← Book details Domin Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 84

Sashe 72

Domin Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

afusace yajuyo yana kallonta yace ba abunda zaki gayamun banason jin komai .....every relationship between us ...has been ended
saurin karasowa tayi wurinsa tanakama hannunsa tace ABI please hear me once for the sake of friendship kabani dama takarshe namaka bayani....

Kuace hannunsa yayi yana fadin duk lokacinda nabaki dama se kinyaudareni ....yanzu duk abunda zaki fada bazan yarda dashiba ....I have died with my baby...now nothing is left ....
Saurindagowa tayi tana kallonsa cikin rawar murya tace ABI abanza kake wannan damuwar akan cikin aysha kawai yaudara....

Bata karasaba yakatseta stop...yana hada tafukan hannayansa wuri guda yace nagayamaki namutu I am a dead body now kome zakifada bazan fahimceki ba kuma bazan iya magana dakeba ...ba abunda yayi saura tsakanina dake ....just go away ....yana kainan yajuya yana rangaji yakoma kan gadonsa ya kwanta yabarta atsaye tana kallonsa hawaye nacigaba dabin kuncinta aranta tana fadin zanjiraka bazanje ko inaba harse lokacinda ka shirya saurarata ...I won't do any mistake today yazama dole kasan duk abunda najima ina boyemaka

Grany tana tsaye apalonta tana faman kai kawo duk tadamu Darashin ganin AK gashi tundazu asma'u ta tafi namansa har yanzu shiru jin karan bude kofa yasa takarasa dasauri tana fadin yawwa Asma'u kindawo ina abidi yake meyasa Baku taho tareba ....ganin aysha datayi atsaye yasa tayi daurin cin birki tana daure fuska tace ke mekike anan

Daure fuska aysha tayi tana kauda kai tace garama kimanta dawata asma'u dankema kinsan AK bazai iya cigaba dazama da wacce tayi sanadiyar mutuwar dansa ba ....tunda ya aureta banda wahala da kunci ba abunda ta tsinana mishi ....kirungumi kaddara kawai ki amince ya aureni saboda ni nafi dacewa dashi ...

wani dogon tsaki grany taja tanamata wani banzan nallo tace allah yatsari abidi da aurenki ai ko mata sunkare kikaga ya aureki to kitabbata bana raye

Aafusace aysha tajuya tana fadin nikuma mutuwace kawai zata hanani aurensa se muzuba muga dani dake wazai riga wani mutuwa ....

tana fita daga bangaren grany takira salim awaya tajima tana ringing kafin yadaga baikaiga maganaba tace kai wai kana ina ne ....

Gida ...yafada atakaice

"kamar ya gida wato kai harma kasamu lokacin Hutu ko ....ko kamanta da videon dake hannun asma'u ne ....idan har tanunama AK ita to wallahi duk kudin ubanka bazai hana yadaureka ba

katseta yayi dafadin ke wai ke uwata tace dazaki kirani tsakar dare kinamun masifa ...to tanuna masa mana seme ...

"Kaga salim nifa ba masifa namaka ba gaskiya nagayamaka tunsafe annemi AK anrasa ga asma'u ta tafi nemanshi dan tanuna masa video kuma kasan hakan bakaramar barazana bane wa kuanciyar hankalinmu idan har asirinmu ya tonu wallahi munshiga uku dan kabar ganin AK bashida mutunci ....

Shiru yayi nadan lokaci sannan yace to yanzu miye abunyi.....kingafa ruwan sama ake sosai

"yawwa kagane yanzu ni zanci gaba daneman asma'u kaikuma katayani Neman AK dan allah inaso nasamu ganinsa kafin videon yakai gareshi ....

baijira tagama maganr ba yakatse kiran yana Jan tsaki yace koke da kuke gida daya bakisan inda sukeba senine zan sani ta inama zanfara neman wani AK acikin darennan kuma aruwan sama mtswwwww

dago dakansa yayi yaganta atsaye tana kallonsa fuska ahade yace malama kinemi wuri kizauna ko kimatsa daganan stop staring at me

Saurin karasowa tayi bakin gadon dan duk atunaninta bacci yake cikin rawar murya tace ABI please katashi innuna maka wani Abu idan baka gamsuba nayarda kadauki duk matakin dakake so akaina

Sauka yayi daga kan gadon yanufi toilet yana fadin kawai kina bata lokacikin ne nagayamaki ba abunda zaki fada nayarda dashi koda nabude kofar bawai inason jin abunda zaki fada bane so just shut ...up

toilet din yashiga yatara kansa apanpo yana zuba ruwa saboda azaban dayake masa yajima ahaka kafin yadago kansa yana fitowa Tamika mashi towel tana fadin to shikenan naji karka saurareni amma dan allah kakira grany taan halin dakake ciki she was so worried ko abinci takasa ci bare kuma ayi zancan bacci kuma kasan hakan illa ne ga lafiyarta ....

Tunda tafara magana yake kallonta seda tayishiru sannan yafizge towel din ahannunta yafara goge fuskansa ita kuma tajuya kan bedside drawer tadauko masa wayarsa

Grany nazaune abakin gadonta ga sarah zaune agefenta sunyi jugum suna kallon kofa sukaji wayar grany na ringing saurin mikewa sarah tayi tadauko wayar tana fadin Yaya
Hannu narawa grany takarbi wayar takai kunne tana fadin abidi kaine ya kake kana lafiya daiko?

"lafiya kalau grany kefa ....

"Yo ni ina naga lafiya abidi akacemaka haka ake dan kayi rashi kuma seka guji kowa ga asma'u tundazu taje nemanaka shiru itama haryanzu ko kuna tare ne ...

Juyowa yayi yakalli asma'u datakafeshi da ido sanann yajuya yana fadin a'a banganta ba kuma bansan inda takeba

Shiru grany tayi nadan lokaci sannan ahankali tace to yaushe zaka dawo gida....

"Ki kunata kihuta grany dasafe zamuyi waya bye.....yana kaiann yakatse kiran hade da kashe wayar gabadaya yayi wurgi da ita kan gado

shiga gabanshi asma'u tayi tana fadin meyasa zakamata karya ...

tagefenta yawuce ya zauna bakin gadon yanaci gaba dagoge kansa yace ba karya nayiba ....we are just at the same place but we are not together ....

jiki asanyaye grany ta ijiye wayar tana kallon sarah kafin tayi magana sarah tadafata tana fadin yadai ....lafiyanshi kalau yaushe zaidawo ....

"bansaniba sarah inaji ajikina suna tare da asma'u sedai inajin tsoron kar yadauki matakinda daga baya zamuzo muna damunsani

"Ba abunda zaifaru grany dazaran tagayasa gaskiyar abunda yafaru komai zai wuce ....

"To ai awuya yatsaya ya saurareta ne nasan halin abidi bai iya fushiba dagajin yanda yayi maganar nasan akwai wani Abu akasa

Kamo hannunta sarah tayi tana murmushi tace ...king a grany ki kuantar dahankalinki baabunda zaifaru Yaya yana tsananin kaunar asma'u kuma insha allahu soyayyar ta agaresa bazata tafi abanza ba wannan Daren seyakasance mafi kyewn dare awajansu insha allahu shine farkon fara sabuwar rayuwarsu

Murmushi grany tayi tace to allah yasa haka sarah danafi kowa farin ciki ....

mikewa sarah tayi daga kan gadon takoma kan kujera tana fadin to ai yanzu tunda kinji muryan angon naki se kikunata kiyi bacci kar hawan jininki yatashi

Dariya tayi zatayi magana kenan aysha tashigo dakin tana yamutsa tace wai sarah haryanzu ba'aji labarin AK bane

Daure fuska sarah tayi takauda kai grany tamakamata harara tana fadin to ai tunda saurayinkine kezaki fimu sanin inda yake kuma kifitarmun adaki dan bazan iya yinbacci ba ina kallon wannan fuskar taki

Juyawa tayi afusace tafita tana banko kofar dakarfi aranta tace zanyi maganinku ne ai dazaran na auri AK duk sekun durkusa akan guywowinku agabana kuma intakaku yanda naga dama

AK na kwance yana kyarman sanyi saboda zazzabin dayarufesa garuwan dayawuni kwarama Kansas ya haifarmasa damura

Asma'u nagefe azaune kanta kasa tana tunani atishawan dataji yana jerawa ne yasa tadago kanta azabure tanufo wurinsa tana fadin ABI are OK .....hannunta takai kan goshinsa taji zafi rau cike datausayi taja blanket tana kokarinrufesa ya fizge ahnnunta cikin muryan maijin sanyi yace stop pretending that u care about me ....I don't need it ...yana kainan yaja bargon yarufe jikinsa gaba daya har kansa yana ci gaba da atishawa

Dube dube tafarayi adakin sedai bataga alamun kettle ko flax ba har bayi taduba amma hitter akashe ba ruwan zafi tajima atsaye tanakallonsa kafintajuya aguje tanufi dakin sani koda taje tagama jikewa daruwa da sauri sauri take dokan kofar saboda ruwan da ake shekawa ballale ne yajiba

Seda yaleko ta window yaganta sannan yabude kofar yana fadin ahh hajiya kece dakanki acikin wannan ruwan

batanira yakarasa maganar ba tace ...sani dan allah ruwan dumi nakeso kozan samu

"Gaskiya babu hajuiya sedai udan zaki ita jira se indoramaki yanzu

Murmushi tayi tace yawwa to doramun badayawa ba kamar cikin kopi kuma idan kayi ajiyar citta kadan hadamun aciki

OK.....yafada yanajuya yanufi dan karamin kitchen dinsa itakuma tamatso jikin kofar yanda ruwa bazai tabata ba

ba'adau lokaci ba yafito da glass cup ahannunsa yamika mata tayi saurinkarba tana masa godiya tajuya cikin ruwan takoma wurin AK

dasauri takarasa bakin gadon tana yayemasa bargon tace ABI tashi gawannan kasha zakaji saukin muran dasafe se muje asibiti

kamar karyatsahi sekuma yatashi zaune da kyar yana kyarma tamikamasa kopin yakai hannu zai karba ya hada dahannunta yarike dakarfi yana fadin why are u doing this
"Saboda nagane kuskurena natafiya danayi nabarka dakuma nuna rashin damuwa dakai danayi yanzu kuma inaso ingyara abunda nabata

"was that the only reason ? Yafada yana karban kopin yasake mata hannu daure fuska tayi tace tunda kace bakaso kaji komai meyasa zanfada .....
Shiru yayi yana kauda kai baice komai ba ita kuma tanufi dressing mirror takuance gyalen datayi rolling tafara goge gashin kanta

kallonta kawai yake da cup din ahannunsa lokaci guda yana tuna chitti dinsa ganin zata juyo yasa yayi saurin kauda kai yana kai kofin bakinsa yafara sha yana yamutsa fuska
Karasowa tayi daga gefen gadon ta tsaya tana kallon yanda yakesha ahankali tace badadi ko ....

Girgiza kai yayi yana maida kopin bakinsa yasha sanann yace yanada zafi dai kuma akwai yaji ....
yanda yayi maganar ne yakusa bata dariya suna hada ido tayi saurin gintseta kallonta yake lokaci guda yana tuna lokacinda ta taba kawomasa ruwan dumi kamar haka farkon aurensu baisan lokacin murmushi ya subuce masa ba yayi saurin kauda kai yana daure fuska seda ya shanye ruwan duka sannan ya ijiye kofin akasa yakuanta nan take bacci yadaukesa

aysha nabacci kiran salim ya tasheta tana dauka yace ya kinga AK din ...

Cike datakaici tace eh nagansa gashima azaune muna cin abinci .....bacewa nayi kai kanemosaba ....kawai inabacci kazo kawani tasheni
"Bacci fa kikace harma kinsamu lokacin bacci to kisani gwara ni so dubu ubana yanada kudin belina ke ubanki megaresa kwanta kici gabada baccin inyaso semutaru muyitayi .....
Zatayi magana kenan yakatse kiran yana wurgi dawayar yace wace kaddara cema tahadani dake badan ina using dinki dansamun abunda nake soba (dukiyar AK) datuni banyi watsi dakeba ....yanzu gashi nibaga dukiyar ba nibaga babyna ba to hell with those women....yafada yana kwantawa kan gado sedai Sam yakasa baccin yana tunanin matakinda AK zai dauka aknsu idanhar yaga videon gashi yamishi karyan yana son kanwarsa ....
Chapter 72 · 0% Book details