← Book details Domin Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 84

Sashe 19

Domin Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hannunsa yakai daidan saitin zuciyarta amma baiji alamun tana bugawa ba nan take jikinsa yafara rawa jijjigata yake dakarfin gaske kamar zai karyata yana fadin a'a a'a sarah please don't leave me keda grany kunake gani naji dadi arayuwata idan kika tafi yazanyi for god sake say something

gefen fuskarta yafara bubbugawa cikin rawar murya yake fadin kitashi namiki alkawarin zan taimaka maki kinji zansa ahmad ya aureki I promise I will make u proud kinsan duk abunda kike so ina maki please wake up ganin ba alaman zata tashine yasa yafashe dakuka ya rungumeta tsam ajikinsa yana surutai kala kala

Ahaka doctor din ya iskosu dasauri AK yamike daga zaunen dayake akasa yanufi doctor yana fadin doctor please help my sister

Bring her to bed ...doctor din yafada yana ijiye briefcase din dake hannunsa

Cak yadauketa yadawrata kan gado doctor yamatso yafara dubata yana fadin idan badamuwa kudan jirani daga waje

AK yakasa fita seda aysha taja hannunsa tafita dashi

Cike da takaici yace wai tun kika ji shiru adakin meyasa baki kirani ba

Nakira mana amma wayanka akashe

Ina mutanen gidan suke

Bansaniba tafada tana ware hannayenta

Bangaran inna ladidi yanufa ahasale yafara buga musu kofa
rai bace tafito tana fadin kai lafiya wayene natsani.....ganin AK datayi atsaye fuskarnan a murtuke yasa ta hadiye sauran maganarta tana fadin oh AK Ashe Kaine

Fuska ahade yake fadin kinji karan knocking din danamaki amma bakiji lokacinda nake balla kofar dakin sarah ba

Meyasamu dakin sarah da ake balla kofar

Mutuwa tayi

Afirgice tace mutuwa kuma AK subhanallahi yo idan ma mutuwar ce fisabilillahi haka zaka fadamun ita salan zuciyata tabuga

Kai yakauda hade da cije lebensa nakasa sannan ya juyo yace

Ankayata wancan babban palon ne badan yazama na ado ko na family meeting ba a'a sedan yazama cibiyar kara donkwan zumunci da kaunar juna manufarsa kenan amma dazaran kunbiya bukatar Ku acan shikenan se kowanne yashige bangaransa bawanda zaisan halin da dan uwansa yake ciki

Kuma nagayamaki kanwata tamutu amma har yanzu dai ke takanki kike wai kada zuciyarki tabuga bana tunanin ma kinada zuciyar ajikinki

Hade fuska tayi tace to wai meyasamu sarah ne naga duk kafita hayyacinka ne

Idan kinso sani kizo kiduba da kanki ....
Yafada yana juya baya yakoma

Dakallo tabisa seda yabace mata sannan ta tabe baki takoma ciki tana fadin dama kasaba ai idan wani Abu yasamu sarah to ko bacci hanamu kake wai mutayata jaje bare kuma ance batada lafiya ai munshiga uku shiyasa na guanmace ni nayi ciwo akan sarah koba komai nasamu nayi bacci mtswwwww

Suna tsaye abakin kofa shida aysha doctor yafito dasawri AK yakarasa wajansa yana fadin doctor ya jikinta meya sameta hop she is OK

Dafa kafadansa doctor yayi yace be strong man kanwarka lafiyarta kalau kawai dai damuwa ce tayimata yawa kuma da alamum tajima rabonta da abinci
Juyowa yayi yakalli aysha saurin sunkuy dakai tayi tana wasa da yatsunta

maida kallonsa yayi kan doctor yace
To yanzu ya jikinta

Jiki dasauki yanzu dai namata allura tana bacci ga wannan idan ta tashi taci abinci tasha wannan se kudan barta tahuta kadan anjima zan dawo

Godiya yama doctor din sannan sukayi sallama yatafi nura narike da briefcase dinshi suka fita

ahankali yatura kofar dakin yashiga aysha nabiye dashi abaya kusa da ita yazauna bakin gadon yana kallon yanda take sauke nunfashi ahankali lokaci guda duk tacanza tayi wujiga wujiga kamar ba sarahn dayasani ba yar gayu mai son kwalliya nan take yaji tawsayinta yakama da ahankali yashafi gashin kanta da ya barbage akan pilon datake kuance akai

Aysha nadaga gefe haushi duk yacikata ganin yanda duk yarude akan sarah har yake fadin wai ita da grany kawai yake gani yaji dadi to ita kuma ko oho kenan ko

Kusa dashi tamatso tadafa kafadansa tana fadin AK naga lokaci yana tafiya ko kama grany maganrmu

Wani gigitaccen kallo dayawatsa mata ne yasa tayi waje tana fadin bari nashirya mata abunda zataci idan tafarka dakallo yabita seda tafita sannan yamike ya gyara mata bargon sannan yafita

bangaren grany yanufa mamaki ne yakamashi ganin yan uwansu makil apalon wasu yaganesu wasu kuma bai sansu ba suna ganinshi suka haw shewar ango ango

Bayabo ba fallasa ya amsa gaisuwarsu ya wuce dakin grany tana zaune kan gado tana lissafa kudi

Tana ganinsa tawashe baki tana fadin ahh abidi karaso mana dazu naje dakinka banganka ba gaka baki ko

zama yayi abakin gado baice komai ba

Lafiya abidi grany tafada tana karantar yanayinsa

Ajiyar zuciya yasauke sannan yace sarah ce ba lafiya grany

Afirgice tace subhanallahi me yasameta

ba wani Abu bane dasauki ma yanzu doctor yaduba ta

Tashi tayi tana fadin bari naje naganta baiwar Allah ai bansaniba kasan ba shiri mukeba

a'a barshi kawai yanzu tana bacci anjima kyaje

Dawowa tayi tazauna tana fadin to Allah yasawake

Ameen yafada yana yana mikar da bayansa kan gadon

Baki grany tawashe tana fadin abidi kaga su bala da shehu sunzo ko

kai yagirgiza yace a'a ban gansuba suna ina

Suna sashen baki dazu suka zo gobe insha allahu zasuje suga magabatan yarinyar dazaka aura tunda ta amince

Damamaki yace ta amince fa kikace koda yake ba abun mamaki bane dan tayi saurin amincewa auren AK hausawee dama nasan za'arina
nan take yaji yarinyar bata kuanta mashi ba dan yafison mace mai aji ba mayyar abun duniya ba wani dogon tsaki yaja hade da kauda kai

Hade fuska grany tayi tace to ana maganar arziki mekuma yakawo tsaki yadai kamata kaje Ku gana da yarinyar taganka kufahimci juna

Mikewa yayi yanufi hanyar fita yana fadin tunda ta amince kafin taganni that means bata bukatar ganina abunda takeso daban

Baki bude grany ke kallonsa har yafita girgiza kai tayi tace gaskiya akwai abunda yake damun yaron nan

Ahmad ne zaune a dining yasa abinci agaba se juya cokalin yake amma yakasa koda loma dayane Momy dake gefe tana kallonsa tafahimci akwai abunda yake damunsa tunda yashigo gida dazu

Kujeran Kusa dashi tajo tazauna tana fadin ahmad wai meyake damunka ne kuana biyu naga kanada damuwa amma kaki fadamun kuma na lura kaman auren sarah ne bakaso to meyasa zaka takura kanka ana dolene

Sunkuy dakai yayi kasa baice komaiba
Dakai nake magana kayi banza dani

Dago kansa yayi yafara bata labarin abunda yafaru tun a airport har izuwa yau

Shiru tayi bayan tagama saurarenshi can tadago tace gaskiya baka kyewta ba ahmad amma banga laifinka ba shi mutum bayada ikon saka so ko cirewa sedai kawai ince Allah yashige mana gaba kuma kasamu AK kabashi hakuri yanada saukin kai nasan zai fahimceka kasan yanda yakeson kanwarsa

Shiru yayi baice komai ba

Murmushi tayi tace oh kai kwa duk yan matan da suke binka kamar hauka karasa wacce zaka so se khadeeja wannan karamar yarinyar

Se alokacin yadago kai yana murmushi yace kai Momy khadeejan ce Karama

Tashi tayi tana fadin nidai kahada ni da aiki da zaka kamun suruka trouble maker

Dariya yayi yace Momy ai irinsu akeso

Abangaren Umma da abba kuwa shiri suke bana wasa ba izuwa yanzu kowa a dangi yasan da zancan auren asma'u kowa yayi farin ciki da wannan ala'amarin

Bakamar khadeeja datake jin kamar tajanyo ranar tadawo yau

Bangaren asma'u kuma duk tafita hayyacinta tsakanin jiya da yau har wata yar rama tayi tana mamakin wane kalan aurene wannan da za'ayishi asati guda kuma har yanzu angon bai nemi yaganta ba bayan tanada tabbacin bai Santa ba

Dakin sarah AK yakoma daga bakin kofar yatsaya yana kallonta ahankali yabude idonta tasaukesu akansa

Saurin karasowa bakin gadon yayi yana fadin Ashe kinfarka murmushin dole tayi tana kallonsa ga hawaye na gangarowa agefen fuskarta

zaunawa yayi
daga gefenta aysha kuma tana tsaye gefen kanta tana kallon ikon rabbi

Yatsansa yasa yana goge mata hawaye cikin muryan lallashi yace stop crying kanwata kukan nan naki yana daga mun hankali ki kuantar da hankalinki Ahmad bashi kadai bane namiji aduniya ba zaki samu Wanda yafishi komai ....

Katsesa tayi dafadin bashi kadai bane namiji aduniya ba amma ni shikadai nakeso kuma shi zan aura he only belongs to me takarshe maganar tana kara fashewa da kuka

Nasan kina sonsa kanwata amma kiyi kokarin danne sonsa kimanta dashi
ahasale yakarashe maganar dafadin just forget him saboda yace bazai aureki ba

😭I can't..... I can't Yaya bazan iya mantawa da ahmad ba and I won't let him go !!!

Kauda kansa yayi gefe guda yana jin wani irin haushin ahmad dayajefa kanwarsa awannan halin

Aysha ce tace ni ina mamakin wace yarinya ce wannan da ahmad yamutu akanta har yake wulakanta sarah

nima dai bansaniba AK yafada yana kallon sarah

Saurin tashi zaune tayi tafara Neman wayanta

Menene inji aysha tana tayata daga bargon dake kan gadon

Kan dressing mirror tanuna mata tana fadin bani wayana

Dauko wayan tayi Tamika mata
Tana karba tafito da photon asma'u Tamika ma AK tana fadin wannan ce yarinyar

Karban wayan yayi yana dubawa zunbur yamike yana fadin wannan ai nasanta
Kafeshi sukayi da ido suna son jin a ina yasanta

Kanshi yashafa yana fadin no wonder shiyasa ranan naganta agidansu ahmad kuma ina yawan ganinta a unguwar amma bansan ko wacece ba

Babanta malamin makaranta ne sunansa malam mahammadu amma ana kiransa magaji sedai yajima da rasuwa

Tunda tafara magana AK yakafeta da ido yanason tuna ina yataba jin sunan

saurin rikota yayi yana fadin wait kika ce babanta malamin makaranta ne sunansa magaji kuma yajima da rasuwa ko

Kai ta gyada mai alamar eh

Zama yayi akan gado tare dasa hannayensa biyu yana shafa sumar Kansa data hargitse lokaci guda

Kusa dashi aysha tamatso tadafashi tana fadin lafiya AK menene kasanta ne

Dago da kansa yayi yana kallon sarah yace itace yarinyar da grany takeso na aura

Dip suka dauke wuta ba mai motsi ba kamar aysha datake jin kamar tasaki fitsari

Wata nannawyan ajiyar zuciya ta sauke arenta take fadin ohh thank god kaga bazata amince da auren AK ba tunda tanason ahmad

Kamar yaji mai tace yayi saurin fadin ina mamakin meyasa zata amince da aurena bayan kuma tana son ahmad
Chapter 19 · 0% Book details