← Book details Domin Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 84

Sashe 75

Domin Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Chitti I am hungry ba abunda mukaci tun jiya I can't wait any longer karkije ko ina abinci zan siyomana yanzu indawo kijira inzo yau tare zamuyi breakfast....

Murmushi tayi tana kara maimaita karatun sannan tazauna kan kujeran dressing tafara gyara gashinta tana fadin wannan safiyar tazama dai cikin ranakun dabazan taba mantawa dasuba arayuwata

sarah dabashir ne suka shigo bangaren grany bayan sungaisa bashir yace grany wai haryanzu Yaya shiru

daure fuska tayi tana hararansa tace kai ina kashiga jiya ba'aganka ba dabakataya Ahmad nemansa ba .....

Shafa kai yayi yana murmushi yace grany nifa tafiya nayi jiya munje katsina dawowata kenan sarah take gayamun abunda yafaru

tabe baki tayi tana kauda kai tace ai aikin kenan Kullun kana yawon bin garuruwa wurin yan mata haryanzu ka kasa ijiye mace

Saurin dago aki sarah tayi takallesa sannan tajuya tana kallon grany kamar zatayi kuka tace grany....yan mata fa kikace ...dama karya yake yawani cemun wai bikin abokinsa zaije

Dariya sukasa gaba daya ita kuma ta tashi tana zunbura baki tawuce dakin grany

Kusan grany bashir yadawo yazauna yana washe baki yace grany kinko ga abunda nagani ....kishifa take

gyada kai grany tayi tace nagani mana basiru ai dama nagayamaka sonka take kawai dai halin sarah ne se ahankali amma kowane lokaci tazauna batada fira setaka
[04/08, 17:27] Hassan Atk: zaune suke suna cin abinci suna fira da dariya gwanin sha'awa kana ganinsu kasan suna cikin tsantsar farin ciki ......

dagowa yayi yana bin dakin dakallo sannan yadawo dakallonsa kanta yana murmushi yace chitti inaga kawai zamu zauna anan mugama honeymoon dinmu semu koma gida

Kallonsa kawai take batace komai ba ganin haka yasa yayi wata malalaciyar dariya yana sunkuy da kai yace don't get me wrong ....abunda nake nufi shine ...wato ....

dakatar dashi tayi tana tura mai dankali abaki tace hmmm I got it ...base kamun bayani ba amma kasan baidace muzauna haka kawai batare da su grany sunsani ba .....
dakyar ya iya hadiye dankalin data turamishi saboda yafi karfin bakinsa cikin shakakkiyar murya yace chitti please.... kifahimci halin danake ciki mana ....kefa matatace ....kema kinsan kawai juriya nake amma I can't bear it anymore....nifa ba katako bane dazan zauna damace kamarki kuma ace banajin komai agamedake .....it's not easy u know .....kuma chitti gaskiya inason babies yakamata ace yanzu mun ijiye koda dayane tunda fa munjima da aure ....Ko Yakikace....
Yakarashe maganar yana dan zungurinta dakafa hade dakashemata ido

Girgiza kai tayi tana murmushi ta ture kafarsa sannan tamike tsaye tana fadin nidai gaskiya bazan zauna ba...dan ba abunda zanyi sena sanarda Umma da grany ....

mikewa yayi tsaye yana riko hannunta yace OK I understand zamu tafi amma idan muka sanardasu zamu dawo nan kin amince

Saurin gyada kai tayi tana murmushi tace eh na amince ....
dariya yayi yana janyota jikinsa yace ohh ashedai kema kinaso kikekai kasuwa .....

Duka takaimasa aciki tana zunbura baki yarungumota jikinsa yana dariya yamanna mata kiss agoshi se alokacin tasaki wani lallausan murmushi suka kara rungume junansu so so romantically....

Motar ahmad ce tasanyo kai cikin harabar gidan aguje sani yakaraso yana mika gaisuwa se sunkuy dakai yake iron namarasa gaskiya fuska adaure ahmad yace kai jiya bacemun kayi AK baizo nan ba

Sosa kai sani yayi yana yana kallon bangarenbAK yace yallabai dama shine yace kar agayawa kowa yananan idan nafada kuma nasan sauran shiyasa nayimaka karya ....amma kayi hakuri yanzu haka yana ciki tareda hajiya tunjiya tazonan....

Dakatar dashi ahmad yayi yana fadin c'mon shut up dallah wa yatambayeka sedan banzan surutu mara anfani ...Toni dakamun karyan kadauka zankyaleka ne ...

hakuri sank yafara bashi baikulasa ba yawuce cikin gidan khadeeja kwa har takai tsakiyar gidan ...zasu Shiga kenann suka hadu dasu AK sunfito zasu tafi

Saurin karasawa wurinsu khadeeja tayi tana riko hannun asma'u cikin rawar murya tace ammah are OK.....meyasa baki kirani ba kuma inata kiranki baki dauka ... kinsan halin dakuka jefamu aciki kuwa ....

harara ahmad yawatsama AK yana Jan tsaki yace wai uwar me kuke anan duk kunbi kusakamu adamuwa ko bacci munkasa yi ashe Ku kunanan kuna shan soyayyarku hankali kwance

murmushi asma'u tayi tana sharema khadeeja hawaye tace Ku kwantar da hankalinku komai yayi daidai yanzu ABI yasan komai kuma ya yarda dani duk abunda yafaru seda nagayamasa ban boyemasa komai ba ....khady ahmad ba abunda zancemaku sedai kawai ince nago....

bata karasaba khadeeja takatseta dafadin a'a ammah nagayamaki banaso ....duk abunda anmiki ammah ban cancanci godiya daga gareki ba ....tun ina karamata kike dawainiya dani alokacin kekanki kina bukatar akula dake ....ke kike kaini makaranta kidawo dani kiabni abinci kimun wanka duk wata bukata da ya take nema awajan ubanta ammah ni kinmun ita kafin natambayeki kinsan abunda nakeso ....bayan nagirma ma bakidaina dawainiya daniba ....kinba Umma gudunmawa wajan kula da tarbiyyata sannan kika zabamun mutum nagari amatsayin mijina ...ammah idan har kezaki godemun akan dan abunda namiki tonikuma mezan miki akan abunda kika mun ....

Rungume juna sukayi suna kuka mai bantausayi AK sarkin tausayi harda yan hawayensa lokaci guda yanaji son asma'u nakaruwa azuciyarsa ita kanta khadeeja junta yake tamkar kanwarsa dasuka fito ciki daya ....

Janyo asma'u yayi yana basu hakuri tajuya tana kuka tarungumesa kam ajikinsa kyaleta yayi seda tayi me isarta sannan yadago da ita yana share mata kwalla yaci gaba da rarrashinta ....

ahmad kamar jira yake suyi shiru ya hausu dafada suna gabansa atsaye sun sunkuy dakai suna murmushi dan abunda dariya yake baau yanda yasasu agaba kamar wasu ya'yansa ....khadeeja nagefensa tayi shiru tana kallonsu matsowa yayi kusanta yana mata rada akunne yace deeja yakuma kikayi shiru kefa kika ce idan mungansu zakimusu fada yanzu nafara kuma kinbarni dasu say something pls...
Saurin shiga gabansu tayi tana yarfa hannu fuska adure tace gaskiya abunda kukayi Baku kyewta ba idan mu yarana ne bakudamu dahalin dazamu shiga ba to su grany fa ...bakwa tunaninsu....

Juyowa sukayi suka kalli juna AK yatabe baki yana Satan kallon khadeeja suna hada ido suka kwashe da dariya gaba dayansu harda maifadan

bayan sun gama gaisawa suka zauna anan wurin suna tattauna abunda yafaru cike da damuwa ahmad yace friend yanaji kayi shiru ne ko kana nufin duk abunda suka maka yatafi abanza kome ....

Wani malalacin murmushi yayi yana gyda kai yace ...friend da ace nikadai sukayiwa to inajin zan ita yafemusu kuma namanta amma bazan yafemusu abunda sukama chitti ba ....bazan dauki wannan ba ...yazama dole sudandana kudarsu shi uncle har yanzu bamada wata shaida datanuna tare suke amma aysha da salim ....their will suffer ....

Murmushi khadeeja tayi tace to mezaka musu Yaya....

"Nikaina bansaniab deeja amma tabbas sena hukuntasu amma bari nasan mezan musu ....ahmad kasamomun cikakken address din Baban salim yau zuwa gobe

Damamaki suke kallonsa atare suka hada baki wajan fadin ...mezakayi ...

Murmushi yayi yanufi motar ahmad yana fadin kuzo muje zanmuku bayani amota ....

Dariya khadeeja tayi tana daka tsalle tarunumo asma'u tana fadin wayyo ni deeja zanyi farin gani ranarda aysha zata fita daga rayuwarku ...kuma kuzama tamkar kowane miji da mata ....

dariya ahmad yayi yabi bayan AK yana fadin nima zanso ganin su aunty na soyayya ....

Haka sukacigaba da tsokanarta har suka iso wurin motar tayi saurin fadawa baya tana rufo kofar dakarfi.....

langabe kai khadeeja tayi tana kallon ahmad tace Tarzan kabani makullin yau nizan tuka ....

atsorace ya juyo yana kallonta yace deeja kinmanta abunda kika mana ranan ne baki kwareba taya zanbaki kituka ...

Buga kafa tayi dakasa tana zunbura baki cikin sigar shagwaba tace kai sweetheart kaifa kace zakabani ...kuma aiyanzu na iya ....tarzan today is a happy day kabani nadan tuka mana ....

shagwabar tace tarudesa badan yasoba haka yayi shahada yamika mata makullin jiki asanyaye yazaga yashiga ita kuma harda dan tsalleta tafada driver sit tazauna se washe baki take tana kokarin tura key amotar su AK dasukayi nisa asoyayyarsu se aloacin suka lura da ita atare suka zaro ido suna fadin waye zai jamu....

Murmushin yake ahmad yayi yana nuna musu khadeeja dayatsa yace .....deeja ce

saurin fita AK yayi amotar asma'u tabi bayansa khadeeja kamar zatayi kuka taleko ta glass tana labace baki tace Yaya miye haka ....meyasa zaku fita
Karasowa yayi jikin window yana kallon ahmad ahmad yace friend yanaga bakada niyyar fita wallahi karufama Lanka asiri kaikadai momy tahaifa haka kawai kaje ka kashe kanka abanzar bazara ba....

baikarasaba khadeeja ta katseshi dafadin kai Yaya kai Yaya....yanzu dama baka yarda daniba har kake tunanin zan kasheka ....yanzu kema ammah bazaki Shiga ba ...danasan ban ita kuma kunsan bazan daukekuba saboda banason abunda zai cutar daku

Karasowa asma'u tayi tagefen ahmad tana fadin dagaske ne khay ta iya driving kuma yaushema tafara koyo a ina ....

Kallon khadeeja yayi yaga dap take datafashe dakuka shikuwa yanda yatsani mutuwarsa haka yatsani ganinta tana kuka juyowa yayi yana kallon asma'u cikin dakewa yace eh mana ta iya ....kuma ni nake koyamata dakaina

tsaye sukayi suna tunani nadan lokaci sannan da kyar asma'u taja jiki tashiga motar...... AK badan yaso ba yafada motar yana bismillah dan har lokacin baigama yarda dazancan ahmad ba

Shikanshi ahmad seda yashafa addu'ar kafin tafigi motar aguje suka fita daga gidan ....

Gaba daya mutanen gidan suntaru apalo ana fira banda aysha da abun duniya ya isheta tarasama ta ina zata bullowa lamarin uncle jamilu nagefe arakube kamar maraya sefaman sauke ajiyar zuciya yake saboda dunbin damuwar data dabaibayeshi gashi baida ko sisi alba'shin ma asma'u taragemasa rabin kudin saboda rashin kwazonsa wurin aiki grany dasarah kuwa kofa ce kawai suka zubama ido suna jiran karasowar AK suji meyake faruwane tsakaninsa da asma'u shine kawai damuwarsu ....

aguje motar tashigo gidan wurin parking ma seda tabugu dasauran motocin gidan shiru bawanda yafito amotar na tsawon mintuna kafin AK yafito aguje yafara kwara amai saurin karasawa wurinsa asma'u tayi jiri nadibarta tadafe masa kai tana mai sannu seda ya amayar da kap abincinda yaci dazu sannan yamike dakyar yana runtse ido yace chitti kibani ruwa
Chapter 75 · 0% Book details