Sashe 47
Domin Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
anan wurin yashinfida sallaya yayi sallah nan khadeeja takamasa tea mai zafi karban tea din yayi ya ijiye yana kallon Abba yace wato malam jiya ina cikin mota azaune ina jiran madam tafito kawai naji ankwakwasa kofa lekowan dazanyi kawai naji anfesa mun wani Abu to daga nan kuma bansan inda nakeba se yanzu shiyasa kaji natambaya ina madam
salati Abba yayi cike da al'ajabi yace allah ya kyewta to miye dalilin haka oho mun gode allah dai tunda basu maka komai ba
Inaga asma'u tafito tajika shiru tazata bacci kake ga dare yayi shiyasa tawuce gida
Karasawa wurin motar khadeeja tayi tana kure wurin da ido tace a'a wani Abu ne yasameta
kallonta sukayi da mamki zugunnawa tayi takasa tadauko sarkan asma'u dake yashe awurin cikin rawar murya tace tabbas wani Abu yasami ammah ga alamun inda tayi kokarin kwace kanta nan ga jakanta akarkashin mota
Azabure suka mike suna nufo wurin hankali tashe fa'iz yaje yakira su Umma nan fa aka fara salati su inna tuni anfara kuka
Nan take khadeeja khadeeja takira wayar AK seda takusa katsewa yadaga yana dariya cikin muryan bacci yace
deeja karfe 2:00 ne daurin auren ko nine angon ai kya barni indan yi bacci ko
Cikin muryan kuka takatseshi da fadin
Yaya ammah tana nan ?
azabure ya zauna bakin gado yana fadin banganeba kardai kice mun ba anan takuana ba tunjiya bata dawo gidannan ba ai
Sulalewa tayi awurin tana sakin wani irin kuka mai cike da tashin hankali
dafata fa'iz yayi yana kuantar mata da hankali Abba kuma yana rarrashin Umma da inna
bashiri AK yasaka kayansa ko wanka baiyiba yafito agurguje daga bangarensa haduwa yayi da sarah ta rikoshi tana fadin
Yaya ina zuwa haka da sassafe
kuace hannunsa yayi yafita yana fadin gidansu asma'u zani akwai matsala zamuyi magana anjima
dakallo tabisa tana murmushin mugunta har yafita sannan ta wuce dakin aysha da gudu tafada kan gado tana murna
atsorace aysha ta tashi tana tambayar menene
Dariya sarah tayi tace gaskiya yau ina cikin farin ciki nacika burina yanzu tunda ahmad yarasa khadeeja ai dole yadawo gareni
da mamki aysha tace wai meyafaru ne kike wannan murnan
Kamo hannunta tayi tana murmushi tabata labarin duk abunda yafaru
Zaro ido aysha tayi tace to yanzu mezaki mata
Dage kafada tayi tace oho ni yanzu nagama nawa duk abunda suka ga dama sumata ba matsalata bace
Komawa aysha tayi ta kuanta tana fadin gaskiya sarah bakida dama se yanzu nakara yarda zaki iya yin komai akan ahmad
Murmushi tayi tadauki wayanta takira JJ yana dauka tace aiki yayi kyew JJ anjima kadan zakaji alert dariya yayi irin ta rikakkun yane fashi sannan cikin muryan mashaya yace nagayamiki aikinki bazai kuana ba kedai kawai ki tabbata kin biyani shine kawai
Karkadamu tafada tana katse kiran
AK na isa wurinsu Abba aka tabbar cewa wani Abu ne yasamu asma'u nan take yakira ahmad yasanar dashi ba bata lokaci ya iso wurin
Nan take suka wuce police station suka yi repot abunka da masu dashi nan take aka shiga Neman asma'u ruwa ajallo har sanarwa akasa gidan TV da Radio
Kafin gari ya waye kowa yasan da batan asma'u hankalin kowa atashe wasu nakuka wasu na rarrashi
AK da ahmad kuwa tare dasu ake nemanta amma har rana tafarayi ba ita ba labarinta
JJ na isa qurin yaran suka bude mashi fuskar asma'u
Saurin ja dabaya yayi yana zabga ashariya
Kallonsu yayi da jajayen idanuwansa yace dan ubanku wane dan jahila ne yakamota acikin
saurin nuna dan uwansa yayi yana fadin oga shine yakamota dama nagayamasa ba ita bace amma yaki saurarona
Cikin rawar murya dayan yace oga kaifa kace kyekkyewa kuma wannan tafi kyew
Wankeshi yayi da wawan wari cikin kakkawsar murya yace kai jahilin inane dan tasha kawai bakaga waccan tafi faso gari bane shine zaku faukomun wannan karamin alhakin inyime da ita
Shiru sukayi kansu akasa suna bashi hakuri
Ahankali asma'u tafara bude idanuwanta har tasaukesu akan wa innan rikakkun mazan saurin ja dabaya tafarayi amma tajita adaure atsorace take kallonsu cikin rawar murya tace su....suwaye Ku....menake anan
kusa da ita yamatso yazugunna yanafadin sorry yan mata tsotsayi ne yahau kanki nuna mata photon yayi yace wannan mukaso kamawa shine muka kamoki inda kike kuma nikaina bansan wurin ba
zatayi magana kenan wayarsa tahau kara ganin sunan sarah yasa yafita daga qurin yana daga wayar
Cike da masifa tace JJ wane kalan aikin banza kamun ne
katseta yayi dafadin hajiya kidan rage muryanki dan allah banason ana cikamun kunne da ihu inace dai kinbani aiki ko to matsalar da akasamu aciki tawace kuma ni zan gyarata kibarni nayi aikina kar kidameni
yana kainan yakatse kiran yana kunduma mata ashar
Dakallo sarah tabi wayarta cike da takaici tace jimun da iska nizai nuna ma dabanci
dafata aysha tayi tana boye dariyarta tace take it easy sarah kinsan mutanan nan ba imani ne dasuba kar su miki wani abun
banza tayi da ita tana zama bakin gado hade da dafe kai
Fita aysha tayi tanufi bangaresu tana murna tasanar dasu abunda yafaru cike dafarin ciki sadiya tarungume ta tana fadin allah sa ma sukashe yar banza wallahi da munji dadi
Dariya uncle jamilu yayi yace sarah nabirgeni akwaita da banzan hali Indai taso Abu to setayi duk yanda tayi tasameshi
dariya aysha tayi tace ni kuma ina anfani dawannan damar ina biyan bukatuna gashi yanzu ina kuance tagama mun aikina natabbata yanzu AK zai dawo kaina tunda waccan dai nasan ba dawowa zatayi ba
Har dare AK da ahmad natare da police suna nemata amma ba labari da kyar ahmad yaja AK suka koma gida saboda dare yayi kan gobe zasu dawo aci gaba da nemanta
komawa cikin gari JJ yayi yabar yaransa hudu tare da asma'u yatafi da biyu akan zai je yaga abunda yakamata yayi
kallonsu yayi yana hura sigari yace kar Wanda yamata wani Abu zanje indawo kafin nan muga abunda abunda yadace idan maidata za'ayi to idan kuma aikata zamuyi duk dai dayane
kuka tafarayi tana rokonsu surabu da ita amma bai kulata ba yafita sauran yaran kuma suka koma gefe suna kora giyarsu suna fira
Jiki asanyaye AK yashigo gida saurin yaroshi grany tayi tana fadin Abidi ya ake ciki har yanzu ba labari
Zama yayi kan kujera yana dafe kai yace har yanzu shiru grany ni ina mamkin suwaye zasu mata haka dafari nayi tunanin kidnapers ne to amma kuma har yanzu ba'akira kowa daga cikinmu ba abun yana dauremun kai
Zama tayi kusa dashi tana salati tace allah sarki asma'u ko awane hali take oho
Allah yakareta daga sharrinsu ...inji inna ameena
Ameen ....suka amsa gaba daya
Daran ranan Sam AK baiyi bacci ba duk Inda yakalla tunanin asma'u kawai yake yakosa safiya tayi yaje nemanta
da sassafe ahmad yazo gidan zasu wuce tare da AK yana shigowa AK yamike dama shikadai yake jira bangarensa yawuce dan yashirya sutafi
Asma'u nazaune banda kuka ba abunda take se rokonsu take su kwanceta tayi sallah amma sunki wai tabari intaje lahira tayi
Dasafe dai cikin yaran yakamata wata busashshiyar waina da pure water ya ijiye kusa da ita bakinsa duk warin giya yace gashi kija yan mata cikin nawa nabaki badan haka bama bazaki ciki komai ba
Kauda kai tayi tanaji kamar zatayi amai
Kuance mata hannu daya yayi yadaure dayan abaya har yajuya yadawo ya kwance agogon hannunta yana murmushi yawuce wurin yan uwansa yana fadin gayu kunga wani dan ubansun agogo kuwa
Kuka tasa tana rokon yabata agogonta amma basu kulata ba dayan yafara tattaba agogon yana fadin alqur'an bantaba ganin agogo irin wannan ba
AK yafito daga dressing room cikin shirinsa na kananun kaya lite blue din gins da farar shirt
Har zaifita kawai yaji wani Abu nakara daga cikin bedside drawer
Kamar yashareshi se kuma yadawo yana janyo drawer yaga agogon da ahmad yabashi yana kara yana nuna Jan danja
Saurin daukar agogon yayi yana sakin wani sassanyan murmushi aguje ya fito daga bangarensa yana kwalama ahmad kira
azabure suka mike tsaye suna kallonsa agogon yamikama ahmad yana fadin friend kalla agogon dakabani natabbata chitti ce ke kirana agogonta yana hannunta
Cike da farin ciki ahmad yakarba agogon yadanna wani wuri sega arrow din yajuya yafara nuna direction
kwace agogon AK yayi yanufi hanyar fita yana fadin friend bari naje kai kaje kutaho da yan sandan zamu rika magana awaya
saurin rikoshi ahmad yayi yana fadin haba AK inazakaje kai kadai bakasan wa yanne irin mutane bane kajira muje tare mana
girgiza kai yayi yana kuace hannunsa yace a'a Ahmad bazan iya jiraba akowane lokaci nashiga matsala tana tare dani har sai taga nawarware to nima gaskiya bazan bata lokaci ba kafin nataimaketa kaidai kawai kazo da police
Riko ahmad grany tayi tana fadin ahmadi yanada gaskiya barshi yatafi allah yana tare dasu
rungumeshi ahmad yayi jikinsa asanyaye yace shikenan friend ka kula dan allah idan kaga wurin da hadari kar kashiga kajira se munzo kaji
To yafada yana juyawa yafita bin bayanshi aysha tayi har yafita tarikoshi tana fadin AK wai mekake shirinyi ne
Juyowa yayi yana fadin abunda yadace
fashewa tayi da kuka AK yaruwarka fa zakasa ahadari saboda asma'u to gaskiya sedai kazaba ko ita ko ni idan har katafi wurinta sedai kahakura dani
Shiru yayi nadan lokaci sannan ya kwace hannunsa daga nata ya juya yana fadin nabarki lafiya
Saurin shangabanshi tayi tana kuka tace AK dagaske tafiya zakayi
Gefen fuskanta yashafo yana murmushi yace aysha nasan kindamu dani shiyasa kike haka amma kiyarda dani ba abunda zai sameni insha allah
Yana kainan yayi gaba dakallo tabisa har yashiga mota yatafi sannan tajuya ahasale tanufi dakin aysha
tana shiga ta isko sarah na Neman JJ awaya hankali tashe yana dauka tace JJ wai kai wane kalan sakarai ne to kasani ga Yayana nan zuwa kuma wallahi kasake yakamaka kai kasani karma ka ambaci sunana
tsaki yayi yace to seme inyazo ke nifa banason takura kingane ko inace ko gama biyana bakiyi ba kinzo kin isheni da surutu kibarshi yazo mana alqur'an ana kamani sunanki zan fada banza yar tasha kawai
saurin katseshi tayi dafadin yi hakuri JJ raina ne abace yanzu kasan meza'ayi
Kawai kasaki yarinyar kubar wajan kafin ya iso kunji