← Book details Domin Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 84

Sashe 12

Domin Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

AK yafito wanka kenan yaji wayarsa na ringing mamaki yayi ganin sabuwar number Da kamar kar yadaga seda takusa tsinkewa se kuma yadaga tare dazama bakin gado

asma'u tana jin alamun andaga kiran takara wayan akunne batace komai ba sun jima ahaka asma'u tadago wayarta taga har yanzu kiran bai katseba gashi katin bayawa
AK yana shirin aje wayar yaji wata siriruwa murya tamishi sallama wayar yamaida akunne tare da lumshe ido ya amsa sallamar shuru suka karayi na yan mintuna
Asma'u haushi duk yacikata ga katinta natafiya ga inna takafeta da ido bare takatse kiran tsaki tayi aranta tana fadin wannan wane irin mutum ne afili kuma ahasale tace ABIDI ne
tadayan bangaran azabure AK yamike yana fadin how dare you call me by that name who the hell are you??
afirgice Asma'u takatse wayar tsaki AK yayi ya ijiye wayar har yajuya sekuma yatuna grany ke kiransa da wannan sunan to ko itace tasa takira dawowa yayi ya dauki wayar yakira asma'u naganin kiran Tamikama inna wayar inna hannunta har rawa yake takarba asma'u ta daidaita mata ita tasa akunne tamike tsaye ta kalli gabas kamar mai Shirin kiran sallah moryarta gaba daya taware ta zabga sallama Seda asma'u ta zabura
AK nashirin magana kenan yaji an kwararo wata doguwar sallama
Assalamu alaikum wa rahamatullahi wa barakatuhu
Seda AK yacire wayar akunne ya duba numban yakara maida wayan akunne ya amsa sallama
Inna tagyara tsayuwa tarike qugu tareda da gyaran murya tace kagane mai magana ? ahankali AK yace a'a aransa kuma yana fadin yau naga takaina shi duk atunaninsa ma ya'uwansa ne na yola murmushi yayi jin inna namai bayanin ko ita wacece dan yaganeta akan dresing mirror yadaura wayar suna fira yana shirinsa dan yanda inna ke magana ba bukatar handsfree asma'u tayi dariyar har tagaji inna namata alama tayi shuru amma takasa sedai inna tafita tabar mata dakin ta koma palo tacigaba da wayarta tun tanajiran inna tagama tabata wayarta har bacci ya dauketa
har AK yagama shirinsa inna nasurutu wayar yadauka yafita yna fadin inna bari nakaiki wurin kawarki yana zuwa ya mika ma grany wayar nanfah yaga cabta dan grany wani dan karamin aikin hajji tayi safa da marwa ta dinga yi daga wannan kujerar zuwa waccan fallon kwa tazagaye shi yafi so ashirin tun AK na kallonta yana dariya har yagaji ya kunna tv yana kallo
fa'iz ne yaleko palon inna ya iskota tanawa grany sallama akan se taganta goben kwashewa yayi da dariya yace wai dama inna waya kikeyi ni har nabiyo da Igiya inace ko kinzauce ne mudaureki Inna dai ba baKin magana se zare ido take tana shafa saman makogwaronta da da yabushe fa'iz yakara kwashewa da dariya yamatso kusa da ita yana fadin gaskiya inna irinku ake bukata awajan da'awa wai wannan murya haka tundaga get nake jiyoki
Inna Tamaka mai harara cikin dasashshiyar muryarta tafara fadin wallahi kafita a ido...... bata karasaba tari ya sarketa da gudu fa'iz yanufi frig ya dawko mata Goran ruwa inna takarba takafa kai seda tayi Rabi ta aje gorar banda dariya ba abunda fa'iz keyi harda rike ciki inna dai ba bakin magana se harare harare

abangaran grany ma haka abun yake koda tagama wayar tayi sharkaf da gumi akan kujera tazube ragwazab tana maida nunfashi Ak yatintsire da dariya yace grany Ashe haka kike waya awahale shiyasa kikace ba kya son rike waya grany dai se binshi take da ido dan har wani jiri jiri takeji shi kanshi AK biyu biyu take ganinsa bashiri tamike tanufi bayi dan watsa ruwa AK ya kwashe da dariya ganin yanda take rangaji kamar mai jin bacci

da yamma misalin karfe 5 ahmad ne zauna akan dakalin kofar gidansu yana waigen waigen ta inda zaiga bullowan khadeeja kamar daga Sama yaganta tashayo kwana cikin uniform dinta na islamiyya wani murmushin farin ciki yasaki khadeeja kamar ance tadaga kanta ta hangeshi azaune gabanta ne yafadi jitayi kamar ta koma se kuma tadake taci gaba da tafiya Ahmad naganin ta kusa isowa yatashi yanufeta yana murmushi ai khadeeja naganin ya nufota ba shiri ta fada wani gida ta turo kofar tana maida nunfashi ahmad yayi tsaye yana mamaki kamar ba ita bace jiya tasa shi agaba tana mai fitsara ba to kodai gaskiyar yayanta ne tanada iskokai
Murmushi yayi Yakoma yazauna yana jiran fitowarta amma har aka kira sallar magriba bata fito ba hakanan yatashi yashiga gida dan yin alwala yana shiga khadeeja tafito dama tana lekenshi ta jikin get din gidan asukwane tabar layin kamar zata tashi sama dan gani take kamar yana binta abaya
koda ahmad yafito kofar gidan ya kalla ya ganta abude murmushi dan dama yaga lokacinda tayi fitar harsashe daga gidan ahankali ya furta
I will find u my flying Bird!!!
[18/07, 15:03] Hubbey Frd Ameena Kn: 📚📚📚📚📚📚
👨‍👧DOMUN KANWATA👩‍👧

🖊na marubuciya Husna kabir zarewa( the mammah girl)

🖊dasunan allah mai rahama mai jinkai......

👨‍👧DOMUN KANWATA👩‍👧

3⃣0⃣⏭3⃣5⃣

aguje khadeeja banke kofa tashiga gida ta maida kofar ta rufe tasa sakata ta sulale akasa tana maida nunfashi asma'u ce tafito da hijab ahannunta da nufin fita tadubo ko lafiya yau khadeeja bata dawo ba da gudu takaraso wurin khadeeja tana fadin khdy lafiya ? Menene? Waya biyoki ? Meya tsaidaki baki dawoba har ana kiran magriba?
Khadeeja tamike tana fadin ammah wannan tambayoyi haka ajere wacce zan amsa maki bari muyi sallah sena fadamaki amma yau allah ne yamun alam nasharaha da sedai kiga nadawo fuska akone asma'u tace subhananllahi garin yaya kenan? Khadeeja bata kulata ba tashiga ciki tana fadin ammah biyomun da jakata asma'u tadauki jakar jiki asanyaye tabi bayan khadeeja
Seda suga gama sallah suna cin abinci khadeeja keba asma'u labarin abinda yafaru asma'u tayi dariya tace to waike gudun da kikayi kina tunanin nufokin da yayi asid zai watsa maki kenan ? Khadeeja takai lomar tuwo bakinta tace to inba haka ba hakuri kike tunanin yazo yabani kome asma'u tayi dariya batace komai ba dan tagane maganan fa'iz ta jiya ita ta tsorata khadeeja

Washegarin ranan da safe AK ne zaune apalon grany yana breakfast grany na gefe tana kokarin tura wani Abu jikanta AK yadago ya kalleta yace wai ni grany ina zakije ne tundazu kike kukarin hada kaya grany tazuge Jakarta tana fadin gidan hajiya Hadiza zanje badan ma zaka fita ba Aida tare zamu tafi ka gaisheta AK yayi murmushi yace a'a kije kawai grany Idan nasamu lokaci zamuje nida ahmad mugaisheta yanagama fadin haka yamike ya dauki wayoyinsa yayi gaba har yakai kofa grany takirashi dawowa yayi yazauna yana fadin gani grany ya akayi grany ta gyara zama tace ABID dagowa yayi ya kalleta saboda idan har yaji takirashi da wannan sunan yasan Abu mai mahinmanci zata gayamai
Grany tadago ta kalleshi tace agaskiya hakurina ya kusa karewa nagaji da ganinka haka ba aure kuma naga Alana bakada niyyar yinsa saboda nace kabani dama inzaba Maka mata kaki kace aysha kake so toh ita dinma nace ka aureta amma katsaya kana bata lokaci ko so kake se na mutu zakayi auren ne?? Dagowa yayi ya kalleta yana murmushi hawayen da yagani a idon grany yasa yamike da sauri ya Matso kusa da ita ya kama hannunta shima kamar zai yi kuka yace haba grany meye abun kuka kuma kina so kidaga mun hankali ne kinsan ba abunda natsana kamar ganin keda sarah adamuwa kuma kinsman kinada hawan jini so kike yatashi dan allah grany kiyi shuru wallahi idan wani Abu yasameki mutuwa zanyi grany tayi murmushi tashare hawayenta tace ABIDI bazaka gane yanda nakeji bane idan na tuna cewa har yanzu bakada aure nakosa naga kaima ka ijiye iyali ABIDI wa'yannan mutanan da kagani agidannan kake wahala akansu yau dazaran akace anwayi gari Baka raye suna gama cinye dukiyar Daka tara watsewa zasuyi su manta dakai iyalinka ne kawai zasu rika maka addu'a akoda yaushe abunda nake ganemaka kenan amma kai ka kasa ganewa
Jikin AK yayi sanyi da bayanan grany ajiyar zuciya ya sauke yadago ya kalleta yace nafahimce ki grany kuma insha allahu namaki alkawarin aysha tana dawowa za'ayi maganar bikin mu amma dan allah kidaina damun kanki da yawa grany tace to shikenan allah ya kaimu
AK ya kureta da ido cikin sigar zolaya yace ha'an yanaga ba kya farin ciki ne ko kishin ne yamotsa grany tayi murmushi tace a'a nida wata yarinya nagani namaka sha'awarta ga hankali ga nutsuwa ga girmama manya gata kekkyawa kamar yar India ina son yariyar jikar hajiya Hadiza ce yarinyar yar gidan mutunci ce babanta malan mahammadu ana cemashi magaji har yarasu kowa yana yabonsa a unguwar kaga gata marainiya tun tana Karama babanta yarasu kuma.........AK ne yakatseta da fadin ya isa haka grany wannan campaign haka to kiyi hakuri ta makaro ni aysha nakeso grany ta kauda kai tana fadin ni banga abun so awajan aysha ba mace kamar allo AK ya mike yana murmushi yafita yana fadin badai auren kikace kinaso ba to zanyi grany ta dauki Jakarta tabi bayansa tana fadin da dai ka daure kaga yarinyar nasan zaka sota
AK bai kulata yanufi wajan motocinsa grany ma wata motar tashiga tama driver kwatancan da inna tamata

Agidan inna grany ta wuni sunsha fira har sun gaji bacci ya kwashesu se bayan la'asar tadawo gida

Bayan kuana biyu ana jibi su sarah zasu dawo tama kasa hakura suyi sati dayan duk ta kosa tadawo taga ahmad dinta kullun seta kirashi awaya wani lokaci yadaga wani lokacin kuma har tagama ringing dinta yana gani baidaga ba ita kuma bata damu ba duk abunda tagani na maza mai kyew sai tasayama ahmad da AK har dariya takeba aysha wani lokacin kuma tabata haushi

Bangaran ahmad kuwa gaba daya yakasa sukuni shikadai sekaga yana murmushi tun Momy na shareshi har tafara tambayan shi amma se yace ba komai Momy tayi dariya tace zauna nan badai kunki aure ba ai dama gwowranci inyayi yawa yana taba kwakwalwa toh naga alama shine yafara zautar da kai saura abokin naka shi bamusan taya zai zomashi ba sedai yayi murmushi ya Sosa kai yace momy lokaci ne momy tace kanku akeji mudai namu ido nayi fadan har nagaji nayi fushin banza se kununa baku masan inayi ba
Chapter 12 · 0% Book details