← Book details Domin Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 84

Sashe 35

Domin Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

AK yana tura kofar palonsa yafara tuna asma'u kujeran da take bacci yakalla yatuna lokacinda yake tashinta da sassafe ya hanata bacci

Kauda kai yayi yawuce daki yana shiga ya hango blanket dinta aninke akan gado murmushi yayi da yatuna draman su tajiya

Zama yayi bakin gado yacire hularsa yana tuna lokacinda takemai dariyar bai iya sa hula ba

Saurin tashi yayi yanufi bathroom yana fadin mema yasa nake tunaninta

Umma nazaune apalo itada inna kasancewar sundawo nan gidan dazama

Cike da damuwa Umma tace inna wai kin aiki khadeeja ne

Inna ta tabe baki tace inafa zan aiketa da wannan daren yarinyar dako darana na aiketa setaga dama takezuwa

Shuru tayi nadan lokaci sannan tasauke ajiyar zuciya tace ni wallahi yau naji gabana na faduwa asma'u nayawan fadomun arai gashi bansan inda khadeeja tajeba rabona da ita tana wurin su Ummi kuma fa'iz yace tun dazu tabar can

Inna tace kikira asma'u mana kiji ko suna tare tunda dai khadeeja ba inda take zuwa da daddare

Daukan waya Umma tayi takira numban asma'u

Su sarah na zaune apalo sukaji waya na ringing

Dauko wayan aysha tayi tana fadin kinga mutuniyar ki tabar wayanta

Kauda kai sarah tayi tana jan tsaki

Aysha tayi dariya tace ba dai ummanta ce lagonta ba to bari mudan buga game

Daukan kiran tayi tana yamutsa fuska

Umma naji andaga kiran tace asma'u ya kike
Tundazu khadeeja tafita bata dawo ba kuna tare ne

Murmushin mugunta aysha tayi sannan tace ba asma'u bace

Da mamaki Umma tace to waye ina asma'u

"Kina magana da aysha

Karkidamu asma'u tana nan zuwa wurinki saboda mijinta ya korota daga gidansa

Kedai inaga bakiyi dacen haihuwa ba yarki khadeeja ma tagudu da saurayi yanzu haka suna tare da ahmad tasa yafasa auren sarah
ga babbar miji ya korota cikin dare
Ta kare maganar tana kwashewa da dariya ....

Nan take jiri yafara dibar Umma zama tayi akan kujera ta dafe kai tana salati

Dafata inna tayi tace lafiya meyafaru
Cikin rawar murya Umma tace inna kinji wannan yarinyar aysha tana mun maganar banza wai Abid yasaki asma'u kuma wai khadeeja sun gudu da ahmad

Salati inna tayi tana fadin anya kwa wannan yarinyar da gaske take nifa banyarda ba

Tashi Umma tayi tana yafa gyale tace inna ana karya da maganar saki ne kuma idan bahaka ba ina khadeeja take nakira wayar ta yafi akirga amma akashe ni gaskiya zanje naga asma'u

Hanyar fita tanufa tana fadin baiwar allah nasanta da zurfin ciki yanzu haka tana tunanin halin dazanshiga shiyasa taki zuwa

Binta inna tayi tana fadin ina zakije cikin wannan daran ki...

Bata karasa ba kawai taga Umma tayi baya tafadi kasa asume

Da gudu takarasa wurinta tana salati tashiga kwala ma Abba kira
aguje suka fito su duka aka nufi asibiti da ita

Fa'iz da baisan meyake faruwa ba ya kira wayar asma'u jin ba adauka ba yakira ta grany ya gayamata Umma ba lafiya tagayama asma'u

Sannan yafara Neman numban khadeeja amma akashe

Asma'u na is a gida tahadu da nusaiba abakin get nan tagayamata labarin da daga mata hankali

Ko gidan bata Shiga ba aguje tanufi asibitin akafa tana rera kuka 😭

ahmad yanata surutunsa khadeeja tayi banza dashi

Kuantar dakansa yayi jikin kujera yana magana shikadai

yace baby yaushe zamuyi aurene

never.....
Khadeeja tafada tana kauda kai

Juyowa yayi yana kallonta yace malama ba dake nakeba tunda kince ba kyasona nima baruwana dake dawata daban nake magana so stay out of it

Daure fuska tayi tace kasan tadi zaka zo wurin aljanar ka meyasa baka ijiyeni agidan mu ba kataho dani

Murmushi yayi yace saboda ina so kisan inada wacce tafiki dan haka kidaina jamun aji

Lumshe ido yayi yana hango khadeeja ranar dayafara ganinta

Murmushi yayi yana shafa kai ahankali ya furta

she was so beautiful like a flower in the garden

Ita dabance acikin mata komai tayi kyew yake mata

Takun tafiyarta daidai yake dakowane bugu naziyata

Idan nakalli idanuwanta yaruwata gaba daya nake hangowa acikinsu

Idan tana magana nakan shagala wajan kallon kyewawan lips dinta har bana iya fahimtar
Metake fada

Idan tayi murmushi jinake kamar nunfashina zai dawke

Idan tana dariya kuma ban kiba nazauna nayita kallonta har tsawon rayuwata

Bantaba sanin ina tsananin sonta ba se lokacinda nafuskanci kalubalen rabuwa da ita

Sunkuy dakai khadeeja tayi tana murmushi dan ko baifada ba tasan da ita yake

Murmushi yayi shima yacigaba dafadin zamuyi aure ta haifamun yan biyu talle da mudi

Saurin dago kai tayi tana fadin allah ya kyewta talle da mudi fa

Juyowa yayi ya kalleta yana dariya yace ke kuma asuwa zaki sakamana baki a firarmu

Kauda kai tayi tana daure fuska dan Sam bata masan lokacinda maganar tafito bakinta ba

Shuru sukayi basu kara cewa komai ba har bacci yadauki khadeeja amma ahmad yakasa bacci yana gadinta

A asibiti kuwa bayan doctor ya duba Umma yace masu zuciyarta ce tabuga zasu mata aiki amma senior doctor din bayanan dole ajira se yazo

Haka suka zauna jigum har asma'u ta iskosu suka gayamata abunda doctor din yace kuka tafara inna na lallashinta gashi annemi khadeeja anrasa

Suna zaune suna jira asma'u se zarya take office din doctor din yana gayamata baizoba sukara jira har safiya tayi shiru

Dasafe grany taja AK sukaje asibitin amma harsuka isa ba ayima Umma aiki ba

Inda tahango su inna azaune tanufa AK nabinta abaya bayan sungaisa Yaje kusan Abba yazauna ita kuma grany tana wurinsu inna

Da mamaki takalli asma'u tace yo kekuma asma'u sekitaho baki gayamun ba haka ake

Shuru asma'u tana sadda kai batace komai ba

Saurin mikewa tayi tanufi doctor din dataga yafito daga office tana fadin doctor har yanzu baizoba

Daure fuska yayi yanufi wani wurin yana fadin malama kinfa dameni sonawa zan gayamaki bai zoba da yazo aida kinganshi ko

Shan gabanshi tayi cikin kakkausar murya tace wai ba kwada tawsayine ??

Tunjiya baiwar allah take wahala amma ko ajikinku ko dabbace yakamata Ku tausayamata bare mace

ko zakaso ganin mahaifiyarka awannan halin

Wucewa yayi abunsa batare dayace kala ba

Durkushewa tayi awurin tana fashewa da kuka mai ban tawsayi tasowa inna tayi takamata tana lallashi

duk abunda suke AK na kallonsu sedai baiji dadin abunda doctor din yayi ba

tashi yayi ahasale yabi bayan doctor din ya cakumo rigarsa cikin daga murya yace mekuke jira ne dabazaku mata aiki ba

Atsorace doctor din yace sorry sir doctor din dazai mata aikine baizoba nakirashi kuma yace karna damesa daga karshema yace in nakara kiransa se yasabamun

Hannu yamika mashi yace bani wayanka

Jiki narawa ya Ciro wayar yayi dialing number yabashi

Seda takusa katsewa yadaga ahasale yace kai wai banace kar ka kara kirana ba wacece ita dazakadameni akanta bazasu iya jira bane ko zan iya hanata mutuwa ne in lokacinta yayi

Runtse ido AK yayi yana shafa kai cike da Bacin rai yace

Kana magana da AK hausawee kuma marar lafiyar mahaifiyata ce wallahi kaji na rantse nabaka nan da minti 30 idan ba'afara mata aiki ba senasa ankulle asibitin nan tunda banga anfaninshiba
Kasan bazaka kula da marasa lafiya ba uban wa yace kabude

atsorace yafara ba AK hakuri

Bai saurareshi ba yakatse kiran yamikamata doctor din yana fadin Ku kaita dakin operation yanzu zaizo

Juyowan dazaiyi yaga asma'u agabansa tana murmushi tana sharan kwalla
Tace

ABI nagode allah yasaka da alkhairi...

Kauda kai yayi yana daure fuska yace badan ke nayi ba

nadauki Umma matsayin uwata ne

kuma naga inna tana kuka ni kuma banaso

To karma kiyi tunanin saboda kene

Murmushi tayi tace duk dahaka ma nagode

Juyawa yayi yatafi baice komai ba

Kusan inna tadawo tazauna tana fadin wai inna ya akayi haka tafaru

Nan inna tabata labarin wayar da Umma tayi da aysha ce sila

ahasale tamike tanufi gidan AK

Da kyar ahmad yasamu mai yasa amotar kana suka baro wurin khadeeja nasa caji kiran fa'iz ya shigo wayar

tana dauka yagayamata halin da Umma take ciki

Asma'u na isa gidan tahadu da sarah da aysha sunfito zasu fita wurinsu tanufa fuska ahade

aysha naganinta tafara dariya tace mekuma yadawo dake ko wayarki kika.....

Bata karasaba taji saukan lafiyayyen marin da yakusa sa tasaki fitsari

Nuna ta tayi da yatsa cikin kakkausar murya tace
wannan kashedi ne idan kika kara irin wannan ni kaina bansan mezan maki ba

Idan ke bakisan darajar uwarki ba to ni nasani kuma wallahi idan wani Abu yasami ummata se nabaki mamaki

Tana kainan tajuya tana fadin banza mara kamun kai

Da kallo aysha tabita tana dafe da kunce har tafita sannan takalli sarah tace wai ni wannan yarinyar zata mara

Motar tashiga tana fadin wallahi sena nuna mata ruwa ba sa'an kuando bane

dayan gefen sarah tazauna tana murmushi tace mezaki mata bayan ta taxi

Tada motar tayi suka fita tana huci tace
badai saboda ummanta tamareni ba to agaban umman nata zan rama marina inyaso tamutu
[18/07, 15:05] Hubbey Frd Ameena Kn: asibiti ahmad yanufa direct khadeeja na gefe se kuka take duk ya gama rudewa ko parking bai gama ba tafita aguje tanufi cikin asibitin

Koda taje har anfito da Umma daga dakin operation tana dayan dakin amma bata farfado ba

Aguje tanufi dakin inna tayi surin riko hannunta ahasale tace

Daga ina kike mara kunyar yarinya ke yanzu bakiji kunyar zuwa nan ba

Rungume inna tayi tana kuka tace inna dan allah kuyi hakuri wallahi bazan kara ba dan allah kibarni inga Umma

Rikota Abba yayi yana fadin zo nan khadeeja daga ina kike meyafaru muna ta nemanki wayanki akashe

Shuru tayi taci gaba da kukanta takasa cewa komai

Shafa kanta yayi yace shikenan yanzu kije gida kuyi abinci keda nusaiba se Ku kawo daga baya mayi magana

tashi tayi jiki asanyaye tafito daga wurin tana sharan kwalla

Karo sukaci da ahmad zai shiga atsorace yace deeja menene yanaga kinfito meyasami Umma

Banza tayi dashi taje jikin mota takifa kai tana rera kuka

dawowa yayi wurinta yana tambayar meyafaru

Daidai nan su sarah suka iso asibitin aguje tanufo inda suke ta matse khadeeja jikin motar tana fadin allah yakamaki munafuka wallahi yau nizanyi ajalinki

Kokarin rabasu ahmad keyi amma yakasa

Kamar mahaukaciya haka sarah tadawo gashi tarike wuyan khadeeja gam taki sakinta
Chapter 35 · 0% Book details