← Book details Domin Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 84

Sashe 39

Domin Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wayarta ta dauka takira numban khadeeja

bugu biyu tadaga tare da sallama

Shiru tayi nadan lokaci sannan cikin dasashshiyar murya tace

sarah ce nakira namiki barka ina tayaki murnan samun ahmad amatsayin mijinki amma ni kuma zanbaku wedding gift din sekun mutu baku manta dani ba kigayama ahmad idan har bashi arayuwata to batada wani anfani

tana kainan takatse kiran

mamaki ne Yakama khadeeja tana maimaita wedding gift

saurin kiran asma'u tayi tana dauka tagayamata yanda sukayi da sarah

atsorace asma'u tamike tana fadin me sarah zata aikata

ohh my god ....tafada tana fitowa dagudu daga dakin

aguje tanufi dakin sarah tana bugamata kofa amma shiru

aysha ce yazo wucewa tadawo tana fadin malama lafiya what is ur problem

Banza tayi da ita takwala ma nura kira yazo suka fara balla kofar

aguje tafada dakin sedai cak tatsaya tana kallon sarah dake kuance ga hannunta duk jni alamun yanka awurin

Durkushewa tayi akusa da ita tana kuka aysha ma hannu tadora akai tafashe da kuka

ganin jinin baitsayaba yasa asma'u tayi saurin yaga gualenta tadaure wurin sannan aysha ta taimaka mata suka kaita mota se asibiti

Suna zuwa aysha takira AK awaya seda takusa katsewa yadaga yana fadin baby I am busy zan kiraki anjima

Cikin rawar murya tace AK sarah ta kashe kanta kayi sawri kazo asibiti

Dariya yayi yakatse kiran yana kallon ahmad dake kusa dashi yace kaji wani shirme wai sarah takashe kanta

azabure ahmad yamike yana salati yace AK yana yiwa dagaske ne kasan sarah fa bata iya shiga damuwa ba

"No wasa ne nasan aysha tana mun irin wannan wasan in tanason ganina

Girgiza kai ahmad yayi yace a'a AK nifa tsoro nakeji kar azo dagaskene kakira grany ko asma'u mana

Wayansa yadauka ya lalubo numban asma'u dayayi saving da chitti yakira
yana fara ringing tadaga tana fadin ABI ina kashiga ina kiranka bana samu

kazo asibiti sarah bata jin dadi

Azabure yamike yana fadin meyasami sarah kina nufin dagaske tamutu

cikin rawar murya tace a'a bata mutu ba ABI kaidai kawai kazo

aguje yafita daga office ahmad nabinsa abaya

Cikin minti 30 suka iso asibiti yana isa doctor nafitowa wurinsa suka nufa atare suna tambayar ya jikinta

Kallonsu yayi daya bayan daya sannan yace dafari dai inaso insan wa yadaure mata hannu da kyalle

baigama rufe baki ba aysha tayi saurin nuna asma'u dayatsa tana fadin wannan ce

juyawa sukayi atare suna kallonta sanan suka maida kallonsu kan doctor

itama asma'u kallonsa take dafargaban abunda zaifada

Murmushi yayi yana kallonta yace gaskiya kinyi dubara mai kyew saboda badan kinyi hakan ba da kafin kuzonan tarasa jni mai yawa kuma jijiyarta zata ita bushewa ko iska yakai ga zuciyarta hakan kuma shi zaisa tarasa ranta amma yanzu alhamdulillah taji sauki zaku iya shiga kuganta sedai akula irin haka kar takara faruwa

Sannan yakalli AK yace muje office ina son ganinka

gaba yayi AK da ahmad suka bisa abaya aysha kuma tashiga dakin da sarah take

Nuance take tana kallon sama hawaye nazuba a idonta ga igiyar Karin jini ana mata
se hannunta da aka ma bandage

Kusa da ita aysha tazauna tana fadin sannu sarah gaskiya AK bai kyewta miki ba koda yake ba laifinsa bane wannan munafukar yarinyar ce tasashi wayasan metagayamasa ...

Muryan asma'u tajiyo tana fadin tashi kifita

Juyowa tayi tana hararenta tace dawa kike kehar kin isa kice nafita

dan karamin table din da ake dora magunguna ta rarumo tanufota dashi bashiri tayi waje aguje har tana bigewa da kofa

ijiye table din asma'u tayi takarasa kusan gadon tana duba hannun sarah

Kwace hannunta tayi tana fadin wayace ki kawoni asibiti meyasa baki bari namutu ba tunda natabbata abunda kike so kenan

Kusa da ita asma'u tazauna tana fadin sarah kina bani mamaki idan kikayi wani abun kamar wacce batayi karatu ba yanzu idan kika kashe kanki riban me zakici Wanda kikayi danshi zai danyi jimamin lokaci kadan daga baya kuma yamanta yayi aurensa yacigaba da rayuwar farinciki

Yanzu dazan tambayeki da allah da ahmad wakika fiso zakice allah amma kuma kinyi kokarin aikata laifin da allah bazai yafemaki ba saboda ahmad

Akan rayuwar duniya kikayi kokarin ruguza ta lahirarki

Miye laifin AK dazaki daga mai hankali yana matukar kokari wurin faranta miki amma ke kanki kawai kika sani bakya tunanin halin dazai shiga idan kika aikata wannan kazamin aiki

Sarah kefa macece mata ansansu da juriya da danne soyayya aransu saboda gudun wulakanci amma ke kinkasa yin hakan shiyasa kike wahala
Ki godewa allah dayabarki da ranki yana sonki shiyasa baidauki rankiba yabaki dama akaro nabiyu dan kyallen danasa maki bashi yahanaki mutuwa ba lokacinkine baiyiba

Bakowa yakesamun irin damar dakika samu ba yau da kin mutu da zaki dawwama kina nadama har abada

ina gayamiki hakane ba amatsayin asma'un dakika tsana ba

Ina gayamikine amatsayin musulma kuma mace yar uwarki

Ga glass nan da wukake kina iya dauka kikara yanka hannunki ko wuyanki amma kisani ba kyada hujjar dazata hana allah yakonaki

tana kainan ta tashi ta fita daga dakin

Tana fita AK da ahmad nashigowa aguje AK yakarasa bakin gadon yana kallonta cikin rawar murya yake fadin

sarah why!! Why sarh!! Why!!

yakasa cigaba da maganarsa se hawaye dake zuba daga idonsa

Itama kukan take tana fadin yaya i am sorry

dafasa ahmad yayi yace friend kaje waje zanyi magana da ita

fita AK yayi yana sharan kwalla gefe guda yaje yazauna hade da dafe kai

AK nafita ahmad yadawo kusan sarah yazauna cikin sassanyar murya yace

Sarah base kinfadamun dalilin dayasa kika aikata hakan ba nasan saboda kinji zanyi aure shiyasa

Na fahimci halin da kike ciki saboda nima nashiga wannan yanayin abaya

sarah nasan kina sona kuma nagode da kaunarki agareni amma bayanda na iya sarah

Ina miki kallon kanwata ne kuma kawata idan kika hakura kika manta dakomai zanci gaba da kallonki ahakan amma idan kika kara aikata wani abun to zaki rasa wannan matsayin awurina

Shiru tayi tana kallonsa takasa cewa komai

tashi asma'u tayi tanufi inda AK kezaune tazauan kusa dashi

Dagowa yayi yakalleta yakara maida kansa kasa

ahankali takai hannunta tadafa kafadansa cikin sigar lallashi tace

kar kadamu kaji she will be fine
dagowa yayi yana kallonta da jajayen idanuwasa cikin rawar murya yace chitti meyasa sarah zatayi abunda ko jahili bazai yiba meyasa zata zabi tarabu dakowa nata tahadu da fushin ubangiji akan tarasa ahmad

bazatayi tunanin halin da zan shiga ba bana kewar iyayenmu saboda ita da grany aduk lokacinda nakalleta fuskan ummarmu nake gani atata

hawayene suka zubo daga idanuwansa yacigaba dafadin

Chitti nasan zakiyi tunanin nabata sarah dayawa ko duk abunda takeso ina mata kinsan dalili ?

Girgiza kai tayi hawayen datake makalewa suka zubo

cije lebensa nakasa yayi yana saita muryansa yace

Tun ina karami nataso ina son yima iyayena hidima inaso naga sunkawo bukatrsu namusu kodan naga murmushi afuskansu ta dalilina

Naci burin yi musu hidima na kyewtata musu in sungirma amma allah bai kaddara ba

Kinga sarah to yadda take haka ummana take ita kuma grany sak yanda take haka abbana yake

daga ranar da suka rasu daga ranar duk wani son danake masu da burin kyewtata masun danake yakoma kan sarah da grany haka nataso har kawo wannan lokacin banason ganin abunda yabata musu rai ko sun nemi Abu sun rasa amma gashi yau nakasa wurin farantama kanwata ...muryanshi ne yakarye yakasa cigaba damagana

Hannu takai tana share mai hawaye cikin muryan kuka tace

ABI kai ba allah bane mutum ne duk yanda kaso ka kyewtata musu dole wata rana sunemi wani abunda su rasa kuma dama haka rayuwa take kowa kaduba akwai abunda yakeso yakasa samu

ABI u are not just a brother but u are a real hero

kayi ita kokarinka sauran kuma sekabarma allah amma please stop blaming ur self

Gyara zamanta tayi tana kallonsa cikin sigar tsokana tace

Yanaga kayi saurin karayane ko kamanta maganr damukayi jiya idan bazaka iya samomata ba ni kabani dama nasamo mata handsome guy

Murmushi yayi yace a'a nizan zaba dakaina ke kinsan handsome ne

haka kawai kije kidaukomata dan jagaliya murasa yazamuyi dashi

Kwaikwayon yadda aysha tashigo jiya tayi tana fadin
wai me kadaukeni ne naga fa kana nema karaina mun class dina

Dariya yayi yace to ya isa masoyiyar tawa kike kwaikwayo komai abunki dai bazaki kaita haduwa ba

"Allah sedai in banyi niyya ba abun ai ba wuya ne dashiba nidai kawai banda lokacinsa ne

tashi yayi suka nufi dakin sarah

Rungumeshi tayi tana kuka tace
Yaya na amince nahakura ahmad ya auri khadeeja

Dagota yayi da mamki yace dagaske kin amince amma abunda da mamaki da zaki kashe kanki yanzu kuma kin amince kodai kin hango malakal mauti ne

kara rungumesa tayi tana murmushi tace Yaya kabari banaso

dariya sukasa gaba dayansu banda aysha dake jifan sarah da kallon tuhuma

Dagowa tayi tana kallon asma'u tace sister nagode dakika ganar dani abunda nakasa ganewa tun tuni
Gaskiya ke tadabance thank u once again

Juyowa AK yayi yana kallon asma'u da murmushi afuskansa

Sunkuy dakanta tayi itama tana murmushin

Da yamma aka sallemesu suka dawo gida dakin sarah suka fara zuwa seda ta kwanta sannan suka fita akabari daga ita se aysha

Bayan kowa yafita aysha tazo tarufe kofar da key takoma kusan sarah da mamaki tace sarah what is ur plan?

kauda kai sarah tayi tace kamar ya ?

"Hahaha sarah kar kirainamun hankali nafasanki kamar yunwar cikina u won't give up easily
Ya akayi haka

Share hawayenta tayi tace to aysha yazanyi ahmad yariga yazama na khadeeja Dana tsaya inaba kaina wahala ba gara nafita hanyarsu ba nima nayi addu'ar allah yabani mijinagari

Hanyar fita aysha tanufa tana fadin kin bani mamaki sarah Ashe bama son Ahmad kike ba kawai cika baki ne

Dakallo sarah tabita har tafita sannan tarufe idonta ahankali hawaye nagangarowa gefen fuskarta

Aysha nafita wurin AK tanufa yana zaune apalo ta iskosa kusa dashi tazauan tana shagwabe fuska tace darling wai mekake jira da yarinyar nan ne naga bakada niyyar korarta daga gidannan
Chapter 39 · 0% Book details