← Book details Domin Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 84

Sashe 1

Domin Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

[18/07, 15:03] Hubbey Frd Ameena Kn: 📚📚📚📚📚📚👨‍👧DOMUN KANWATA 👩‍👧

🖊Na marubuciya husna kabir zarewa (the mammah girl)

🖊Da sunan Allah mai rahma mai jinkai.......

Inama dukkanin masoya manzan allah (s.a.w) fatan alkhairi arayuwar Ku dafatan zaku bani hadin kai da goyan baya domin gani nakare wannan littafin nawa asa'a kuma Allah yabamu ikon aiki da abinda ke cikinsa na alkhairi ameen...
idan nayi kuskure ina fata zaku tunatar dani daga mai sanku ako da yaushe HUSNA ( the mammah girl)

👨‍👧DOMUN KANWATA👩‍👧

1⃣⏭5⃣

Kuance take akan gado ta rufa da bargo baccinta take hankali kuance Wata kekkyawar mata ce tashigo dakin wadda akalla shekarunta baza su wuce 45 ba bargo ta janye tare dakiran sunanta Asma'u!!! ke Asma'u wai bazaki tashi bane baccin yasa isa haka rana fa tafito

Cikin muryar bacci take fadin
Umma Dan Allah kidan barni minti biyar kawai zan kara Umma tayi murmushi tace tun dazu kike fadin minti 5 dinnan kizo kikai mun nikan nan insamu inyi kosan nan kar Kuyi Lattin makaranta Asma'u bata ce komai kuma bata motsa ba ganin haka yasa Umma tanufi hanyar fita daga dakin tana fadin to bari ma kawai in tashi khadeeja ta yo mun nikan ai kafin Umma tarufe baki tuni Asma'u ta diro daga kan gadon a'a Umma base kin tashe taba zan je dakaina Umma tayi murmushi tafita daga dakin Asma'u bayi tawuce tana mutsitsike ido
Bayan kamar minti 10 tafito kitchen tanufa ta iske Umma ta ijeye mata robar nikan da kudin akai ta dauka ta wuce daga gidan Asma'u kenan kekkyawa ta bugawa ajarida shekarun baza su wuce 20 ba tana da tsayi daidai guarguado tana kyan jiki ta yadda ko mace takalleta se takara kallonta tanada far'a Da son mutane ba komai ne yake bata mata rai ba tana da hakuri da kaw dakai wannan kenan....

Daga wanka yafito da towel daure akugunsa da wani Dan karami akan sa yana goge gashin kansa wayarsa ce tayi kara bai kula ta ba se da takusa katsewa yana daga tare da amsa sallamar da aka mishi ban ji me aka ce tadayan ban garan ba naji yace mu hadu a office tare da ijiye wayar ya ci gaba da shirinsa yana gamawa ya fito daga bangaran sa ya sauko kasa se alokacin naga Ashe babban gida ne ba na wasa ba daga kasa akwai katon falon da girmansa ya kai na wani gidan tsayawa fadan tsaruwar falon bata lokaci ne akwai dakuna sunfi talatin akasa se matattakalai kuda biyu daya yayi dama daya kuma hagu acan sama ma dakuna barkatai abun dai sai Wanda ya gani da gani kai kasan dukiya ta yi kuka awurin domin idan baka fito za ka dauka akasar waje kake....
Yana saukowa kasa ba kowa afalon se masu aiki da suke kai kawo direct wani bangare yanufa anan kasan Shiva yayi tare dayin sallama wata dattijuwa ce zaune akasan kapet din falon tana cin abinci ta na ganinsa ta fadada far'arta ta amsa mishi sallama tare dafadin ABID katashi??
Karasowa yayi kusa da ita ya zauna tare dafin eh GRANY ina kuana tace lafiya kalau ga abincin ka can a dining kasan ni Nafi son kasan nan murmushi yayi tare da wucewa dining din yafara zuba abinci

ABID kenan wankan tarwada ne dogo mai dan matsakaicin jiki kyakkyawa bana wasa ba
yafara ci abinci kenan kenan wata matashiya ce da shekarunta bazasu wuce 22 tashigo falon tare da sallama grany ce ta amsa batare data dago takalleta ba itama yarinyar bata kalli grany tawuce direct zuwa dining tana sanye da farad doguwar riga tamata Kew sosai tana isa dining din taja kujere ta zauna tare da fadin good morning bro ABID yadago murmushi dauke afuskar shi ya amsa da morning KANWATA kin tashi?? murmushi tare da cewa yaya ina alkawari na yace name fan!!!?
Shagwabe fuska tayi tace yaya tafiyan dazamuyi ni da aysha mana
Yace to ai nace se kinfara girmama grany kuma ni banga kinfara ba
Yaya Allah nafara bakaga da nashigo namata sallama ba zai yi magana carab grany ta ce yo da kika mun sallama kin kalli inda nake ne bare ma ki gaidani sallaman ma daba Dan kinsan ABID na nan ba ai da bakiyi ta ba kuma ma wai uban me zaku je kuyi a London duka duka yaushe kuka dawo
ABID laifinka ne wallahi kai kasangarta SARAH abinda take so shi lake mata shi yasa kwata kwata bata ganin girmana
Sarah ta hade fuska takalli ABID tace yanzu yaya maganar nan se da kagayawa grant bayan kasan idan ta grany ne ko abincin gidan nan se naroka za'abani tana gama fadan haka ta fice daga palon grany tabita da harara
ABID ma tashi yayi ya dauki wayoyinsa yama grany sallama yana fita direct wurin motocinsa ya nufa motocin sun fi goma kowa da kalarta amma bakake sunfi yawa bodyguard dinsa suna gani ya fito suka mike suna mika gaisuwa sannan aka fito da motoci biyar bakake guda hudu sunsa fara daya atsakiya wurin farar yanufa aka bude mashi baya ya shiga suma suka shiga sauran aka wangale masu katon gate din gidan suka fice

ASM'U ce tadawo daga kai nikan a kitchen ta isko Umma tana dama koko Umma tace kindawo??
Eh Umma nadawo khadeeja ta tashi Umma tace a'a kema kinsan tashin khadeeja ai sai ke damma tace yau se 10 takeda lectures ai da tamakara
To ummah bari in tasheta dakin da khadeeja taken tanufa ta tura kufar tashiga tare da sallama tana kuance tana baccinta tsaye tayi tana kallonta tana murmushi ahankali takarasa ta zauna bakin gadon ta Dora hannunta akan khadija tana kiran sunanta khdy!!!
khadeeja takara gyara kuanciyanta taja bargo Asma'u tayi murmushi taje ta zuge labule rana ta haska fuskan khadeeja takara jan bargo ta rufe fuskanta cikin muryan shagwaba Ahmm Ahmm amma kibarni inyi bacci matsowa kusa da ita tayi tadagota tana fadin khdy zakiyi latti garama kitashi kafin Umma tazo da ruwan sanyi tashi tayi tana zumbure baki tashiga bayi Asma'u tabita da murmushi ta bude drowan khadeeja ta fito mata da uniform da jakanta ta dauko mata takalminta da safa ta ajiye mata kana tawuce kitchen tana taya Umma suyan kosai bayan sun gama ta zuba kosai a plate ta zuba kunu a cup ta koma dakin khadeeja ta iske khadeeja ta gama sa uniform ta na sa takalminta na makaranta Asma'u ta ijeyi plate din hannunta kan dressing mirror ta natso ta karba takalmin hannun hkadeeja ta tsugunna tafara saka mata khadeeja dai se binta take da ido har tagama saka mata ta dago suka hada ido Asma'u tace kallon fah khadeeja tai murmushi batace komai tadauki kosan da kunu tafara sha Umma tana zaune apalo suka fito khadeeja taje ta rugumeta tace Umma ina kuana Umma hmm ni dagani yanzu kuma ai saidai ai zancan wuni ina tunanin ranarda Asma'u zatayi aure bansan ya zakiyi ba khdeeja Ta shagwabe fuka tace ai tare zamu tafi ko yaya Asma'u tai murmushi sosai ma KANWATA khadeeja ta tashi ta musu sallama ta fita asma'u ma ta wuce dakinta ta shirya tama Umma sallama ta fita

Hkadeeja kanwa ce awurin Asma'u suna kama sosai sedai ita khadeeja wankan tarwada sabanin Asma'u fake fara shekarun khadeeja 17 tana ajin karshe a scndry school asma'u kuma level 200 a gwagwalada university fake nan abuja su biyu iyayensu suka Haifa asma'u tana bala'in son khadeeja tun tana karama tazama tamkar uwa agareta khadeeja tasha yin laifi amma Asma'u se tace ita tayi kawai dan kar adaki khadeeja zata iya yin komai AKAN khadeeja
baban su bakano ne se kuma mamansu bafulatanar Adamawa ce suna zaune a unguwar life camp dake abuja ba wasu masu hali bane se dai rufin asiri da wadatar zuci babansu Allah ya yimai rasuwa tun khadeeja tana Karama ada mamansu taso takoma garinsu dayaran amma yayan babansu yahana Wanda yake anan abujan shima dazama yana da mata da yara 2 nusaiba da fa'iz Se mamanshi datake zaune agidan shi wato kakar su asma'u kenan
To wannan dalilin ne yasa Umma take zaune a abuja saboda bazata iya Barin yaranta tatafi ba

Da yamma misalin karfe 5 Motocin ABID suka shigo haraban gidan ana gama parking dai daga cikin guards dinshi yazo yabude mashi baya yafito cikin takunshi na kasaita ya karasa cikin babban palon gidan yana shiga ya iske palon a cike da ain gidan kasancewar gidan family house ne duka aciki family suke

tuna baya!!!!!!
Chapter 1 · 0% Book details