← Book details Domin Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 84

Sashe 26

Domin Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga nan bawanda yayi magana har suka karasa gida

Suna isa yaran inna ladidi salma da amir suka zo dagudu suka rungumeshi

Rungumesu yayi yana dariya yace yaushe kuka dawo

Atare sukace dazu mukazo grany tace kamana aunty ina take
Bayansa yanuna musu yana fadin gatanan zuwa

Aguje suka je suna mata oyoyo

Washegari tunda safe suka shirya sukama grany sallam suka fito kallon aysha yayi yakashe mata ido

dariya tayi tana rufe bakinta datafin hannunta dan kar agane

Driver ne kejansu basuyi tafiyar awa dayaba suka iso Barcelona hotel bayan yayi parking AK yafito yana mika sannan yaleka yacema asma'u to ai sekifito ko hajiya

Fitowa tayi tana zunbura baki

Bude but yayi yaciro akwati daya yayi gaba baice komai ba

Dayan akwatin tadauka
Tabi bayansa tana fadin inane nan kakawomu

Airport....
Yafada atakaice

Daure fuska tayi tace I am not a fool

Murmushi yayi yace nasan dai baki taba shiga jirgi ba wannan ne karo nafarko

Shiru tayi batace komai ba

Wurin reception yanufa yana fadin jirani anan bari nakarbo mana passing cards dinmu

Dakallo tabisa har yaje yakarbo makullin daki yadawo ya dauki akwati ya nufi wata hanya yana fadin muje karmu rasa flight

Tsaki tayi tace wai mekadaukeni ne ko angayamaka banyi makaranta bani

Wani daki yakaita bayan sun shiga yace

Yarinya anan zakiyi honeymoon dinki kuana hudun nan se sunzame maki tamkar shekara 4 anan wurin
Zama tayi bakin gado tace
Tunda dai karaboni dawancan gidan kabiyani dama zaka barni anan har natsawon rayuwata da ina so

Jan dayan akwatin yayi yafita yana fadin natafi wurin masoyiyata idan kina son wani Abu karki kirani

Tasowa tayi tarufe kofar tana fadin Allah raka taki gona
Bai kulata ba yayi gaba abunsa

Farm house dinsa yanufa yana isa kiran aysha nashigo wayarsa yana dagawa tace ya ake ciki

Dariya yayi yace yanzu na ijiyeta ahotel anjima zanzo
To meyasa bazakazo yanzuba

a'a kinmanta yaw Sunday inada program senagama zanzo

Kashe wayar tayi tana wani malalacin murmushi tace zanyi farin ciki idan Maman asma'u takalli program dinka nayau zatasan karya kuke ba inda kukaje

Yaronsa nagidan mai suna sani yakira yace ya Ciro mai akwatinshi abayan but

Yana fito da akwatin AK yace

Bude zakaga wata bakar jaket asama kabani

Dariya ce ta kwacema sani yayi saurin danneta yana fadin yallabai wannan ai kayan matane a akwatin

afirgice yace what !!!
Dafe kansa yayi dayatuna yabar akwatinsa ahotel yadauko na asma'u

Asma'u nafitowa wanka ta janyo akwati tabude
Ido tazaro ganin kayan AK a akwati
Gashi tariga tawanke nata yazatayi

Hakanan tadauki kayansa tasaka

Murmushi sani yayi yace hakan yana faruwa akan masoya yallabai

Keep quite dan Allah!!!

Shiru sani yayi yana danne dariyarsa

Makullin mota yakarba ahannun driver yashiga aguje yabar wurin

Yana isa yafara bubbuga mata kofa

Tana kunce tasa eyepiece akunne tana bacci

Yajima yana bugawa amma bata budeba gashi lokaci natafiya dole ya karbo spare key yabude dakin

Bakin gadon yakaraso yana mamakin ya akayi bataji karan buga kofar ba

eyepiece din yaciro yasa akunnensa

yagirgiza kai yayi yana fadin shiyasa kagi nan ahargitse

Kamar ance tabude idonta atsorace ta tashi zaune tana fadin wai meya dawo dakai kuma

Damamaki yake kallon rigar dake jikinta

Blanket din yafara janyewa yana fadin bala'i badai kayana kika sakaba

Rirrike blanket din tayi cikin muryan mai shirin fashewa dakuka tace wai me kakeyine haka bakai katafi dakayana to mekakeso insa

Wayanshine yafara ringing tsaki yayi yadaga yana fadin wallahi kicremun kayana kinji nagayamiki

To idan nacire mezansaka haka zan zauna

Dip nunfashin aysha yadauke sandarewa tayi awurin takasa cewa komai

AK yayita hello hello yaji shuru wurgi yayi dawayan kan gado yana kallon Asma'u yace dakinsan tsadan rigarnan tajikinki to ko biyanki akayi bazaki sakata ba
Yau inada program kuma ita zan saka dan haka cireta

Cikin rawar murya tace to kabani tajikinka se inbaka wanna

Cire rigarsa yafara yi tayi saurin kulle idonta tana fadin wai meyasa bakada kunya ne

Jefo mata Rigan yayi yana fadin yi sauri banda lokaci

Bayi tanufa tasanyo rigar tafito masa da waccan

Fizge rigan yayi ahannunta yasaka yana mata dariyan yanda takoma acikin kayanshi

Daure fuska tayi tana tattare wandon dayamata yawa

Akwatinsa ya ja yana fadin kice abunda kike so kisha abunda kike so ki kalli abunda kike so Abu daya ne bazaki samu ba saurayinki ahmad dan tun aranar nasan yagama dake
Kauda kai tayi tace eh naji dan Allah tafi
Rigan jikinta ta shinshina tana yamutse fuska

Fita yayi daga dakin yana fadin dakayannan zaki kare kuanakin ki anan

Seda yafita shima ya shinshina rigar jikinshi yana yamutsa fuska kamar yanda yaga tayi

Aysha takasa hakuri seda taje farm house din AK tana isa sani yacemata ai yakoma wurin matarsa nan take taji jiri na deebarta

Tafito kenan tahadu da AK zai shiga dan baisamu damar yin program dinsa ba lokaci yakure

Damamaki yace me kike anan

Kai zan tanbaya daga ina kake

Daga gidan abokina

Kusan shi tamatso tace daga gidan abokin naka ne kasamo turaren mata

Kauda kai yayi baice komai ba

Fashewa tayi da kuka tace AK meyasa zakamun haka kasan ina sonka amma inaga kaina kawai nakeba wahala gara ma kawai nahakura dakai

Saurin rikota yayi yana fadin come on aysha stop this drama please

Me kike tunani wai ina kula waccan yarinyar kome

Kema kinsan she is not my type mezanyi da ita

Kima daina tada hankalinki akan wannan

Da kyar ya lallasheta tayi shiru sannan yajata suka fita shakatawa

Da kyar Umma tashayo kan khadeeja takira mata Asma'u

Bayan sun gaisa Umma ke tambayanta sun isa

Eh ta amsa atakaice

To ina maigidan nanki

Yana bayi ...

Karban wayan khadeeja tayi cikin sassanyar murya tace ammah ya kike
Lafiya kalau khady ...

I hate it when u lied to me

Cike da mamaki Umma tace meke faruwa ne meyasa kika ce haka

Saurin hannunta khadeeja tayi dan Sam tamanta agaban Umma take

Cikin dakewa tayi murmushi tace kai Umma kincika tsoro kawai dai nasan bata zuwaba kuma tayi nesa damu dole zataji badadi

Katse kiran asma'u hade da sulalewa akasa tafashe dawani irin kuka maiban tawsayi """"

Urs....
*MHD*
[18/07, 15:04] Hubbey Frd Ameena Kn: 📚📚📚📚📚📚
👨‍👧 _DOMUN KANWATA_ 👩‍👧

Na( Maryam Muhammad jibril)

8⃣0⃣

Khadeeja ce tazo wucewa ta layin gidansu ahmad ta gansa yafito daga masallaci
Karasawa wurinsa tayi tana boye hawayenta

Yana ganinta ya kauda kai yana fadin
why are u flowing me since u have no feelings for me

Sadda kanta tayi kasa tace nazo ne naji wace shawara kayanke akan maganar da mukayi jiya

Khadeeja kigane ni bazan iya abunda kike so ba
Bazan iya auren sarah ba bana sonta
Zaka sota daga baya just try it

Bazai yuwo ba khadeeja mutum baya iya sakama kansa son wani

Kenan haduwata dake da fadan da mukayi duk ke kika shirya

a'a bani nashirya kawai yafaru ne

To kigane so faruwa yake dan na auri sarah bashi zaisa AK yaso asma'u ba

Nace miki kibarni ni zan daw mataki akai

Bawani matakin dazaka dauka abunda AK yayi
Yayishine domin kanwarsa
Nima kuma zan hakura dakai ne saboda yayata kai kuma kahakura dani dan farin cikina idan har kana sona ...

Tana kainan tajuya ta tafi tana sharan kwalla

Dunkule hannu yayi yanawshi iska yana cije lebe

Motansa yashiga yafigeta aguje kamar mai shirin barin gari

zaune suke cikin katuwar runfar gidan suna hutawa bayan sundawo daga shakatawa

AK nifa ina jin tsoro dan Allah kar wannan yarinyar ta rudaka

Wai aysha so nawa zan gayamaki ba abunda zai faru baki yarda dani bane kome

Mezanyi dawannan chitti din kawai jira nake ahmad ya auri sarah nayi waje da'ita

Miye kuma chitti ??

Yaren India ne yana nufin karamin abu

Dariya tayi tace nakosa naga ranar da asirinta zai tonu mu koreta daga gidan

Shiru yayi kamar mai nazari yanaji bai kyewta ba dayama grany karyan yayi tafiya kuma baikamata yakai yar mutane hotel ya ijiyeta ba har tsawon kwana hudu

Dafashi aysha tayi tace kana tunanin matarka ne

Kauda kai yayi yana furzar da iska bai ce komai ba

Asma'u nazaune adaki ita kadai
Bayan AK ya aikomata da kayanta tasa

Jitayi zaman ya gundureta tafito waje tasha iska
Restaurant din wurin tanufa

Daidai yahaya yazo wucewa ya hangota

Cike da mamaki yake kallonta shidai yasan ance sunyi tafiya da AK to meyakawota nan kuma

Wayarsa yadauka ya kira grany yana daga gefe

Bayan sun gaisa yake tambayarta yallabai nagari

a'a bayanan sunyi tafiya da amaryansa kuma kar wanda yadamesa da kira

Lafiya kake tambaya ..

a'a ba komai grany dama wata nagani kamar asma'u shiyasa nake tambayar ko sunfasa tafiyar ne

Cike da mamaki tace a ina kaga asma'u

Bai bata amsa ba yakatse kiran yana lalubo numban asma'u yana daga nesa yana kallonta amma ita Sam bata gansa ba

Tana zaune taji wayanta na ringing mamaki tayi ganin numban yahya
Afili ta furta yahya kuma to lafiya

Tajima kafin tadaga wayar tare da sallama

Bayan ya amsa sallamarta yace dama nakira ne naji kun isa lafiya

Lafiya kalau Yaya...

Kinga Lagos ko? Nasan baki taba zuwa ba ...

Eh Yaya yanzu haka ma muna wurin hutawa gwanin sha'awa Ashe Lagos tanada kyew haka

ya wajansu Umma

Lafiya ....
Yafada yana katse Kiran da mamakin meyasa sukayi karyan sunyi tafiya
Me asma'u take ahotal ita kadai ina AK yake
Dole akwai wani Abu

Wani mutum ne yazo yazauna kusa da asma'u dawata jaka ahannunsa yana leken police din dasuka shigo restaurant din

Tunda tagansa taji bai kuanta mata ba daure fuska tayi tace malam yi hakuri katashi ni matar aure ce

Murmushi yayi yamike yana fadin yi hakuri ban saniba
Karasowa police din sukayi cikin restaurant din suna bincika ko ina

Da manager ya tambayesu suka ce sunsamu labarin anshigo da drugs restaurant din dan haka dole su binciki kowa anan

Suna cikin bincike suka iso wurin asma'u

Daukan jakan yayi yana fadin madam is this urs

Atsorace tazaro ido tace no batawa bace

Bude jakan sukayi sega drugs makil acikin jakar

Murmushi yayi yace kinbani mamaki gaki kamar mutuniyar arziki Ashe ke annoba ce kina matsayin mace da darajarki amma kinwatsar da ita kina cutar ya'yan jama'a
Chapter 26 · 0% Book details