← Book details Domin Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 84

Sashe 60

Domin Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

duk inda yake tunanin zaisamu kudin yanema amma ba wani labari mai dadi har wurin grany yaje tabashi rance sema tarufeshi da masifa tace abunda take jiyemasu kenan amma basa gani lokacinda AK kebasu kudi intayi magana se suga kamar bakin ciki take masu yanzu gashi da AK baida kudin gaba dayansu sunshiga matsala

Wurin aysha yazo yace taje wurin AK tace tana son kudi yasan duk inda suke zai nemo yabata

Zaune ta iskosa apalon kasa yana kallo kafin sutafi office

Kusanshi tazauna tana marairaicewa tace AK ......

bata karasaba yace menene .....

kauda kai tayi tace shikenan ma kawai nasan ko nafada ba bani zakayiba

"Kifada mana indai inada meyasa bazan baki ba

"Kudi nakeso akwai abunda zanyi

"to ai sekibari har indawo da yamma ko yanzu banada ko sisi

kukan shagwaba tafarayi tana buga kafa tace allah ni yanzu nakeso idan baka baniba kwa sedai inzubar da cikinnan tunda duk shi yakesa ina son abubuwa

Riko hannunta yayi cikin sigar lallashai yace cmon baby meyayi zafi nagayamaki kidaina cewa zaki zubar da cikinnan banaso badai kudi ba jirani ina zuwa

tashi yayi yanufi bangarensu ita kuma ta gyara zamanta tana binsa da kallo tace ai nasan bazaka rasa kudi ba

yana Shiga ya hadu da asma'u zata fito karo sukaci tayi saurin ja dabaya tana ina kuma zakaje muda zamu tafi yanzu

Wucewa yayi cikin daki yana fadin ba inda zanje yau kije kawai

Bin bayansa tayi har cikin dakin tana kallon agogo tace AK cmon yaufa munada meeting kuma lokaci yakure ka ijiye wannan rigimar taka idan mundawo sekayi

Kuantawa yayi kan gado yana kallonta yace nifa ba inda zaje hutawa zanyi ....dole ne se kinje dani da can dabana zuwa ya kikeyi

Juyawa tayi zata fita yayi saurin tashi zaune yana fadin zanje amma dasharadi

Juyowa tayi tana kallonsa tace me kenan..

"Zaki biyani kudin aikina na yau tun yanzu

wani malalacin murmushi tayi tace ...me kadaukeni ....ai ba haka mukayi da kai ba ....ni bazanyi cinikin kifi aruwa ba

Kuantawa yayi yaja bargo yana fadin to jiki Umma tagaida Aisha ....

Har tajuya zata tafi tasake dawowa wurinsa tana Jan bargon tace fine tashi naji zan biyaka amma se kagayamun mezakayi da kudin

tashi zaune yayi yana hada tafukan hannayansa wuri guda yace lady boss for God sake idan bazaki bani kudinnan ba kitafi kibarni inyi baccina wai ana dole ne

Jakanta ta ijiye kan kafafuwansa taciro kudi masu yawa tafara lissafo masa nasa sebin kudin yake da ido yana tayata lissafin har ta gama Tamika masa ya karba yana sakkowa daga kan gadon yafita cike da farin ciki

Binsa tayi da kallo tana murmushi sannan tadauki Jakarta tabi bayansa tana fadin wannan karfa ya gudu ina nan tsaye

Yana zuwa ya mikama aysha kudin yana murmushi kin karba tayi tana bin kudin da kallon raini sannan tadago tana kallonsa tace banganeba ......badai kana nufin iya kudin dazaka bani ba kenan ....ina maka maganar makudan kudi shine zaka ban wa'innan to inyi medasu

Kallonta yake cike da mamaki sanann yakalli kudin yana fadin wai da nawa kikeso to awurina aysha da dayanzu badaya bane kinga wannan kudin sune kawai mallakina anan gidan suma ko aikin banyiba tamkar bashi nadauko su kuma ke kanki shaidace

tashi tayi tana Jan tsaki ta wuce dakinta tabarshi atsaye rike da kudin juyowa yayi yaga asma'u atsaye tana kallonsa yayi saurin boye damuwarsa yana fadin miye kuma kinwani kafeni da ido ....lokaci guda kinjuyani daga attajiri nadawo faqiri .....go and celebrate

daure fuska tayi tanufi hanyar fita yabi bayanta yanaci gaba da masifarsa

Ganin lokaci natafiya kuma yarasa inda zai sami kudin yasa ya yanke wata shawara bari yayi anfani da sarah yasami kudin cikin sauki

Sarah nazaune Palo tare dasu grany wayarta yayi kara ganin sabuwar numba yasa taki dauka har saida aka sake kira sannan tadaga batare datayi magana ba

Daga dayan bangaren akace sannunki sarah aikinki na kyew kinacikin daula kina jin dadinki kinmanta cewa baki gama biyana kudina ba ko

cike da takaici tace ...bangane mai maganar ba waye

JJ .....akafada tadayan bangaren

Saurin mikewa tayi tamatsa daga gefe tana fadin lafiya zaka kirani kuma ni bansan kudin dakake magana akai ba saboda bakamun aikin da nasaka ba

Dariya yayi irin ta marasa mutunci sannan yace bakin rijiya ba wurin wasan makaho bane .....dama nakiraki ne dan nagayamaki cewa... Nayi recoding duk wayar damukayi lokacinda kika bani aiki kuma ina tunanin lokaci yayi dayakamata AK ya saurari koda daya daga cikinsu ne

Saurin katseshi tayi dafadin no ....no JJ please don't this to me ....idan kudinka ne zanbiyaka amma dan allah kar kamun haka

Dariya yasake yi yace yawwa yar gari kinsan ance mutunci yafi kudi to bawasu kudi dayawa nake soba kawai dai 5M zan karba ahannunki dan indan rage zafi kuma nan da gobe nakesonsu inafata kingane

"What nonsense.... Wane kalan 5M haka mukayi dakai wannan ai shirmene
"Shekenan se nashigo anjima ....yafada yana kokarin katse kiran tayi saurin fadin a'a dakata JJ dan allah karkazo naji zan baka kudin but please Kadan karamun lokaci wallahi yanzu yayana bashida kudi

katse kiran yayi batare da yagama jin mezata fada ba cike dafarin ciki yace yes!!! ga hanya mafi sauki natsaya ina ba kaina wahala da tuntuni ma nasamu kudin

bin wayar tayi dakallo cike da tashin hankali tafara tunanin inda zata sami kudin

jin andafata tabaya yasa tayi saurin juyowa aysha tagani atsaye tana fadin lafiya dawa kike waya naganki atsorace

Kakalo murmushi tayi tana share zufan goshinta tace ba kowa wata friend dita ce

Kureta da ido aysha tayi tana fadin kawarki ce keneman 5M ahannunki ....sarah nifa kawarki ce muna gayawa juna sirrinmu kigayamun meyake damunki inga kozan iya taimakonki

Jan hannunta tayi suka nufi daki sannan tabata labarin abunda yafaru

Shiru aysha tayi tana tunanin tabbas babanta ne ke ma sarah barazana dan yasamu kudin ahnnunta amma bazata so sarah tasan hakan

Dago dakanta tayi tana kallonta da damuwa tace to yanzu sarah yazakiyi .....ko zaki je wurin AK kiga ko zaki samu

shiru sarah tayi batace komai ba dan tasan kana ganin AK kasan bai ijiye dubu 10 bama bare 5M

tashi tayi tafara safa da marwa adakin tana tunanin ta ina zata fara neman miliyan biyar kafin gobe da yamma
[20/07, 18:48] Hassan Atk: 📚📚📚📚📚📚
👨‍👧 _DOMUN KANWATA_ 👩‍👧

Na( *Maryam Mhd*)

1⃣7⃣0⃣

tana shigowa kowa ya mike atsaye aka fara gaidata cike da girmamawa

Seda tazauna sannan kowa yazauna suka fara abunda ya tarasu

Sunkusan shafe awa 2 suna abu daya bayan daya take tuhumar kowanne akan wasa da aikinsu da kuma matsalar dahakan yajanyo wa harkan kasuwancin su

gaba dayansu kai yadau caji har ahmad bata ragama ba bare su uncle jamilu da kowa yatashi magana se yace laifinsa ne saboda shine mai kula da komai kasancewar AK da ahmad basa zuwa kuana biyu

Zuwa wannan lokacin ran asma'u yagama baci har wani ja idanuwanta sukayi jitake kamar tarufe uncle jamilu da duka dan takaici

shikuma ya takure wuri guda se zare ido yake banda kadawa ba abunda cikinshi keyi dan duk yanda yake kallon asma'u ashe tawuce tunaninsa dan gaba daya tambayoyinta sun gama ruda shi

juyowa tayi tana kallon daya daga cikinsu tace Mannir naga anciri wasu kudade masu yawa akan wai zaku dinka bedsheets wa sababbin collections din dazasu shigo .....
Kuma dazu danaje banga wata alama data nuna kuna sababbin dinkuna ba .....ko zaka iya gayamun inda kudin suka shiga

tunda tafara magana yake kallonta da mamaki har ta gama sannan yayi wata yar dariya me dan sauti yana fadin what....ma ni bansan da wannan zancan ba inba yanzu danaji kinfada ba ko lokacin AK yana nan bama fara dinki har sai kayan sun iso munduba sannan zamu San kalan dinkin dazamuyi

Runtse idanuwanta tayi tana kauda kai sannan tajuyo tana kallon jamilu tace jamilu .....

saurin dagowa yayi yana fadin ye....ye....yes ....ma

kureshi da ido ahmad yayi kamar yasani yajuyo suka hada ido ya zabgamai wata uwar harara bashiri yayi kasa da kansa yana kunshe dariyarsa

"jamilu naga sa hannunka akan wasu kayan da aka fitar se dai banga kudaden sun shigo ba ya akayi haka

Handkerchief ya zaro a aljihunsa yashiga goge zufar dake kan goshinsa yana kame kame irin namarasa gaskiya

tsawa ta daka masa tana dukan table din tace jamilu don't waste our time kagayamana ina kudin suka shiga

atsorace yadago yana kallonta cike da takaici jiyake da zai samu bindiga ba abunda zai hana ya bindigeta

lumshe ido tayi tana shafa goshinta cikin murya mai kaman rada tace jamilu ina kudin suke ......ko sun bata ne ....?

saurin gyada kai yayi yana fadin eh.....eh....bata sukayi ....ma

Kallonsa ahmad yayi yana kwashewa da dariya sauran ma suka tayasa dan yanda yayi maganar yabasu dariya

Ita kanta asma'u seda tadanyi murmushi sannan tadakatar dasu tana kallon ahmad tace

Ahmad tsawon wata biyu kenan ba ashigo da sababbin kaya ba inaso cikin satin nan kafito mana da zane .....kar kamanta satin nan nace

Murmushi yayi yace ok ma insha allah dama najima da farawa kawai dai ban karasaba ne

haka sukaci gaba da tattauna yanda zasu magance matsalolin da suka samu kuma sunji dadin yanda take Neman shawarar su akan komai sun yaba yanda takeda kaifin tunani da hangen nesa irin namanya shi kanshi Ahmad ta birgeshi yanda take aikinta cike da kwarewa

Koda suka gama meeting din ita tafara fita sannan kowa yafita suka koma bakin aiki se nuna uncle jamilu ake ana gulmarsa wasu kuma namasa dariya

yana ganin asma'u tashiga office dinta yabita ahasale ya banka kofar yashiga
Bata juyo takallesa ba tawuce direct kan kujerarta tazauna tana fadin shigo mana uncle dama nasan zakazo amma bandauka da wuri haka ba

karasowa yayi kusan table din yana huci yace ke ni zaki zubarma mutunci agaban mutane ....ko dan kinga ina ragamaki.... to bari kiji hawainiyarki ta kiyayi ramata tun muna mu biyu kidaina shigar mun hanci da kudunduni.....

wani malalacin murmushi tayi tana kirgiza kai tace borin kunyarne kazo zaka mun ....menayi maka nazubar da mutunci .....kawai dan na tuhumeka akan abunda kai kanka kasan cewa ka aikata shi ....kuma kamar yanda natambayi kowa haka natambayeka .....meyasa su basuji haushina ba se kai....saboda kasan ....
Chapter 60 · 0% Book details