← Book details Domin Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 84

Sashe 62

Domin Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tajuya zata tafi ya riko hannunta ya juyo da ita dakarfi har saida tafado jikinsa matseta yayi a kirjinsa suna kallon juna cikin murya mai kaman rada yace
idan bakya sona meyasa baki tafi kinbarni ba tunda kinsamu abunda kike so .....meyasa ba kya iya kallon kwayar idona aduk lokacinda zakimun kike mun magana .....meyasa se kin runtse idanuwanki kike iya kiran sunana ....kullun ke kike tashina abacci ki ijiye mun coffee dina kafin nafito daga wanka aduk lokacinda kika ganni cikin damuwa ba kya iya boye damuwarki akaina why......chitti har yaushe zaki rika wahalar damu ne..... ada munyi aure ne domun kanninmu amma ayanzu muna tare ne dan bazamu iya rayuwa batare da juna ba chitti ki.....

Kokarin kwace kanta tafarayi tana maida hawayen dake neman zubo mata cikin rawar murya tace miye haka kakeyi .....sakemun hannuna please... Na gayamaka bana sonka.... ina zaune dakai ne kawai saboda ina tausayawa grany bansan halin dazata shiga ba idan kuka bar gidannan ....kadaina bata lokacinka wajan tunanin inasonka ne shiyasa ......

Bata karasaba yasaki hannunta yana ja dabaya cikin daga murya yace karya kike asma'u aduk lokacinda nakalli kwayan idonki zallar so nake hangowa aciki ..... kawai dai kina danneshi ne saboda wani dalili naki .....

Tsayawa yayi yana kallon yanda take share kwalla cikin sassanyar murya yace chitti please nagaji da abunda kike mun ....I was blinded by ur love .....kinmun abunda yakamata ace naji haushi amma nakasa yin fushi dake bansan meyasa kika canza ba .....nagani kinyi kyew kin iya dressing kin iya make up u are so pretty amma .......ni wannan duk bai dameni ba .....ina so kidawo yanda kike da wannan asma'un dabata iya kwalliya ba ....bata iya sa kananun kaya ba ....ni ita nakeso she was the most beautiful and prettiest girl I ever seen in my life ....yakarashe maganar yana murmushi amma idonsa pal kwalla

juyawa tayi tana share hawayenta tanufi dakin aysha batare datace komai ba amma kuka ne kincinta aciki jitake kamar taje ta rungumesa tasaki kukanta ko taji sauki

tsaye yayi yana binta da kallo har tabacemasa sannan ya juya jiki asanyaye ya nufi bangarensu yana fadin bazan kara tambayarki ba kuma nima zanyi kokarin cire sonki araina nasaka na aysha tunda ita take sona kuma zan aureta inshafa maki lafiya silly girl .....dawanann surutan ya isa bangarensu yafara aikin data bashi

tazo daidai wurin dakin aysha kenan taga wucewarta tana waige waige tanufi hanyar fita

Saurin labewa tayi bayan kofa tana kallonta har tafita sannan tayi saurin bin bayanta har harabar gidan

Daga nesa ta tsaya tana kallon yanda suka rungume juna da salim har yana sunkuyawa daidai cikinta yamanna mata kiss tayi saurin ture kansa tana waige waige

Kallonsu take cike da mamaki dan ko ba afada ba tasan tabbas wannan shine uban dan duk yanda taso taga fuskansa takasa saboda wurin akwai duhu gashi yabata baya tajima azugunne tana lekensu ganin ya juya ai tafi yasa tayi saurin komawa ciki wurin dining tanufa ta ijiye bowl din dake hannunta sannan tadawo Palo ta tsaya

Aysha nashigowa taga Asma'u atsaye taharde hannaye tana kallonta fuska adaure ba alamar wasa atare da ita

Kauda kai tayi tana daure fuska tanufi hanyar dakinta zata wuce asma'u tafizgota ta wurgata kan kujera tana jifanta da kallon tuhuma

Sake da baki aysha ke kallonta cikin rawar murya tace ha'an...malama..miye haka ya zaki wani turani ko kinmanta halin danake ciki ne

"Cmon shut up .....bandamu da halin dakike ciki ba saboda banhada komai da abunda ke cikinki ba .....kuma inaso insan waye wannan dayazo wurinki cikin wannan Daren

Saurin dagowa aysha tayi tana kallonta atsorace dan batayi zaton taganta ba kame kame tafara irin namarasa gaskiya

Sunkuyowa asma'u tayi tana dafa kujerar datake zaune cikin murya mai kaman rada tace tun muna mu biyu kigayamun waye wannan saboda shakka babu shine uban dan dake cikinki

Zaro ido aysha tayi tana fadin what nonsense.... Are u daunting me ..?

"No I'm not .....saboda dama nasan cikinnan bana AK bane nayi shiru ne saboda banada wata hujja amma yanzu nagani da idona saboda haka kigayamun waye wannan mutumin da naganko tare

Wani wahalallen murmushi aysha tayi tana kallon asma'u tace wannan ai zancan banza ne .....baizama dole kisan waye wannan ba saboda bayada wata alaka da cikinnan .....kawai dai kice bakin ciki kike ji saboda naba AK kyewtar dake kika kasa basa amatsayinki namatarsa

nunata tayi dayatsa lokaci guda idonta yakade cikin kakkausar murya tace watch ur tongue...... kisan irin maganar dazata rika fitowa daga kazamin bakinki idan bahaka ba yanzu nagyara miki zama.....wai Ku wa'yanne irin mutane ne ....meyasa ko kadan ba kwa tsoron allah ne ....mutumin dabayada wani buri da yawuce yaga ya kyewtata muku kullun yana kokari yaga yajiyamuku dadi kuci mai kyew kusha mai kyew kusa sutura mai kyew .....kuma duk daga jikinsa kuke ciro kudin amma bakwada wani buri da yawuce kucutar dashi Ku wulakanta shi saboda me....don't u have any shame .....kirasa wanda zaki lakawa cikinki se shi .....koma wane dan iska ne yamiki shi tunda yanasonki meyasa bai aureki ba ....

katseta tayi dafadin dallah dakata mezaki gayamun ke har kinada bakin magana wace cutarwa ce baki mishiba tunda kika kwace dukiyarsa ai kingama wulakantashi kenan....
Kuma wallahi kifita daga harkata nalura kuana biyu kinasamun ido akan harkokina to ya isheki haka

Kafeta da ido asma'u tayi cike da takaici tama rasa mezatace mata kawai tajuya afusace tanufi bangaren grany

zaro ido aysha tayi tana fadin to mekuma zatajeyi wurin grany nashiga uku ...bin bayanta tayi cikin sanda har cikin palo ta labe daga bakin kofa tana sauraransu

Tafa hannu grany tayi tana salati tace ohh ni ya'su kice sharri tamasa .....haba nifa nayi mamaki shiyasa har yanzu banyarda cewa abidi zai aikata wannan abunba .....to ai yanzu bazama zakiyi ba tashi zakiyi ki gayamasa gaskiyar magana yama daina wahalda kansa akanta munafuka mai bakin hali irin na ubanta

saurin komawa dakinta tayi cike datashin hankali takira salim tana gayamasa abunda yafaru

Wata magana yagayamata tayi shiru tana sauraransa sannan ta ijiye wayar tana murmushi tanufi bangaren AK

Dagowa asma'u tayi tana kallon grany tace grany ina jin tsoro dawuya ya yarda dani kinfa san yanda ya kwallafa rai akan cikinnan ba lalle ne ya yarda cewa banasa bane

"Tashi dai kije asma'u ai yasan aysha bashi kadai take kulawa ba kinga zai iya yarda da maganarki ......kuma ai bazamu barshi haka ba yayita wahala akanta alhali munsan ba cikinsa bane

aysha nashiga palon tafara kuka saurin mikewa AK yayi yanufota yana tambayar lafiya

kara volume din kukanta tayi tana fadin ba matarka bace .....haka kawai tahau zagina wai ni yar iska ce nadauko cikin shege wai banada tarbiya .....kuma wai zata gayamaka cewa cikinnan banaka bane dan karka aureni kuma harda tarani tayi dakarfi har nabige da gado tana fadin wai seta kashe abunda ke cikina .......

wani malalacin murmushi yasaki yana fadin haba aysha .....nasan wacece asma'u bazata taba aikata haka ba kawai inaga baki fahimceta bane kuma kila ranta ne abace shiyasa amma ai ita ma tanason abunda ke cikinki kema shaidace duk abunda kike so tana sayamaki ......

kara fashewa tayi dakuka zatayi magana kenan asma'u tashigo kallon yanda aysha ke kuka tayi se duk jikinta yayi sanyi tana tsoron abunda zai biyo baya idan tagayamasa

ahankali takarasa wurinsa cikin sassanyar murya tace .....inaso zamuyi wata magana

Go ahead ......yafada yana kafeta da ido

shiru tayi nadan lokaci sannan tadago tasaci kallon aysha sannan tamaida kallonta kansa cikin rawar murya tace ....in ....private

"She is my wife to be kuma uwar Dana so zaki iya fadan komiye agabanta .....inajinki

riko hannunsa tayi tana fadin karya take maka AK cikin dake jikinta banaka bane she is just blackmailing u da tacimma wata manufa ta....

bata karasaba yayi saurin kwace hannunsa yana fadin enough!!! Ashe dama gaskiya tafada har ina karyatata ....kinbani mamaki Ashe dama son dakike nunawa cikinta duk yaudara ne ....wai meyake damunki ne asma'u dama haka halinki yake ko kudine suka sa kika canza halayenki masu kyew

Idonta ne yaciko da kwalla tana kallonsa cikin muryan kuka tace AK believe me gaskiya nake fadamaka ba cikinka bane wanann kawai......

hannu yadaga zai mareta se kuma yadakata yana dunkule hannunsa yanunata da yatsa yace .....ya isheki haka bana bukatar jin komai daga gareki cikinnan nawane inasonshi daga shi har uwarshi kuma dazaran ta haihu zan aureta .....zamu tafi gaba daya mubar miki gidan kiyi abunda kika ga dama dashi

Jan hannun aysha yayi zasu fita tayi saurin shan gabanshi tana kuka tace AK please listen to me kuskure kake aikatawa babba Wanda nan gaba zakayi nadamarshi

tureta yayi daga gabansa yana fadin ba abunda yashafeki dani najima dayin nadamar saninki arayuwata ....kuma bari kiji ....idan nakara jin wannan maganar abakinki ko abakin wani daban I will show u the other side of me ....yana kainan ya wuce yabarta atsaye tana binsu da kallo hawaye na tsere afuskanta

Juyowa aysha tayi tana murmushin gefe takai hannunta tashafo cikinta tana kashemata ido har suka fita daga palon

Durkushewa tayi awurin tanafashewa da kuka yace ABI why don't u believe me .....meyasa ka amince da mutanen da ke kokarin ganin bayanka ne .....oh allah kataimakeni ....abun yamun yawa da wanne zanji

Washegari dasafe kafin ta tashi har ya gama aikin databashi yayi shirin zuwa office yana fitowa ya hadu da sarah idonta jajir da alama bataga bacci ba gashi fuskanta dauke da damuwa

Wurinsa ta nufo tana boye damuwarta tace Yaya dama kai nake jira ...

Gyara tsayuwarsa yayi yana fadin to gani fadin matsalarki lil sis

Murmushi tayi tana Sosa kai tace Yaya .....dama ......wasu yan kudi nake bukata ahannunka kozan samu.....

Hannunsa yakai aljihu yana fadin bari mugani inaga baza'a rasaba wata kudaddiyar dubu daya yaciro daga aljihunsa duk ta kudundune seda ya bubbudeta sannan ya mikamata yana murmushi yace gashi je kisamo canji kiraba biyu kikamun sauran zansha coffee anjima

sake da baki take kallon kudin kamar zatayi kuka tace Yaya ....banganeba ....mezanyi dawannan nida nake naman 5M

Zaro ido yayi yana gadin 5M fa kikace sarah......kodai banjiki da kyew bane mezakiyi da kudi masu yawa haka

saurin juyawa tayi tanufi dakinta tana fadin barshi kawai dawasa ma nake maka
Chapter 62 · 0% Book details