← Book details Domin Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 84

Sashe 44

Domin Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dariya tayi tace kima gode allah kinsamu mai gayamiki banzar magana ni kallon banza ma bansamu wanda yamun ba

Idan baki manta ba nayi alkawarin senasa kin zubar da kwalla kamar yanda nayi I always keep my promises

ko baki fada ba nasani AK yasakeki saboda naga lokacinda yabaki takarda dasafe karki bata mana lokaci kitashi ki fice daga gidan nan kafin AK yadawo yasameki

Tashi tayi tafita daga dakin tana fadin idan kinje gidanku kyayi kukan da hujja

dakallo tabita har tafita tana takaicin hali irin na sarah

rungume photon tayi dakarfi tana fashewa dakuka mai cin rai tajima ahaka sannan da kyar ta tashi tana rike da frame din tasaka shi a akuatinta sannan tadauki farar takardar da AK yabata kafin ya fita tasaka ajakanta tana karema dakin kallo tafita kamar wacce batada jini ajikinta

ahankali take takunta tana janye da trolley dinta har ta iso palon kasa

azaune ta isko sarah da aysha suna jiran sakkowarta suna ganinta suka hau dariya suna gayamata bakaken maganganu

Dariya aysha tayi tana kallon asma'u taje sarah anya kwa bazamu duba akwatinnan ba kinsan halin yan can...

dariya sarah tayi tamike tanufi wurin asma'u tana fadin aysha ni bandamu da me tadauka ba kawai dai tabarmana gida shine damuwata

Jan hannunta tayi tanufi hanyar fita da ita itadai asma'u jikinta gaba daya yayi weak tamakasa magana ita abunda yadameta daban fatanta tasamu damar dazatama AK kallon karshe gashi rabonta dashi tunsafe

dakarfi sarah ta turata waje yar kara tayi zata fadi kawai tajita akan kirjin mutum

lumshe ido tayi tana shakar kanshin turarensa mai kuantar da hankali

Janyeta yayi daga jikinsa yana maidata gefe

su grany dake bayansa suka karaso dasauri suna tambayar meyafaru

Dagudu taje ta rungume grany tana fashewa da kuka

atsorace grany tarikota tana fadin asma'u lafiya menene ganin takasa bata amsa yasa tajuyo tana kallon sarah tace ke wai lafiya meyake faruwa ne

daidai lokacin khadeeja takaraso wurin tana riko asma'u tace ammah mesuka miki kike kuka kigayamun idan sun miki wani abu

karasowa sarah tayi ta finciko asma'u tana fadin karma ganin grany yasa kigara tunanin zakici gaba dazama anan gidan wallahi se kinfita tunda....

bata karasaba khadeeja tadauketa dawani wawan mari tana nunata dayatsa cikin kakkausar murya tace

Mind ur business winch gidannan ko rayuwarta ce aciki zata barshi saboda ba farin ciki acikinsa amma kibari mai gidan ya koreta bake ba

Kai wai meyake faruwane .....
Grany tafada tana daka musu tsawa

ahasale sarah tace grany barin gidan zatayi saboda AK yasaketa dalilin kamata dayayi tana cin aman....

Bata karasaba AK yadaka mata tsawa yana fadin sarah shut up

Juyawa sukayi gaba daya suka kallesa banda asma'u dakanta ke kasa tana murza yatsunta dakarfi har tana jin zafi

karasawa wurinsa sarah tayi tana riko hannunsa tace Yaya meyasa zanyi shiru bayan abune dayazama dole kowa yasani

Kuace hannunsa yayi cikin kakkawsar murya yace bai zama dole kowa yasani ba saboda duk abunda yafaru ba gaskiya bane kawai munzargeta ne akan abunda bata aikata ba

Saurin dagowa asma'u tayi tana kallonsa da mamaki
Haka ma sarah take kalkon asma'u da mamki tace yaya kamar ya bata aikata ba takawo maka shaidar ne

kallon grany yayi yafara bata labarin duk abunda yafaru sannan yakare dafadin

daga baya nagane duk plan ne shiryashi akayi dan afitar da ita daga gidan kuma bakowa bane yashirya se sarah

Yana fada yana nunata da yatsa atsorace tadago tana kallonsa da tsananin mamakin ya akayi yasan haka

Aysha kuwa jitayi kamar taruga da gudu saboda tsoro amma jin an ambaci sunan sarah yasa tasauke ajiyar zuciya tana lumshe ido

Juyowa sukayi gaba daya suna kallonta

Cike datakaici yace kinyi mamakin ya akayi nasani ko to kisani ita karya fure take bata ya'ya

Kwarai dafari nayarda cewa ta aikata hakan kuma nayi niyyar idan har bata kamun shaida ba zan saketa saboda Sam naji banason ganinta na tsaneta amma daga baya nasamu shaidar data nuna mun cewa sharri aka mata ke kika shirya komai dan kicimma burinki na korarta daga gidannan

Wayarshi yaciro daga aljihu yamika mata yana fadin gashi idan baki yarda ba zaki iya dubawa

Idan Baku manta ba ranar da su grany zasu tafi amir yana yawo da camera yana daukan video sarah takoresa daga wurin dan bataso yana daukanta

Shi kuma ganin haka yasa yaje dakinta ya ijiye camerar jiya bayan nadawo daga masallaci na iskoshi apalo yana kallon video din ranar dayadauka yana ganin nazauna yamika mun laptin din yace inkalla

Ban kulashiba saboda alokacin ina cikin damuwar abunda yafaru har zanrufe laptop din kawai naga abunda ya birkita mun tunanina lokacinda sarah take take bama aysha labarin yanda tashirya plan dinta

I was shocked saboda ban taba tunanin sarah zata aikata irin wannan kazamin aikin ba

Juyowa yayi yana kallon sarah cike da takaici yace I feel ashamed to call u my sister kin bani mamaki kinbani kunya sarah yaushe kika zama haka

fashewa tayi da kuka tana kallonsa cikin daga murya tace

Ni kaina bansan yaushe nazama haka ba amma komai nayi Kaine sila kasabamun komai nakeso kana mun amma lokaci guda da wannan tashigo rayuwarka kacanza mun kai dakanka kadawo kana ruguza mun farincikina wai dan kafaranta mata da yan uwanta kai kafi kowa sanin cewa duk abunda nakeso to zanyi komai dan ganin nasamesa

Saboda haka dole ne namallaki abunda nakeso kuma dole tabar gidannan saboda kasaketa

wurin asma'u tanufa tana jan hannunta tace wallahi dole kibar gidannan

Fizgota AK yayi yasaukemata lafiyayyen mari atsorace tadafe kuncinta tana kallonsa cikin sassanyar murya tace kamun duk abunda kaga dama amma koda zan rasa raina setabar gidannan

Hannu yamika ma asma'u yana fadin bani takardar

Tana mikamasa yawarware takardar yana nuna ma sarah
Ido tazaro tana kallon farar takardar daba komai aciki

" kingani saboda haka ba dalilin dazaisa tabar gidannan u can die if u want

saurin dagowa tayi tana kallonsa da jajayen idanuwanta dasuke zubar da kwalla

jadabaya tafarayi tana fadin AK kabani mamaki gaba daya kacanza mun yau Kaine kecewa namutu in inaso saboda wannan banzar

juyawa tayi takoma ciki aguje tana fadin AK natsaneka I hate u Ku dukanku senasa kunyi nadamar abunda kuka mun u won't get away With this

Saurin bin bayanta aysha tayi dan gudun kar adawo kanta

hannu grany ta tafa tana salati tace oh ni mairo wai ina sarah tadauko dabi'ar turawa ne gaba daya yarinya tacanza

cike da farin ciki khadeeja ta rungume asma'u tana tayata murna

Dariya inna ameena tayi tana kallon AK tace

To gaskiya kabatama matarka rai kacutar da ita se kabata hakuri

Kallonta yayi aransa yana fadin toh fah here comes the love teacher

daure fuska tayi tana fadin bada kai nakeba katsaya kana karemun kallo

karasawa yayi wurin asma'u yatsaya yana kallonta da murmushi afuskansa sassauta muryansa yayi yace
dagaske sena bada hakuri kin.....

baikarasaba yaji tarungumesa dakarfi kamar zata shige cikinsa

Cak ya tsaya nadan lokaci sannan ahankali yakai hannunsa bayanta yarungumota yana lumshe idanuwansa

Juyawa khadeeja tayi tana boye fuskarta ajikin inna ameena dariya sukayi inna tace kajita sekace batasan komai ba ai idan ma kunyar kikeji gara ma ki ijiyeta dan ahmadi bai San kunya ba

janyeta yayi daga jikinsa yana kallon grany yace

grany mukarasa mana kuhuta ga inna ameena ko jakan bata ajeba kodai dakudi acikine

saurin karban jakan khadeeja tayi tana fadin inna kikawo jakan kuje kawai zan biyoku da ita

dariya sukasa gaba daya suka wuce bangaren grany suna raha

[19/07, 17:04] Hubbey Frd Ameena Kn: Suna shiga ciki khadeeja takira ahmad awaya tana basa labarin abunda yafaru bai ma tsaya yagama jin karshen labarin ba yakatse wayar cike dafarin ciki ya yanufo gidan
yana zuwa aka bude sabon shafin fira anan suka tsaida magana kan bikin ahmad daza'ayi bada jimawa ba dazaran ahmad yadawo daga tafiyar dazaiyi gobe tunda komai ashirye yake kuma magabata sunsan damaganar

su ahmad baki yaki rufuwa se Satan kallon khadeeja yake yana ji kamar ya rungumota dan farin ciki

agidan suka wuni ranan sedare ahmad da khadeeja suka tafi

bayan AK yarakasu yadawo bangarensa yawuce yana kallon dakin sarah datuanin halin datake ciki ahakanli yataka har yaje kofan dakin hannunsa yakai kan handle din kofar kamar yashiga sekuma yajuya yanufi bangarensa

yana shiga dakin ya isko asma'u tana maida kayanta a drawer
coat dinsa yacire yadora akan gado sannan yagyara tsayuwarsa yasa hannayensa a alijihu yana binta dakallo

daukan coat din tayi daga kan gado tamaidata wurinta

Ganinsa atsaye kamar gunki yasa tajuyo tana kallonsa fuska ahade tace what??

kauda kai yayi yana shafa bayan wuyansa yace nothing kawaidai inaso nabaki hakuri ne akan zarginki danayi duk dacewa kinyi kokarin fahimtar dani amma naki sauraronki I am really so.....

Hannunta takai bakinsa tana girgiza kai da murmushi afuskanta cikin sassanyar murya tace

ABI baka bukatar bani hakuri saboda ko kadan banga laifinda kamun ba in fact ka rufamin asiri hatta iyayena bawanda yasan da maganar ni yakamata nagodemaka akan alfarmar dakamun thank you thank you
Janye hannunta yayi daga kan bakinsa yana murmushi yace come on chitti stop being romantic baya maki kyew

kauda kai tayi tana daure fuska tace wai ni komai sekace baya mun kyew kabar ganina haka fa kanemi karainamun class duk abunda wayayyar mace zatayi nima zan iya ko aysha kar nake kallonta dan ba abunda zata nunamun

Dariya yayi yace ohhh really so u can do anything

dan kwali ta turo gaban goshi tana karkada kafa tace kwarai kuwa idan baka yardaba bet me and see

"Ok tunda kince zaki iya yin duk abunda aysha tayi let's see

Aysha tafara cewa tana sona kafin nace ina sonta can u do that ?

dressing mirror tanufa tana fadin kai bazan iyaba saboda me zanyi karya bayan bana sonka after all ni bantaba cewa inason wani ba so it's not easy for me

Dariya yayi yana zama bakin gado yace dama nagayamiki har yanzu dasauranki kidaina hada kanki da aysha ita tafada dagaske ke kuma pretending ma kinkasa

Dawowa tayi wurinsa tatsaya tana fadin ok fine I will do it ai ba wuya ne dashiba

tashi tsaye yayi yana danne dariyarsa yace ok kuma kiyishi in a romantic way bawai kai tsaye ba

gyaran murya tayi tana saita nutsuwarta kanta akasa tace I ....I...
Chapter 44 · 0% Book details