← Book details Domin Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 84

Sashe 43

Domin Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yana isa gida yakira khadeeja tasamesa afilin gida damamaki tace Ali lafiya wai meyake damunka ne

shakan iska yayi yafurzar sannan yace deeja yau kunyi waya da asma'u ?

girgiza kai tayi tana fadin a'a lafiya

"I don't know amma dan allah idan bakya komai kidan lekata mana kiga yatake

matsawa tayi kusa dashi tana fadin Ali bangane naje nadubata ba meyasameta

zaiyi magana kenan sukaji anturo kofa atare suka juya ganin asma'u yasa khadeeja tayi saurin isa wurinta cike da damuwa take kallonta tace ammah meyasameki yanaganki haka bakida lafiya ne

Karasowa wurinta Ali yayi cikin rawar murya yace asma'u are u ok ina kiran wayarki kinki dagawa I was so worried ina fata dai ba....

bai karasa ba yaji saukan lafiyayyen marin dayahanasa karasa magamarsa

atsorace khadeeja tadafe kuncinta dan yanda taji marin bazata tadauka ita aka mara

cin kwalar shi asma'u tayi cikin sheshshekar kuka tace Ali menamaka zaka mun haka meyasa tunda baka shafamun bakin painti ba seda nayi aure meyasa.....

Takarashe maganar tana sulalewa akasa tadora kanta akan kafarsa tana fashewa dawani irin kuka mai ban tausayi

lokaci guda itama khadeeja tafara kukan durkusawa tayi kusa da ita tana dafata tace ammah meyasameki meyake damunki ne yaushe kika fara boyemun damuwarki ..

Ganin asma'u takasa bata amsa yasa tamike tsaye tana jifan Ali dakallon tuhuma cikin wata iriyar murya tace mekamata tunda naganta awannan halin natabbata kamata abunda yafi karfin tunaninta

kauda kai yayi dan tuni kukan dayake dannewa yaci karfinsa cikin kukan yake fadin

deeja ni kaina bansan meyake faruwa ba jiya wannan yarinyar aysha tagayyaceni gidansu wai nazo tana son ganina ta amince dani dafari ban yardaba amma tunda ta turomun wasu banzayen pictures da videos dasuka sa narasa natsuwata kawai naji ba abunda nakeso irin na ganni kusa da ita amma wallahi banje gidan dawata manufa ba ...

katseshi asma'u tayi dafadin wannan zancan banza kake Ali idan har wurin aysha kaje dagaske meyakaika dakina akan gadon mijina what kind of rubbish is that

dafe kansa yayi yana fadin yes nasan nashiga daki amma bansan ko nawaye ba karki manta ni bako ne ita tamun kuatancen dakin tace mun natane nasameta acan amma ni bansan cewa dakinki bane kuma kema kinsan ba halina bane ...yana kainan yawuce cikin gidan rai bace

tunda yafara magana khadeeja kebinsa da ido tana jin zancan nasa banbanrakwai dan basosai ma takejin meyake fadaba saboda yanda maganar ke fita dakyar daga bakinsa

Durkusawa tayi tana share mata hawaye cikin sassanyar murya tace ammah dan allah kigayamun meyake faruwane ko naje nagayama Umma ne

a'a muje kirakani gida zan gayamaki...

fita sukayi daga gidan akan hanya take bama khadeeja labarin duk abunda yafaru har lokacinda AK yabata natakawo masa shaida ko tabar masa gida

takare zancan dafadin khady wasu lokutan baka sanin yakake ji agame damutum se karabu dashi bansan miye so ba bantaba yiba amma inada tabbacin abunda nakeji agame da ABI shine so kowa da yadda kaddarar soyayyarsa take zuwa masa arayuwa amma ni tawa inaga bata zomun a saa'a ba

ajiyar zuciya khadeeja tasauke datagama jin bayanin yayartata

cike da tausayi tace ammah inaga AK yabullo dawannan hanyar ne dan yasamu yarabu dake cikin sauki batare da anga laifinsa ba dama Yajima yana Neman hujjar dazata sa yasakeki to bare yanzu dayasameta ahannu gashi kuma grany batanan

kawai kisa aranki ba abunda zai faru sai alkhairi idan rabuwa kukayi ma kidauka hakan shine yafi maki alkhairi tunda dama can ba wani dacewa kukayi ba tunda bazaman aure kuke atsakaninku ba

Murmushin dayafi kuka ciwo asma'u tayi tana girgiza kanta tace khady bazaki gane bane nasan bazaman mata da miji muke dashiba amma kuma inason zama dashi ahakan duk danasan cewa hakan ba mai yuwa bane saboda banada wata shaidar dazata hana faruwar hakan

Shiru sukayi kowa da tunanin dayake aransa har suka isa gida seda khadeeja tarakata har bangarenta sannan tamata sallama akan se sunyi waya anjima

Tana fita tahadu da AK zai shigo nufota yayi yana fadin ohhh hi little sis yaushe kikazo

Tagefensa tabi tawuce batako kallesa ba bare yayi tunanin zata amsa masa

saurin shan gabanta yayi yana murmushi yace wait wait deeja ba fada me yakawo gaba ko baki ganeni bane nine fa ....

katseshi tayi dafadin Yaya wai ya kake acting kamar bakasan mekayi bane karo nafarko nahango rauni da kasawa a idanuwan yayata kuma duk tadalilinka

yaya bansan ya kagansu ba maybe atsaye ne ,azaune ko akuance wuri guda abu daya nasani shine koda mutanen duniyar nan gaba daya zasu taru su zargeta akan wannan abun to ni khadeeja (tafada tana nuna kanta dayatsa )
Zan shaideta akan bazata taba aikata makamancin wannan kazamin aikin ba

hawayen fuskarta tashare sannan cikin rawar murya tace Yaya gatanan kayimata abunda kaga dama amma kasani idan har wani abu yasameta tadalilin wannan case din to nmbanajin zan taba yafemaka

tana kainan tayi gaba abunta tana gyara fuskarta dayajike dahawaye

dakallo yabita yana murmushi har tafita sannan yawuce ciki

apalo yazauna yana kallo can anjima asma'u tazo zata wuce yakirata nan take taji gabanta yafadi dan tasan baiwuce zaimata tuni da lokacinda yabata bane
Jiki asanyaye takaraso wurinsa daga gefe tazugunna tana jira taji mezaice

Bring my coffee.... yafada batare dayakalleta ba

da mamaki tadago tana kallon fuskarsa bayabo ba fallasa juyowa yayi yakalleta suka hada ido tayi sawrin sadda kai kasa tana murza yan yatsunta
kureta yayi da ido nadan lokaci sannan yace matsalarki ta tashi daga kan ido takoma kan kunnene kome nace kikamun coffee dina ko bakijiba

saurin tashi tayi tafita ba'adau lokaciba tadawo dauke da coffee din sedai ta isko aysha apalon tana zaune kamar zata shigemai jiki se fira suke suna dariya

Mikamasa coffee din tayi tana daure fuska bata ma yarda tasake kallonsuba

Kin karban coffee din yayi ahnnunta seda yaga tana kokarin ijiyewa sannan ya karba yana kallon fuskarta yace yanaga kin dame fuska ne tunda saurayinki zai iya zuwa wurinki to miye dan budurwata tazo wurina

saurin juyawa tayi zata bar wurin yacabko hannunta cak tatsaya batare datajuyo ba shima kuma bai janyota ba cikin murya mai kaman rada yace inafata baki manta yanda mukayi dakeba

"ban manta ba

"zuwa gobe idan har baki kawomun ba zaki tafi gida

share hawayenta tayi da dayan hannun batare data juyoba tace

yaune ba gobe ba saboda haka yau din zantafi

Murmushi yayi shima batare da yadago yakalleta ba yace gobe zaki tafi saboda naga alama kinada bukatar Karin lokaci

shiru tayi batace komai ba dan tana bude bakinta kuka ne zaifito da kyar ta iya fadin free my hand

sakin hannunta yayi tawuce daki ta rufo kofar tana sulalewa awurin tasaki kukanta mai ban tausayi

cike da bacin rai aysha tace AK bangane ka karamata lokaciba ko shekara zatayi batada wata shaidar dazata gabatar garama kawai kabarta ta tafi

Juyowa yayi yana kallonta yace ya akayi kikasan bazata taba samun shaida ba tukunna ma ya akayi kika San inda maganar mu tadosa bayan nidai nasan bamuyita dakeba ko ita tagayamaki

Saurin girgiza kai tayi atsorace dan se alokacinma tagane subutar bakinda tayi

Da daddare asma'u tafara hada kayanta tana sakawa a akwati har wannan lokacin bata bar kuka ba rigar AK tagani acikin drowarta wacce ta taba sakawa a hotel dawkota tayi tadawo bakin gado tazauan tana tunano dramar dasukayi ranan rungume rigar tayi tanashakan kanshin turarensa hawaye na tsere akan kuncinta

jin anturo kofa yasa tayi saurin ijiye rigar tana share hawayen fuskarta

karasowa yayi bakin gado yana daga rigarsa yana murmushi yace ohh my favorite shirt kallon asma'u yayi cikin sigar tsokana yace ina data dai ba saceta zakiyi ba

kauda kai tayi batace komaiba

Ijiye rigar yayi saman akuatinta yana fadin ok I understand zakiyi missing dina shiyasa kike bukatar wani abu nawa dazaki rika tunawa dani ko

Runtse idonta tayi tana damke bedsheets dakarfin gaske aranta tana fadin yes zanyi missing dinka ABI amma bana bukatar abunda zai tunamun dakai saboda bazan taba mantawa dakaiba

Dawkan gyalenta yayi yana dariya yace nima kinga sekibani wannan lippayan taki dan inrinka tunawa dake ...yakarashe maganar yana labace baki irin nayara

kwace gyalenta tayi tana fadin bazan badaba mezakayi dashi kuma ba lippaya bane gyale ne

hannu yakai zai dauka tayi saurin rufe akwatin tana tureshi daga wurin tace ABI dan allah kabarni kar kakara tabamun kayana

Dariya yayi yace chitti tsaya mana miye nafada kuma muda zamu rabu gobe kinga kin huta dani kamata yayi yau mukuana muna fira tunda itace ranar karshe awurinmu

turasa tayi har bakin kofa tana fadin jeka banaso ko yanzu kabarmun abubuwa da dama dabazan manta ba ya isheni haka

bude hannayensa yayi yanufota yana fadin chitti I'm gonna miss uuuuu

saurin turasa tayi tana rufe kofa tana share hawaye tadawo tacigaba da hada kayanta

Dakin sarah yanufa ya iskota zaune da aysha suna fira zama yayi akaci gaba dafirar dashi
[19/07, 17:04] Hubbey Frd Ameena Kn: 📚📚📚📚📚📚
👨‍👧 _DOMUN KANWATA_ 👩‍👧

Na( *Maryam Mhd*)

1⃣3⃣5⃣

washegari dasafe.....

daki tashigo rike da coffee din AK cikin flax da mug tadoroshi akan faranti har wannan lokacin tana hawaye jikinta gabadaya yayi sanyi kan bedside drawer tadorashi tana kallon photon AK dake ijiye awurin yana sanye da faran shirt da murmushi afuskansa yayi kyew sosai

ahankali takai hannu tadauki frame din tana murmushi tashafo fuskansa hawayenta nadiga akan frame din

rungume photon tayi akirjinta tana runtse idanuwanta hade da cije lebenta nakasa hawaye na tsere afuskanta

zama tayi bakin gadon tana kallon photon cikin rawar murya tace

ABI meyasa bazaka yarda daniba ABI nasaba dakai meyasa kake kokarin nisantani ga gareka lokacinda nafi bukatarka arayuwata

tayu natakuraka kana so karabu dani kodan ka auri wacce kake so

ABI it's very difficult for me to leave without u

Sarah ce taturo kofar dakin tashigo tana nunata dayatsa ta kwashe da dariya

saurin juyawa tayi da mamaki tana kallonta

karasowa tayi tadafa kafadanta sannan tasa yatsa tatabo kwallan dake kuncin asma'u cikin murya mai kaman rada tace

ohhhh abun ba dadi ko ?

nataba shiga wannan halin amma bawanda yadamu dahakan bawanda ya tausayamun bawanda ya rarrasheni

saboda haka kema kiji abunda naji

cike da mamaki tace sarah wannan wace kalan banzar magana kike gayamun
Chapter 43 · 0% Book details