← Book details Domin Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 84

Sashe 81

Domin Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

dago dakai yayi yana kallonta cikin rawar murya yace eh ...wato Sarah yakamata ace munsan inda muka sa gaba ...kingafa kullum kara girma muke lokaci tafiya yake ...nagaji da ganinmu ahaka...wato ina nufin yakamata ace kinsan matsayinki awurina ...akwai abunda najima ina boyewa azuciyata wanda naga yakamata ace yanzu kinsan halin danake ciki .....

Farin ciki ne yalullubeta gaba daya ta tattara hankalinta duk tafahimci inda zancansa yadosa amma bata nuna hakan ba saboda tanaso taji wannan Kalmar daga bakinsa wannan ranar zata kasance dai cikin ranakun dabazata taba mantawa dasuba arayuwarta

Jin yayi shiru yasa takallesa damamaki tace Yakuma kayi shiru bashir kafadamun miye wanann dakake boyewa ....

Kauda kai yayi yana cije lebe aransa yace idiot tafasan menake nufi amma takeso tawahalar dani ...yasan tana sonsa amma yarasa dalilindayasa yake shakkar furta mata yana sonta zuciyara se bugawa take dakarfi ita kwa takafesa da ido ko kiftawa batayi sunyi nisa cikin wani yanayi basuma San lokacinda AK da Asma'u sukazo Kansu sukatsaya ba suna kallonsu

Dakyar yatattaro nutsuwara cikin wata iriyar murya yakira sunanta sarah....!!!

seda taji gabanta yafadi ahankali tadago kai tana fadin na'am suna had a ido tayi saurin sunkuy dakai masa tana wasa dazoben yatsarta

Ajiyar xuciya yasauke sannan yafara magana kamar haka ....

Sarah...ban gayamaki abunda keraina bane saboda awaccan lokacin Sam bana gabanki...am just a friend to u...najima ina jin wani yanayi agame dake sedai ayarintata nadauka shakuwace da soyayya irin ta yanuwantaka ...seda girma yafara zomun naga abun karuwa yake baya raguwa ... banada wani buri daywuce naganki atare dani ...farin cikinki kawai nakeson gani koda hakan nanufin bakinciki awajena idan narufe idanuwa na kenake gani ...kullun kece atunanina ...ko bacci nake kece amafarkina ...daga lokacin natabbatar cewa nayi nisa asonki....sedai kash awannan lokacin nafahimci zuciyarki takamu dason wanina.... Sarah tsayawa baki labarin halin danashuga awanccan lokacin bata lokaci ne ....nayi kokarin cire sonki azuciyata amma abun yacutura Sam nakasa controlling kaina akanki duk lokacinda kika matso kusa dani nunfashina nakusan daukewa ... zuciyata tafara bugawa dakarfi ...inason fito da abunda kecikinta amma bakina seyakasa furta koda kalma dayace fatana kawai dazaki kalli kwayar idona awannan lokacin dakinhangi tsantsar son danake maki ....bayan nagama yankewa kinmun nisa arayuwata kwatsam allah yadawomun dake daga lokacin nayi alkawarin bazan kara yin sake ko kubucemunba ...nayanke shawar gayamaki halin danake ciki koda kwa amsarki bazata faranta raina ba ....sarah I love you with all my heart ...body...and soul kuma zancigaba dasonki har bayan raina ...dama daya zaki bani zan kasance abokin rayuwarki nahar abada....

wasu yan siraran hawayan farincikine suka gangaro akan kuncinta cikin muryan kuka tace bashir meyasa kabata lokaci kafin kasanar dani abunda najima inason ji daga gareka najima dafara Sonka bashir bangayamaka bane saboda...ina tsoron abunda yafaru dani abaya yasake faruwa dani akanka ...bazan iya jure hakan ba bashir saboda banajin zan iya cigaba darayuwa batare dakaiba ....ina sonka bashir ...inamaka sonda baki bazai iya furtashi ba I love you so so so much bashir.....

tapin dasukaji anayine yadawo dasu hayyacinsu atare suka dago cike da mamaki suna kallon AK da Asma'u dake tsaye suna faman tapa musu suna dariya kunyace takama sarah tayi kasa dakai tana murmushi bashir kwa ko ajikinsa aguje ya karasa wurin AK ya rungumosa dakarfi yana jijjigashi yace yaya kaji sarah tace tana sona ...tana sona Yaya...oh am so lucky ....

Dariya AK yayi cike dafarin ciki yace kaga komai yazo adaidai tunda kun daidaita kanku se ahada bikinku danasu Ahmad kawai ayisa gaba daya ....

Kara rungumosa bashir yayi yana fadin ohh sweet kill meoooo ..wallahi Yaya munshirya kawai ayi ai munjima dafahimtar juna kuma ni ashirye nake alqur'an koyauma adaura ....

Duka Asma'u takaimasa dajakar hannunta tana fadin kai waiku meyasa bakwada kunyane ko amazan ma gaskiya kudin nadabanne ....

Dariya suka samata taja hannun sarah suka haura sama sukuma suka nufi wurin Ahmad da fara shirye shirye

Uncle jamilu dake tsaye daga Mesa yana kallonsu idonsa yakada yayi ja jikinsa har rawa yake ga wata zufa datawankemasa goshi se cije lebe yana huci aransa yana fadin yazama dole nadauki mataki akanku danbazaku sakani cikin bakin cikiba kuzo kuna farinciki bazan iya jure ganinku haka ba dolene kuma kudandana bakincikin dakuka sakamu nida ya'ta

[19/08, 06:18] Hassan Atk: Har zai juya tafito daga bayi tana kwasar duguwar wedding gown dinta dake Jan kasa .....

tsaye yayi daga bakin kofa yaharde hannaye akirji yana kallonta da murmushi afuskarsa kokadan batasan yana tsaye ba har takoma bakin gadon tana shirin zama tagansa atsaye suna hada ido tasakar masa wani lallausan murmushi dayaji gaba daya tatafi da hankalinsa saboda baitaba ganin tayi kyau irin haka ba kafeta yayi da lumsassun idanuwansa

yanayin kallon dayake mata yasa tayi saurin sadda kanta kasa cikin sassanyar murya tace yanda kakosa wannan ranan tazo bantaba tunanin zaka bata lokaci haka ba harnafara tunanin kiranka awaya ....

dakyar ya iya tattaro kuzarinsa yakarasa cikin dakin yana fadin chitti kowace amarya ana iskota zaune kan gado amma ke ko irin dan lullubin nanma na amare babu....

Zunbura baki tayi tana nufar dressing mirror tace to mutum yanajin fitsari bazaiyiba ....kuma ma aini ba amarya bace

Rungumota yayi tabaya yana shakar kanshin jikinta hade da lumshe ido yace miye banbancinki da amaren ....muma fa seyau zamu fara rayuwar aurenmu ko kinmanta .....

Juyowa tayi tana fuskantarsa da murmushi afuskarta tace to ina tsarabar amarcina ......

Ware hannayensa yayi alamar babu nantake tahade fuska tana turesa daga gabanta tace nikuma indai ba amun irin nakowace amarya ba to sedai kowa yakuana abangarensa dan bazancan amarci......

bata karasaba yayi saurin Shiga gabanta yana fadin dakata mana chitti ....wasafa nake maki nazo dashi yana Palo muje innuna miki ....

dariya tayi tana kama hannunshi suka nufi Palo seda suka biyu da plate da glass cups sannan suka dawo dakin ....

Sallah suka farayi suka mika godiyarsu ga ubangiji da yakawosu wannan lokacin sannan suka zauna anan kasa kamar koyaushe suna cin abinci suna firarsu gwanin sha'awa ...

dadin nama yakaimata karo tace ABI yakamata ace nacanja maka suna ....
Dariya yayi yace da mai nama zaki kirani kome....

"dagaske fa nake kaga kowa yana kiran mijinshi dasuna mai dadi nasoyayya nima zan fara kiranka da sweetheart....

Girgiza kai yayi yana yamutsa fuska yace banason sunan....
"To darling....
"Gara ma nafarkon....
"To yagaka Mine ...nasan tabbas wannan zai maka dadi .....tayi maganar tana washe baki
Mikewa tsaye yayi yanufi bathroom yana fadin am yours amma sunan baimun ba .....

Bin bayansa tayi sukayi brush din atare tanaci gaba dazano mai sunaye amma kowanne seyace badadi har tagaji dan kanta tayi shiru sedai tana tsaye akansa Sam taki yarda tazauna ....
mikewa yayi daga zaunan dayake yana riko hannayanta yace OK fine....naji kizabamun kowane irin sunane ko badadi zan amsa kinji....

dariya tayi tana kallon yanda yalangabe kai tace wasa nakemaka ABI ....you are always my ABI kuma zakaci gaba dazama ahaka har karshen rayuwata ....
Murmushi yayi yana janyota jikinsa suka rungume juna cikin rada yafurta ina sonki chitti ....

Itama cikin rada tafurta nima ina sonka ABI ....

Ahankali yadago dakanta yana kallon kyakkyawar fuskarta idonta alumshe yana kokarin kissing dinta tayi saurin dakatar dashi tana dora tafin hannunta akan lips dinsa

Saurin bude lumsassun idanuwansa yayi yana shirin magana yaji bakinta anasa cike damamaki yazaro ido yana janyo jikinsa daga nata yakafeta da ido yamakasa magana ....

Wani malalacin murmushi tayi tana cije lebenta nakasa tajanyo wuyan rigarsa yazo dap da ita harsuna musayar nunfashi cikin wani irin salo tace kana mamaki ne ....ko kamanta nataba gayamaka idan lokaci yazo zammaka abunda kwakwalwarka zata kasa dauka ....that time has come handsome....

kallonta yake kamar baitaba ganinta ba cike dafarin ciki yasaki yar surprise dariya yana sa hannayansa yaturata baya tafadi reran akan tankamemen gadonsu ....

cwani fitinannan kallo yake binta dashi yana cije lebensa nakasa yacire rigarsa tasama yayi wurgi da ita tsakiyar dakin sannan yabita kan gadon yana rungumota jikinsa dakarfi sukasa dariya mai nuna tsantsar farin cikin dasuke ciki....

wannan Daren yakasance daraen alkhairi mai kunshe da dunbin farin ciki ga duk family dinsu musamman wa'innan ma'auratan dasukafi kowa farin ciki awannan daren saboda shine mafarin rayuwar aurensu mai kunshe da so dakaunar junansu ....

Se mice allah yabasu zaman lafiya da albarkar aure......

Kamar yadda suka tsara sati daya bayan bikinsu suka wuce honeymoon dinsu inda suka zaga kasashe da dama kuma suka samu isashshen lokacin kebewa da junansu inda alakarsu takara karfi soyayya kuma tasamu gindin zama azukatansu....

Daga karshe suka biya masa mai tsarki dan sauke farali inda kowannensu yazage yanemi bukatunsa wurin ubangiji....

Kashin hamsin na addu'ar AK to bai wuce allah yabar mishi asma'unsa ba dakuma haihuwa masu albarka ....

Bayan wani lokaci.....

Haka rayuwa taci gaba datafiya tare dalokaci arzikin AK da Ahmad sedai ace alhmdlillah dan habaka yake bakadan ba sukuma sun dage wajan taimaka ma bayin allah Abba ma tuni AK yakara masa jari kuma allah ya albarkaci kasuwancinsa inda yanzu sedai ya taimakama wani

Hankalin kowa yakwanta saboda
kowannensu na zaune lafiya da abokin zamansa ...

Aysha ce kawai take dan fuskantar matsala daga wurin kishiyarta wato hafsat amma soyayyar da salim kenuna mata yasa abunda yake zuwa mata da sauki ....

Hafsat tasami karuwar da namiji har wannan lokacin aysha kobatan wata bata taba yiba hakan kuma nadaga mata hankali bakadan ba saboda kullun bata rabuwa da habaice habaice daga bakin Hafsat dan tuni tasan dazancan cikin da salim yataba yimata dakuma dalilin zubewarsa maganar duniya ance bata boyuwa ... sedai bawanda yasan halin datake ciki banda Asma'u da AK dan tadaukesu wasu aminanta dabata iya boyemasu sirrinta kuma sukan taimaka mata da shawarwari masu kuantar dahankali ....

Sarah da bashir ma sunsamu karuwar ya mace inda taci sunan Asma'u suna kiranta Malika ....

Khadeeja ma tana dauke da juna biyu haihuwa yau ko gobe zo kaga farin ciki wurin Ahmad ai ko tsinke baya bari tana dauka matukar yana nan ko fita ma bayayi da kyar AK kejansa sufita shima baya jimawa zaidawo yabarosa saboda kokadan hankalinsa baya kwanciya idan baya kusa da ita....

Karatunta hanata yayi dole tadakatar idan tahaihu setaci gaba wani lokacin setasamasa kuka yake barinta tafita ....

Wata safiya ta tashi da nakuda hankali tashe suka nufi asibiti da ita
Chapter 81 · 0% Book details