← Book details Domin Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 84

Sashe 80

Domin Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"stop it ABI kaje kayi wanka lokaci yana tafiya karka ruguza mana shiri
kokarin kwace kanta take amma takasa saboda riko yamata bana wasa ba seda tagaji dan kanta tahakura tayi lamo akirjinsa tana maida nunfashi cikin sassanyar murya tace ABI kana ganin bawata matsala nidai tsoro nakeji .....

hannu yasa yadago dafuskarta yana kallon cikin idanuwanta damurmushi afuskarsa yace don't u trust me....

"I trust u but....

yatsansa yadora akan labbanta yana girgiza kai yace to banason jin komai idan har kina tare dani banada sauran wata fargaba nasan komai yakusan zuwa karshe dayardar allah ......

murmushi tayi tana maida kanta kan kirjinsa tace ina sonka ABI....

"nima ina sonki chitti ....

karan buga kofa ne yakatsemasu nishadinsu atare suka kalli kofar kafin yayi magana khadeeja tace wai ance ana kiran Romeo....

dafe goshi AK yayi yana buga kafa dakasa kamar zaiyi kuka yace ohh ni yazanyi da deeja ne ...bazata taba barinmu muji dadi ba

dariya Asma'u tayi tanufi kofar tana fadin aurar da ita kawai zakayi muhuta .......
[15/08, 18:05] Hassan Atk: Bayan akai aysha dakinta kowa yawatse aka barta ita kadai tana zaune bakin gado har wanann lokacin kuka take duk da tana jiyo motsin mutane daga waje amma bata damu datasan kosuwaye ba

(gidan mai kyau bangare biyu daya Asama daya kuma akasa se Babban palon kasa da kitchen da dining area bangarenta ne asama Palo daya se dakuna biyu da dan karamin kitchen dinta ko ina yasha ado ankayatashi dakaya na alfarma gadonta kawai abun kallo ne tana gaminsa tasan daga company su AK yake harda kujerun palon da komai nabangarenta AK ne yayi )

tana nan zaune har dare yafarayi can bayan sallar isha'i taji anturo kofar ahankali kanta akasa batadago ba natsawon lokaci jin ba alamar motsin mutum yasa tadago kai ahankali tana kallon salim dake tsaye abakin kofar yana kallonta fuska amurtuke tamkar bai taba dariya ba itama daure fuskar tayi tana kauda kai aranta tace duk abunda yakoroka to atsaye ya iskoni dan kome kake ji nafika jinsa ...nakama nafila ne akan nawa

takowa yafarayi cikin dakin har ya iso dap da ita ya tsaya fuska ahade yace urban was yahanaki daukan kirana ...meyasa kika amince da aurena ...wato kinyi kwantai awajan AK asirinki ya Tonu shine ni aka jangwalamun ke ko...

cike da mamaki tadago tana kallonsa fuska adaure tace wane kalan shirmene wanann salim...ni kake gayawa haka...ko shayeshayan dakasabayi ne kaje yauma kayi adaren aurenka ....

Bata karasa maganar ba taji saukan lafiyayyan mari atsorace tadafe kuncinta tana dirowa daga kan gadon tace yau nikamara salim ...adaren farkona zaka dauki hannu kamareni...how dare you ...

afusace yadamko kafadunta yanakafeta da manyan idamuwansa cikin kakkausar murya yace kigode allah kafin kizo na gidan nahuce abunda kamun amma dani kaina bansan iya abunda zammiki ba ....bansan meyasa kika amince da aurenaba amma kisani ...kinyi Babban kuskure aysha... idan ma kina tunanin ina sonki ne then u are mistaken...salim din dakika sani ada bashine nayanzu ba idan nace inajin sonki azuciyata nayi karya....

Saurin dago kai tayi tana kallonsa da jajayan idanuwanta dake zubar da kwalla mamaki datakaici ne bayyane afuskarta bakinta narawa tanaso tayi magana amma takasa furta komai

Gyada kai yayi yanaci gaba dafadin yes...bana kaunarki aysha saboda tuni nasamu wacce tamaye mun gurbinki ....kuma ina mai farin cikin sanar dake cewa tare aka dauramuku aure dani ...yanzu haka tana cikin gidannan amatsayin matata kuma abar sona...yakarashe maganar yanasake mata kafaunta hade da nunata da yatsa yace uma bari namiki kashedi ...idan har kikayi kokarin nuna mana bakin halinki anan to wallahi senamiki abunda zaki mutu kina nadamar Sanina arayuwarki ....yana kainan yajuya afusace yanufi hanyar fita haryakai kofa yaja yatsaya batare daya juyo yakalletaba yace idan kingama kukan asararki sekifito munajiranki kuma idan kika batamana lokaci zanzo dakaina nafito dake hakan kuma bazai miki dadin ba kinfi kowa sanina....

tsaye take kamar gunki tana kallonsa hawaye wani nabin wani haryanzu ganin abun take kamar amafarki yana fita ta durkushe awurin tana sakin wani irin kuka mai tsuma zuciya sedatayi mai isarta sannan tamike zunbur tawuce bayi tawanko fuskarta tasauka kasa tana cigaba da share kwallar dake zarya akuncinta

zaune ta iskosu kan 3sitter tundaga nesa takafe amaryar da ido bayarinya bace zasuzo sa'anni kota girmi aysha dakadan ba laifi ita kyakkyawace sedai dagani bakaramar wayayya bace dan ko irin yar kunyar nan ta amare babu tazage se zuba shagwaba take yana biyemata suna ganinta suka daure fuska itama daure fuskar tayi tanemi wuri daga gefe tazauna batare datasake kallon inda suke ba

Tajima dazama kafin salim yayi gyaran murya yafara da addu'a dasauran bayanin da kowane mai gidan keyi arana irin wannan sedai ga dukkan alamu dayar amaryar tasa batasan matsalar dake tsakaninsa da aysha ba dan ko abayaninsabai bari tafuskanci wani Abu ba

Juyowayayi yana kallonta cikin sassanyar murya yace hafsat kece uwargida ko banza kingirmi aysha ...kidauketa matsayin kanwarki ...yar uwarki kuma kawarki ...kikama girmanki seta girmamaki ...ke yar uwatace tajini kuma nasan kinasona kamar yadda nakesonki dafatan zaku hada kanku kubani damar tafiyar dagidana yanda yakamata ....bawacce tafi wata acikinku kuduka matana ne kuma ina sonku zaman aurene yakawoku nan bafilin gasa ba dan haka seku natsu kuyi abunda zanyi alfahari daku ...bazan dauki shashanci agidana ba duk wacce tayi laifi to zan hukuntata daidai da laifinta ....

Juyowa yayi yana kallon aysha yacigaba dafadin ke kuma aysha kece Karama kibata girmanta kuzauna lafiya ..banaso naji wasu kananun maganganu natashi atsakaninku ...nasan zaman tare dole wata rana asamu sabani kafin abun yayi girma kusanar dani kar kusake injiyo labarin matsalarku daga waje niyadace Nafi kowa sanin halin da matana suke ciki ...kudaukeni amatsayin abokinku kuma abokin shawararku ....nima zanyi iya bakin kokarina wajan ganin nayi adalci atsakaninku ....zancan girki kuma duk ranar girki dayarku inaso dayar tafito tayata wasu ayyukan komai kuyishi tare danbana bukatar yar aiki agidana sannan idan angama zamu zauna anan muci gaba daya ...idan har kukayi anfani da abunda nafada to insha allahu zamu samu zaman lafiya da fahimtar juna atsakaninmu ...inafata kunfahimceni....

Shiru aysha tayi kanta akasa batace komaiba Hafsat tagyara zama tana kashe murya tace munfahimceka dear kuma insha allahu zamu kiyaye allah yashigemana gaba ...

Murmushi yayi cike dajin dadin furucinta yace yayi kyew haka ake so yanzu se zancan girki kwana nawa nawa kuke so arikayi

dariya hafsat tayi tace gaskiya ni idan nazaba to zanyi sonkai nabarma aysha tayanke mana ....

atare suka juyo suna kallon aysha dasam hankalinta baya Kansu seda salim yakira sunanta sannan tadago ahankali tana kallonsu se alokacin Hafsat taga fuskarta nan take taji jikinta yayi sanyi dan aysha tafita kyau nesa ba kusaba sedai hakan bazai da tayi masa aguywa ba zatayi anfani da tata kwarewar wajan karkato dahankalin mijinsu yadawo kanta

Cikin muryan datasha kuka aysha tace ni....banada...wani zabi...duk abunda kuka yanke yayi

Kamo hannunsa hafsat tayi tana murmushi tace kaga dear mu bamusaniba kawai kayanke mana ...

murmushi yayi yana shafa kai yace OK...bari mugani...kwana daya daya yayi ko...

zunbura baki tayi cikin muryan shagwaba tace kai dear kuana daya gaskiya ba baiyiba ina laifin biyu biyu ma ....

Dariya yayi yana Jan kumatunta yace dama gwadaki nake dakince bakisani ba yanzu bagashi kinfada ba

Juyowa Hafsat tayi tana kallon aysha cikin sigar tsokana tace amarsu kinji abunda mijinki yace ko wai kuana biyu hakan yamiki

mikewa tsaye aysha tayi tana fadin yayi ...nizanje inkwanta seda safenku ....

Damamaki hafast tace ahh yakuma zakitafi bamuci abinci ba

"Kuci kawai nakoshi....takarashe maganar tana hayewa kan stairs

dakallo suka bita har tahaura sama sanann Hafsat tajuyo tana kallon slim tace dear kamar akwai abunda yake damunta ko

Ajiyar zuciya ya sauke yana janyo ledar dake gabansa yace yunwa nakeji yanzu dai muci abinci dasafe mayi magna

aysha nashiga daki tazube abakin kofa tana fashewa dakuka kamar ranta zaifita tajima ahaka kafin tamike xunbur tadauko wayarta takira numban uncle jamilu bugu biyu yadaga kafin yayi magana yajuyo sautin kukanta natashi hankali tashe yamike tsaye yana tambayarta meyafaru

Tanaso tayi magana amma kuka yaci karfinta se fadin take dady zan mutu bazan iya zama anan ba kazo kadaukeni dan allah .....
Duk yanda yaso tanatsu tamai bayani takasa karshema kashe wayar tayi gaba daya tafada kan gado tana cigaba dakukanta

Hankali tashe yafara saga a marwa apalo yana kiran wayarta akashe jiyake kamar yasa ihu aduniya bawanda yatsana yanzu irin AK da Asma'u yasha alwashin se kuntata musu koda kwa zairasa ransa ne seyarabasu dafarin cikinsu .....

AK da Asma'u nazaune apalo suna kallo tadora kafafuwanta kan cinyarsa yana daddana mata suna firansu gwanin sha'awa

Ahankali yakai hannunsa kan mararta yana fadin ya ciwon mara

murmushi tayi tadora hannunta Kannasa tace dasauki yadaina mun

"Gaskiya abunnan yamun shigar sauri yanzu senakara hakurin kuana biyar ....

Duka takaimasa dakafarta aciki tana fadin shiru dallah ...kayi hakurin tsawon lokaci kuana biyar ne zaigagareka ....nidai bawannan yazancan bikinsu ahmad ne

dariya yayi yana Sosa inda tadakeshi yace bikinsu Ahmad kawai harda namu ai nagayamiki komai tare za'ayi shiyasa nace zamuyi komai cikin kuana biyar kinga kafin lokacin wannan maigadin naki yatafi ...se insamu damar kashe boss da zukekiyar amaryata

Pilo tadauko tashiga dukansa yana karewa dahannu suna dariya har tagaji dankanta tafada jikinsa sukaci gaba dafiransu har bacci yadaukesu ahaka....tana kwance akan kirjinsa yarungumota daduka hannayansa biyu suna sauke nunfashinsu atare kana ganinsu kaga asalin masoya

da dadare kafin salim ya kuanta seda yazo yaduba aysha tana bacci ahankali yakaraso bakin gadon yana kallon yanda take faman sauke nunfashi dagani kasan taci kuka bakadan ba durkusawa yayi saitin kanta yana cigaba da kallon kyakkyawar fuskarta har yanzu yana son aysha sedai yazama dole yamata haka dan gudun kartamasa abunda tayi niyyar yima AK duk adacewa yasan dagaske take sonsa amma ance idan kaga gemun dan uwanka Yakama dawuta seka yayyafama naka ruwan sanyi

Ahankali yakai dan yatsansa yashafo hawayen dake makale agefen idonta yajima awurin yana kallonta kafin yamike yagayara mata kuanciyarta hade darufamata bargo sannan yafita bayan yakashe mata wutar dakin

Washe gari dasafe Sarah nazaune apalon masa bashir yazo kusa da ita yazauna bayan sungaisa tafahimci yanason magana da ita ne cikin sassanyar murya tace yadai bashir kamar akwai abunda kakeson gayamun ko
Chapter 80 · 0% Book details