← Book details Domin Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 84

Sashe 41

Domin Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kin tashi tayi seda yajanyota ya zaunar da ita sannan yayi tsaye kusa da ita yana kallonta

Tureshi tayi daga wurin tana fadin to katafi bazan iya yi kana kallona ba

fita yayi daga dakin yana murmushi seda yadan jima sannan yaleka yana fadin wai haryanzu baki gama ba

juyowa tayi tana kallonsa yayi saurin ja dabaya yana salati yace chitti mezan gani haka to ai dawannan gara babu
muka fita haka ai watsewa za'ayi abamu waje ya salam!!!

Langwabar dakai tayi tace to ni gaskiya ban iyaba nama fasa fita kawai kacemusu bana jin dadi

Karasowa yayi wurinta yace je kiwanko fuskarki kizo namiki dakaina natabbata sena fiki iyawa

Tashi tayi tana dariya tanufi bayi tana fadin ashe kwa zamu kuana anan bamu gama ba

tana shiga bayi ya fiffito dakayan kwalliyar yana karanta yanda ake anfani dasu koda tafito yagama tsab yaware wanda zai bukata gefe guda tana zama ya nannande hannun rigarsa ya shigayimata simple make up yana yi tana mai dariya bayan yagama da fuska yakoma bayanta ya warware ribbon din data daure gashinta dashi kallonta yayi tajikin mirror yace chitti umma bafulatana ce ko buzuwa

Dariya tayi tace bakatapiya ce
Shima dariyar yayi yagyara gashin yamata parking mai kyew sannan yagyara mata gyalen

ba'adau lokaciba yagama yana murmushi yace to duba kiga

Mamaki tayi bakadan ba ganin yadda tacanza lokaci guda la lips din nan sunsha janbaki tayi kyew bakadan ba

Juyowa tayi tana kallonsa da mamaki tace ABI dama ka iya ne

girgiza mata kai yayi yamikar da ita yana fadin bantaba yiba se akanki yanzu muje kinga ahmad najirana amma dan allah bakinki alekum nasan ki talkative ce saura kigayama khadeeja ni namiki kwalliyar mushiga uku

suna fitowa kallo yakoma Kansu nan take aka hau tapi ana shewa da gudu khadeeja tazo tarungume asma'u tana dariya tace ammah kinganki kuwa gaskiya yau kinyi kyew bakadan ba

Juyowa tayi takalli AK sukama juna murmushi janta gefe khadeeja tayi tana fadin ammah zo gayamun miye sirrin nidai nasan baki iya make up ba

Hannaye taware tana fadin bansaniba ba

Khadeeja zatayi wata maganar ta kwace hannunta tabar wajan tana murmushi

Da kallo tabita tana fadin this is the beginning of ur love story sis

Karasowa ahmad yayi kusanta yana fadin deeja kina ganin abunda nake gani kuwa

Dariya tayi tace ohh ni tarzan ashe kaima ka iya gulma

Dariya yayi yace deeja asma'u da AK sun bala'in haduwa

"wallahi inama suna son junansu dase sunfi kyew

"Zama suso ne ai naga andawko hanya

tunda suka fara magana sarah ke kallonsu tana sharan kwalla kusa da ita aysha tamatso tana fadin sarah wai meyake damunki ne ni nasan wallahi karya kike kice kin hakura da ahmad yanzu gashi kinkasa juran ganinsu tare bare kuma ace sunyi aure

Barin wurin tayi batare datace mata komai ba

Khadeeja da ahmad sunzo wucewa kan stairs kenan kawai taji anturata dakarfi zata fadi kasa ahmad yayi saurin janyota tafado kansa da gudu asma'u da fa'iz suka karasa wurinsu suna tambayar lafiya

Rike kanta tayi tana runtse ido arude ahmad yadauketa yakaita bangaren AK

Kan 3sitter yakwantar da ita yana tambayar bataji ciwo ba

Dafe kanta tayi tana kallon asma'u tace ammah ba faduwa naje yiba turani akayi

Damamaki suka kalleta suna fadin turawa fa khadeeja to wa zai turaki

Murmushin takaici fa'iz yayi yana kauda kai yace ya wuce wannan busassar yarinyar aysha ai naga lokacinda tabi bayan Ku dazaku haura sama

azabure ahmad yamike zaifita asma'u tarikoshi tana fadin a'a ahmad barshi kawai zanmata magana dakaina ba laille ne yakasance ita bace saboda banga dalilin dazaisa tanemi hallaka khadeeja ba

girgiza kai ahmad yayi yace ammah bakisan suwaye wa innan matan ba zasu iya yin komai wayasani ko tana taya sarah kishine nasanta bata da mutunci

aysha ce tasigo dakin sarah tana tafa hannu tace Weldon sarah nice try natabbata nan gaba bazakiyi kuskure wajan aikata lahira ba

damamaki sarah tajiyo tana kallonta tace kamar ya ban...gane ...akan wa kike magana ba

Dariya aysha tayi tana zama kan kujera tadaura kafa daya kan daya tace sarah karki manta da aysha kike magana ba AK ko asma'u dazaki iya deceiving ba ko kinaso kicemun bake kika turo khadeeja daga sama ba

Shiru Sarah tayi tana kauda kai da hawaye a fuskanta

murmushi aysha tayi tace karkice mun a'a saboda da idona naga lokacinda kika turata kuma naga lokacinda kika zuba wani Abu a jus dazu kika bama nura yakai mata amma kafin yakai glass din yafadi yafashe kinji haushi har kika mareshi daga nan nafara samiki ido dan nasan dole akwai abunda kike shiryawa

sarah nasanki kamar yunwar cikina I know u will never change for good

Saitin window sarah takarasa ta tsaya tana kallon waje cikin muryar takaici tace

Kwata kwata yaushe tashigo rayuwarsa wacece asma'u bare wata kanwarta lokaci guda yamanta ni kanwarsa ce ya dauki farin cikina yadanka ma wata baare

Hawayen fuskarta tashare tana cije lebe tacigaba dafadin

sunyi wawta dasuka yarda cewa wai ni sarah nacanza

Dariyar keta tayi tajuyo tana kallon aysha tace banso kowa yasan abunda nake shiryawa ba amma bakomai tunda kece kika gani ba wani ba aysha ina ma ahmad sonda ni kaina bansan yanda zan fadeshiba

Tunda AK yariga ya yanke cewa Ahmad zai auri khadeeja to tabass zai aureta

amma kuma ai setana raye zai aureta ko idan har nacigaba da nuna adawata akansu to dazaran wani Abu ya sameta ni za'afara zargi shiyasa nafito dawannan hanyar

Nuna kanta tayi dayatsa tace idan har ni sarah ban auri ahmad to ba wacce ta isa ta aureshi
sedai idan bana nunfashi adoron kasa

asma'u ce taturo kofa tashigo sauri juyawa sukayi suna kallonta

Murmushi sarah tayi tace ohh hello sister karaso mana

Karasowa asma'u tayi fuska ahade tace nasan cewa faduwar khadeeja ba haka kawai bane someone is behind it

atsorace suka kalli juna sannan sarah takalli asma'u da damuwa tace to waye zai yi kokarin cutar da khadeeja akan wane dalili

kallon aysha asma'u tayi tana fadin aysha ce ta turata dalilin kuma shinazo inji daga gareta

Azabure aysha tamike tana fadin what nonsense

alama sarah tamata datayi shiru sannan takalli asma'u tace kintabbata itace ?

"To waye zaiyi hakan inba itaba

Juyowa sarh tayi tana kallon aysha cikin daga murya tace how dare u
akan wane dalili zaki aikata wannan shirmen idan ma kina tunanin kishi kike tayi to u are westing ur time saboda ni khadeeja matsayin kanwa nadauketa idan kika kara aikata makamancin wannan to ba abunda zai hana namikaki ga police

Kasheta kike so kiyi

baki bude aysha ke kallonta cike da takaici tama kasa magana

dafa sarah asma'u tayi tana murmushi tace kibarta kawai sarah basai takai ga police ba mutuncin gidan nan ne zai zube

sannan tajuyo tana kallon aysha tace wannan yazama na farko kuma nakarshe idan kika kuskura kikayi na biyu to ina tabbatar maki cewa u won't get another chance to do the last one

Tana kainan tafita tana banko kofar dakarfi

juyowa aysha tayi tana kallon sarah da mamaki tace miye haka kikayi akan me zaki dawra mun alifin da ba ninayi
ba

Zama sarah tayi kan kujera tana dafe goshi tace I am seeking tried of this girl wallahi ba karamin dakewa nakeba kafin natsaya agabanta ina mata magana

jdagowa tayi takalli aysha tace wai yakukayi da AK ne akan zancan barinta gidannan meyake jira da ita

tsaki ausha tayi tana zaunawa bakin gado tace na tambayeshi yatsaya mun kame kame wai muduba grany..... batada lafiya .....yana bukatr hujja kafin yasaketa

dariyar mugunta sarah tayi tana kuantar dakanta kan kujera tace hujja ko ???

To ni zan bashi hujja just wait and see

grany ce kawai zata bani matsala

Cike da farin ciki aysha tace idan ma grany ne bakida matsala saboda naji tace gobe zasuje Kaduna itada inna ameena amma kuana 2 kawai zasuyi

Murmushin mugunta sarah tayi tace good

Ina wannan Alin cousin dinta dakika ce yana damunki awaya

yamutsa fuska aysha tayi tace yana nan miye

Tashi tayi tafita tana fadin ki tabbata kunyi fira mai dadi dashi ayaw har ya yarda cewa kin amince dashi gobe zan gayamaki sauran plan din

Dakallo aysha tabita tana murmushi har tafita sannan takuanta tana fadin bakida kyew sarah ni kuma zanci gaba da binki ahaka har nacimma burina na auren AK daga nan kuma I will show u the worst part of me

[19/07, 17:03] Hubbey Frd Ameena Kn: 📚📚📚📚📚📚
👨‍👧 _DOMUN KANWATA_ 👩‍👧

Na(Maryam Mhd)

1⃣2⃣5⃣

Washegari dasafe sarah ta isko asma'u apalo kusa da ita tazauna tace sister dan allah wata alfarma nakeso kimun

murmushi asma'u tayi tace ina jinki menene

Rada tamata akunne asma'u tayi murshi tace OK badamuwa amma mezai hana kigayama AK ainasan bazai hana ba

Rungumeta tayi tace thank u sister amma banaso Yaya yasani nafiso semun daidaita tukunna

tashi asma'u tayi tanufi kitchen tana fadin to bari nadora yanzu kar yazo bamu gamaba

tana tashi aysha tazo tazauna kusan sarah tana fadin wow good acthing sarah naga kamar ta yarda ko?

"eh amma ina fata dai kinyi abunda nace

Nuna mata wayar ta tayi tana fadin kalla kiga garan har ya amince shima naga alama kamar dan hannu ne har da fadin wai inaga ba matsala idan yazo badasanin AK ba

Dariya sarah tayi suka tafa

Kowa nazaune apalo grany suka fito cikin shirin tafiya AK yayi jigum kamar zaiyi kuka se tsokanarsa asma'u keyi tana dariya

Amir yaron inna ladidi se yawo yake da camera ahannunsa yana musu video

Tashi sukayi gaba daya zasu raka grany airport ganin asma'u batada niyyar tafiya yasa AK yace chitti muje mana

Langwabar dakai tayi tace ABI kuje kawai banajin dadi bazan samu damar zuwaba

kureta yayi da ido nadan lokaci sannan yace anya kuwaaaa ni banga kinyi kama damara lafiya ba

Jan hannunshi sarah tayi tana fadin Yaya muje mana tace batajin dadi dolene

Sallama suka mata suka tafi bayan kowa yashiga mota suntafi aka bar aysha da sarh atsaye jikin motarsu kamar zasu shiga suna ganin kowa yatafi sarah taja hannun aysha suka koma ciki suka labe awani daki batare da asma'u tagansu ba cikin rada sarah tace aysha kintabbata zaizo kuwa
Chapter 41 · 0% Book details