← Book details Domin Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 84

Sashe 23

Domin Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana gama fadan haka tamike tanufi wurin MC wata magana tamasa akunne naga yayi murmushi

Sannan yanemi kowa Yakoma yazauna

Bayan kowa yazauna sannan ya nemi ganin kannin amarya guda biyu

Kallon kallon aka fara tsakanin fa'iz da khadeeja
Sannan tamai alama dasuje

Tsakiyar filin suka je suka tsaya cike da birgewa kowa ke kallonsu saboda Kansu daya gashi suna yanayi wasuma sunzata yan biyu ne

Bayan sun gaisa dakowa sannan MC yabukaci ganin kannin ango guda biyu

Nan take aka hau tapi da shewa ganin sarah da aysha sun fito cikin shiga tariga da wando sunyi kyew sosai

Juyowa asma'u tayi takalli AK dake gefenta azaune tana fadin wai mezasuyi??

Hannayensa yaware yace ohoo yanda kike da ido biyu nima haka nakedasu to muzubasu muyi kallo

Kauda kai tayi cike dajin haushin kanta dan Sam bata San lokacinda ta tambayesa ba

MC yabukaci kowa ya nutsu yanzu za'a kalli gasan rawa tsakanin kannin ango da amarya

Cike da firgici khadeeja takalli fa'iz
Sedai ga mamakinsa murmushi taga yanayi

Zunguranshi tayi tana fadin kai wai kaji abunda yace Kuwa

Dariya yayi yace haba deeja wani ma yayi rawa bare dan makadi haka kawai ma mun zage mun tiki rawa bare kuma abikin ammah shima kuma wai gasa

Kansu sarah aka fara inda suka zabi wakar dasuke so dakansu

Nan take DJ yasaki kida su sarah da aysha suka fara takawa rawa suke bata wasa ba amma sarah tafi aysha iyawa

Har suka gama su khadeeja nagefe suna kallonsu

Tapi aka hau yi ana shewa kowa nayaba rawansu

Bayan hayaniya talafa MC yabukaci kannin amarya su shigo fili
Fa'iz yakalli khadeeja yana fadin deeja muje mana

Jadabaya tafarayi tana fadin gaskiya fa'iz bazan iyaba mutane sunyi yawa kunya nakeji

Nan take aka hau nunasu dayatsa ana dariya

Juyowa AK yayi yana kallon asma'u yaga fuskanta ta canza tana kallon fa'iz daya sadda kai yakasa motsawa

Sarah da aysha kuma se dariya suke suna tapa hannu (ni kwa nace girma yafadi😏)

Dariya yayi yace inaga kanwarki bakinta kawai ta iya sarrafawa amma banda gangar jiki hahaha

Sadda kanta tayi kasa batace komai ba

Kallonta khadeeja tayi setaji duk bataji dadi ba kamar takoma amma tayaya

Karban microphone din fa'iz yayi cikin dakewa yafara fadin

Hello guys!!! kanwata ba guduwa tayiba kuma batsoro taji ba

Kunsan duk macen da tacika mace ansanta da Jan aji da basarwa

Rawanta Nada tsada so u have to beg for it !!!

nan take aka fara tapi ana kiran deeja!!! Deeja!!! Deeja!!!

Karasowa fa'iz yayi kusa da ita cikin rada yace deeja please u have to this for our sister kalla kiga yanda angonta kemata dariya duk danasan wasa ne amma bazataji dadiba

Murmushi tayi tace ok let's do it

Hannunta yakamo suka dawo filin rawan

nan aka hau tapi ana daukan su photo saboda sunbirge kowa awurin

Karban microphone din MC yayi yana fadin
ok twins which song are u ready to dance on ??

Kallon mutanen wurin khadeeja tayi tana fadin mun basu zabi

Tapi aka haw yi ana shewa kowa nafadan wakan dayakeso

Nan dai DJ yasakar musu wakar humma song suka fara rawa

Haba ai nan take kowa yamike akafara daukansu video saboda yanda suke bin kidan suke rawa kuma komai tare suke yinshi gwanin sha'awa

Shi kanshi AK sunbirgeshi

Tun kafin sugama kowa yafara tafa musu ana basu winning
Haushi ne Yakama sarah cike da takaici taja aysha suka bar wurin

Har suka gaji amma anki bari su sauka daga wannan wakar takare se asaka wannan se da kyer suka kwace kansu

Dariya asma'u tayi tamike tsaye tana kallon AK tace

Inafata kanada isashshen jinin da za'adiba akarama kanninka dan naga sunada bukatarsa

Zai yi magana kenan ya hango ahmad atsaye agabansu kaman gunki yana kallonsu

Murmushi yayi ya mike yanufosa yana fadin ohhh welcome back Friend

Shuru ahmad yayi yakasa magana yana mamakin me kuma yayar khadeeja take anan

Asma'u kuma data basu baya Sam bataga ahmad ba

Hannu AK yasa yajanyota yana fadin meet my wife

Cike da masifa ta jiyo da nufin magana amma cak tatsaya ganin ahmad agabanta
Sadda kanta tayi kasa bawanda yace komai

Wani malalacin murmushi AK yayi daya hango mamaki karara afuskar Ahmad

Jadabaya AK yayi yana murmushi yace bari nadan Baku waje kuyi magana sannan ya juya yanufi wurin da yahango aysha atsaye

Yana tafiya ahmad yakalli asma'u cike da mamaki yace wai dama kece AK ya aura garin Yaya dama kunsan juna ne

Dagowa tayi ta kallesa cikin rawar murya tace yanzu ba lokacin magana bane Ahmad khadeeja tana nan wurin ga sarah

dan Allah katafi banaso sugane akwai wani Abu atsakaninku
Tana kainan ta juya tanufi bangaren grany tana boye kwallar data cika mata ido

Da kallon tawsayi yabita ahankali ya furta something is fishy

Sarah ce tazo kusa dashi tana murmushin mugunta tana girgiza kai
tace ohhh so sad !!!

Kayi mamakin ganin budurwanka anan gidan ko sannan ta langwabar dakanta tacigaba dafadin
to ya na iya naso nafita hanyarka amma nakasa shiyasa nadauki wannan matakin

Wani kallo mai cike da tsana yawatsa mata yaraba tagefenta zai wuce tayi saurin riko hannunshi tace tsaya mana Yaya baka tambayeni ya akayi yarinyar dakake ikrarin tana sonka tayi saurin amincewa auran wani batare da saninka ba

Daidai nan khadeeja tazo wucewa tahangosu kamar ance yadaga kansa kawai ya hangota tana barin wurin da sauri har tana hadawa da gudu

Cike da takaici yabige hannun sarah yana fadin kirike tatsuniyarki bana bukatarta

Sannan yabi bayan khadeeja yana kiran sunanta

Ahasale sarah tanufi bangarenta tana fashewa da kuka

Tafiya kawai khadeeja take bata Masan inda tanufa ba sedai kawai taganta a garden shakan wani iska mai dadi tayi ta lumshe ido sannan tazauna adaya daga kujerun wurin tana kallon katon seeming pool din dake gabanta

Kusa da ita ahmad yazo yazauna

Sunjima ahaka bawanda yace kala

Secan tasauke ajiyar zuciya batare data kalleshiba tace yaushe kadawo??

Dazu....
Yafada atakaice batare daya kalleta ba shima

Meyasa baka gayamun ba

Nakiraki wayanki akashe

Daganan kuma suka kara yin shiru nadan lokaci kana cikin cikin sassanyar murya ahmad yace
I am sorry...

Se alokacin tajuyo takalleshi tana murmushi tace no I'm sorry

Kallonta yayi yana murmushi baice komai ba

Sadda kanta tayi kasa ahankali tafurta I missed u

Missed u more yafada cikin jin fadin maganarta

dagowa yayi yana kallonta yace meyasa baki gayamun AK yana son yayarki ba

Fuskar tawsayi tayi tace nima kaina bansan AK ne zai aureta ba sedaga baya

damamaki yace kamarya ??

Nan tabashi labarin abunda yafaru

Ajiyar zuciya ya sawke Dayagama jin bayaninta sannan yadago yakalleta da damuwa afuskarsa yace deeja ni inada shakku akan wannan auren

Meyasa kace haka

Ranarda asma'u tazo office dina sarah taganta kuma aranar nake gayamata bazan aureta ba inada wacce nakeso to setayi tunanin asma'u ce wacce nakeso din

Shakan iska yayi ya furzar sannan yacigaba da fadin

Deeja nasan wacece sarah tana kokarin ganin tasamu duk wani abunda takeso
Shikuma AK zai iya yin komai dan farincikin ta

Ni bansan meyake faruwa ba amma hankalina yakasa kuanciya da aurenan

Cike da damuwa khadeeja tace nima nayi wannan tunanin saboda dazu nazo wucewa naga AK tare dawannan cousin din tasa aysha kuma ayanda nagansu hankalina bai kuanta ba shiyasa nazo inaso na tambayi ammah

Sekuma naganka da sarah
Ahankali ta furta meyake faruwa ne

ki kuantar da hankalinki balalle ne abunda muke zargi yazamo gaskiya ba

Saurin barin wurin tayi tana fadin bari naje naga ammah

Asma'u ce tashigo bangarensu azaune taga AK apalo yadafe kai

tsaye tayi tana kallonsa aranta tana fadin to shikuma wannan meke damunsa

Dagowa yayi ya kalleta cikin kakkawsar murya yace kallon me kike mun bayan duk ke kika sakani awannan halin

Shiru tayi tasadda kanta kasa batace komai ba

Tasowa yayi yakaraso wurinta yana fadin duk lokacinda abokina yayi tafiya idan zai dawo ni nake Zuwa natarboshi na rungumeshi nakawoshi gida muci abinci tare muyi fita tare amma yanzu ta dalilinki ko sannu dazuwa mai kyew nakasa yimai

Kin ruguza mun rayuwata kin rusa mun farin cikina kin cutar da aminina bazan taba yafemaki ba
Yana kainan ya tureta daga bakin kofar seda tafadi ahasale yabanke kofar yafita

Cak yatsaya yana kallon khadeeja dake tsaye abakin kofar fuskarta sharkap da hawaye tana jifanshi dawani kallo mai cike da tsana

tagefenta yaraba ya wuce batare dayasake kallonta ba

Kamar kartashiga har ta juya sekuma tasa kai cikin dakin

asma'u naganinta ta tashi azaunen datake akasa tana share hawayen fuskarta

Rungumeta khadeeja tayi tafashe dawani irin kuka mai ban tausayi

Dafa kanta asma'u tayi cikin rawar murya tace khady menene lafiya meyafaru

Cikin kuka khadeeja tace ammah meyasa !!! Meyasa!!! Kika boyemun halin da kike ciki

Mutuwar tsaye asma'u tayi dan Sam bataso khadeeja tasan halin datake ciki ba

Dagota tayi tafara Share mata hawaye cikin rawar murya take fadin

Ni ba abunda yake damuna khady I like the house ...
the family was nice..
And I like my husband he is good man ...

And grany was taken care of me ..

Kuma kince Umma tana farin ciki

Wannan kadaima.. ya isheni...

Katseta khadeeja tayi dafadin

a'a ammah bazai yuwu ba mutanen nan basa sonki kawai yaudarar ki sukayi Sam baki dace dasuba
Jan hannun asma'u tanafadin kizo mukoma gida kawai
Rikota asma'u tayi cikin muryan kuka tace no khady please bazan iya tafiya ba kiyi tunanin kuana daya da bikina aganni agida me mutane zasuce za'ama su abba dariya wane hali Umma da inna zasu shiga kinsan basuda cikakkiyar lafiya idan abba yaji kanshi zai dorawa laifi zaice shi yajamun bazai yafema kansaba

Kuma narabu dasu kanki zasu koma bazasu kyaleki ba

Sulalewa kasa khadeeja tayi tana wani irin kuka mai cin rai dogowa tayi takalli Asma'u data safe kai saboda bata iya jurar kukan khadeeja

Cikin muryan kuka khadeeja tace ammah
Tun ina Karama kike wahala akaina yanzu na girma ma amma baki huta ba zaki kara fuskantar wata rayuwar akaina wallahi hakan yasa natsani kaina ...

Saurin toshe mata baki cikin rawar murya tace a'a khady kidaina fadan haka wannan nadaukeshi amtsayin jarabawa ne daga Allah kuma nakarbeta hannu biyu inafata Allah yabani ikon cin jarabawar
Chapter 23 · 0% Book details