← Book details Domin Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 84

Sashe 42

Domin Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"eh mana yacemun yana hanya fatana dai kawai AK yadawo kar yakwapsa mana

"Karki damu nasan zai dawo

Suna nan atsaye Sega Ali ya shigo gidan se shan kanshi yake yana shafa saje

Dariya sukayi suka tafa hannu

kiran aysha yayi awaya tadauka cikin muryanta mai jan hankali tace sweetheart ka iso

"eh baby kina ina ne nakosa naganki

danni inba naganki akusa dani ba bazan yarda wai dagaske bane

Tabe baki tayi tace I am in my room can u meet me there

" tsalle yadaka yana cije yatsa yace why not baby just tell me where is the room

dariya tayi suka tafa da sarah sannan tamai kuatancen dakin su asma'u tace yasameta acan

Dakallo suka bisa har ya haura sama sannan suka fito suka shiga dakin aysha sarah tace idan muka tabbatar yashiga se murufe kofar kinga idan AK yadawo ba abunda zai hana yagansu tare daga nan kuma .....
Kinsan sauran

ahankali yatura kofar yashiga sedai yaga bakowa adakin zai juya kenan yaji motsi a dressing room
Komawa yayi ya kuanta kan gado yana fadin come out baby i can't wait to see u!!!!

asma'u na dressing room tana sa kaya batasan meke faruwa ba tana fitowa tagansa rigingine kan gado

cak ta tsaya tana kallonsa kamar amafarki tama kasa tantance mafarki takene ko gaske Alin datasani ne ko maikama dashi daga ina yake meyakawosa dakinta

tana nan tsaye taji anturo kofa atsorace suka kalli kofar suduka

Nunfashinta ne yakusa daukewa ganin AK tsaye bakin kofa kamar gunki se rawa jikinsa keyi ga idonsa daya rikide yayi ja kamar gawta
sorry.....
Yafada cikin wata iriyar murya yana barin dakin dakyer yake tafiya danwani jiri ne ke dibarsa

wasu zafafan hawayene suka zuboma asma'u cikin rawar murya tace Ali meyakawoka dakina mekakeyi anan Ali wannan wane kalan tumasanci ne kayi haka

atsorace yamike tsaye yana fadin asma'u mekike nufi kar kicemun nan dakinkine nashigo dan allah

Girgiza kai tayi tafita daga dakin tana sharan kwalla

apalon kasa ta isko AK azaune yadafe kai matsowa tayi kusansa adan tsorace tace ABI I....

Dakatar da ita yayi tahanyar daga mata hannu yace no don't say anything

Saboda komai zaki fada bazai maki anfani ba chitti u why ..........just leave
Juyawa tayi tana fashewa da kuka

karo sukaci da Ali yana sakkowa zaiyi magana tadakatar dashi cikin rawar murya tace

Bansan meyasa kayi hakan ba amma kasani idan har wani Abu yasami aurena I won't spare u

tana kainan tawuce da gudu tashige bangaresu
[19/07, 17:03] Hubbey Frd Ameena Kn: bayanda batayi da AK ba akan ya yarda da ita amma yaki cikin sheshshekar kuka tace ABI wai me kadaukeni ne
Taya kake tunanin zan aikata abunda tun ina gidanmu banyishi ba se yanzu dayagiyar aure ta haw kaina why will I do that

Dagowa yayi yana kallonta da jajayen idanuwansa cikin kakkawsar murya yace ni ne zantambayeki mekika daukeni asma'u da ace bani naganku da idona ba wani yagayamun dabazan taba yarda dashiba amma kinbani mamaki bansan dalilin dayasa kika kasance haka ba amma kisani na ysaneki banason ganin fuskar ki kije.....

atsorace takai hannu ta toshe mai baki cikin tsananin kuka tace a'a a'a ABI dan allah karkamun haka

katausayama ummata wallahi zata iya rasa ranta

ABI kayarda dani wallahi bantaba aikata irin wannan kazamin aikin ba bansan meyakawoshi dakina ba I am confuse ni kaina bansan meyake faruwa ba

Bige hannunta yayi daga kan bakinsa ya mike tsaye yana juya mata baya yace

Sanin kanki ne cewa koda ina sonki bazan iya cigaba dazama dakeba karma kiyi tunanin kishinki nake a'a kawai ina takaicin yanda kika ari rigar mutunci kike aikata abunda kikaso kowane mai laifi daya musanta lafinsa yana bukatar abashi dama yagabatar da shaida

Juyowa yayi yana kallonta yace to nima zan baki dama just 24 hours kikamun wata shaida dazata nuna baki aikata abunda nake zarginki akai ba yana kainan yaraba tagefenta yawuce yana fadin karki manta awa 24 kawai nabaki idan har suka cika baki kawomun shaida ba to karma kijira se nakoreki dakaina dan bazaki ji dadi ba

Dakallo tabisa har yabacemata sannan takuantar dakanta kan kujera tana rera dan marayan kukanta mai ban tausayi

sarah dake labe tana lekenta ta wuce daki tana kwashewa da dariyar mugunta seda tayi mai Isarta sannan aysha tace sarah nifa binki kawai nake a plan dinnan amma bangane Kansa ba

Dariya tayi tana zama kan kujera seda tajima tana dariyar keta sannan tanatsu tafara magana kamar haka

idan baki manta ba kintaba gayamun cewa kinji lokacinda asma'u ke ba AK labarin wannan Alin yaso ya aureta which means tsohon saurayinta ne

Su maza suna wani hali Wanda koda basa son mace to dazaran andaura musu aure da ita zakiga suna kishinta

Shikuma kishi yana daga cikin abubuwan dakesa maza saurin sakin mace musamman irin wannan

Nabukaci dakija hankalin Ali ajiya saboda inaso ya yarda cewa kinasonsa dan musamu yamana aiki cikin sauki

danatabbatr ya amince zai zo yau to se nafara tunanin hanyar dazanbi nahana asma'u fita raka grany batare dakowa yasan ni nahanata ba

Shiyasa naje nasameta dacewa akwai wani saurayina dazaizo yau kuma banaso kowa yasan dazuwansa inaso tazauna mumasa girki dasauran su ba bata lokaci ta amince

lakacinda taki tafiya raka grany nahango rashin yarda da ita karara a fuskan AK kuma hakan shiya taimaka aikina yazo dasauki

Bayan Ali yazo muka turashi dakin asma'u naso ace munje munkulle kofar dakin sekowa yadawo ya iskosu tare bansan meyadawo da AK dawuriba amma duk dahaka komai ya je daidai

Dariya aysha tayi tana tafa hannu ta jinjina ma Sarah sannan tace to ya ake ciki yasaketa ne

girgiza kai tayi hade da tashi tafara kaikawo adakin tana fadin baisaketa ba bansan meyasa yake tausaya ma wannan ummar tata ba

yabukaci takawomai shaidar dazata wanketa amma nasan ko mezatayi bazata taba samun shaida ba ina mai tabbatar miki dacewa nan da gobe dole tabar gidannan daga nan kuma senaji da khadeeja

dariya aysha tayi cike dafarin ciki aranta tana fadin Weldon sarah kinmaida mun aikina mai sauki batare Dana wahala ba

AK yana fita wurin ahmad yanufa yazayyane masa kap abunda yafaru har lokacinda yabama asma'u

damamaki ahmad ke kallonsa har yagama bashin labarin sannan yamike cike da takaici yace AK badai kana nufin kayarda asma'u zata aikata abunda kake zarginta dashiba bansan wacece itaba amma I am 100% sure bazata taba aikata haka ba

"oh to zanmata karyane ko kuma ni makaho ne incemaka da idona nagansa haba ahmad

adakina fa nagansa akan gadona she was standing there looking at him kuma kacemun wai bazatayi hakan ba

To gayamun meyakaishi dakina meyake akan gadona idan ziyara yakamata meyasa basu zauna apalo ba haba ahmad nifa ba sakarai bane

ajiyar zuciya ahmad yasauke yana zama kusa da AK cikin sassanyar murya yace

inaganin kamar dama yayi hakan dawata manufa ne maybe yanajin haushin auren datayi ne.... ko kuma har yanzu yana sonta ...badai banza ba AK amma baikamata kazargi asma'u ba tunda baka kamasu suna aikata hakan ba in fact bama wuri daya kagansu azaune ba so u have no right to accuse her

girgiza kai AK yayi yana dafe goshi yace ahmad bazaka gane bane saboda bakai ne ahalin danake ciki ba

Murmushi ahmad yayi yace are u jealous

"No I am not kawai dai ina kokarin kare mutuncina ne

Daddare asma'u tashigo dakinsu sedai cak tatsaya tana kallon yanda AK yayi watsi dakomai nadakin gabadaya yabirkita dakin bedsheets da pililluka duk yawatsar dasu gefe

Azaune tagangosa kan kujera yakuantar dakansa idonsa alumshe kamar mai bacci amma yana shafa goshinsa ahankali

adan tsorace take takunta har ta isa kusansa cikin rawar murya tace ABI are alright ?

azabure yamike yana damko kafadunta dakarfi seda nunfashinta yakusa daukewa saboda tsoro

matseta yayi jikin bango har tana jin bugun zuciyarsa

Hannunsa daya yasa ya damko kugunta yamatseta dajikinshi dayan hannun kuma ya zagayo dashi bayan wuyanta

Nan take jikinta yafara rawa muryanta har rawa take saboda tsoro

Kokarin kwace kanta tafarayi tana fadin ABI what are u doing let go of me please

Bakinsa yakai saitin kunnenta cikin rada yace meyasa zan kyaleki .....niba mijinki bane....tunda har zaki iya bari wani yatabaki why not me.....I see u can feel my touch why don't u like it

Tureshi tayi tana shigewa dressing room ta fashe dawani irin kuka mai cin rai

tajima tana kukan secan cikin dare tafito amma bataga kowa adakin ba ahankali ta tura kofa taleka Palo

Kuance tahangosa kan 3sitter da alama ba bacci yakeba dan har yanzu yana murza goshinsa

Komawa tayi tafara tattare dakin kamar wacce aka zarewa lakka banda kuka ba abunda take

bayan tagama tazauna abakin gado tana rungume pilo jin kanta take awani irin yanayi datakasa banbance wane iri ne tarasa meyasa take fargaban rabuwa da AK kuma tasan hakan yazama dole tunda batada wata shaidar dazata gabatar mashi dazai hana yasaketa gobe
[19/07, 17:03] Hubbey Frd Ameena Kn: 📚📚📚📚📚📚
👨‍👧 _DOMUN KANWATA_ 👩‍👧

Na( *Maryam Mhd*)

1⃣3⃣0⃣

daren ranar haka asma'u tayishi banda kuka ba abunda take har garin allah yawaye idanuwanta sun kunbura sunyi ja
lokaci guda har tarame

bangaren Ali ma haka yawuni ya kuana cike da damuwar rashin sanin halin da asma'u keciki gashi tunjiya yakeso yagayama AK gaskiyar abunda yafaru amma yaki sauraronsa

har saida su inna suka fahimci akwai abunda kedamunsa ba tambayar dabasu masa ba amma yaki yace komai

kasa hakuri yayi safiya tayi ana gama sallar asuba yanufi gidansu asma'u

haduwa yayi da AK yafito daga masallaci yana ganinsa yakauda kai kamar bai gansa ba

yana kokarin shiga gida yayi saurin shan gabanshi yana hada hannayensa yace AK dan allah katsaya ka saurareni tun jiya nake bibiyanka kabani dama nama bayanin gaskiyar lamarinnan

dagowa yayi yana kallonsa da rinannun idanuwansa cikin murya mai kaman rada yace

mezaka gayamun Ali wane bayanine zakamun Wanda ban saniba darajar su inna kakeci narufama asiri amma idan katakuramun wallahi se Insa adaureka ...

yana kainan yayi gaba yabarsa atsaye yana binsa dakallo

Yajima atsaye yana kallon get din gidan jiyake kamar yashiga yaga halin da asma'u take ciki amma yana tsoron abunda zai biyo baya hakanan yahakura ya juya yana takaicin abunda ya aikata
Chapter 42 · 0% Book details