← Book details Zazzafan So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 88

Sashe 88

Zazzafan So Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Ta rasa yadda zata nuna mishi jin dadin ta.. sai kawai ta bashi ~warm hug~sosai yake jinta shima.
_Thank you my luv u're really such a good caring and loving husband.._
"Kiyi shuru mace ta gari..ni da ke babu godia fa."

Haka yake fad'a mata yawancin lukuta idan tana mishi irin wannan godiyar.

Sun dawo gida. Hafsah ta sanar wa da Mama an kammala gidan ta tura musu photonan sassan gidan. Mama tayi murna sosai dasa albarka gidan ya kawatu a wajenta matuk'a ta kuma gode wa Allah yarta ce zata zauna cikin shi.

Hafsah taji godiyar da tayi bata mata ba don haka suna zaune suna daddana wayoyinsu ta ta fa "Thank you dear husband.'
Ya ga abin kamar gizo sunan ta ya bayyana ta turo mishi text. Ya duba ya kalleta sai ta mishi murmurshi. Ya nuna ta da yatsa kin ganki koh."
Sai ta kumshe fuska tana dariya.

Haka suke tafiyar da rayuwar su cikin jin kulawa da gujewa b'acin ran juna su kanyi duk wani abu da zai sa musu nishadi. Misali a lukuta irin na weekend ko sanda bashi da ayyuka sosai in yana gida Hafsah na kirkirar musu abubuwa funny things da zasu sashi nishadi."
Takan ce ya karanta mata ko it ta karanta mishi wani Littafi sai ta kwanta tana sauraron shi tanajin dad'in muryarshi da yanda yake furta turancin.. Yana iya daurewa ya karanta mata da dan dama? kafin tana ganin ya tsaya ko ya chanja yanayin shi zata kwaikwaye kafin ya fada ta rigashi."
"Na gaji ban iya karanta abubuwan nan naku fah."

Ya nuna kanshi ni kike tsokana koh. Tayi saurin girgiza "A'a..Aa."
Tasan halinshi yanzu zai mata mugunta ko ya matse mata hannu ko baki, kuma bilhaqqi tanajin zafi. Ta ma kasa gane shin soyayya ce ko kuma mugunta irin ta maza ko baisan tanajin zafin bane."? Ko laifi ta mishi wani lokacin da haka yake hukuntata har sai tayi ihu sannan ya nuna ya tsorata harya bata hak'uri. Shi yana son ya kwaikwaye ta amma ita baison yaji ta kwaikwaye shi sam indai tayi haka sai yayi amfani da wata hikima wajen hukunta ta. Misali yayi ta sata K'ananan ayyuka dakko wannan dakko wannan har sai ta gaji ita kuma b'ata kinyi. Idan kuma ta mishi complain ko ta nemi ya mata 'massage' (tausa) sai yai ta mata dariya sannan cikin wasa yaki yi mata sannan ya nuna mata ai punishing dinta yayi. Sai yaga zata yi kuka sannan ya hau yi mata waqa sai kuma yayi mata.

Yana taimaka mata a komai saboda cikin jikinta.. har wata rana sun dawo daga siyayya yake son gwada ta don ya san raguwa ce ko da ma bare yanzu. Ya dauki wasu kayan sannan yayi mata nuni data dakko wata dundumemiyar jarkar mai.
"Please biyo ni da wannan store maman biyu.!! Yayi nuni da jarkar. Ai yadda ta zaro ida ya bashi dariya yaje yakai ya dawo Sannan ya kinkimi jarkar. Hafsah cike da tsokana ta dunkule hannu alamar jinjina tace "kaga mazaah"!
Ya waro mata ido yana mata wani irin kallo.
Ya dakata Sannan yace mazaje koh."? Tom bara na dawo kiga."
Babu shiri ta rufe baki da zura da gudu zuwa bedroom.
Ya bita da kallo cike da k'auna yana dariya yana girgiza kai tafi ahankali kada kimin asara..!!!!

Ya ajye jarkar ma shima ya bita.....

ALHAMDULILAH ALHAMDULILAH.

HAK'IKA NA DAUKI DOGON LOKACI FIYE DA SHEKARA DA FARA WANNAN TYPING SAI YAU ALLAH YAYI NA HATTAMA..
ALLAH NA GODE MAKA..
INA ROKON ALLAH YA SA MU AMFANA DA A BINDA KE CIKI KUSKURE KUMA ALLAH YA YAFE MANA...

*To readers*📔📚

NA GODE BISA SOYAYAYYA ALLAH YABAR ZUMUNCI..
KUMA INA FATAN ZAKU DAUKI ABINDA YAKE MAI AMFANI ACIKI KU ZUBAR DA MARASA AMFANI.. SANNAN KUYI HAKURI BISA YADDA KARSHEN LITTAFIN YAZO A TAKAICE.

NAGODE..
ALLAH YA KAWO MANA KARSHEN WANNAN MUSIBA DA TA ADDABI DUNIYA AMIIN DON ALFARMAR ANNABI (SAW)
NAGODE.

*Karima Tijjani Mansur*
*HAJEEYAH KHAREEMERH*

Like Karima Tijjani novels on Facebook.
Follow on instagram @ Hajeeyah-khareemerh Tee-em.

Thnk you all
*Saturday 18/04/2020*

TARIHIN WRITER A TAKAICE..

_An haifi Karima Tijjani Mansur a garin kano ashekarar 1998 a watan April. Tayi karatun ta duka na addini da na boko a garin kano. In da yanzu take karatu a jami'ar Yusuf mai tama Sule YUMSUK (NRTHWST KANO.)_

ZAZZAFAN SO Shine littafin ta na farko wanda ta fara futarwa amma kafin shi ta fara rubuta wasu amma ba'a buga ba ko a online ko publish..
Karima Tijjani matashiya ce yar kimanin shekaru 22.
Kuma ta fara rubuta Littafi tun tana kimanin shekara 15. Sai dai bata fitar da shi ba..
Chapter 88 · 0% Book details