← Book details Domin Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 84

Sashe 53

Domin Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rike cikinta tayi tanajin wata azababbiyar yunwa na damunta gashi tarasa inda AK yaje cikin wannan dajin jin kamar motsin mutun yasa tayi saurin mikewa atsorace taleko waje

ganin AK datayi zaune abakin rafi yasa tasauke wata nannauyar ajiyar zuciya tana murmushi ta nufo inda yake

Dagowa yayi yana kallonta da murmushi afuskansa yace kin tashi

Kusa dashi tazauna tana dafa kafadansa tace ya jikinka

Mangoron dayawanke yamika mata yana fadin naji sauki tundazu yunwa ta tasheni bashiri natafi neman abinci

Murmushi tayi tana kai mangoron bakinta tace thank you

kafanta yariko da hannunsa yadora kan cinyarsa yafara kwance daurin yana mata sannu

dagowa yayi yana kallonta yace kidaina taka kafan kinga ya kunbura sosai yanzu kibarshi haka yanashan iska kar yazame maki babban ciwo

Shiru tayi batace komai ba tacigaba da shan mangoronta tana kokarin hada kalmomin dazatayi anfani dasu wurin gayamasa abunda ke ranta

Wanke hannunsa yayi shima yadauki mangoron yafara sha suna kallon ruwan dake gabansu bawanda yasake magana

Sun jima ahaka secan yadago yana kallonta da murmushi afuskansa cikin sassanyar murya yace

Kinkosa ki koma gida ko ?

girgiza kai tayi tace nayi kewar gida amma I like it here

"Why

dagowa tayi tana kallonsa suka hada ido lokaci guda suka tsinci Kansu awani irin yanayin dasuka kasa fassara ma'anarsa

Cikin murya mai kaman rada tace ABI aduk lokacinda nake tare dakai banadamuwa da kowane wuri muke cikin dadi ne ko wahala duk hakan baidameni ba indai zan kasance kusa dakai ada nadauka sabone ko shakuwa amma daga baya natabbatar dacewa abunda nakeji shi ake cewa SO

Bansan yaushe kuma a ina nafara sonka ba amma abunda nasani kawai shine sonka yajima azuciyata

ABI so dayawa mutane suna tsoron fito da sirrin zuciyarsu ne saboda gudun kar su rasa kulawar dasuke samu daga wurin wa' inda suke so

Ni kaina abunda nake tsoro kenan amma bazan iya ci gaba da boye sonka araina ba

tunda tafara magana yake kallon kwayan idanuwanta ko kiftawa bayayi yana hango tsantsar kaunarsa acikinsu

Kauda kansa yayi cikin wani irin yanayi dayayi mai kama da mafarki

Hannunta tasa ta janyo fuskarsa saitin tata idonta cike da hawaye cikin sassanyar murya tace

ABI I am not asking u to love me

base kasoni ba kawai kabarni naci gaba da sonka and please kar kacanza mun nariga nasaba dakai idan kayi nesa dani bazan iya jurewa ba

tana kainan ta tashi tanufi runfarsu aguje tana sharan kwalla

Da kallo yabita har tashige runfar bai kauda kansaba lokaci guda kalamanta namai yawo akwakwalwa yana tuna rayuwarsu tabaya da wadda sukayi acikin dajin nan

mikewa yayi tsaye yasa hannayansa a aljihu yana safa da marwa awurin yarasa meyake damunsa awani hali yake ahin shima yana sonta ko kuwa

yana cikin haka kamar daga sama yaji maganar yaran JJ akusa dasu

saurin juyawa yayi aguje yanufi runfarsu

Zaune ya iskota kan tabarma ta takure wuri guda tana jin haushin kanta datagayamasa tana sonsa yanzu tasan shikenan abunda take gudu ne zai faru zai janye jikinsa daga gareta

Saurin karasawa yayi wurinta ya durkusa agabanta cikin rada yace chitti gasunan sun iso kitashi mugudu

atsorace tamike tsaye tana zare idanuwa

riko hannunta yayi aguje suka fito daga cikin runfar sedai kafin sugudu JJ sun iso wurin shan gabansu yayi ya saitasu da bindiga yana kwashewa da dariyar keta yace

Dakata mana AK ina kuma zakuje ai gudu yakare daga yanzu zaku huta muma muhuta da wahalar bibiyarku

Cak sukatsaya suna kallonsa ba alaman tsoro atare dasu

cike da takaici AK yace to mekake jira kaharbemu mana

Wancan karon ma sakacinka ne yasa muka gudu to yanzu ma inkayi wasa guduwa zamuyi

kuma kasake nabar nan wurin to daganan nine zanfara nemanka kana guduwa idan kuma nakamaka bazaka taba samun damar dazakayi kwakkwaran motsi bama bare kayi yunkurin guduwa

Kallon yaransa yayi suka tuntsire da dariya seda sukayi mai isarsu sannan ya saita bindigarsa kan AK yana kirga uku

Kuka asma'u take tana kankame AK ajikinta se rokonsu take karsu kasheshi amma banda dariya ba abunda suke dai daga cikin yaran yasaitata da bidiga yana fadin kar kidamu yan mata ai tare zaku tafi bahaka kuke soba

rungumota AK yayi akirjinsa takara kankamesa dakarfi tana runtse idanuwanta

JJ na kirga uku yadora yatsansa kan kunamar bindigar zai harba kenan yan sanda suka iso wurin tare da ahmad

nan fa aka fara musayar wuta tsakanin yan sandan da su JJ

Tundaga nesa ahmad ke kwalama AK kira yana fadin su gudu

tsaye AK yayi cike dafarin ciki yana kallon ahmad se washe baki yake yakasa motsawa gashi se harbi ake da bindiga amma ko ajikinsa

Jan hannunsa asma'u tayi dakyar yabar wurin suka ruga aguje sukayi wata doguwar hanyar dasuka gani

Sunyi tafiya mai nisa kafin suka iso wata kasuwar kauye da mutane dayawa awurin kowa na harkan gabansa

tsaye sukayi awurin suna maida nunfashi

Cike da takaici AK ya kalli mutanen wurin yana jan tsaki yace yanzu duk wahalar da mukasha ashe akwai dubban mutane anan wurin amma ko tsuntsu bamu gani ba
[19/07, 17:05] Hubbey Frd Ameena Kn: 📚📚📚📚📚📚
👨‍👧 _DOMUN KANWATA_ 👩‍👧

Na( *Maryam Mhd*)

1⃣5⃣5⃣

hannunta narawa takarbi result din tana dubawa tajima azaune awurin hawaye natsere akan kuncinta dakyar tamike tsaye tana neman faduwa saboda jirin dake dibarta

saurin mikewa doctor yayi yana fadin easy madam are u alright

Bata kula saba tafita daga office din tana Jan kafa kamar wacce aka zarewa lakka

zama tayi acikin motarta tadafe kai cikin rawar murya tace what....what... have I done ...I am ...such a fool

garin ya nabari haka tafaru wane mataki dady zai dauka akaina ya AK zai yi idan yasan ina dauke da *cikin da banashi ba*

fashewa tayi da kuka tana fadin *SALIM* kacuceni yanzu yazanyi ni aysha nashiga uku

Tajima tana kuka kafin tayi saurin daukar wayar ta takira wata number

Tajima tana ringing kafin yadaga cikin muryan bacci yace

Baby kintuna dani yau shine zakimun kiran asuba na....

Katseshi tayi da fadin salim kana ina ne we have a problem

Dariya yayi yace anzo wurin dama ai bakya nemana se kinada matsala

fashewa tayi da kuka tana fadin salim please it's a serious problem I am .....

Saurin tashi zaune yayi yana fadin ohh my god baby are u crying

Shiru tayi batace komai ba taci gaba da kukanta

Ajiyar zuciya ya sauke yana kallon agogon dakin yace ok ni... ina gida yanzu zakizoni ko inzo insameki

tada motar tayi tana fadin a'a ganinan zuwa yanzu

daidai wani katafaren estate tayi horn mai gadin yaleko yana ganinta ya washe baki yana fadin ahhh beautiful barka dazuwa ....

Harara tamaka mai tana jan tsaki tace kai dallah open the get for me I don't have time for u nonsense

Budemata get din yayi tashiga tana gama parking tafito da gudu gudu take hawa stairs

ahawa nabiyu tatsaya dadai wani hadadden apartment tayi knocking

bata jima atsaye ba aka bude kofar

wani dan kyekkyewan saurayi ne atsaye yana mata murmushi

( salim kenan saurayin aysha ne tun tafiyar dasukayi London itada sarah tahadu dashi tun tana wulakanta shi har tafara kulashi saboda tako ina yahadu yasan duk wata hanya dazaibi yashawo kan mace ya iya soyayya gashi yana sakemata kudi kamar hauka

Kwararen lawya ne maizaman kansa yanada kudi daidai gwargwado gashi shikadai ne awurin babansa shiyasa yazama dan gata duk abunda yakeso shi akemai

Wata rana aysha tazo gidansa tana kuka saboda damuwar rashin kulawar AK dabata samu

Garin lallashinta ne har suka wuce gona da iri shine wanda yafara saninta ya'mace kuma daga ranar ciki yashigeta

Idan yamata maganar aure setace tana so se ta mallake dukiyar AK gaba daya sannan zata aureshi saboda shine burinta da na iyayenta

tun bayaso har tanuna mai irin ribar dazasu samu tagayamai kadan daga cikin kadarorin AK tun daga lokacin shima yafara kwadayin dukiyar )

kauda kai tayi tana share kwalla

Janyota yayi ciki yana rungumeta yace baby I missed u so much

Turesa tayi tawuce Palo tazauna tana rabka uban tagumi

Karowa yayi kusa da ita yazauna yana fadin come on baby banason ganinki haka gayamun damuwarki kinsan uwarki ta haifeki ne dan kikawo matsala nikuma uwata ta haifeni dan na magance maki ita

hararansa tayi tace kafara ko???

Dariya yayi yana shafa kai yace sorry namanta ne yanzu gayamun meyake damunki

ciro result din tayi daga Jakarta tana nuna masa tace salim inacikin babbar matsala dama na gayamaka banajin dadi to yanzu haka daga asibiti nake doctor ya tabbatar mun inada ciki

shiru yayi yana kallon result din nadan lokaci sannan yadago yana kallonta yace

look aysha nafasan halinki idan kina bukatar kudi ba abunda bazakiyi ba idan kinsan karya kike to garama kifito kigayamun sannan kinsan ko nawa kike so zan iya baki but don't play games with me

riko hannunsa tayi tana kuka tace salim allah dagaske nake idan baka yarda ba muje tare dakai kagani

Dafe kai yayi yana tunanin ta inda zai bulloma lamarin kamar daga sama yaji tace

Salim nidai tsoro nakeji gaskiya muje acire cikinnan

Saurin dagowa yayi yana nunata dayatsa cikin kakkausar murya yace

Kar ma kifara aysha bakida hankali ne zubarwa fa kikace

to wallahi kinji narantse kar ki kuskura kizubar mun da ciki kinji ko ina son abuna

rungumeshi tayi tana fashewa da kuka tace salim tsoro nakeji idan dady yasani zai kasheni sannan kuma .....AK idan yagane inada ciki zai rabu dani kaga bazai aureni ba bare har mucimma burinmu

Shafa kanta yayi yana fadin stop crying baby nothing bad will happen kin manta ina tare dake yanzu dai zauna muyi magana

Zaunawa tayi tana ci gaba dakukanta

Share mata hawaye ya shigayi yana fadin ya isa haka kidaina kuka mana ko kinaso wani abu yasami babynmu ne

girgiza kai tayi tana shafa cikinta hannunsa yadora kan nata yana murmushi yace love u my baby

tashi yayi yanufi kitchen bayan dan lokaci yafito rike da fresh jus acikin glass cup yamika mata

Kusa da ita yazauna yana sauke ajiyar zuciya yace yawwa to yanzu kinsan ya za'ayi

Girgiza kai tayi tana ijiye cup din hannunta akan table takureshi da ido takosa taji mezai fadamata

murmushi yayi yace ya zancan AK anganshi kuwa ?

Kauda kai tayi tana fadin sundawo jiya
Chapter 53 · 0% Book details