansa daga cikin bargon yana bin dakin dakallo ganin bakowa yasa ya sauko ahankali daga kan gadon

Itama tasauko suka nufi kofa

turata yayi gaba yakoma baya yana fadin lady first

Saurin dawowa baya tayi tana fadin to ai kai namiji ne kamata yayi ma kace inzauna kaje kaduba

Wata wahalalliyar dariya yana kara turata gaba yace
to ai saboda naga yawanci nabaya akafi fara cabkewa shiyasa nasaki gaba

wata zungureriyar kwalba tadauka tarike ahannunta dayan kuma tana bude kofar dashi

seda suka dudduba ko ina bakowa sannan taga wayarta akan table

Ijiye kwalban tayi tadauki wayarta tana kallon AK tace kamar wayata aka kawofa

Murmushin yake yayi yana waskewa yace dama ai nasan ba komai kawai ina gwadaki ne naga ko kinada tsoro ashe ke matsoraciya ce

kallon ka rainamun hankali take mai seda yagama sannan tasaki yar kara atsorace tana nuna bayansa

Haba lokaci guda yadaka tsalle se gashi agabanta

Dariya tafara mishi harda rike ciki tawuce daki

Binbayanta yayi yana murmushi

Suna shiga daki yadauke blanket dinta daga kasa yadora kan gado

daukan blanket din tayi tana fadin miye haka malan

kwace blanket din yayi yadora kan gado yace nan zaki kuana yau kina tare mun hanya idan natashi dasafe

buga kafa tafarayi dakasa tana fadin ni gaskiya ban yardaba daacan bakace haka ba seyau dakake jin tsoro

pilulluka yajera atsakiyar gadon ya kuanta yana fadin ga wurinkinan ki kuanta idan ma kina tunanin wuri daya nakeso mukuana

Kuma kika ki allah gobe zan gayama grany gaskiya akan aurenmu

zagayawa tayi takuanta tana zunbura baki

Murmushi yayi yana Jan bargo yajiyo yana kallonta yace chitti

Kyaleni.....
Tafada tana juya baya

[19/07, 17:03] Hubbey Frd Ameena Kn: 📚📚📚📚📚📚
👨‍👧 _DOMUN KANWATA_ 👩‍👧

Na( *Maryam Mhd*)

1⃣1⃣5⃣

Gyara zamansa yayi yana kallonta dakyew yace aysha ni nakasa gane wannan lamari abun yadaina bani mamaki yafara bani tsoro tunda naga AK ya yima sarah haka akan yarinyarnan to tabbas akwai wani Abu atsakaninsu

sadiya tace nima dai haka nagani Abba aysha halin da namiji ne bakisani ba yarinya kar azo garin kallon ruwa kwado yamana kafa tanadin da mukayi shekara da shekaru yazo yaruguje mana muzama yan kallo

Dariya aysha tayi tana tafa hannu tace kai wallahi kun ban dariya ai wallahi ba Wanda zaishiga tsakanina da AK koda kuwa grany ce dakanta bare wata banza wai asma'u

Ku kwantar da hankalinku dady insha allahu wannan dukiyar tamuce mu kadai bawanda zaicita se mu

dariya jamilu yayi harda kyajyatawa yace ai nasanki ya'ta bakya wasa kunsan me duk lokacinda narufe idona kawai jina nake natashi daga jamilu nadawo jamil hausawee

Dariya sadiya tayi tace ni kuma Mr's jamil hausawee

Mikewa aysha tayi tafita tana fadin ni kuma Mr's AK hausawee

ladidi da bashir ne zaune adaki suna fira

ladidi tace wai kai bashir har yanzu ba'abaka albashinka bane

Murmushin gefe yayi yace to in anbani meza'ayi dashi badai inbaki ba

Daure fuska tayi tace kai kar kamun rashin kunya kaji ko wai kai kodan ciwa ciwa da babakere dinnan ma duk baka iya ba company nan fa nakune kabude aljihunka kadiba kudi amma katsaya wasa

Girgiza kai yayi yace a'a mama nifa ba abunda yakaini wurin ba kenan nayarad idan ina son kudi intambayi AK yabani amma bawai insata ba

" yo wayace kayi sata kai kowafa daka gani agidannan tasa ce takawosa kowa soyake yakwasa na kwasa kafin ayi waje dashi

saboda haka kaima kasan nayi gaka jamilu da wannan kinibabbar matar tasa allah kadai yasan abunda aysha ke kwaso masu a aljihun AK

amma kai katsaya wasa to tsaya kaji dazaran AK ya auri aysha to tamu takare agidannan dan wallahi gaba daya kawye zasu maidamu daga ita se iyayanta ne zasu muri wannan dukiyar

yashi yayi yana fadin insha allahu ma bazai aureta ba dan da ace matar nan tasa ta kile irin yan duniyan nan ne to wallahi ko kallon aysha bazai yi ba

tsaki tayi tana binsa da kallo har yafita sannan tace aikin banza ana ga maciji kana ga tsutsa dadin ya'mace kenan wallahi da ameena na nan dayanzu ta taimaka mun ga salma tayi Karama bata San komai ba ...

sarah na kuance kan gado da photon ahmad ahannunta tana kallo idonta sunyi ja sun kunbura tun hawaye nazuba har sun kafe

Tunowa tayi da AK kefadin wai tahakura da ahmad tunda khadeeja zai aura

Wurgi tayi da photon tafara wawwatsa kayan dakin tana fadin ina bazai yuwu ba sedai idan bana raye bawacce ta isa ta auri ahmad seni

Kwalba tadauka tarusa madubin dressing mirror tasulale akasa cikin dasashshiyar muryanta tana fadin

nawa ne nikadai ....ni kadai nake sonshi...kuma ni zan aureshi...inba haka ba zan mutu
Chapter 38 · 0% Book details