← Book details Domin Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 84

Sashe 57

Domin Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ahankali ta furta meyasa ....meyasa
Sukeso suga bayansa bayan bayada wani buri da yawuce ya kyewtata musu duk wahalar dayake saboda su yakeyi baya samun isashshen bacci baya samun hutu baidamu da duk wani jin dadi irin namasu kudi ba kawai saboda baya iya yin komai se tare dasu amma burinsu shine sumallake abunda yasha wahala da guminsa yatara why....why...takarashe maganar tana durkushewa awurin hade dasakin wani kuka mai cin rai bata damu da mutanen dake kallonta ba dan ita kadai tasan halin da take ciki

Cikin kukan take fadin ina bazai yiwu ba bazan taba bari su cutar dakai ba se inda karfina ya kare I will fight for u ABI that's my promise
amma taya tana ina zan fara ko zan mutu ina rantsuwa ABI bazaka yarda da abunda zan fada ba ....

kanta takai kasa tana kankame jikinta cikin kuka tace ya allah kataimakeni I am helpless😭

bayan AK yadawo gida da yamma bangaren grany yawuce yagaidata se dube dube yake ta inda zai hango asma'u amma bai ganta ba hakanan yatashi yanufi bangarensu dan yasan tana can

Seda yafara leka dakin aysha ya iskota zaune da sarah suna fira daga bakin kofar suka gaisa ya wuce bangarensa

Murmushi sarah tayi tana kallon aysha tace sister wai miye sirrine naga kuana iyu Yaya yadamu dake ba kamar da ba

Dariya tayi suna tafa hannu tace ba wani sirri kinsan ance true love never end

Yana isa bangarensu yatura kofar yashiga da sallama sedai wayam ba kowa daki yawuce nan ma bakowa ahankali ya tura kofar dressing room har bathroom nan ma bakowa

Jiki asanyaye yadawo yazauna yana cire agogonsa duk se yaji baiji dadin rashin ganinta ba wayarsa yadauka kamar ya kirata se kuma ya ijiye yana fadin control ur self man kansa yadafe da hannu biyu yana cukurkuda gashinsa yace wai meyake damuna ne

wasa wasa har dare asma'u bata dawo ba tun yana hakuri har yagaji yakira wayanta amma akashe wayan khadeeja yakira tace yau Sam ma bataje gidan ba

Wurin grany yanufa itama tace bata San inda tajeba nan fa aka fara nemanta sama da kasa amma ba ita ba labarinta

Nan take gida yadauka ba asma'u yar karamar hauka AK yayi dan yarasa ta inda zai fara se safa da marwa yake yana neman numbanta amma baya shiga police station yaso yaje grany tace yayi hakuri har zuwa safe suga idan ba'aganta ba

cikin Daren ya kira ahmad suka fita nemanta se yawo suke sun rasa ta ina zasu fara nemanta

Haka ma khadeeja da fa'iz duk inda sukasan tana zuwa sunje amma ba'aganta ba

Har dare yaraba suna yawo amota da kyar ahmad ya lallashesa akan sukoma gida gobe dasafe sucigaba da nemanta

Badan yaso ba haka ya hakura suka kama hanyar gida

akan hanyarsu sukaga mutane sun taru ana kallon wani Abu

Tabo ahmad yayi yana fadin dakata friend bari muduba nan muga

Baijira amsa ba kawai yabude motar yafita cikin sauri yakarasa wurin mutanen yana tambayar meyafaru

Cike da tausayi wani mutum yace

Allah sarki wata yarinya ce mota takade yanzu suka nufi asibiti amma yarinyar kam gaskiya bance akwai sauran nunfashi atare da ita ba ....

Baijira yaji karshen maganar ba ya kutsa ta cikin mutanen yashiga ahmad nabinsa abaya

Jini malala awurin kai daga ganin jinin kasan da kyar yarinyar zata rayu

Nan take jikinsa yahau rawa durkushew yayi akan guywowinsa yana jiyo maganar mutanen wurin sama sama saboda tuni jiri yafara dibarsa baki bude yake kallon jinin

Ahankali yakai hannunsa yatabo jinin yana kallo lokaci guda wasu hawaye masu zafi suka ziraro akan kuncinsa

Dafa kafadansa ahmad yayi shikansa yakasa danne tashin hankalinsa cikin sassanyar murya yace AK control ur self ba lalle ne ya kasance asma'u ce tayi hatsarin ba

Dagowa yayi yana kallon ahmad da jayayen idanuwansa cikin rawar murya yace are.....are u sure ?

Shiru ahmad yayi yana kauda kai dan baisan mezai cemasa ba

Sun jima ahaka kafin da kyar ahmad ya dagosa yana fadin friend let's go home

Bin bayansa yayi suka tafi batare dayace komai ba amma har sukayi nisa yana waigen jinin dake kasa

Ahmad nagaba yana tafiya jiki asanyaye yana boye hawayen fuskarsa dan ba karamin tausayi AK yabasa ba fatansa daya allah yasa ba asma'u bace tayi hatsarin dan kwa in itace to gaskiya sedai suce allah yajikanta

Yana cikin wannan tunanin kawai yaji karan faduwan Abu abayansa saurin juyowa yayi dan ganin komiye

AK yagani akwance kamar gawa dagudu yakarasa wajansa yana kiran sunansa da karfi har saida mutane suka juyo

Durkusawa yayi kusa dashi yadagosa yana fadin heyyyyy friend....wake up miye haka .....katashi mana

Bubbuga gefen fuskansa yafarayi yana kiran sunansa dakarfi amma shiru cikin mutanen wurin ne akasamu Wanda suka taimaka masa yasaka sa amota se asibiti

Suna isa aka wuce emergency dashi har lokacin ba alaman nunfashi atare dashi

Nan take ahmad yakira gida yasanar dasu kan kace me har asibitin tacika da yan gida harda su Umma

Kuka inna take kamar karamar yarinya tana fadin bayin allah abun tausayi duka duka yaushe suka fita daga wata wahalar yanzu kuma ga wata shi wannan akwance ita waccan allah kadai yasan inda take

Ansha wahala kafin da taimakon allah aka shawo kan matsalar

Bayan anakaisa dakin hutu doctor yasanardasu cewa damuwa ce tamai yawa nan kowa yafara tofa albarkacin bakinsa kan canzawar AK cikin kuana biyu

bashi yafarka ba se dasafe bayan sallar asuba ahmad ne kawai zaune kusa dashi dan ba abarin mutun sama da daya sushiga in percent yana bacci

ahankali yabude idanuwansa yana bin dakin da kallo har yazo kan ahmad da yake faman jera mai sannu

Lumshe idanuwansa Lokaci guda yana tuna duk abunda yafaru

Saurin dago hannunsa yayi yana kallon jinin daya bushe akan yatsunsa

juyowa yayi yana kallon ahmad cikin dasashshiyar murya yace har yanzu batazo ba

Sunkuy dakai ahmad yayi yakasa cewa komai

"Kun gayamata cewa banada lafiya ...?

kagaymata cewa idan maganar da banayine yasa ta tafi to nadaina zan dawo yanda nake zan fara magana kamar da zan tsokaneta zan mata fira amma bazan iya rayuwa batare da ita ba tayi hakuri tadawo

tasowa ahmad yayi yazauna kusa dashi yana boye hawayen fuskarsa yace friend asma'u tana nan daranta ba abunda yasameta ba ita bace wannan yarinyar kadaina damun kanka kana bukatar Hutu

Riko hannun ahmad yayi yana fadin to idan ba ita bace tana ina meyasa har yanzu bata zoba duk lokacinda nashiga matsala she is always there for me to yanzu ya akayi ban ganta ba

kagayamata tazo kaji tell her that I am really sorry I feel lonely without her by my side

Tashi ahmad yayi yafita daga dakin yana share kwalla dan bazai iya juran ganin abokinsa ahaka ba

ta wurinsu grany ya wuce amma baice musu komai ba bin bayansa khadeeja tayi tana kiran sunansa

Saurin mikewa sukayi gaba daya suka shiga dakin

binsu yake da kallo daya bayan daya har yazo kan Umma sannan yasakemata lallausan murmushi yana mata alama da tazo

Karasawa tayi wurinsa tana sharan kwalla tace sannu abid

Riko hannunta yayi yana murmushi yace hmmm Umma kinsan me ?

Girgiza kai tayi wasu hawayen nakara gangarowa

Cije lebe yayi yana runtse ido yace ur daughter was a little disturbed

taga mun damu da ita shiyasa take bamu wahala ko

Daga mishi kai tayi bakinta narawa takasa cewa komai

Murmushi seda hakoransa suka fito lokaci guda hawaye na gangarowa daga idonsa cikin rawar murya yace ance uwa tana ji ajikinta idan wani Abu yasami yarta now tell me is she ok ?

Kwace hannunta tayi tafita daga dakin tana fashewa da kuka

Karasowa wurinsa grany tayi tana shafa kansa tace Abidi kazama jarumi mana idan kai kana haka mu kuma matan yazamuyi ka kuantar da hankalinka ba abunda yasameta kaji insha allahu za'aganta

Rungumesa sarah tayi tana gashewa da kuka dan ba karamin tausayi yabata ba

Hannunsa yakai yana shafa kanta se alokacin yagane halin da tashiga lokacinda tarasa ahmad baiga laifinta ba dan koshi yanzu ji yake ba abunda bazai iyaba indai asma'u zata dawo

Kuanan su biyu a asibiti aka sallamesu har lokacin AK baidawo hayyacinsa ba gaba daya yazama kamar mai tabin hankali maganganunsa kadai sun isa Susa mutun zubar da kwalla

Har wannan lokacin ba asma'u ba labarinta ahmad kullun yana zarya police station amma bawani labari mai dadi se antsinci gawar wata ansamu wata tayi accident ansamu wacce aka ma fyade har bayason zuwa dan kullun yaje se ranshi yabace

Kuance yake akan gado gefen da asma'u ke kuanciya idonsa alumshe kamar mai bacci amma yayi zurfi cikin tunani

Ahmad ne yashigo rike bowl din fruit salad aciki dan seda dubara yake cin abinci

Kusa dashi yazauna yana fadin Mr Romeo dan tashi kaci wannan mana

Banza yayi dashi yana gyara kuanciyarsa yabashi baya

Shiru yayi nadan lokaci sannan yace da wane suna ma asma'u ke kiranka .......miye ma

Murmushi AK yayi batare da ya juyo ba yace ABI

Dariya ahmad yayi yace ehhh haka fa ABI to ABI wannan fruit salad din ranar da asma'u zata tafi tayishi tasa a frig saboda tasan zaka bukace shi

Tashi yayi yafita yana fadin gashinan idan baza kaci ba zan turo nura ya dauka

Yana ganin ya fita ya tashi zaune yana murmushi yadauki bowl din yafara sha harda lumshe ido

haka dai yacigaba da jinyar zuciyarsa shi kadai yasan halin da yake ciki lokaci guda ya rame gaba daya yafita hayyacinsa ba inda yakezuwa daga bangaren grany se wurin Umma kullun firarsa bata wuce ta asma'u shiyasa yakeson zama da khadeeja dan tayita bashi labarin rayuwarsu shikuma yana dariya

kullun da tunaninta yake kuana yake wuni idan abun ya isheshi sedai ya shige daki yarungume kayanta yayita rusa kuka se yayi mai isarsa dan kanshi ya hakura wayarsa kuma sallace kawai kerabasu kullun tana hannunsa yana kallon photon asma'u

Zaune suke da ahmad apalo yana tayasa cin abinci

Cike da tausayi ahmad ke kallonsa yace AK kasan kana son asma'u meyasa baka gayamata ba

Murmushin dayafi kuka ciwo yayi yana hadiye lomar da kyar yace
Chapter 57 · 0% Book details