← Book details Domin Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 84

Sashe 36

Domin Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ahasale yafizgota daga jikin khadeeja yayi wurgi da ita gefe seda tafadi sannan yanunata da yatsa yace wallahi kika kara tabata se tattakaki awurin mahaukaciyar banza kawai

Tasowa tayi tanufosa tana kuka tace eh nayarda ni mahaukaciya ce ahmad amma kuma kai kahaukatani

Riko hannunsa tayi tana nuna khadeeja tace dame wannan tafini ahmad mezakayi dawannan karamar yarinyar dabata masan miye soba

Nice nakesonka da gaske ahmad zan iya mutuwa in narasaka

Kwace hannunsa yayi yabudema khadeeja mota tashiga sannan shima yazaga yashiga suka wuce

Da kallo tabisu baki bude se hawaye dasuka wanke mata fuska

Jan hannunta aysha tayi suka koma mota suma suka bar wurin

Bayan dan lokaci Umma tafarfado tana kiran asma'u

Aguje suka fada dakin su duka kusanta asma'u taje tazauna tana kuka tace na'am Umma

Shafo gefen fuskanta tayi cikin muryar mara lafiya tace asma'u dagaske ne AK yasakeki da gaske khadeeja tagudu da ahmad

Shiru asma'u tayi takasa cewa komai se hawaye dake diga daga idonta

Damamaki grany tace wane saki kuma take magana kodai tayi mafarkine

Shuru kowa yayi adakin bawanda yabata amsa
Juyowa tayi tana jifan AK da kallon tuhuma

Saurin matsawa yayi kusan gadon yakamo hannun Umma yana murmushi yace haba umma wace irin magana ce wannan taya zan saki asma'u haka kawai batayimun komai ba bayan ina sonta koma wa yafadamaki karyane kidaina damun kanki yan....

Bai karasaba takatseshi dafadin amma dagaskene ahmad yafasa auren sarah sun gudu da khadeeja ko

Kauda kai yayi ya zare hannunsa daga nata yana fadin Umma kibar wannan maganar khadeeja tana nan bataje ko ina ba yanzu dai kina bukatar hutu kidaina daga hankalinki

fita yayi yana fadin bari naje doctor nason ganina kudan barta tahuta

Binbayansa asma'u tayi sukashiga office din doctor din

Bayan yagama yan rubuce rubucensa yadago yana murmushi yace waye nata acikinku?

Atare sukace ni..
Juyowa sukayi suka kalli juna sannan AK yakalli doctor din yace muduka ya'yanta ne meyafaru

Cire glass din idonsa yayi yana sauke ajiyar zuciya yace well
Wato zuciyarta ce tabuga sanadin ji ko ganin wani abunda yadaga mata hankali dama kuma tana fama da ciwon zuciya to yanzu dai munyi nasarar yimata aiki amma akiyaye nan gaba kar irin haka takara faruwa zaku iya rasata duk wani abunda zai bata mata rai akiyayeshi

sannan akula sosai da maganinta

Bayan yagama yimasu bayani yabasu list din magungunan daza abukata da sauran abubuwan sannan suka fito

Wurin Abba AK yanufa yabashi takardar sannan yace zaije mota yadauko kudi se asiyo maganin

Gudiya yamasa yana samai albarka

Murmushi yayi yace Abba bana bukatar godiyarku ni Dane awurinku kome nayimaku addu'a kawai zakumun ita nafi bukata ba godiya ba

Yana kainan yaraba tagefen asma'u yawuce batare da yakalleta ba

Da kallo tabisa tana murmushi yar yabacema ganinta sannan tazauna tana sauke ajiyar zuciya

Washegari da yamma aka sallami Umma gaba dayansu suka koma gida harda su grany

Bayan sunci abinci sundan yi fira suka shirya zasu tafi

Ganin asma'u batada niyyar tafiya yasa Umma tace asma'u kitashi kutafi mana

Langwabe kai tayi tace Umma kidan barni nazauna har kiji sauki

"a'a tashi kitafi ni naji sauki alhamdu lillahi kuma ga inna da Ummi ai ba nikadaibace

Shagwabe fuska tayi tana kallon grany tace grany kirokammun Umma tabarni se gobe

Murmushi grany tayi tace a'a ni ba ruwana tashi ga mijinki can awaje kitambayeshi idan yabarki ba matsala

Ganin dagaske suke yasa bashiri tafito waje Neman AK

Cikin mota ta iskoshi zaune yana jiransu

Karasawa tayi jikin motar tatsaya kanta akasa tana tunanin mema zatacemasa

Sauke glass din motar yayi yaleko yana fadin kinada magana ne

Sosa kai tayi tace dama dama sonake inkuana anan harzuwa gobe

Kauda kai yayi yana maida glass din motar yace u don't need to ask me dama zaki zauna gaba daya sonake

Shuru tayi takasa cewa komai kuma takasa motsawa seda tadan jima kana tajuya takoma ciki tana mamakin meyasa taji zafin maganarsa bayan tasan ba sonta yakeba

[19/07, 16:58] Hubbey Frd Ameena Kn: 📚📚📚📚📚📚
👨‍👧 _DOMUN KANWATA_ 👩‍👧

Na( *Maryam mhd*)

1⃣0⃣5⃣

Washegari dasafe AK yasauko daga bangarensa yana naman sarah dan tun jiya rabonshi da ita aysha ya tambaya tace sarah tana dakinta tun jiya take kuka har yanzu bataci komai ba

Dakinta yanufa ahankali yatura kofar yana sallama

Can karshan gado ya iskota zaune tasa kai aguywa tana aikin kuka

Yajima atsaye bakin kofar yana kallonta kafin ahankali yataka zuwa inda take
Kusa da ita yazauna yana shafa kanta cikin sigar lallashi yace

Sarah idan nace nasan halin dakike ciki nayi karya saboda duk yanda ake fadin soyayya ni bahaka nasanta ba

nakanyi mamakin yanda mutane keshiga tashin hankali idan suka rasa masoyansu

Nasan zakaji zafi amma bansan yazafin yakeba

Ni hasali ma banyarda akwai wata aba ba wai soyayya

ganinki awannan halin yasa nafara tawsaya ma masoya kuma hakan yasa tafita araina tunda ba komai acikinta se kunci dawahala

Nasan kina son ahmad kina kaunarsa kina son rayuwa dashi amtsayin mijinki

Amma inaso kigane akan yima mace auren dole tazauna amma ba namiji ba

ada nadauka ahmad zai iya aurenki yazauna dake ahakan amma lokacinda nagansa da khadeeja natabbata koda kin auresa bazaki ji dadin zama dashiba saboda nafuskanci bakaramun so yakemata ba

Dan haka kiyi hakuri kimanta da ahmad kiyi addu'ar allah yabaki miji nagari Wanda yafi ahmad kuma yasoki fiye da yanda zaki soshi

Ko kuma ni kibani dama cikin abokanaina nazaba miki Wanda nayarda dashi nasan zakiji dadin zama dashi

Tunda yafara magana bata dago takallesa ba sema kukanta dayakaru

seda yasa hannu yadago kanta sannan tabude jajayen idanuwanta tana kallonsa

Handkerchief yaciro a aljihunsa yafara share mata hawaye yana fadin kinyi shiru bakice komaiba ko kinbani damar nazaba miki ne

Kauda kai tayi cikin dasashshiyar muryanta tace

Yaya ni nagirma nakai lokacinda zan tantance abunda yadace dani da Wanda baidace ba basai kazabamun ba

Ko limamin kasar maka zaka kamun bana bukatarsa kuma bazan so shiba ni ahmad nakeso kuma shi kadai zan aura idan bazaka sa ya aureni ba leave it to me ni zan iya ...

Cike da mamaki yake kallonta tunda tafara magana

Cikin wata iriyar murya yace sarah ni kike gayama haka

Ni kike gayama kin girma kinsan abunda yadace dake

Koda yake ba laifinki bane ni nabata ki

tun kina Karama nareneki da hannuna duk abunda kikeso shi nake maki baki taba Neman wani Abu kinrasaba sedai inyafi karfina

nayi kokarin bata abotar dake tsakanina da ahmad duk saboda ke

amma yanzu ki kalli kwayan idona kina gayamun wai basai nazabamaki ba kinsan abunda yadace dake

Tashi yayi yanufi hanyar fita daga dakin yana fadin
Fine nabarki kizabi abunda yadace dake amma karki kara sakani cikin duk wata damuwarki

Saurin tashi tayi tarungumo shi tabaya tana rusa kuka tace Yaya dan allah kayi hakuri bahaka nake nufi ba raina ne abace I am sorry

janyeta yayi daga jikinshi yafita batare da yace komai ba

bangaren grany yanufa bayan yayi breakfast yakwanta anan Palo yana kallo

Fitowa grany tayi daga daki tazauna daga gefe tana fadin abidi yau kaje kaduba Maman su asma'u kuwa

girgiza kai yayi alamar a'a

"Bangane a'a ba to tashi kaje daga can ma kabiyo da matarka

Pilo yasa yarufe kansa kamar zai yi kuka yace ooooo grany dan allah kibarni nadan huta ita batasan hanya ba da intaje ni nake zuwa dawkota

Haba tarike tana salati tace yau naga abunda yafi karfina ni mairo

Kai yanzu abidi matarka bata kuana gida ba amma kana mitar zuwa dawkota
anya kwa abidi kanada cikakkiyar lafiya kuwa

tashi yayi yana yarfa hannu yafita daga Palon

zaune yake abayan mota driver ketukasa har suka isa

fa'iz dake filin gidan yana buga kwallo ne yazo yabude masu get

bayan yashiga yayi parking AK yafito daga motar yana kallon fa'iz dayayi kamar baisanshiba

Murmushi yayi yakarasa wurinsa yafara buga ball din

tsaye fa'iz yayi yana daure fuska yagaidashi ciki ciki kamar mai koyon magana

Dafashi AK yayi yana amsa gaisuwarsa yace come on boy wai fushi kayi dan namareka ranan

Kauda kai fa'iz yayi baice komai ba

"OK I am sorry bansan meyakaika dakin ba amma nasan abunda tafada karyane

She is my sister kaga bazanso hakan yafaru da ita ba
Kaima kuma kanina ne bazan so ace ka aikata hakan ba

Amma nagane rashin fahimta aka samu tsakaninku

Karkato da kuncinsa yayi yana shagwabe fuska irin nayara yace
Idan kuma kana fushine dan namareka to gashi Karama

Dariya fa'iz yayi yana fadin haba yaya allah ya kyewta

Dariya shima yayi ya wuce cikin gidan yana fadin bari nagaida Umma nazo muyi kwallo

Yana tura kofar palon yahadu da khadeeja tafito daga kitchen rike da plate din indomie ahannunta

Sunkuy dakai tayi tana gaidashi

Bayabo ba fallasa ya amshi gaisuwarta yana zama apalon

Ciki ta wuce ta sanardasu ga AK yazo

Bayan sunfito suka gaisa yakoma kusan Umma yazauna yana fadin Umma ya kike ji yanzu bawata matsala daiko

Murmushi tayi tace ba komai abid nagode da kulawa allah yasaka da alkhairi

Ameen yafada yana kallon inna yace inna kefa

nifa harmukaje asibiti banyarda Umma ce batada lafiya ba nadauka kece

Daure fuska tayi tace ni makiyiyarka ko to ta allah bataka ba

Dariya yayi yace allah baki hakuri daga magana ai ni masoyinki ne

kallon khadeeja Umma tayi tana fadin Ashe abunda wainnan sakarkarun yaran sukayi kenan ai da kazanemun ita wallahi khadeeja bataji ko ina ita ina ahmad oho

Tashi tayi tafita idonta cike da kwalla

Murmushi inna tayi tace harkan yara se hakuri
Sannan takalli AK tace kungaisa da Abba kuwa

Girgiza kai yayi yace a'a ni yanzu nashigo yana nan ne

"eh yana bangarensa

Tashi yayi yanufi bangarensu Abba

yana Isa ya iskosu zaune apalo suna fira harda asma'u

Bayan sungaisa yashiga firan anayi dashi sedai jifa jifa yana kallon ALi da asma'u dasuka koma gefe suna tasu firar

kiran khadeeja tagani yashigo wayanta da mamaki tatashi tafito daga palon

karo sukaci da khadeeja zata shigo fuskanta sharkaf hawaye

Gefe tajata tana fadin lafiya khady meyafaru kike kuka AK yamiki wata maganar ne

Daidai nan AK yazo wucewa yatsaya yana sauraronsu

Cikin rawar murya khadeeja tace baicemun komai ba amma naji kunyar hada ido dashi

Gaskiya koda son ahmad zai kasheni dolene nahakura dashi saboda bandace dashiba
Chapter 36 · 0% Book details