← Book details Domin Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 84

Sashe 25

Domin Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zaunawa asma'u tayi kusa da grany sukaci gaba da feransu

Inna ladidi ce tafito tazauna asma'u tagadaita

Bayabo ba fallasa ta amsa mata gaisuwar

Sannan take gayama grany sunyi waya da aunty sadiya tace suna hanya yau zasu dawo

Bashir ne yashigo ya zauna daga kasa kusan asma'u yana fadin matar yaya kintashi lafiya

Lafiya kalau tafada tana murmushi

Sannan yajuya yana kashema grany ido yace kin iya zabe nima kisamo mun

Jifanshi tayi da pilo tana fadin kadai karata can akan yan matanka bazan kawo maka yar mutane kakasheta ba

Dariya yayi sukaci gaba da firansu banda inna ladidi datadaure fuska

Da yamma misalin karfe biyar su uncle jamilu suka iso

Bayan sun huta anyi sallan magriba grany ta aika kiransa

Yana zuwa ya gaidata yana washe baki yasan bai wuce zancan auren AK da aysha ba

Sedai ga mamakinsa yaji sabanin haka yafara banbanmi yana masifa grany ta taka mai birki tace yaje ya tuhumi yar'sa ita taki amincewa auren tunda fari dahaka bata faru ba

Ahasale ya banke kofar yafita bangarensa yanufa yana kwalama aysha kira

Tana dakin aunty sadiya tana karban tsarabarta

Atsorace tafara yarfa hannu tana fadin wayyo nashiga uku

Dakin ya iskota yana zuwa yadaka mata tsawa yana fadin wane kalan shirme naji abakin grany wai ke kika ki auren AK hakane

Atsorace tace abba yi hakuri amma ai daga baya nace nahakura amma ya.....
Bata karasa ba taji saukan mari

Dafe kuncinta tayi hade dafashewa da kuka

Saurin rikota aunty sadiya tayi tana fadin lafiya abban aysha yau Kaine da Marin aysha meyake faruwa ne

Fizgo aysha yayi ahnnunta danufin kara mata wani tayi saurin rike hannunshi tana bashi hakuri tace ya tsaya ya saurareta sakinta yayi yana fadin to gayamun meyafaru

Nan tagayamishi cewa grany ce tazaba AK wannan matar amma shi baya sonta ita yakeso kuma har yanzu suna tare yamata alkawarin zancan aurensu yana nan

wani dogon tsaki aunty sadiya taja tana fadin ni dama wallahi najima da sanin tsohuwarnan bason auren yaran nan take ba taga zamu samu abun arziki bari takawo yar uwarta saboda suji dadin cin dukiya to wallahi bata isaba

Girgiza kai uncle jamilu yayi yana cije lebe sannan ya dafa kan aysha yace sorry baby raina ne yabace kinsan yanda najima da borin ganin kin auri AK to kuma lokaci guda naji bai aurekiba ya auri wata can daban kinga ai bazanji dadiba amma dakika mun bayani naji dadi kuma namiki alkawarin idan dai ina raye se mun cimma burinmu

Murmushi tayi tarungumeshi tana fadin ba komai dady

Daganan yanemi ganin matar AK

Suna babban palo tafito tagaidasu aunty sadiya ce kawai tadaure fuska amma uncle jamilu

Da far'arsa suka gaisa har yana tsokanarta wai tayi kama da yan India

Hakan yabata mamaki matuka ba ita kadaiba har grany tayi mamakin yanda tasan jamilu da bakar zuciya taya yasakema asma'u

Koda dare yayi asma'u tahadama AK coffee dakanta takaimasa tas yashanye shi har yana mitar takamasa dan kadan wayasanima ko ita tashanyeshi

Bata kula saba tadauki pilonta da blanket tanufi Palo """

Urs......✍
👩‍💻Maryam Mhd
[18/07, 15:04] Hubbey Frd Ameena Kn: 📚📚📚📚📚📚
👨‍👧 _DOMUN KANWATA_ 👩‍👧

Na( Maryam Muhammad jibril)

7⃣5⃣

Washegari tunda yadawo daga sallar asuba ya wuceta akuance apalo tana bacci hankali kuance ga darduman datayi sallah nan agefe

Har ya wuce daki se kuma yadawo kan daya daga kujerun palon yazauna sannan yadauki remote ya kunna TV
Tana jinshi tayi banza dashi taja blanket tarufe kanta

Kura volume din yayi karshe

Bubbuga kafa tafara yi kaman tafashe dakuka ta tashi tana fadin wai miye haka dan Allah

Daure fuska yayi yace yarinya tunda kika auri dan Babban gida to kinkare da baccin safe
Kuma nan palona ne inada damar yin abunda naga dama aciki

Tashi tayi tana mutsitstsike ido tanufi ciki tana gunaguni

Bayi tanufa tayi wanka tasaka doguwar rigarta ta less mai kyew sannan tayafa gyale tafito

Inda tabarshi anan ta iskoshi yana gyangyadi

Fita tayi batare da tasake kallonsa ba

Yana ganin tafita ya kashi TV yanufi daki yana hamma

Babban kitchen din gidan tanufa
Nan ta isko ma aikata nata aiki abinci kala kala an juyewa akula

Wurin wata dattijuwa tanufa tagaidata

Damamaki matar ke amsa gaisuwarta

Bayan sun gaisa tace baba meyasa ba ajera abincin a dining ne
Tabe baki tsohuwar tayi tace haka suke yan gidan nan sedai aje atambayi kowannensu meyakeso sannan akaimasa inda yabukata

Gyada kai asma'u tayi sannan tafita
Bangaren grany tanufa bayan tagaidata tace grany ni kwa meyasa ba ahaduwa wuri guda aci abinci ne tunda akwai Babban dining table din dazai dauki gaba daya yan gidan nan

Dariya grany tayi tace hakane fa asma'u kinka shawara me kyew kinsan balokaci guda ake tashi agidan nan ba shiyasa amma yau insha Allah zanyi musu magana za'arika haduwa ana cin abinci

Nan tazauna bangaren grany tashari baccinta se Tara ta farka kamar ance taduba dining kawai tahango mutum azaune yana breakfast

Kuada kai yayi kamar bai ganta ba

Fuska tayi itama tana gyara gyalenta da yafadi

Grany ce tafito tanufi da murmushi afuskarta tace albishirinku

Shiru AK yayi se asma'u ce tace goro fari grany

Wata takarda Tamika ma AK tace ga visan kunan yafito nashirya muku honeymoon zuwa kanada

Afirgice AK yace honeymoon kuma grany

Eh ....
Tafada tana daure fuska
Ko bazaka bane

Sadda kai yayi yana fadin gaskiya grany inada aiki agabana banada lokacin wani honeymoon

Daure fuska tayi tace. To shikenan tunda ban isa nasaka Abu kamun ba dama can ina zargin baka kyewtatama yarinyar nan dan kaganta shuru shuru to wallahi kaji tsoron Allah

Harara ya jefama asma'u yanaji kaman yashakota

Shikenan grany zan je amma gaskiya kanada yayi nisa kuana hudu kawai zamuyi yanzu dai zamu fara zuwa Lagos inyaso karshen watannan semuje honeymoon din

Baki tawashe tace ba komai ni dama sunake kusamu lokaci Ku kafahimci juna

Tana kainan tayi gaba abunta

Tashi yayi yafita yana kallon asma'u aransa yana fadin nasan ke kika cusa ma grany wannan ra'ayin inba haka ba ina tasan wani honeymoon

Yana bangarensa azaune aysha tashigo tana zunbura baki tace wai dagaske honeymoon zakuje

Tsakai yayi yace wane honeymoon niba inda zanje dawannan yarinyar ai se arainani

To yazakayi da grany

I have a plan yafada yana leken kofa

Khaddeja lafiya kince kina son ganina

Eh hakane Tarzan abunda muke zargi gaskiyane

Haba dama nafada maki ni nasan ba banza ba kawai zanje nasamu AK inji akan wane dalili zai cutar da baiwar Allah akan wani selfish reason dinsa

Dakatar dashi tayi dafadin
a'a idan kamishi magana zaije ya sauke akan yayata ne mafita dayace

Wacce kenan

Ka auri sarah !!!

Na aureta fa kikace khadeeja bayan kinsan bana sonta

Amma ai kai kace mun zaka iya yin komai dan farin cikina nikuma farin cikin yayata shine nawa idan har ka auri sarah nasan AK zai daina muzguna mata zasu zauna lafiya

Girgiza kai yayi cike da damuwa yace khadeeja nasan waye AK bazai taba son asma'u ba

Ni kuma nasan yayata abune mai sauki tasa yasota kuma ni nafada maka wannan

Idan har kana sona da gaske to ka auri sarah idan kuma bahaka kawai kamanta dani kar kakara nemana kafita daga rayuwata

Tana kai nan ta juya ta tafi tana share hawayen fuskarta

Dakallo yabita yakasa koda motsa yatsar sane

Tafiya take tana kukan bakin ciki har tabacema ganinsa

Grany ce ta tasa AK agaba akan seyaje da asma'u tayi ma su Umma ban kuana tunda gobe ne tafiyarsu

Ba yanda ya iya haka yasa driver yajasu suka tafi gidan inna suka fara zuwa sunsamu tarba mai kyew abba ma yadawo suka gaidashi cike da fadin ciki yake kallonsu yanama Allah godiya dayaba asma'u miji nagari

Sunjima agidan sannan suka nufi gidan Umma

Dagudu asma'u tashiga gidan tana kiran umma !!! Umma!!!
Fitowa Umma tayi da mamaki tarungumeta tana tambayar asma'u kece yanaganki haka kuma

Bayan AK yashigo sun gaisa yake gayamata zancan tafiyarsu tayi farinciki sosai tamusu addu'a

Fita yayi waje yana jiran asma'u tafito

Khadeejace tazo shiga gida kamar daga sama tagansa akofar gida

Tagefensa taraba tawuce amma batace komai ba

Se yaji duk baiji dadin ganinta haka ba kamar yamata magana se kuma ya kyaleta

Tana shiga asma'u tazo da gudu ta rungumeta

Cikin sassanyar murya khadeeja tace ammah ya kike
Lafiya kalau asma'u tafada tana mata alama fa kar Umma tagane

Tadan jima agidan kafin da kyar Umma ta fito da ita waje tace tabar mijinta na jiranta tundaga gida sukayi sallama da khadeeja tana mamkin ina AK zai kai asma'u

Umma ce tarakota har wurin mota sannan Tamika mashi wata leda tace gashi tashice zatamai anfani
Godiya yamata sannan sukabar kofan gidan

Seda suka biya wurin Momy itama suka gaidata amma basu sami ahmad agida

Momy tafuskanci akwai matsala atsakaninsa da ahmad kamar tayi magana sekuma tayi shiru
Tace intayi tsami maji
Sundan jima awurinta sannan suka fito sunzo fita sukaci karo da ahmad zai shiga gida kauda yayi kaman bai gansu ba ya wuce ciki

AK baiji dadin hakan ba amma yasan komai zai wuce

Ahanya yabude ledar yaciro abunda ke ciki
Wata sweater ce mai kyew irin tasakannan
Rigan tabirgeshi amma kawai dan Neman tsokana

Yadaga rigar sama yana fadin wai ni Umma zataba wannan rigar ai sedai ingoge window da ita

Nan take fuskan asma'u ya canza idonta ya cicciko da hawaye cikin muryan kuka tace Umma fa tasakata da hannunta she gave it to u with love amma zaka fadi haka takarashe maganar tana fashewa da kuka

Damamaki yace ohhh to ai ni bansani ba nadauka takice ai

Batace komai ba taci gaba dasharan kwalla

Leko fuskanta yayi yana fadin wai kuka kike
Kauda kanta tayi batace komai se sheshshekar kukanta dake tashi

Dafe kansa yayi yace dan Allah kiyi shiru natsani kuka arayuwata sannan yadago yakalleta yace idan ma jira kike nabaki hakori to gara ma kiyi shiru

Nan madai bata daina kukan ba

Yacema driver yayi playing music

Ai kamar yakara mata kukan ne

Bashiri yace yakashe

Cikin sassanyar muryan dabata taba zaton yanada ita ba taji yace ok I am sorry rigan tayi kyew kuma ina sonta kawai dai nafada ne

Damamaki tadago takallesa yayi saurin kauda kai kaman bashi yayi maganr ba

Shiru tayi tana share hawayenta
Chapter 25 · 0% Book details