← Book details Domin Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 84

Sashe 37

Domin Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sarah tana sonsa idan ya aureta ahankali zai fara sonta

Farin cikin sarah shine na AK ni kuma naki shine nawa

Gaskiya dole ne ahmad yazaba ko ya auri sarah ko yahakura damu gaba daya amma ni bazan iya aurensa ba

Barin wurin AK yayi yanufi motarsa yashiga

fa'iz yabudemasu get yana fadin Yaya har zaka tafi bakace zamuyi kwallo ba

Murmushi yayi yana daga mai hannu harsuka fita batare da yatankasa ba

Yana fita yakira ahmad awaya seda takusa katsewa yadaga

Bayan sungaisa sama sama AK yace kana gida ne

eh.....
Yafada atakaice

Katse kiran yayi yagayama driver gidansu ahmad zaikaishi

Numban sarah yakira amma har yamata 5 missed call bata daga ba

Shuru yayi ya jingina da kujera hade da lumshe ido yana tunani kala kala aransa har suka isa

yana isa bangaren ahmad yatura kofar yashiga zaune ya iskosa apalo

Ahmad naganinsa yamike tsaye

Kusa dashi yamatso yadafa kafadarsa yace

Friend inaso ka rufe idanuwanka kamanta lokacinda muka fara samun matsala dakai kamanta lokacinda sarah da khadeeja suka shigo rayuwarka katuna lokacinda muke dagani sekai kana kirana supper hero ina kiranka supper man

Lokacinda dayanmu baya iya bacci se yatabbatar da lafiyan dan uwansa lokacinda za'a dakeka amma nine zanyi kuka lokacinda banada lafiya amma kai ne kejinya lokacinda zanji ciwo amma sekafini jin radadinsa

Shuru ahmad yayi idonsa arufe yana tuna duk abunda AK kefada seyaga kamar lokacin abun ke faruwa baisan lokacinda hawaye suka fara zuba daga idonsa ba

Cikin rawar murya AK yace

Yanzu gani agabanka ba amtsayin AK hausawee ba

amatsayin supper hero dinka

shin zaka amince ka auri wacce nakeso takasance matarka ??

Rungumesa ahmad yayi yana fashewa da kuka yace na amince supper hero nayarda zan aureta ko yanzu kake so muje adauramana aure wallahi zan zauna da ita kuma zan kula da ita

Jan hannunsa AK yayi yana sharan kualla suka fita daga gidan

Kofar gidansu khadeeja driver yayi parking
da mamki ahmad yace amma wannan ai gidansu khadeeja ne nan nakawota jiya meyasa muka zonan

Murmushi AK yayi yace inaso mubasu hakuri ne kuma kuyi bankuana da khadeeja kagayamata ka amince da auren tunda itama haka takeso

Bude kofa ahmad yayi yafita baice komaiba

Murmushi AK yayi yafito suka shiga tare

tunda AK yafita sarah ke kuka tana ganin kiransa amma taki dauka aysha dake kusa da ita tace sarah AK yamiki 5missed call amma baki daga ba

Kauda kai sarah tayi tana sharan kwalla

Daukan wayan aysha tayi takira numban amma yabarta amota har takatse ba adaga ba

Zama tayi kusa da sarah tana fadin meyasa baki dauki kiransa ba kikasan kome zai gayamaki

Numban drivernsa takira bugu biyu yadaga yana gaidata

Bata ansa ba tace kuna tare da AK ne

"Eh munatare dashi amma yanzu sunshiga wani gida shida sir ahmad

" ahmad fa kace wane gida suka shiga kenan

"bansani madam amma naji suna zancan wai sir ahmad ya amince zai yi aure

wurgi tayi dawayan tana daka tsalle tace sarah barka natayaki murna ahmad ya amince zai aureki

Saurin tashi sarh tayi tana washe baki tace allah dagaske wa yagayamiki

Kama hannunta tayi tana jujjuyata tace yanzu driver yacemun AK natare da ahmad kuma ya amince zai aureki

tsalle sarah tayi tafada kan gado cike da farin ciki tana kankame pilo

zaune suke apalon inna sunyi jigum jigum suna jiran abunda AK zai fada

ajiyar zuciya ya sauke yana kallon Umma yace

Umma kintabbata bakida matsala akan duk hukuncin da nayanke

Gyada tayi tace kwarai kwa abid nabaka dama kayanke musu duk hukuncin dayadace

Murmushi yayi yana kallon inna yace inna kefa

Tabe baki tayi tana juya furar dake hannunta tace yo ni meruwana dasu

Fa'iz dake kusa da ita se hadiyar yawu yake nabin furar dakallo

harara tabankamai yayi saurin kauda kai yana hade fuska

sunkuy da kai AK yayi yace

To ba wani Abu bane dama ahmad nazabama mata kuma ya amince da aurenta to shine nazo Baku hakuri akan abunda yafaru

Dagowa ahmad yayi yakalli khadeeja suka hada ido tayi saurin kauda kanta tana share hawaye

Murmushi AK yayi yana kallon ahmad yace

Friend zan baka auren kanwata kariketa amana da gaskiya ka kularmun da ita yanda yadace idan kacutar da ita to zan manta kai abokina ne nayima rashin mutunci

Shuru sukayi gaba daya ba Wanda yace wani Abu

Idon asma'u ne yakawo kwalla tana kallon kanwarta cike da tawsayi Umma ma haka kawai dai juriya take

Maida kallonsa yayi kan khadeeja yace
Deeja ga abokina nan nasan kina sonsa to kiyimai biyayya kuzauna lafiya banda rashin ji idan har kika muzguna masa to kema zanmanta cewa kanwata ce ke zan iskoki har gidanki nahukuntaki kinji ko?

Gaba daya suka dago suna kallonsa cike da mamaki

Murmushi yayi yace yakuke kallona ko baku gane menake nufi bane

cike da farin ciki ahmad yace friend kana nufin ka amince na auri khadeeja

Gyada kai yayi yace bama amincewa kadai ba nizan shirya komai kuma agidana za'ayi komai

Rungumesa yayi yana dariya mai sauti har yakasa magana

Cike dafarin ciki asma'u tadaka tsalle tafada kan khadeeja suka rungume juna suna murna

Ganin kowa ya rungume dan uwansa fa'iz yajuya yana washe baki garin rungume inna yabige furar dake hannunta tawatsamata afuska

Sadap sadap yatashi yabar wurin tun kafin tabude idonta

Sunjima ahaka kafin kowa ya natsu juyowan da AK zaiyi yaga fuskan inna sharkaf da fura har ba'aganin komai se idonta atsorace yamatsa gefe yana salati

Se alokacin kowa yalura gaba daya suka kwashe mata da dariya seda sukayi mai isarsu tana zaune tana binsu da ido

Daure fuska tayi tace kun gama ai kamar ta ce suci gaba suka kara sa wata dariyar

Tashi tayi tafita tana kwalama fa'iz kira

Umma tace amma abid idan akayi haka ba'ama sarah adalci ba

Murmushi yayi yace Umma nasan zataji wani iri amma kuma hakan shine yadace

Idan taga ahmad zai auri khadeeja dole tahakura dashi tunda tace batason kishiya

" to shikenan amma gaskiya ba agidanka za'ayiba abun seyamata yawa

Kusa da ita yazauna yana fadin ohhhh Umma kefa kikace duk hukuncin danayanke bakida matsala kuma tun ba'aje ko inaba kinfara complain

Murmushi Umma tayi batace komai ba tana gode allah dayabata suruki irin abid Wanda yadauketa tamkar uwa

Kallonsu Asma'u take da murmushi afuskanta tana jin wani yanayi datakasa fassara shi

Daki tawuce khadeeja nabinta
Abaya

Rungumota tayi tabaya tace ammah I am so happy gaskiya AK daban ne what a wonderful surprise !!!

Juyo daita asma'u tayi tana murmushi tace nima nayi farin ciki kanwata zata auri Wanda takeso

Murmushi khadeeja tayi cikin sigar tsokana tace

hmmmm kodai abunda kike ma farinciki daban ba ammah nahango wani Abu a kwayan idonki kamar kinfara son.....

Bata karasaba asma'u tayi saurin fadawa bayi hade da banko kofar da karfi kamar mai tsoron akamata

Dariya khadeeja tayi tafada kan gado tana ma allah godiya

Mutanan gidan kowa nazaune apalo sarah da aysha suka sauko cike dafarin ciki aysha tace kushirya fa zamu sha biki ahmad ya amince zai auri sarah

Carab grany ta amsa da fadin to in yakara guduwa fa

Dariya akasa gabadaya
Inna ameena tace nidai nashajin amarya tagudu ranan aure amma ango kam se akan sarah

Bashir yace gaskiya wannan karon inyagudu za'afara tsoron sarah

sadiya tace sedai muba dai cikin ma'aikatan mu

ahasale sarah ta dakatar dasu akan zata gayama AK inyadawo bashiri sukayi shiru

tashi AK yayi yama Umma sallama suka fita ita kuma tawuce daki kiran asma'u

Suna bakin mota ta iskosu

Bayn mota AK yashiga yana kallon ahmad yace muje ko??

dariya ahmad yayi yajuya yana fadin muje ina ??
Hahaha kuje dai ni sena gana da masoyiyata

Kofar asma'u takama zata shiga yarike yana fadin malama ina zaki shiga

Nan ...tafada tana nuna gefensa

Harara ya watsamata yana nuna mata daga gaba kusan driver yace ga wurinki can inzaki shiga inbakyaso kuma dama kinsaba da hawa mashin

Ganin ba alamun wasa afuskansa yasa tabude gidan gaba tashiga suka tafi
[19/07, 16:58] Hubbey Frd Ameena Kn: 📚📚📚📚📚📚
👨‍👧 _DOMUN KANWATA_ 👩‍👧

Na( *Maryam Mhd*)

1⃣1⃣0⃣

suna isa sarah tazo dagudu tarungumeshi tana fadin Yaya u are the best thank you so much

Dagota yayi daga jikinsa yace banganeba why are u thanking me
menayi

karasowa wurinsu aysha tayi tana dariya tace hmmmm kana so kamana surprise ko to nariga nasani Ahmad zai auri sarah yanzuma daga wurinsa kake

Kusa da grany yaje yazauana yana fadin

Ahmad zaiyi aure amma khadeeja zai aura ba sarah ba kuma nariga nagama magana karnaji wani yace wani abu

Cak sarah tatsaya tana kallonsa da mamaki bakinta bude amma takasa magana

Juyawa tayi wurin asma'u dagudu tahadata da bango cikin gunjin kuka tana fadin wallahi basu isa ba sedai bayan ranta

Saurin tasowa yayi yabanbaro sarah daga jikinta yana fadin sarah wai meyake damunki ne wai yaushe kika zama so stubborn ne

Kwace hannunta tayi takara nufan asma'u tana surutai

Fizgan hannunta yayi yanufi sama da ita yana zuwa dakinta ya wurgata kan gado cikin kakkausar murya yace wallahi kika kara tabata se nasabamiki what is wrong with u

Da mamaki take kallonsa cikin rawar murya tace Yaya ...ni...akan waccan ..

Katseta yayi dafadin ba laifinta bane sarah tayi kokarin hadaki da ahmad amma hakan baiyuwu ba ni nashirya auren dakaina badan nakuntata miki ba sedan kihakura da ahmad kinema wani

Saurin dirowa tayi daga kan gadon tanufi hanyar fita tana fadin wallahi banyarda kai kayi hakan ba Yaya itace tashirya komai kuma wallahi bazan barta ba

Janyota yayi tana kokarin kwacewa baisan lokacinda yadauketa dawani gigitaccen mari ba jikake tasssss

Cak sukatsaya daga ita harshi kamar gumaka

jadabaya tafarayi tana jifansa dawani irin kallo mai cike da mamakin abunda ya aikata

Hannunsa yakalla sannan yakalleta yana matsawa kusa da ita cikin rawar murya yace sarah I am sorry bansan...

Katseshi tayi dafadin karkatabani katafi kabani waje kai ba Yayana bane Yayana bai taba kai hannunsa ajikina danufin dukana ba

Tabata yaje yi tayi saurin shigewa bayi hade da banko kofar da karfi tana kara fashewa da kuka

Fita yayi daga dakin yanufi bangarensa

Dakarfi yatura kofar yashiga hade dazama kan kujera yana dafe kai

Kusa dashi asma'u tamatso adan tsorace tace

Ya....sarah...take...
is she ok...
Chapter 37 · 0% Book details