← Book details Zazzafan So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 85 OF 88

Sashe 85

Zazzafan So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta girgiza kai sannan ta d'ora.

Na tarar da Samha cikin wani irin yanayi a gidan su. Da alama ba mahaifiyarta ce a gidan ba. Kuma na tabbatar da hakan bayan nayi kwanaki a gidan saboda yadda naga suna fada da matar gidan kamar sa'ar ta. Kusan kowa na gidan basa shiri dasu kuma ta raina su.

Ranar dana isa gidan ma suna ce-ce-ku-ce da matar gidan.

Na bata labarin duk abinda ya faru dani a gidanmu da yadda 'sir Garba' ya yaudareni.
Amma sai naga ita hakan bai zama damuwa a wajenta ba.

Ta nuna min babu komai har da bani shawarar "na zubar mana ai ba kaina farau ba.

Ban yarda da hakan ba amma bansan me ya faru ba na wayi gari cikin ciwo kuma bayan munje asibiti aka tabbatar da zubewar ciki na. Nayi jinya sosai ta watanni duk a gidan su Samha. Ni kaina ina mamakin gidansu babu ruwan kowa da rayuwarmu ni da ita shiyasa nake zamana cikin kwanciyar hankali a wajenta.

Na zargi Samha kan zubewar ciki na amma sai nabar abin cikin iya zuciyata saboda itace ci na itace sha na.

Na zauna gidan su tsahon watanni da suka kusa rufa shekara.

Samha kullum sai tace in shirya nasa 'spare' uniform dinta muje makaranta amma sam naki saboda na tsani makarantar ma gaba-d'aya. Sai dai na bata sak'o a wajen Sir kan cin asabar daya min duk da baya makarantar yanxu amma ta isar d'in.

Nabar gidan su Samha bisa dalilai da dama na yau da gobe da kuma halayen Samha wanda na kasa ganewa.
Na fahimci Samha tafini wayewa da budewar idanuwa kafin daga bisani na fahimci ta shallake tunanina tunda har takan iya maida mata maza a wajenta.

Bansan tana da wannan dabi'ar ba sanda muna makaranta sai dai babu tabbaci kan ko batayi ne a lokacin amma sanda gwada min haka take lokacin naji bazan iya cigaba da zama da ita ba.

Rayuwar danayi a unguwar su yasa na saba da wasu makobtansu ciki har da wata mata maiwa yan aiki hanya.

Na je har gidanta na roketa kan ta samamin aiki na gaji da zaman gida.
Bayan dogon kallo daga matar sannan ta min shagub'e kan me zai kaini aikatau bayan ina k'awar Samha."? Duk wayewar mu. Domin babu wanda a unguwar baisan ni ba kawar Samha bace.
Wani abin mamaki shine yadda babu kunya matar ta ke tambaya ta. "Kodai abin ya daina karbar ki ne."? Inada wani malami da zai dawo miki da tauraruwar ki."!!

Banyi fushi ba kuma ban nuna mata ba haka nake ba tunda bani da mafita. Sai dai na nuna mata matuk'ar buk'atar aikin wanda daga k'arshe ta yarda zata kaini sai dai ta yanka min wasu kudade da zan biya ta idan na fara aikin. Ta nuna min tasan inda zata kaini. Bangane nufin ta ba sai dai naji tace..
Na fahimci k'afa kike nema so zan kaiki inda zaki k'ara goge wa dama haka irin ku kuke lumbe-lumbu kuke kuyi kwanton bauna ku goge sannan ku gagari masu gida.."!!

Sai ta sheke da dariya.

Na rok'eta hadi da bata cin hanci kan kada ta fad'awa Samha ina neman aiki. Ta nemi dalili ta rasa. Wanda da kyar na samu ta yarda duk da tana ta mamakin dalilin boyewa ta.

Mun saci jiki sau da dama munje gidanmu nida Samha na kwaso kayana sanda mahaifina bayanan. Mahaifiya ta nuna tsayawar ta duk da sanda baba zai koreni bata nuna wani abu ba domin tasan halin sa zai iya hadamu ya kora.

Nasha gwada in koma gidan mu amma babu damar hakan har mahaifiyata ta gwada min in saduda.

Daga karshe dai matar nan ta samar min aikin kuma nayi mamakin gidan da ta kaini. Gida ne na mata masu zaman kansu.

Takamaimai bansan wa zan dinga yiwa aiki agidan ba sai dai an fada min aikina.
Share-share da wanke-wanke da aike shine aiki na.

Sanda suka ganni sunyi complain kan nayi musu girma harda masu cewa ni uwar mata ce ko suce sumumu-kasau... da kyar suka yarda na fara aiki wanda dole nazama tamkar wata doluwa.

Nasha wuya sosai agidan nan mara dadin tunawa.
Domin mata ne su wajen goma sha amma babu yadda za'ayi wata ta sani aiki wata bata sani ba idan nabar na daya nasha zagi har da duka. Maza ke tururuwa a gidan ba dare ba rana haka kawai ake kyara ta wai mazansu na kallo na ni munafuka ceh..
Sun sha cewa zasu koreni amma ina basu hakuri har da kuka..

Azaman da nake a gidan ne tunanina ya fara sauyawa kan irin rayuwar da suke anya nima bazan fada ba domin neman mafita ta."?
Amma wallahi dana tuno ki sai inji bazan iya ba.

Nayi akallah shekara agidan kafin wani mutumi da yake zuwa wajen wata ya yaudare ni.
Mutumin ya dade yana nuna min wasu abubuwa har saida yasan yadda yayi ya fita dani a motar shi kan zan karbo wa uwar dakina sako a wajen shi.

Mutumin ya kasance mutum na biyu wanda bazan taba mantawa dasu ba a rayuwata. Zan sa shi layin wadanda suka taimaka wajen gurbacewar rayuwata.

Ya huren kunne da hilata kala kala wanda tun bana yarda da shi har na fara sakin jiki.

Naci duka sanda suka gane haka a lokacin ne suka nemi su koreni...
Aunty sadia kawarsu ce don tana yawan zuwa gidan. Allah ne ya kawo ta Aranar ta ceceni itace ta tafi dani gidan ta lokacin ina ga ina da shekaru 18 lokacin tasan yan ajinmu sunyi candy.

Na kasa gane irin rayuwar da take ko irin tasu ce. Nasan dai tana business sai sai yawan bak'i maza a gidan ya zarce misali.

Ta nemi taji tarihi na daga bakina da kuma gaskiyar abinda ya faru dani. Na fada mata komai a lokacin ta gargade ni kuma tayi min fada mai shiga zuciya.

_Ke yarinya ce kinyi kankanta kisa rayuwarki cikin wannan abubuwan kada in kara jin hakan ya faru.. tunda komai daya faru a rayuwar ki ki d'auka kaddara ne mu idan zaki ji namu tarihin zaki ji naki ba komai bane._

Tayi min jan ido wajen cewa duk ranar da taga wani abu shigen wanda nayi acan to zamana ya k'are.
Tayi min wani gargadi da cewa "Ki bar manya suyi ke yarinya ceh."
Na kasa fahimtar me take nufi sai dai na gimtse abun nabita yadda taxo min. Nidai nasan na wuce sahun yara kuma zuwa lokacin nasan abubuwa da dama..

Mun zauna nida ita tana kula dani har yau bazan manta da ita ba.
Jamila ta share hawaye.

Ta yi kokarin maida ni gida sanda tayi wani tunani a kaina amma baba ya koremu. Cewar shi naje na k'ara tambadewa sannan zan kara dawo mishi gida. Har Allah ya isa yayi hadi da tsinuwa idan har na k'ara zuwar mishi gida. Duk abin matan gidan sai da suka bashi hakuri amma yaki hak'ura.

Mun rayu da ita babu tsangwama tayi min komai ban rasa komai ba amma kullum gargadinta dani akan na fita harkar maza ne.

Tana yawan fada min cewa "Maza mayaudara ne badon yaudarar su ba da bata zata tsinci kanta cikin wannan rayuwar ba."

Bata taba ban labarin ta ba har muka rabu amma nasan tasha wuya fiye da tawa.
Mamakina shine yadda yan uwanta ke zuwa gidan ciki harda mahaifiyar ta kuma suyi hira sannan su tafi da kayan arziki.

Na goge da rayuwa a zamana da ita tayi min komai sai dai bata taba min tayin maida ni makaranta ba kuma nima ban zarge ta ba.
Tayi min abinda iyayen a basu min ba ina sa mai kyau inci mai kyau sai dai na fahimci yan uwanta basa k'auna ta.

Na gane ne da irin kallo da kyarar da suke min.

Munyi shekaru a kallah uku kafin dole Aunty ta sallama ni nake tsayawa da samari. Sai lokacin na sake fahimtar yadda mutane suka bata rayuwar su. Yawanci basa zuwa da alak'ar gaskiya Sao dai kowa da manufar shi.

Sanda na lura aunty ta rage tara maza a gidan ta ma'ana sun rage zirga-zirga shine sanda wani mutumi ya nuna yana son zai aureta. Tayi murna sosai nima kuma naji dadi sai dai kash sai da komai yazo daf da daf komai ya ruguje..
Mutumin yasan komai game da ita sai don bazance zaman da take yi ne ita daya bai sani ba. Sai dai lamarin ya tsayawa jama'a da dama aransu musamman k'awayen ta yadda suke ganin zata daga ta barsu.
Ban taba ganin matar nan cikin tashin hankali ba kamar lokacin nan tasha kuka wiwi a gabana. Ta dinga fadamin maganganu kamar ba cikin hayyaci ba kamar ta manta dawa take maganganun.

"Jamila nasan nayi rayuwar da bata dace ba amma na dade da dainawa na tuba yanzu ba da bace halak d'ina nake nema amma meyasa mutane zasuyi min haka."?
Maganganu ta dinga furtawa wasu ma sirrikan ta ne. Nima babu abinda nake sai kuka da bata hakuri.

Anduki lokaci mai dan tsaho kafin aunty ta dawo daidai.

Takan barni nayi mu'amala ta da samari na sam bata hana ni fita da samari. Har mu fita.
Sai dai a kullum zancen ta daya "Kiyi taka tsantsan."

Har kamar ranar da muka hadu dake. Amma nida kaina nake baya baya da mutanen saboda yadda suke nuna min wuce makad'i da rawa.

Aunty da kanta ta sama min hanyar samun kudi a cewarta dogara da abin wani ke jawowa komai ke faruwa.

Na koyi kwalliyar zamani wato makeover da ita nake yiwa kaina abubuwa da dama. Lokacin na k'ara tunowa da gidanmu. Dole na k'ara nemar gida domin bani da wanda inda ya fishi. Ina kaiwa mahaifiya ta alkhairan da wataran har shi mahaifina ake ciki domin komai ya k'are mishi. Kowa a gidan ta kanshi yake.

Da wannan abin nake samun damar zuwa gidanmu kai tsaye.

Sanda nazo wajenki lokacin aunty tayi min alkawarin zuwa dani Dubai domin siye siyan kaya. Nima tace na k'ara gogewa da sanin rayuwa.
Chapter 85 · 0% Book details