← Book details Domin Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 84

Sashe 58

Domin Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

nadamar danake ako dayaushe kenan nayanke shawar gayamata amma inaso in mata surprise in shirya komai yanda zai tsaya akwakwalwarta har karshen rayuwarta naso najiyamata dadin dako wace ya'mace keburin samu agidan mijinta

Ahmad bantaba sanin cewa inason chitti ba seda tabarni bansan a ina take ba awane hali take amma jikina yana bani tana raye

Dafasa kafadansa ahmad yayi cikin sugar lallashi yace

Nima ina fatan haka amma kacigaba da hakuri kuma mudage da addu'ar allah ya bayyana mana ita

Share kwallansa yayi yace shiyasa akace idan kanason mutum kagayamasa maybe lokacinda zakaso yasani ko zaka shekara kana ihu bazai jikaba

Kawai sonake naganta koda so dayane nagayamata cewa ina sonta

Shiru ahmad yayi baice komai yana ni dayasan inda take dako birnin seen ne se yanemota kodan abokinsa yafita daga wannan halin

abubuwa dayawa sun canza gaba daya farin ciki ya kawaracewa gidajen biyu ahmad da khadeeja kuwa tuni sun ijiye zancan urensu gefe

Kasuwancin AK gaba daya yakoma baya saboda kokadan ba abunda yake kaishi office ahmad kuma shikadai abun yamasa shima yana kokarin bude nasa companyn a Lagos so baicika zama ba kullun yana zirga zirga ga damuwar halin da AK keciki ko yana gari to kullun suna tare da AK

Su uncle jamilu sun samu abunda sukeso se yayi Kane Kane a company wadaka suke da dukiya son ransu

Aysha kuma tana nan tana renon cikinta tana jira lokaci yayi dazata fara aikinta

sarah ma gaba daya jikinta yayi sanyi da yanayin da yayanta yake ciki ko baifada mata ba yanzu tasan yana son asma'u shi yasa take tausayamasa dan tasan irin wannan yanayin narasa Wanda kakeso

Su Umma da grany kuma tun suna kuka har sun gaji sun fawwala wa allah komai amma kowane dare na allah se Umma tayi kukan rashin sanin halin da yarta take ciki

Khadeeja ma juriya kawai take amma gaba daya ta canza duk wannan rahar da masifar tata duk tadaina tadawo so silent karatu kawai sukasa agaba itada fa'iz sedai ko a aji ta tuna asma'u sedai kawai aga tana rusa kuka sedai tafita waje tayi mai isarta ta hakura tun fa'iz natayata har yagaji sedai ya lallasheta

💔💔🕐🕒🕓🕕🕖🕗🕘🕙🕚🕛💔💔

*Bayan wata daya....!!!*

wata safiyar lahadi misalin karfe 9 ruwan sama ya sauka gari yayi sanyi ga wani daddadan iska dake kadawa mai dauke da kamshin damuna

AK nazaune agarden ya harde hannaye yana kallon fararen tantabaru dake zagaye dashi kamar zasu hau jikinsa saboda sabon dasukayi dashi cikin wata daya kullun awurinsu yake wuni sallace kawai kefitar dashi se bacci

daidai wannan lokacin wata arniyar mota ash color kiran BMW sabuwa gal tayi parking aharabar gidan

Bakin glass din motar shi yahana agane Wanda keciki
gaba daya ma'aikatan gidan sunyi cirko cirko suna kallon motar baki bude sunkosa suga waye aciki

motar takai kusan minti goma da tsayuwa amma bawanda yafito daga ciki

Ahankali aka turo murfin motar kusan minti biyar tadauka kafin tafito daga motar tana tura murfin dakafarta tarufe motar sannan ta gyara tsayuwarta tana bin gidan da kallo
[19/07, 17:05] Hubbey Frd Ameena Kn: 📚📚📚📚📚📚
👨‍👧 _DOMUN KANWATA_ 👩‍👧

Na( *Maryam Mhd*)

1⃣6⃣0⃣

cikin sanda tashigo bangaren grany tana leken palon ganin grany ne ce kadai azaune yasa ahankali takarasa cikin palon tayi tsaye daga nesa tana kallon grany idonta pal kwalla

Dagowa grany tayi tana kallonta nadan lokaci sannan............. tasaki wani lallausan murmushi tana fadin karaso mana asma'u

saurin karasawa tayi tafada jikin grany tana fashewa da wani irin kuka mai cin rai

Shafa kanta grany tayi cikin sigar lallashi tace a'a asma'u miye kuma na kuka ai ba haka mukayi da keba

Cikin muryan kuka tace grany bazan iya ci gaba da wannan aikin ba bazan iya jurar ganin ABI awannan halin ba kuma fa kinji me Umma tace wai sedai in nemi wata uwar ba ita ba

Katseta grany tayi dafadin zaki iya asma'u tunda fari nasan zaki iya shiyasa nasakaki kimanta da Abidi nasan shi yanada juriya da tawakkali ba abunda zai sameshi kuma naga alama bai yarda cewa yaudararsa kikayi ba ita kuma ummanki ranta ne yabace amma ba abunda zata miki kici gaba da aikinki wata rana dakanta zata yi alfahari dake

Shiru tayi tana share hawayenta sannan tadago tana kallon grany tace kin lura da uncle jamilu dazu kinga yanda yake subutar baki

Tabe baki grany tayi tace hmm bari kedai ai tun da kika shigo nakafesu da ido se alokacin nakara yarda da abunda kika fada mun godema allah dakika jiyo zancansu dasedai muje mu asalansa

Dariya asma'u tayi tace amma grany kince in nazo zaki bani labarin yanda ABI da bana nan

Dariya grany tayi har tafa hannu tace kedai bari asma'u ai ni naga ikon allah ke mutuminki Ashe yana sone yana kai kasuwa bawan allah da kinganshi lokacin se kin tausayamai

Fuskar tausayi asma'u tayi tace gashi naga duk yarame kamar ba shiba

"hmmm ba kin dawoba ai yanzu zai maida kibansa amma gaskiya kinyi kokari da inata tsoron kar aje kikasa yin abunda muka tsara shirinmu ya lalace

"Grany ai ba karamar dakewa nayi ba kafin nayi wannan acting din bama danaga Umma ji nayi kamar inzo dagudu in rungumeta

Kallon kofar dakin inna ameena grany tayi sannan tace ai gara da kika dake kinga daganan mutananki zasu fara shakkar ki dan na hango tsoro karara afuskarsu

Shuru tayi nadan lokaci sannan tace yanzu gobe insha allahu zan fara zuwa office nasan ansamu canji sosai kasancewar ABI da Ahmad basa zama kuana biyu duk yanda ake ciki idan nadawo zan sanardake

shuru sukayi nadan lokaci sannan grany tadago tana dariya tace yi fa hakuri dazu nawankeki da mari

Itama dariya tayi tana shafa kuncinta tace ba komai ai duk cikin aikin ne sannan ta tashi zaune tana riko hannun grany tace amma gaskiya dazafi nan gaba inzaki mareni kidan min signal dan nashirya dan gaskiya na tsorata dazu

Dariya suka sa gaba daya daidai lokacin inna ameena ta turo kofar dakinta tafito

Grany na ganinta tayi saurin kwace hannunta cikin kakkausar murya tace eh anmareki din ko zuwa kikayi kirama ne

alama tama asma'u da ido sannan taci gaba da fadin tanbayar ki nake ko zaki rama ne

tashi tsaye asma'u tayi tana kallon grany fuska adaure tace ba ramawa nazo yiba zuwa nayi inmaki kashedin kar ki kara kai hannunki jikina da nufin marina namaki hakurin nayau saboda rashin sani amma nan gaba kika sake banajin zan iya kyaleki

Tana kainan ta juya tafita ko kallon inna ameena batayi ba bare tasan taganta

Saurin karasowa inna ameena tayi cikin palon tana fadin nashiga uku ni ameenatu wai kenan dai dagaske yarinyar nan take tazama mara mutunci

tsaki grany tayi tana kauda kai kamar dagaske tace nayi nadamar aura ma abidi yarinyar nan ina tunanin namishi zabi na kwarai ashe na dauko abun zai cutar damune ......takarashe maganar tana sharan kwalla

Dafata inna ameena tayi cike da tausayi tafara lallashinta

ahankali ta tura kofar dakinsu tashiga tsaye tayi tana kallon AK dake kuance kan gado idonsa alumshe kamar mai bacci

Dagowa yayi yana kallonta nadan lokaci sannan ya gyara kuanciyarsa ya juya mata baya

kallonsa taci gaba dayi hawaye masu zafi na tsere akan kuncinta

Jin kamar ana kallonsa yasa ya juyo ahankali yana kallonta saurin kauda kai tayi tawuce dressing room

can anjima tafito sanye da kayan baccinta riga da wando takwanta agefen datake kwanciya da

yana jin ta kwanta yamike tsaye hade da daukan pilo yabar dakin

Da kallo tabisa har yafita sannan tarungume pilo tana fashewa da kuka mai ban tausayi har bacci yadauketa

washegari dasafe tana cikin dressing room tana saka kayanta a drowanta AK ya fito daga bathroom daga shi sai towel aqugunsa suna hada ido yayi saurin juyawa yakoma ciki yana fadin what are u doing here

Ci gaba da aikinta tayi tana fadin meye kuma zaka wani juya bayan kasha cire kaya agabana

daga cikin bayin yace daba ni agaban chitti nake cire kaya bakeba lady boss

Rigarsa tamika mishi tana fadin fito kabani waje wanka zanyi kar namakara

Kwace rigarsa yayi ahannunta yana fadin karki kara tabamun kayana with ur dirty hands

juyawa tayi tafara Ciro dogayen rigunanta daga drawer tana sasu adayan drowar

Saurin saka rigarsa yayi yafito yana fadin ke wai mezakiyi

Bata kallesa ba tace wai meyasa kakeson shiga abunda bai shafeka bane kayana zan saka awurin

Janyeta yayi daga wurin yana maida kayan cikin drowa yace kinemi inda zakisa fitsararrun kayanki nan drowar chitti ne dan haka baki isa kicire mata kayanta aciki ba kuma I can't share my closet with u

Se alokacin tadago tana kallonsa da murmushi tace karfa kamanta nan gidana ne inada damar dazan ijiye kayana aduk inda nakeso

lokaci guda fuskarsa ta canza yana kallonta ko kiftawa ba yayi yajima ahaka sannan yariko kafadunta dakarfi cikin wata iriyar murya yace bansan meyasa kika yi hakan ba amma kisani ko kadan hakan bai bata min rai ba abunda yafiyi mani zafi shine karyar dakika mun cewa kina sona idan kudi kikeso ko nawa kika tambayeni ni mai iya bakine saboda kinfimun komai arayuwata ada amma ayanzu bakida wata kima a idona u can do what ever u wont with my money amma kisani ina nan dake sena kwato dukiyata ahannunki nan bada jimawa ba....yana kainan yasaketa yana daukan kayansa a drawer ya wuce daki

Durkushewa tayi awurin tana toshe bakinta dan kar kukan ya fita seda tayi mai isarta ganin lokaci yana tafiya yasa ta wuce bayi tayi wanka sannan ta dawo dressing room ta shirya cikin wasu riga da wandon bakake sannan tadoro jacket irin tajiya ruwan toka tayi rolling da karamin gyale shima ruwan toka se takalmin kafarta kalan gyalen tayi kyew matuka kamar bala rabiya tana fitowa AK yabita da kallo tundaga sama har kasa aransa yana fadin wai dama haka chitti tahadu bansaniba ganin tana kallona yasa yayi saurin kauda kai yana daure fuska

Dressing mirror tanufa tafeshe jikinta da turare sannan tazana light make up shap shap tagama tadauki jakarta sauri sauri tanufi hanyar fita tana duban agogon hannunta

dakallo yabita har tafita sannan yaci gaba da abunda yake yana fadin zamuga yanda zakiyi aikin yarinya tunda angayamaki make up ne dazaki iya koyanshi cikin wata daya
Chapter 58 · 0% Book details