← Book details Domin Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 84

Sashe 31

Domin Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kofa yanuna mata yana fadin dan Allah malama je ki kuanta kindameni
Talkative girl kawai

Dariya tayi tashinfida blanket dinta akasa tace ai ni yau ma nan zan kuana yafi dadi ...

Washegari dasafe...

Asma'u na goge goge apalo AK yafito cikin shirinsa tsap se kanshi ketashi

Kallonsa tayi tana dariya tace wai har kashiraya wannan har kafi amaryar zumudi

Harara ya watsamata yafita yana fadin Dan allah dai yau dai kiyi shigar kwarai kar kibani kunya gaban abokanai

Yana sakkowa kasa daidai yan sanda sun shigo gidan

Dariya yayi yana kallonsu yace malamai ba yau bane daurin auren gobene

Karasowa sukayi kusa dashi babbansu yace yallabai ba daurin aure mukazoba munzo tafiya dakai ne

Ahasale sarah tace kai karamin da iska mind ur language
Kasan dawa kake magana kuwa

Katseta grany tayi tahanyar daga mata hannu sannan takalli dan sandan tace akan wane dalili zaku kamashi

Shidai AK yayi shuru yakasa magana dan ko ba'afada ba yasan laifinsa

Kallon grany police din yayi yace hajiya yaronki yayi tukin ganganci jiya da da daddare har yakade wani mutun kuma bai tsayaba yagudu da motar to acikin mutanen wurin wani yarike numban motarsa shine suka shigar da kara kuma sunyi kashedin idan dai ba abimusu hakkinsu ba zasu yada ma yan jaridu amatsayin sa na Babban mutum kwa hakan ba karamin bakin jini zai janyomasa ba

Salati inna tayi tana kallonsa tace abidi yaushe haka tafaru baka sanardani ba

Cikin karfin hali yakalli dan sandan yace kunada wata hujjar datanuna ni nayi laifin

Murmushi dan sandan yayi yace kwarai kuwa yallabai saboda mutumin daka kade yaganka lokacinda kake kokarin fitowa daga motar kuma ya tabbatar mana akwai wata mace atare dakai cikin motar sedai bai tantance fuskartaba amma kai yashaidaka

Kuma muje muna so muduba motarka nasan zamu samu wata shaida tunda mutumin akan mashin ka kadesa dole motarka zata nuna

Fita sukayi gaba daya asma'u dafitowar kenan taji abunda yafaru tayi saurin bin bayansu

Waya sarah tadauka takira aysha bugu biyu tadaga cike da takaici sarah tace jiya kunyi accident da AK meyasa baki gayamun ba

Meyafaru ....
Aysha tafada tana yamutsa fuska

Yan sanda sunzo nemanku kina ina ...

Bata karasa ba aysha tayi saurin katse kiran atsorace tama kasheta gaba daya

Suna isa wurin motocin AK yayi saurin nufar motarsa yana kare scratch din dake jikin motar kusa dashi asma'u taje tana fadin jiya kunyi accident ne ?

Girgiza kai yayi baice komaiba
Matsardashi tayi tana kallon scratch din tace to meyasamu motarka
Juyowa yan sandan sukayi suna kallon motar

Dafe kai AK yayi yana fadin ohhhhh chitti bazaki iya yin magana ahankali bane

Janshi tayi gefe cike da damuwa tace jiya da natambayeka meyasa baka gayamun ba kai da waye amotar

Indai bake bace to kinsan aysha ce kidaina mun wawiyar tambaya

Murmushi dan sandan yayi yace yallabai shaidu sun nuna kai kade mutuminnan saboda haka zamu tafi dakai mudawki statement dinka sannan kagayamana wacece tare dakai amotar

Kauda kai yayi yace bakowa atare dani ni kadaine

Kuka grany tafara tana basu hakuri

Riko hannunta yayi yace grany ki kuantar da hankalinki yanzu zan dawo kawai bayanaina zasu dawka

Yana kai nan yashiga motarsa tare da biyu daga cikin yan sandan sukuma suka shiga tasu suka tafi

Cikin gida grany takoma dasauran mutanan gidan

Asma'u kuma nan take tabi bayansu police station

Tana zuwa tayi magana da police din akan yataimaka yahadata da mutumin da aka kade se dakyar yahadata da mutumin

Dafari kin sauraronta yayi seda tahadashi da Allah sannan yatsaya sukayi magana tarokeshi yajanye karar sa base takai ga yan jariduba

Ya yarda zai janye amma setabashi kudi masu yawa

Bayan AK yadawo gida yanemi ganin lawyoyinsa akan maganar

Sunce gaskiya case din yanada girma saboda yahada da tukin ganganci kuma dole se mutumin ya janye kararsa kafin aji da police

Gida asma'u tadawo tadauki sarka da yan kunnanta na zinare da abbanta yataba sayamata
Tazo fita kenan tahadu da AK

Cike da takaici yake kallonta har tafita yana fadin ba ma abunda yadameta yawo kawai tasa agaba

Camun dai ake amma kowa na zillimin abunda zai faru da AK

da rana sega yan sandan sundawo da mutumin da aka kade yasha bandage hannu dakafa

Tunda grany tagansu tafara kuka cike da damuwa sarah tarike AK tana fadin Yaya dan Allah karka bari sutafi dakai

Umma dabatasan abunda yafaru ba tace lafiya mekuma yaka yan sanda

Inna ta katseta tana washe baki tace
Inaga kamun sukazo suma

Juyawa AK yayi yana kallon asma'u dake kan dining tana cin abincinta hankali kuance jiyayi kamar yaje ya shakota dan takaici

Wurin yan sandan yanufa yana fadin muje karna batamuku lokaci

Rikosa dan sandan yayi yana murmushi yace sorry sir bamunzo tafiya dakai bane munzo baka hakuri ne akan shiga lokacinka da mukayi

Da mamaki kowa ke kallonsu

Kamar ya ....

AK yafada yana kallon Wanda yakade

Police din ya nuna mutumin yace wannan ne Wanda ka kade shi yashigar da kara kuma yanzu ya janye

Tukin gangancin dakayi kuma matarka tace bakai bane ke driving din ita tace tana so tayi shine kake koyamata Muncita tara tabiya kuma tabada hakurin hakan bazata kara faruwa ba

Saboda haka zamu tafi se anjima

Tunda yafara magana AK ke kallon sa cike da mamaki yakasa magana har suka fita

Cike da farin ciki grany takalli Wanda aka kade tana mai godiya

Murmushi yayi yace hajiya bani zaki godemawa ba waccan yarinyar zaku godema saboda ita tasa najanye karar

Alama asma'u tamishi da yayi shiru

Murmushi yayi yace a'a yarnan barni nafada kin birgeni matuka da kika tsaya akan matsalar mijinki dan kirufamai asiri najima banga mace kamarki ba

Sarah takatseshi dafadin dallah malam dakata tunda kajanye karar ai sekabar nan da kudin wa tabiya tarar ba kudin gidan nan ba

Bawanda yakulata

Sarkan yanuna ma grany yana fadin kinga abunda tabani akan najanye karar

Da mamki Umma tace asma'u wannan basarkan da babanki yabaki bane shine zaki sayar

Murmushi tayi tace Umma meyasa zan ijiyeta bayan ga anfaninta yazo

Cike da farin ciki grany tace ma mutumin yasaida mata sarkan bada bata lokaci ba ya amince tabashi kudi masu yawa yatafi

Godiya tama asma'u tana samata albarka sannan tabata sarkanta tace kar takara saida sarkan tanada mahinmanci tunda babanta yabata

Bangarensu tanufa dan ijiye sarkan

Aysha ce tashigo gidan adan tsorace dan tahadu da yan sandan suna fita

Kusan AK tamatso cikin rada tace AK naga yan sandan sunfita Allah sa dai baka fadamusu tare Muke ba

Da mamaki yake binta dawani irin kallo yakasa cewa komai
📚📚📚📚📚📚
👨‍👧 _DOMUN KaNWATA_ 👩‍👧

9⃣0⃣

Sosa kai tayi tana kame kame tace kar kamun wata fassara kawaidai natambaya ne

Ahasale yace meyasa kanki kawai kika damu dashi kina ikrarin kina sona ita wacce bata sona bana sonta ta ysaya mun alokacinda nake Neman taimako

Ke kina ina awannan lokacin kuma inada tabbacin kinsan da zancan amma baki dawo ba seyanzu kuma kina tambayar wai nafadi sunanki

Juyawa yayi ahasale yabar wurin
Hannu tadora akai tace nashiga uku ni aysha

Wurin Asma'u yanufa tana shirin shiga wanka ya iskota

Chitti bansan meyasa kika yi haka ba akan wane dalili amma thank you

Daure fuska tayi tace nagayamaka kadaina kirana chitti kuma karma kayi tunanin nadamu dakaine saboda Umma da grany nayi hakan nasan bazasuji dadi idan aka kamaka ba shiyasa so stop thanking me..

tana kainan tawuce bayi

Murmushi yayi yajuya yafita

Yana sauka kasa yazauna kusa da inna yana tambayarta abba

Fira suka fara yi suna dariya

Kusan sarah aysha tamatsa tana gayamata yanda sukayi da AK takare dafadin

Yanzu zaiga kamar asma'u tafi damuwa dashi ni bandamu ba

Sarah tace to ai dagaskiyansa kema wayakaiki yimai wannan tambayar

Tsaki aysha tayi tana kallon Ali tace ni wallahi guy dincan tunda nashigo yake kallona bai San haushi yake bani ba
Dariya sarah tayi tabar wurin

Kiran kowa tayi akan za'afara rawa sawrayi da budurwa mata da miji

Ai kaman jira Ali yake yazo wurin aysha wai suje suyi rawa Da har taki amma dataga AK na kallonsu tamike suka fara rawa

Inna ameena tace AK yatashi suyi da Asma'u

Dariya yayi yace bata iya rawa ba

Daure fuska tayi tace kamar ya daga ganinta zatayi kyew da rawa kirata kuyi

Murmushi yayi yace kedai kawai kice tabirgeki amma wane kyew da rawa yarinya kullun alullube

To ai shine kyen ni duk nan wajan banga yarinyar da lullubi yakema kyew ba kamar Asma'u

Dariya yayi yace akwaisu dayawa ma

Ina suke

Waige waige yafara can yahango wata yarinya atsaye ta juya baya tana magana dawata

Nuna ta yayi dayatsa yace gawata can

To tashi kirata muganta

Gyara kuanciyar sa yayi kan 3siter yana fadin dan Allah kibarni ba inda zani

Jan kafanshi tafara tana fadin tashi dai ka kira ta inkasan da gaske kake ni ban yarda ba se naganta

Tashi yayi yana yarfa hannu yanufi yarinyar

Bayanta yatsaya yace hello !!!

tana juyowa yaga asma'u tana murmushi tace hi!!!
How me I help u

Juyowa yayi yakalli inna ameena tana kwasan dariya
Sannan yakalli asma'u da mamaki yace meyasa zaki canza kayan jikinki

Murmushi tayi tace saboda nayi wanka idan abunda kazo tambayata kenan sekatafi ....

tana kai nan tayi gaba abunta

Juyawa yayi yana kallon su aysha dake rawa haushi yaji yabar wurin

Murmushi tayi dan ganin AK yana kishinta

tana ganin yatafi tadaina rawan takoma tazauna

Kusa da ita sarah tazo tazauna tana mata magana akunne suna kallon fa'iz da yadage yana daukan khadeeja photo
Ita kwa se daure fuska take tana kauda kai

Dariya sukayi suka tafa hannu sannan sarah tace je kifito da jakan kidora kan gado bari nakirashi

Aysha natafiya sarah takira fa'iz tace yaje dakinta ya dawkomata jakanta yaso yaki tace zata gayama Umma hakanan yatafi yana gunaguni

Aysha nashiga dakin AK yaturo kofar atsorace ta jiyo tana kallonsa

Kusa da ita yamatso yana fadin rawa kike dawani agabana ko ??

Murmushi tayi tace to ai nadauka kadaina sona ne tunda kayi aure
Ashe kana kishina

Rungumota yayi yace ina sonki amma kishindai ban saniba dan banji komai ba lokacinda naganko
Chapter 31 · 0% Book details