← Book details Domin Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 84

Sashe 63

Domin Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Binta yayi dakallo aransa yana fadin tabbas akwai abunda take shirin yi.....I won't forgive u if u did something stupid this time

dasafe sukayi meeting a company inda ahmad ya gabatar da hadadden Zane mai bala'in kyew amatsayin sababbin collections din dazasu shigo

bayan antashi takara jaddada ma uncle jamilu cewa karyamanta yaune ranarshi takarshe idan bai biya kudin ba zaiga sammaci

sedai ga mamkinta murmushi taga yayi yana kallon zanen dake hannun ahmad hakan yasa tayi zargin wani abu sedai takasa gano meyake shirin aikatawa

Sarah duk tagama fita hayyacinta gashi uncle jamilu se barazana yakemata duk inda take tunanin zata samu kudi tanema babu

fadawa tayi kan gado tana fashewa dakuka cike da nadamar abunda ta aikata yanzu gashi bakin halinta yajamata tashin hankali kuma Wanda tayi danshima batasameshi ba

ahaka aysha tashigo tasameta karasowa tayi kusanta tafara lallashinta seda tayi shiru sannan tace tashi inbaki wata shawara amma bansan kozaki iyaba

Saurin tashi zaune tayi tana share hawayenta tace allah zan iya fadamun menene

Kallon kofa aysha tayi sanann tamatso kusanta cikin rada tace naji ance company sun fitarda sabon zane

tsaki tayi tace to miye alakar wannan da matsalata ina ruwana da zanensu ni kiyamun ida zansamu kudin shine damuwata

Dariya ysha tayi tace to ai baki bari kinji karshen zancanba .....kinsan wanann zanen yanada matukar mahimmanci idan har kika sameshi to matsalarki ta kau saboda bakaramin tsada ne dashiba

"Kamar ya banganeba ......taya zansameshi .....kuma waye zai sayi Zane ahannuna har kina maganar wai zaiyi tsada

Duka aysha ta kaimata akafada tana fadin ke yanzu kanki bai kawo wuta ko kadan .....kinsan company dake Lagos suna dan takun saka da su AK saboda sun fisu kwarewa dasanin kan aiki kuma sun lunkasu customers shiyasa basa jittuwa idan har kikayi kokarin samo zanen to inagayamiki da gudu zasu sayeshi ahannunki for just one clap zaki samu 5M dinki cash ....

"Gaskiya aysha bazan iyaba sata fa kenan kuma idan Yaya yasan ni nadauka wallahi kasheni zaiyi

tsaki aysha tayi cike da takaici ganin plan dinsu zai ruguje tayi saurin fadin wane irin sata kuma ko kinmanta cewa yanzufa company bana AK bane na asma'u ne kinga kwa ai rama cuta ga macuci ibada ce

Murmushi sarah tayi cike dafarin ciki tarungume aysha tana fadin nagode aysha gaskiya shawarar nan tayi amma ina zansamu zanen

Murmushi tayi tana mata kallon gara wasai tace Zane yana office din ahmad se kisan yanda zakiyi kisatoshi batare da kowa ya ganki ba

nan take ta shirya tanufi office din ahmad aguje tafada office dinsa tana fadin wayyo Yaya ka taimakeni

Azabure ya mike cike da mamki yanufota yana fadin subhanallahi .....sarah menene dake dawa......

Dafe kujera tayi tana haki tace Yaya .....wa.....wasune suka biyoni suna..... nan waje....

zaunar da ita yayi kan kujera yafita da sauri dan ganin ko suwaye

yana fita tamike tana leken kofa tashiga bubbude drowowi tana Neman zanen sedai duk Wanda tadauka setaga ansa date din akayi zanen haka taci gaba da dubawa har takai ga sabon zanen tayi saurin daukoshi sedai tarasa inda zatashi saboda takardar tanada girma kuma bazata iya nadeta ba

Window takalla taga ba komai awurin se shukeshuke tayi saurin janye glass din ta wurga zanen waje daidai nan ahmad yashigo

saurin juyowa tayi tana kallonsa atsorace sedai murmushin dataga yayi shi yatabbatar mata cewa baiga abunda tayiba

Karasowa yayi wurinta yana fadin sarah kodai gamo kikayi ne naduba ko ina banga kowa ba kuma natambayi securities sunce ke kadai kika shigo

Sosa kai tayi tana murmushin yake tace to ni dai bansaniba amma wasu naga suna bina zasu kamani

Kujera ya nuna mata yana fadin to zauna bari nakira AK se musan abinyi

Zaro ido tayi tana girgiza kai tace a'a Yaya karka kira kowa karma kagayusu nazo nan .....bari kawai natafi sauri nake

Cike da mamaki yace sarah are u alright.... Ko inzo in rakaki gida ne

"a'a kabarshi kawai yi aikinka zan iya tafiya nikadai .....takarashe maganar tana fita daga office din

Dage kafada yayi yana tabe baki ya zauna kan kujerarsa yaci gaba da aikinsa

tana fita tazagaya cikin sanda tadauki zanen batare dakowa yaganta ba har tafita bawanda ya lura da abunda hannunta saboda securities din sun Santa ko kallonta basuyiba har tafita get """""

📚📚📚📚📚📚
📚📚📚📚📚📚
👨‍👧 _DOMUN KANWATA_ 👩‍👧

1⃣8⃣0⃣

Ahmad yana cikin aiki ya tuna cewa baisa date ajikin zanen ba yajanyo drawer zaidauko yaga wayam bakomai
cike da mamaki yafara duba ko ina amma baigani ba
wasa wasa seda yagama bincike office dinsa kap amma ba zanen nan take hankalinsa yatashi har wata zufa take karyomashi saboda awannan lokacin ya tabbata cewa sace zanen akayi

da gudu gudu yanufi office din AK dan sanar dashi abunda ke faruwa

Yana zuwa ko nocking baiyiba ya tura kofar yashiga

AK yana zaune kan kujerarsa yadora kafafuwansa kan table da goran ruwa ahannunsa yanasha ganin ahmad atsaye yasa yasaki murmushi yana fadin karaso mana friend dama ina nemanka wato wannan karon dan kaga Lady boss ce shine kafito da zanen dabaka taba yin mai kyensa ba .....wato ni karaina ko

Jiki asanyaye ahmad yakaraso yana fadin friend nashiga uku ...... wallahi akwai matsala

Goran ruwan yakai bakinsa yana lumshe ido yace ni ai matsala tazama jinin jikina ......dan haka fadi inji miye ..

"Friend dazu bayan mun gama meeting asma'u tabani zanen tace in ijiye awajena yanzu kuma naduba sama da kasa banganshiba ......

Saurin cire gorar yayi yana hadiye ruwan bakinsa yace what .....?

Kauda kai ahmad yayi yana shafa kai yama rasa mezai ce
sauke kafafuwansa yayi yamike tsaye yana nufo ahmad yace garin ya haka tafaru .....kodai kamanta inda ka ijiye ne ...muje mukara dubawa

Girgiza kai ahmad yayi kamar zaiyi kuka yace bansan ya akayi ba .... naduba ko ina bangani ba kai har dustbin seda naduba amma banganshiba ....yanzu bansan mezan cemata ba ....gashi naganta yau se ahankali...no mutunci

Zaunawa AK yayi akan table din yana zabga tagumi yace badaga nan matsalan take ba.... idan har Wanda yasata saidawa zaiyi to ya kashemu ....saboda anriga antura zanen kuma sunsaya kaga idan sukaji zasuyi tunanin basu kadai muka sayarwa da zanen ba hakan zai iya zama silar rugujewar alakarmu dasu

"To yanzu miye abin yi

"abunyi dayane muje mugayamata komai dan asan yanda za'ayi tunda wuri ...natabbata acikin ma'aikatan nan ne wani ya dauka kaga idan akayi bincike za'aganoshi tun kafin ya sayarda zanen

"Friend wallahi tsoronta nakeji gaskiya bansan ta ina zan fara mata bayani ba ....kuma databani seda jamun kunne kan namai ijiya mai ....ni abunda yake dauremun kai bafa inda naje

Wani dogon tsaki AK yaja yana mai kallon kabada maza yace muje ni zan mata bayani inyaso ta cinyeni danye

Jiki asanyaye ahmad yabi bayanshi har suka isa office dinta cike da gadara AK yayi knocking yana daure fuska wai dan kar taga damarsu daga ciki tabasu izinin shiga Suka sa kai cikin office din ahmad se kokarin boyewa yake abayan AK danji yayi kamar yajuya

Dagowa tayi tana kallonsu fuska adaure tace meke tafe daku

Hannu ahmad yasa yana Jan rigan AK tabaya alamar yayi magana shikuwa AK idonsa ne kawai akanta amma hankalinsa yana wurin tunanin ta ina zai fara mata bayani

kafesu tayi da ido batare datasake cewa komai ba shikuwa ahmad se murmushin yaake yake yana cigaba databo AK ganin yaki motsawa yasa hannayansa biyu ya turasa gaban table dinta yana fadin kamata bayani mana

kara daure fuska tayi tana kallon AK tace idan bakuda abunyi ni inada kufadi abunda yakawoku kufitar mun daga office

Juyowa yayi yakalli ahmad dake bayansa yana mai alamar yayi magana mana
Maida kallonsa kanta cikin rawar murya yace well.....am....dama

"dama me ....

"dama ahmad ne ya....

Saurin karasowa ahmad yayi yana fadin dama nine nayi me .....

"kunga idan baku yanke shawarar abunda zaku fadamun ba Ku koma anjima kudawo kuna bata mun lokaci

runtse ido ahmad yayi yana sadda kai yace dama zanen dakika bani ne dazu aka sace nadu....

azabure ta mike tsaye tana fadin what.....garin ya kabari haka tafaru ....seda nagayamaka ka tabbatar ka anadashi saboda irin haka ....shine yanzu zaka zo kana gayamun wai ansace

Karasowa tayi wurinsu tana kallon AK cike da damuwa tace AK idan wasa kuke kudaina wannan ba abun wasa bane kunfini sanin haka ya za'ayi ace ansace zane abunda ba'ataba yiba

Dafa kafadanta yayi cikin sigar lallashi yace lady boss ki kuantar da hankalinki zamu binciki kowa mugani insha allah zamu sameshi

Nan take takira securities tasanar dasu kar subar kowa yafita sannan tafita daga office din afusace tanufi office din uncle jamilu tana fadin nasan Wanda ya dauki zanen nan kuma wallahi bazan barshiba

saurin bin bayanta sukayi har sukaje office din tana masifa tura kofar tayi dakarfi tashiga yana tsaye jikin window suna waya da aysha yana mata bayanin yanda zata taimaka ma sarah su saida zanen

Saurin katse kiran yayi ya juyo afusace dan ganin kowaye ganin asma'u atsaye yasa ya daure fuska yana fadin dan ina kasa dake baya nufin zaki iya shigomun office batare da izinina ba

aguje tanufi wurinsa tacakume kwalarsa tahadasa da window idonta jajir cikin kakkausar murya tace wallahi yau bazan barka ba seka fitomun da zanena azzalimi kawai .....sena kasheka jamilu wallahi na tsaneka

kokarin kuace kansa yake amma yakasa idanuwansa sun fito waje zuru zuru saboda tsabar shakar da yasha aguje AK ya karaso wunrinsu yana Jan asma'u amma taki sakinshi

janyo jacket din yayi tasakemasa ita segata daga dogon wando se shirt taci stoking zaro ido yayi yana kallonta sannan ya juya yana kallon ahmad dayayi saurin kauda kai yana murmushi

janyota yayi dakarfi yariketa gam ajikinsa sannan jamilu ya kwace yana tarin wahala se zare ido yake yana dura mata ashar

Fizge jacket dinta tayi ahannun AK tamaida sannan tajuya tana kallon jamilu fuska ahade tace jamilu tun muna mu biyu ka fito mun da ....

Katseta AK yayi dafadin wannan wace irin magana ce asma'u .....duk cikin ma'aikatanki kirasa Wanda zaki zarga se shi

Juyowa tayi tana kallonsa tace ba ruwanka tsakanina dashine ni nasan dalilin dayasa nazargeshi

Cike da takaici jamilu yace eh ai dama dole kizargeni wato gani makiyinki to ba gaki acikin office dina kiduba mana
Chapter 63 · 0% Book details